SANARWA: Na rubuta wannan sharhin a safiyar ranar da su Balaraba Mohammed suka rasu, da nufin ya fito a mujallar Fim ta watan jiya)
INA masu cewa 'yan fim ba su son yin aure? Ku zo, yau da ku zan yi magana. Idan kun tuna, a kwanan baya na rubuta cewa wata ki la wasu masu karanta wannan mujallar ta koma ta aure-aure. Dalili shi ne a cikin watanni kamar hudu da suka wuce, dukkan manyan labaranmu a kan batun auren 'yan fim muka yi su. Haka kuma akwai kananan labarai da aka buga a cikin mujallar wadanda aka yi kan auren 'yan fim.
Ba yanzu muka fara ba. Zan iya bugun kirji in ce babu wata kafar watsa labarai da taba ba da labarin auren 'yan fim din Hausa irin mujallar Fim. Duk wani aure da aka yi ko ake hasashen za a yi, in dai ya hado da wata ko wani dan Industry, to a cikin mujallar ake ba da shi. Wannan yana daya daga cikin dabi'un mujallar,domin ta kudiri ba da labarin dukkan abubuwan karuwa da na raguwa a sana'ar shirin fim na Hausa.
Bayan wannan shimfidar, bari in koma kan tsokacin da wasu ke yi cewa 'yan fim ba su son yin aure. Wannan ra'ayin dai ya taso ne daga wadansu al'amuran terere da suka faru a fagen fim, da kuma rashin cikakken la'akari ko nazari daga masu kallon finafinai da sauran jama'a. Wadannan abubuwan tereren sun hada da mutuwar auren wasu 'yan wasa mata, wato su Halima Adamu Yahaya da Jamila Haruna Yakasai. A lokacin da abubuwan suka faru, mutane da dama sun tausaya wa wadannan matan. To amma faruwarsu ta rage wa 'yan fim daraja a idanun jama'a, sa'annan masu kin 'yan fim sun samu tsanin da suka hau suka iza wutar sukarsu.
A nan ne nake ganin akwai rashin nazari mai zurfi daga masu kallo, ko kuma ma rashin fahimta. Duk wanda ya ce 'yan fim ba su son yin aure, bai dubi al'amarin da kyau ba. Dalilina nafadar haka shi ne ai aure-auren da aka yi sun fi mace-macen auren 'yan fim yawa. Domin kuwa a cikin shekara kamar biyu zuwa yanzu, da wuya ka kirga aure biyar da suka mutu na 'yan fim. Ni dai hudu na sani, ga su: auren Halima, Jamila, Talatun Sani Mai Iska, da wata a Kaduna mai suna Safiya Mu'azu. Idan ka san ta biyar din, ka rubuto mani. Kuma ba aikina ba ne in fadi laifin waye har aurarrakin suka mutu; na dai san cewa komai mukaddari ne. Idan ka dubi aure-auren da aka yi, wai, yawansu ma kusan a ce ya fi gaban kirgawa. In ka manta da wasu, bari in tunasasshe ka. Na daya, na san dai kila ba ka manta da auren Fati Mohammed ta farko ba (wato Fatin Ki Yarda Da Ni), wanda aka yi a cikin 1999. Har yanzu tana nan da mijinta Malam Musa Badara na Jami'ar Bayero. Ban da ita akwai Fati Mohammed ta 2, wadda ta auri jarumi Sani Musa Mai Iska a cikin Yuli,2001. Ga kuma Maijidda Abdulkadir da ta auri Abubakar a ran 6 ga Mayu, 2001.
Akwari auren zabiyoyi shida: Jamila, Fati Abubakar, Zuwaira Isma'il Durumin-Iya, Rabi Mustapha, Asabe Mohammed (wadda ta yi wakar shirin Imani) da Maryam Saleh (Fantumoti). Kwanan nan muke jin cewa Aminu A. Shariff (Momo) zai auri zabiya Maryam Mohammed, sa'annan zabiyar nan Jamila Sa'id ibrahim ta yi ritaya daga aikin waka a situdiyon 'Iyan-Tama Multimedia,' ta koma gida tana jiran ranar daurin aurenta. Wasu matan da suka yi aure su ne Salma Mohammed ta cikin Sidiqu, fim din da bai fito ba, wadda ta auri dan wasa Mika'il Hassan (Gidigo ko Hanci-Ciki-da-Falo), Hadiza Fijo, Dayyaba Isyaku, Halisa Mohammed, Bilkisu Sufi (Kilu Ta Ja Bau), da Rumasa'u Abdullahi, wato jaruma kuma furodusar shirin Tarkon Mugunta. Haka kuma marubuciyar littattafan nan ta Katsina, Talatu Wada Ahmed, wadda furodusa ce, ta yi aure a ran 10 ga Nuwamba, 2001. Wasu 'yan harkar fim da suka yi aure, maza ne. Sun hada da jarumi Sunusi Burhan Daneji (Mukhar),furodusa Habibu Sani Kofar-Soro, jarumi Tahir Mohammed Fagge, furodusa Dan'azumi Baba, dan wasa Tijjani Asase, Ashiru Sani Bazanga (Sawun Keke), furodusa/daraka Magaji Suleiman Zaria, dan wasa Sani Idris Kauru (Moda), jaruumi Akilu Mohammed (Baban Mulika), dan wasa Dailami Mustapha (Daula), dan wasa Shafi'u Magaji Usman, manazarcin shirin fim Bashir Yahuza,furodusa Ibrahim HassanAdamu, jarumi Aliyu Abdullahi Gusau, furodusa Musa Liman Jalingo, dan wasa Isma'il Baffa Ahmad (Cinnaka), dan wasa Iliyasu Tantiri, da kuma uwa-uba, Sardaunan Furodusoshin Arewa, Alh. Abdu Haro Mashi. Kada kuma ka dauka na manta da auren tarihi da aka yi a watan jiya tsakanin Shu'aibu Lawan (Kumurci) da jaruma Balaraba Mohammed.
Duk wadannan aure-auren sun faru, ba almara ba ne. Kuma an fade su a mujallar Fim a daidai lokacin da suka faru. Don haka komai taurin kan mutum wajen sukan 'yan fim, idan zai yi adalci tilas ya yarda da cewa lallai 'yan fim suna yin aure. Sukan auri daga cikin wadanda ba 'yan fim ba,kuma sukan aura daga cikin ya-su-ya-su.
A nan gaba ma akwai aure-auren 'yan fim da ake kyautata zaton za su faru. Ga misali: Aminu Shariff (Momo) da zabiya Maryam Mohammed; A'isha Musa (Shamsiyya) da Ali Nayara; A'isha Ibrahim (Saliha) da Oumaten Atta; Abida Mohammed da furodusa Hamza Mohammed Danzaki (lokacin maulud mai zuwa); sa'annan watakila tsakanin Ahmed S. Nuhu da Maryam Umar (Mushaqqa), Zulkifilu Muhammad da Wasila Isma'il, Hajara Usman da Kabiru Maikaba, Ali Nuhu da wata yarinya a Kaduna mai suna Maimuna, sai Saratu Gidado da wani furodusa. Bugu da kari, akwai hasashen wasu furodusoshi da daraktoci da za su kara aure, to amma ba zan fade su ba yanzu don gudun kada matansu su yi masu tawaye a gida.
Wani dalilin da ke sa ake cewa 'yan fim ba su son su yi aure (bisa kuskure!) shi ne rashin yin auren wasu 'yan wasa mata. Ana yi ma wadannan matan wannan kallon ne ba domin komai ba sai domin ficen da suka yi a harkar, da kuma bambanci da ake nuna wa mata a nan kasar. (Matan sun hada da Hauwa Ali Dodo da Hindatu Bashir). Dalilina na fadar haka shi ne ai akwai wasu 'yan fim da suka girmi matan ko sa'o'insu wadanda kuma ba su yi auren ba, amma ba a dame su ba. Sun hada da daractoci uku: Ishaq Sidi Ishaq, Hafizu Bello da Mohammed Garba Kabara, furodusa Nura Ilu Dambazau, da sauransu. Sa'annan su ma sauran masu matan ai addini ya ba su filin kara aure (matan aure ku yafe ni!). Irin bambancin da ake nuna wa mata ya sa idan wani abu ya faru ga auren 'yar fim sai a fi yin kwakwazo a kansa fiye da in da abin ya faru ne ga namiji. Yau idan (abin Allah ya kiyaye) wata 'yar fim da ta yi aure ta fito sai an fi kwazzabarta fiye da yadda za a dami namiji idan ya saki matarsa. Lokaci ya yi da za a yi wa 'yan fim alkalanci bisa
adalci. Masu cewa 'yan fim ba su son yin aure, su daina, domin kuwa ga hujjoji nan na bayar. Idan ka dubi hujjojin za ka fahimci cewa kila ma aure-auren da 'yan fim ke yi ya fi na wadanda ba 'yan fim ba suke yi. Kuma ni na tabbatar aurarrakin da ke mutuwa a nan Arewa idan an bincika za a ga cewa na wadanda ba 'yan fim ba sun fi yawa. Idan ka yi gardama, ka je kowace kotu a nan arewa, da wuya ka tarar da wasu ma'aurata 'yan fim a gaban kuliya. Wani abin sha'awa shi ne wadanda ba 'yan fim ba su ke zuwa suna sure 'yan fim mata zuwa rayuwar aure. Dubi Halisa, Bilkin Kilu, Rabi Mustapha, Rumasa'u, da kuma A'isha Ibrahim. Wannan ya nuna mana cewa duk mai son ya auri 'yar fim zai iya in dai da gaske yake. A ganina, su 'yan fim mata sun ma fi son su auri wanda ba dan fim ba ne duk da yake idan sun samu 'yan fim din ba su cewa a'a. Saboda haka yana da kyau duk mai son ya auri 'yar fim ya zo ya taya. Su kuma 'yan fim wadanda ba su yi aure ba, musamman matan, kada su damu kansu da sukar da mutane ke yi masu. Aure mukaddari ne kuma Hausawa sun ce habo ne, idan ya taso babu makawa za a yi shi. Duk wadda ta sami miji, ta je aurenta. Kamar yadda wani mawaki ke cewa, "Duniya rawar 'yan mata ce, na gaba ya koma baya." Saboda haka 'yan mata idan kin taka taki rawar ki ja baya wata ma ta zo ta taka tata.