Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 28   Afrilu 2002


BABBAN SHAFI
Mu Leka Mu Gani
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 1
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 2
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 3
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 4
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 5
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 6
Malam Zurke
Ra'ayin Mujallar Fim
Hajjin Bana
Sauran Labarai
Ra'ayi Ba Gaba ne
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN

 
If you had a new browser, you would be able to view this java applet. Akwai:  


Gidauniyar Tunawa Da Balaraba

A SAFIYAR ranar da su Balaraba suka rasu, na zauna a falon gidana a Kaduna ina karyawa ina santi. Ban san lokacin da na fara ba matata labarin soyayyar Shu'aibu Lawan da Balaraba ba. Jiya-jiyan nan (Jumma'a) an yi taron daurin aurensu, kuma taro ne na tarihi wanda in ba taron siyasa a zamanin NPN ba, da ire-iren wadannan tarurrukan, ba a taba yin irinsa a bikin aure a garin ba. Za ka iya kwatanta shi ne kawai da taron daurin auren Fati Mohammed a Kano. A wannan safiyar ina gama sallah ban yi komai ba sai na zauna a kan gadona na rubuta sharhina na filin "Mu Leka Mu Gani," wanda na yi a kan batun aruren 'yan fim. Doki ne ya kama ni ganin irin nasarar da 'yan fim ke ta kara samu a kan masu cewa 'yan fim ba su son yin (ko ba su yin) aure. (A nan gaba zan buga sharhin). Ina gama karyawata da santina da labarin soyayyar Balaraba da Kumurci sai na nufi ofis. Na hau komfuta na shiga tsara fitowar mujallar Fim ta watan Afrilu. Ina murnar muna da dadadan labarai, musamman ma kan auren su Balaraba da auren Musa Liman Jalingo (furodusan Izaya), da labarin hajjin su Sani Musa Danja, da sauransu. Can sai ga wakilinmu na Kaduna, Aliyu Abdullahi Gora II, ya shigo ofishin. Bai ko zauna ba na ce masa, "Ina fatan dai kun tattauna da Balaraba jiya." Ya ce, "Kwarai kuwa. Hatta baban da babar tata, da kawaye kamar su Saima, duk mun tattauna da su. Ka san ni dan gidan ne."

Na san nufinsa. Babu dan jaridar da ya sami karbuwa a gidan su Balaraba kamar Aliyu Gora. Farkon zuwansa gidan shi ne lokacin da ya je ji ra'ayin iyayen Balaraba a kan barazanar da wasu Katsinawa suka yi cewa Balaraba diyarsu ce da ta bace tun tana karama, wai sun gane ta da suka gan ta a fim din Tawakkali 2. Gora ya sami nasarar tattara wancan labarin tare da hadin kan yayyen Balaraba da mahaifiyarsu. Ya ci gaba da zuwa gidan a kai a kai har suka saba da iyayen da 'ya'yan. Don haka da auren kyakkywar jarumar ya taso shi Gora ji yake kamar a gidansu ake bikin.

Muna tattauna yadda za a rubuta labarin, sai daraktan mujallar Fim, Alh. Garba Dangida ya leko muka gaisa. Daga nan ya koma ofishinsa ya yi waya. Ba a jima ba sai ga shi ya dawo a kidime ya same mu ni da Gora. "Kai kun ji abin da ke faruwa kuwa? Wai yarinyar nan Balaraba wadda aka daura ma aure jiya sun yi hadarin mota ta mutu!"

Da farko mun ji labarin bambarakwai kamar almara. Wallahi, ni dai ban gaskata ba. Duk da haka na ce, "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Don Allah ka bari! Ba'a kake!" Alhaji Garba ya koma ofis dinsa ya sake buga waya gidan wani attajiri mamallakin asibitin da aka kwantar da su goggon Balaraba, aka kara tabbatar masa da abin da aka riga aka gaya masa. Shi kuma sai ya garzayo ya dawo ya kara gaya mana. To amma ko kafin ya zo, na ba Aliyu makullin motata ya sheka asibitin. Ko da Dangida ya kara gaya mani labarin sai na mike tsaye na ce, "Allah, Allah, Allah Ka sa wannan labarin kuskure ne! Allah Ka sa wasu ne daban suka yi hadarin, ba su Balaraba ba!"

A daidai wannan lokacin, wani abokina, Ibrahim Lawal Danhalilu, wanda jami'i ne a ofishin jakadancin Amerika da ke Abuja, ya shigo ofis din. Na sanar da shi abin da ke faruwa kuma na ce masa mu bi sawun Aliyu can asibitin; ba zan iya jira har sai ya dawo ba. Muka ko fada mota muka tafi. Jama'a, ai fa sai labari ya zama dahir. Allahu Akbar!

Magariba ta yi a lokacin. Ko sallah ba mu yi ba ni da Aliyu Gora, na sallami Danhalilu, muka garzaya gidan su Balaraba. Muna isa, muka tarar da daidaikun mutane a kofa, yawancinsu yaran unguwar, sun yi cirko-ciko. Muka ce, "Me ake cikin yanzu?" Wani ya ce, "An tafi yin jana'iza." Na ce, "Ina?" Aka ce, "Makabartar Kawo." Mun juya za mu tafi can wani mutum ya ce bari ya bi mu.

Muna isa makabartar sai muka tarar an cika makil. A nan muka hadu da wasu 'yan fim kamar su tsohon shugaban furodusoshi Kano Auwalu Marshal, da Dan'azumi Usamn da Mu'azzam Boss da Abdulmunafi Sani. Da Mu'azzam ya gan ni sai ya ce, "Zo mu je." Yana rike da kyamarar bidiyo yana ta daukar hoto. Muka kutsa kai zuwa cikin hurumin,wanda jama'a suka yi dafifi cikinsa, har zuwa sababbin kaburburan, muka tarar wani yana kakkabe cebur din da ya zuba kasa kan gawarwakin su Balaraba. A nan muka duka tare da sauran jama'a, muka kewaye kaburburan, muka shiga addu'o'i. Gwiwata tana jikin kabarin Jummai, a gefena daga dama kuma ga kabarin Balaraba. Araina na rika cewa, "Yanzu nan Balaraba ce a nan ciki? Babu sarki sai Allah!"

A wurin fitowa daga makabartar, ni ne na karshe. Da kyar nake jan kafa, har sai da mai kulle kofar ya dan dafa ni a kafada, yana cewa, "Mu je, mu je." Rabon da in yi kwalla an yi shekaru, amma sai na ji dumin hawaye a kumatuna. Na goge da bayan hannu. Daga wannan wurin, muka koma gidan su Balaraba. Muka tarar ya cika da jama'a. Na tsaya a cikin taron mata da yara, ina jin labaran abubuwan da Balaraba ta yi ko ta ce a ranar. A lokacin, su iyayen Balaraba suna can asibti an kwantar da su saboda gararin da suka shiga.

A kan hanyata ta zuwa gida a cikin daren nan, hankalina na gun Balaraba da Kumurci. Ga shi dai mutum hudu ne suka rasu, amma ji nake kamar Balaraba ce kadai, sa'annan ji nake mutuwar tata kamar mutuwar mutum dari ce sanannu a gare ni.

A gaskiya, ban shaku da Balaraba kamar yadda na shaku da wasu 'yan wasan ba. Ta fi shakuwa da wadansu ma'aikata na mujallar Fim, musamman editanmu Ashafa da wakilinmu Aliyu Gora. Duk da haka, duk inda ta gan ni za mu gaisa. Ni na fi shakuwa da Shu'aibu. Sau biyu na gan ta a cikin wannan shekarar. Na farko a cikin watan Janairu, a Kano, lokacin da ta zo neman Kumurci a ofishin hada hotunan bidiyo na 'Kwality' da ke kan 'Zoo Road'. A nan ta same mu tare da shi. Kai da ganin yadda suke kallon juna ko suke yi wa juna, ka san akwai soyayya tsakaninsu wadda babu yaudara a cikinta. Haduwarmu ta biyu ta faru ne a Kaduna a watan Fabrairu, a lokacin da ta je suna daukar shirin Tasiri 2 a wani gida a Malali. Ni kuma na je kallo. Mun tsaya a kofar gidan ni da Ali Nuhu muna labari, ta zo muka gaisa. Suka yi magana da Ali, ta koma ciki. A ranar ne ma ta yi shahararriyar hirar nan tata da mujallar Fim, inda ta ce tana kaunar Shu'aibu ko da a rami zai saka ta. Tare da Aliyu Gora suka yi hirar. Ganina da ita na karshe kenan. Allahu Akbar!

Kamar kowa, na shiga kogin tunanin yadda Shu'aibu zai ji wannan mutuwar ta matarsa a ranar da za su fara rayuwar aure. Nakan yi tunanin irin soyayyar da ke tsakaninsu. Ban taba ganin soyayya irinta ba sai a fim ko a littafin hikaya. Na tuna, wata rana a Kano, a Daula Hotel, mun je bikin taya su Abida murnar cin gasar Arewa, na hadu da Kumurci da Balaraba a daren. Da ma ina neman Kumurci domin ba shi gayyatar yin wasa a fim dina mai suna Gagarabadau, wanda za a fara dauka cikin mako na gaba a lokacin. Da na gan shi na ba shi gayyatar, sai ya ce, "Ina fatan dai akwai mutuniyar tawa a fim din. Domin ka san duk inda zan tafi ba na jin dadi idan ba ta tare da ni, haka ita ma. Ka ga idan mun je Kaduna tare, lafiya lau kenan, tunda garinsu ne."

Kash! Babu Balaraba a fim din. Ya nemi ya dan hada ni da ita cikin raha ("Kin ga,wai Sheme zai yi fim amma bai sa ki a ciki ba!"). Ita kuma ta ce, "Sheme wato abin haka ne, ko? Lallai ne!" Na ce, "Na yi maki alkawarin idan za mu tafi yin part two na fim din, zan sa ki."

A zamanmu a Kaduna lokacin daukar Gagarabadau, cikin Nuwamba, 2001, a koyaushe Shu'aibu yana tunanin tare da magana kan Balaraba.Rannan da dare a otal din mu ya ce in raka shi ya yi mata waya a shagon yin waya (phone booth). Ita tana Kano. Muka tafi. A hanya babu abin da yake yi sai ba ni labarin kaunarsu. Muka je ya yi waya, muka doshi otal. Na ce, "Lallai Shu'aibu kana ji da Balaraba. Wai yaya maganar aurenku? Ya kamata ka kyale mu mu sanar a mujalla." Ya amsa, "Ai za mu yi magana. Mutane ne suka ce in bari kada in yi magana a mujalla har sai komai ya tabbata."

A lokacin Kumurci bai san gidan su Balaraba ba tukuna. Da ya tambaye ni, na gaya masa wajajen da gidan yake. Ya ce insha Allahu za mu je su gaisa kafin mu koma, Kano. To amma da muka kare shooting, babu isasshen lokaci na zuwa gidan.

Saboda haka dai na san wadannan bayin Allah bakin gwargado. Zan iya ruwaito cewa a yayin da 'yan fim da dama suke yin soyayyar karya da yaudara da shashanci, ta su Kumurci a zahiri soyayyar gaskiya ce. A karshe ma ga shi sun auri juna. Kodayake wasu za su ga kamar su Shu'aibu ba su ci moriyar aurensu ba tunda ba su zauna ba, ni ina ganin sun ci. Balaraba dai ta yi ritaya daga wasan fim, ta bi umurnin sunna da na iyaye ta yi aure. Sa'annan ta mutu ba a kan hanyar zuwa yaji ba, a'a a kan hanyar zuwa gidan miji. Allah Masani, ba mu san irin tanajin da Rabbih ya yi mata ba a inda take, amma muna fata tareda kyautata zaton sakayyar alkhairi ce. Dubi addu'o'i da ake ta yi mata.

Shi kuma Shu'aibu, ya zama abin tausayi. Abin jajantawa. Abin yi wa addu'a. Ya nuna bajinta da tawakkali da tawali'u da bai bari rasuwar amaryarsa ta zauta shi ba. Ya karbi kaddara. Ladar abin da ya yi (wato aure) Allah kadai ya san iyakarta.

Ba zan rufe wannan juyayin nawa ba sai na yi roko. Don Allah, don Allah 'yan fim ku yi wani abu na karrama Balaraba. Na san kun yi addu'o'i, kun je ta'aziyya. Amma ku kara da aikata wani kwakkwaran aiki na tunawa da wannan baiwar Allah 'yar'uwarku. So nake ku taru ku kafa Gidauniyar Tunawa Da Balaraba Mohammed (a Turance, Balaraba Mohammed Memorial Fund). Ba sai kun gina gida a Abuja ba irin na tunawa da Janar Shehu 'Yar'Aduwa. A'a, a yi daidai ruwa daidai kurji. Misali, a tara wasu 'yan kudi ko yaya suke, shugabannin shirin fim su tafi su kai wa iyayen Balaraba. Ko a saya masu gida nasu na kansu. Kowane furodusa ya yi ta-maza, ya ba da gudunmawar N1,000 kacal, sannan kowane dan wasa ya ba da N500 kacal. Na tabbatar a tsakanin Kano da Kaduna da Filato da Bauchi da Gombe da Katsina da Sokoto da Zamfara (jihohin da aka fi yin fim) za a iya tara abin da ba zai gaza rabin miliyan ba. Kai, ko naira dari-dari aka tara, ya fi a ce ba a yi komai ba. In kuma akwai abin da ba na kudi ba ne da za a iya yi, in dai zai alamta karramawa ga mamaci, to a yi.

Yin hakan zai faranta wa iyayen Balaraba da mu masoyanta rai. Zai ba iyaye a ko'ina kwarin gwiwar sakin jiki 'ya'yansu su yi harkar fim. Zai kara gyara mutuncin 'yan fim a idon jama'a. Zai nuna cewa shugabannin shirin fim sun san abin da suke yi.

Na san an fara yin wani abu makamancin haka a lokacin rasuwar su Aminu Hassan, aka tara wajen N7,500. To amma ai ya dace a ci gaba a kan wani. Haka kuma na san ba laifin kowa ba ne rasuwar su Balaraba, amma laifin kowa ne idan kowa ya ki yin wani abu don karrama ta. Sa'annan na san akwai burbushin rashin hadin kai, da gulmace-gulmace, kai har da gaba da tsolanci a tsakanin wasu 'yan fim, amma fa a lura wannan mutuwa ce, tana kan kowa. Gidauniyar Karrama Balaraba za ta kasance abin tarihi a harkar fim na Hausa. Kuma na tabbatar idan har an kirkiri gidauniyar, to ba za ta zama tangaran fadi-ka-mutu ba. Za ta zama tukunyar karfe wadda ba mu ba ma har 'ya'yanmu da jikoki za su zo su ci moriyarta. Kuma kada a bar aikin a kan wadanda Balaraba ta yi wa aiki su kadai, ko wadanda ake ganin ta fi shiri ko zumunci da su. A'a, wannan aiki ne na kowa da kowa, domin gudunmawar da ta bayar ga habakar shirin fim ta shafi kowa da kowa.

Su Iyan-Tama da Mandawari da Maikano da Ability da Tijjani da Abdulkareem da Hajiya Balaraba Ramat, gare ku!

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin