Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 30   Yuni 2002
MU LEKA MU GANI


BABBAN SHAFI
RA'AYI
Zuwa Ga Masu Karatu
Wasiku
Balaraba Muhammad (1983-2002) 
Rayuwarmu
Duk Sun Yi Aure
Malam Zurke
Ra'ayin Mujallar Fim
Bukukuwa
Sauran Labarai
Ra'ayi Ba Gaba ne
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka Bangon FIM ta 29
Bangon FIM ta 28
Bangon FIM ta 27
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da ra'ayin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


Makaho bai san ana ganin sa ba...

Martani ga Magaji Sulaiman Zariya

DAGA ABUBAKAR SALE HASKE

GAISUWA mai tawa tare da fatan alheri, da fatan kuna nan lafiya kamar yadda nake a nan lafiya. Yaya aiki? Ina fatan komai yana tafiya daidai.

Zan so a ce za ku ban dama domin in isar da sakona ko in ce martani a kan wasu maganganu da wani furodusa, Magaji Suleiman Zaria, ya yi a Fim ta watan Mayu 2002, inda ya mayar wa da Ibrahim Sheme martani a kan cikarku shekara uku da kafuwa. Da fatan za ku daure ku buga min shi a cikin mujallarku ta watan Yuni. Ga martanin kamar haka:

NA yi mamaki da aka ce kalaman da aka rubuta a wannan mujallar a filin Fadi Son Ka sun fito daga bakin wanda ake ce wa fiurodusa, domin a gaskiya in har ba a jinjina wa mawallafin wannan mujallar ba, to kuwa ba za a kushe masa ba.

Zan fara da maganar da ya yi a kan cewa Ibrahim Sheme yana yabon kansa da kansa, duk da yake masu karatu za su zama shaida a kan maganganun da Sheme ya fada, amma ban yi tsammani cewa waccan magana da Sheme ya yi wadda ya gabatar a kan cikar mujallar Fim shekara uku da kafuwa, wadda yake nuna cewa mujallar ta kai matsayin da za a hada ta da sauran mujallun duniya wadanda suke buga labarum da suka shafi finafinai. To a kashin gaskiya, Magaji, in har za ka yi tunani a karan kanka, tun lokacin da aka kafa Nijeriya zuwa yanzu, babu wata mujalla ta harshen Hausa wadda ta yi tasiri ta kuma karbu a ko'ina a duniya, kamar mujallar Fim. Sannan kuma dadin dadawa ita ce mujallar farko wadda ake yi da harshen Hausa da ta fara shiga cikin fasahar zamani, wato Intanet. A wannan kadai ya isa Sheme ya jinjina ma kansa, saboda namijin kokarin da ya yi na habaka harshen Hausa.

To don haka in ya yabi kansa bisa wannan kokarin da yake yi, ba shi ne ake nufi da yabon kai ba. Yanzu idan ka duba, ko 'yan siyasa, in har sun kai adadin wani lokaci, sukan fito su bayyana wa jama'arsu irin ci-gaban da aka samu ta bangaren shugabancin da suke musu.

Sannan kuma maganar da ka yi a kan abin da Sheme ya fadda, cewa duk rubuce-rubucen da aka yi a halin yanzu, ba a yinsa da nufin durkusar da shirin fim. Ka kara da cewa wai Sheme yana da wata boyayyiyar manufa, kuma yana yin kokarin fito-na-fito da masu shirya finafinan Hausa da wasu da suke ganin dimbin kura-kuran da ake yi a fagen gudanar da shirin finafinai na kasar Hausa. Ka kuma ce idan ya tashi magana ba ya cewa wadansu sai dai ya ce duk.

A gaskiya na so in bayyana wasu hujjojina waddanda za su nuna cewa Sheme yana da damar da zai yi bayani a matsayinsa na dan jarida, sai kuna tunawa da maganar da Sheme ya yi wanda yake cewa, "Yawancinsu ba su taba saduwa da aikin jarida ba, suka san muhimmancinsa a gare su ba, shi ya sa yanzu idonsu yake buddewa suna gane dawan-garin".

To alal hakika zancen haka yake idan a ce masu irin wannan guna-gunin za su fara duba daya daga cikin mujallun da ake bugawa a sauran kasashe wadanda suka shafi finafinai, to za su tabbatar da cewa wannan mujallar ba ta buga daya-bisa-ukun irin wadannan labarai wadanda wadansu suke gani kamar tsegumi ne.

Ka nuna cewar yana fito-na-fito da ku. To a magana ta gaskiya, abin da ya kama daga furodusoshi, daraktoci, mawaka, da sauran masu gudanar da shirin fim, in ka dauke 'yan wasa, to kashi 95 cikin dari ba a san su ba a matsayinsu na jigon yin fim illa bayan fitowar mujallar Fim da ta tallata su har mutane suka gane cewa ba 'yan wasan ne kadai jigon fim ba, akwai wasu wadanda ake ganin kamar su ne jigon yin fim.

Zan so a ce ka dan tuna shekarun baya lokacin da ake kokarin kafa shari'ar Musulunci a Jihar Kano, lokacin da gwamnati take kokarin hana shirin fim a jihar. In ban da wadansu daidaikun furodusoshi babu wata kafa wadda ta kai mujallar Fim kokarin kare martabar wannan sana'a da ka ce suna kokarin durkusarwa ta wajen rubuce-rubuce da zai nuna wa gwamnatimuhimmancin wannan sana'a taku.

Baya ga wannan, ka duba ka ga damar da ta bai wa duk wani wanda yake cikin harkar shirya wasan kwaikwayo ta ba da labarin abin da ya shafe shi na farin ciki, wato kamar aure da suna, kai har ma da ziyarar da wani zai kai wasu kasashe, kamar Kasa Mai Tsarki, duk kuma a kyauta. Amma kuma in da a ce wani ne wanda ba ya cikin harkar in ya zo domin a ba da labarinsa makamancin wannan, to sai an caje shi adadain wasu kudi masu yawa.

Amma duk da wannan kokarin da yake maku, da zarar ya fito ya bayyana muku wani kuskure da yake so a gyara amma sai kuka dauka cewa yana kokarin durkusar da harkar ne! To a nan zan tambaye ku, idan har ba ta wannan hanyar ba ta yaya zai bayyana irin gyaran da yake so ku yi? Ko kuma so kuke yi ya dinga hada taro ya ce zai bayyana muku irin abin da bai dace ba a matsayinsa na dan jarida?

Maganar da ka yi ta cewa yana hada ku a jumlace, to a gaskiya ba haka zancen yake ba. Zan so a ce ka karanta sharhin da ya yi.

Sannan ina so in ce wani abu kan maganar da ka fada cewa Sheme ya ce, "A cikin shekaru uku din nan tone-tonen da za a ce mun yi ba su kai ko cikin cokali ba na kogin abubuwan asshan da ake tafkawa a shirin fim." Kafin na fara ba da bayani a kan wannan batu, ina bukatar duk wanda wannan abin ya shafa ya dan nutsu ya fahimci abin da zan fada da idon basira, da fatan zai dubi Allah ya yanke hukunci na gaskiya a kan abin da na fada. Domin sai da na tabbatar da sahihancinsa kafin na fada. Zan so in ce wani ya ba ni amsar tambayar da na dade ina neman amsarta. Tambayar tawa ita ce: wacce gudunmawa masu shirya finafinai da kuma masu yi suke bayarwa ga ci-gaban al'ummarmu? Ko kuma ana yi ne domin nishadi da neman kudi kawai?

Abin da ya sa na yi wannan tambayar shi ne, kusan galibun hirar da 'yan mujallar Fim suke yi da masu harkar fim sukan nuna cewa sun shigo harkar fim ne domin ilimantar da jama'a ta hanyar wasan kwaikwayo. To a nan masu harkar fim sun zama malamai kenan. A al'adance mukan kyautata zaton samun kyawawan halaye a wajen malamai ta wajen fadar magana da kuma wajen aikata alheri a zahiri, shi ne ya sa wani lokaci akan kai yara wajen malamai domin su dabi'antu da halayensa baya ga karatu da zai koya musu. Amma a duniyar finafinai irin hakan tana faruwa kuwa? Amsa ta rage taku masu karatu. Ni dai a nan ga dan nawa binciken da na yi. Duk da yake ba a cikin harkar nake ba amma kuma ina matukar kaunar harkar tun da farko har zuwa yau din nan, shi ya sa a kullum ba ka raba ni da kaset ko mujalla ta 'yan wasan Hausa.

Amma kuma daga wani bangare sai ka ji wadansu mutane suna sukar wadannan mutane saboda halayyar da suke nunawa maras kyau. Shi ya sa na ga ya dace in yi dogon nazari a kan wacce hujja wadancan mutane suka dogara da ita suke sukar 'yan fim da maganganu marasa dadi, da ni kuma hujjar da zan ba su idan irin wadannan mutane sun zo min da sukar 'yan fim, ganin cewar mu muna ra'ayin 'yan fim. Saboda haka na yanke shawarar bin wajajen da 'yan wasa ke mu'amalarsu ta yau da kullum domin tabbatar da gaskiyar al'amari.

Na fara da zuwa Gidan Dan Hausa a Kano a lokacin da wani furodusa da ke Kano yana gudanar da fim dinsa. Na shafe lokaci mai yawa a wannan waje ina ganin yadda 'yan wasa da masu gudanarwa ke mu'amalarsu. A wannan lokaci ne na tabbatar wa kaina duk wannan guna-gunin da masu sukar masu harkar dirama suke yi suna yi ne don son ransu, ganin yadda 'yan wasa suka yi shiga irin ta kamala da kuma irin sigar yadda suke yin kalamansu da kuma bin umarnin wanda yake shugabantarsu a lokacin. Dadin dadawa, irin kamewar da matan suka yi kai ka ce a gaban iyayensu suke.

Na dawo gida tare da tinkaho, ganin na fara ganin daya daga cikin hujjojin da zan bai wa masu sukar harkar fim. Kwanaki kadan sai na sake nikar gari domin zuwa wani wajen da ake daukar fim. Ina zuwa sai na shiga domin da ma gidan abokina ne suka ara. Ina shiga sai hankalina ya yi matukar tashi ganin wata irin shiga da wadansu daga cikin matan suka yi, kai ka ce a wajen da ake kira kulob suke, ga shi kuma in ban da tafka kwamacala babu abin da suke yi. Kuma abin haushi ma a gaban yara kanana wanda in da a ce aure suka yi da wuri to sun haifi kamarsu. A lokacin sai na rasa waye yake shugabantar 'yan wasan, domin wanda nake tsammani yana shugabatarsu ya zama abin da masu iya magana ke cewa, "Sauna kira mana shashasha in ka ga sakarai ku taho tare".

Tun daga wannan lokacin nake bin kadin yadda masu harkar fim suke gudanar da al'amuransu na yau da kullum. Amma kashi 70 na wuraren da na ziyarta nakan samu wajen ba tsari kamar yadda na ambata da farko.

To a nan, Malam Magaji Suleiman Zaria, a mtsayinka na furodusa, wacce gudunmawar kake da ita wanda za ta tsabtace wannan sana'a taku da mu kanmu da muke tunkaho da ita? To a bar ma ta taka, hatta su kansu kungiyoyin furodusoshi da na 'yan wasa ba su da wani kwamiti ko tsari a rubuce wanda zai dinga cusa da'a ko kuma sa ido a kan yadda ake gudanar da wannan sana'a taku.

To ka ga a nan don Sheme ya fito ya nuna muku cewa duniya fa tana sane da irin abin da ke faruwa a wannan harka, ya kuma nuna maku cewa yana bukatar a yi gyara, a nawa ra'ayin, gaskiya ban ga laifinsa ba, domin Hausawa suna cewa gyara kayanka ba ya zama sauke mu raba.

Malam Abubakar ya rubuto daga Danejawa Avenue, Tudun Maliki, Kano.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin