Tsakanin Mandawari, annabawa da sahabbai (1)
Daga Ibrahim Sheme
Idan ana maganar 'yan wasan kwaikwayon Hausa na wannan zamanin da wuya ne a kirga 'yan wasa uku maza ba a ambaci Ibrahim Mohammed Mandawari ba. Tun lokacin da ya fara wasan kwaikwayo akalla shekaru 15 da suka gabata, har zuwa yau bai fasa ba, kuma ga alama bai gaji ba, sai ma kara kaimi yake yi a harkar. Hasali ma dai Mandawari da mutane irin su marigayi Aminu Hassan Yakasai ne suka assasa kafuwar harkar shirya "fim" na bidiyo a bisa kan ginshikin da magabatansu irin su Alhaji Mustapha Mohammed (Danhaki) suka gina. Don haka Mandawari yana daga cikin manyan 'yan fim wadanda ya dace a ce idan za su yi magana, to su tabbatar sun ciza sun hura kafin su furta ta. Sai dai kash! wani lokacin sukan bari sanyin esi ko dadin ana kallonsu ya sa su yi maganar da daga bisani za a yi ta dubansu da ita.
Ban halarci taron bikin cikar mujallarGarkuwa shekaru biyu ba wanda aka yi a Kaduna a ran 8 ga Yuni, 2002, domin a lokacin ina Kano gun aikin hada hotunan shirinmu mai suna Daren Farko. Duk da haka, wakilina da na tura wurin ya kawo mani kaset na jawabin da Alh. Mandawari ya yi a wurin. A cikinsa, na ji wani kalami da ya yi wanda aka ce ya jefa kowa cikin kogin tunani, har wasu na neman jin bahasin kalamin. Ni ma na yi mamakin jin kalamin. Har yanzu ban ji Mandawari ya fito ya yi karin haske kan abin da ya fadi ba, saboda haka yanzu an dauka abin nan dai da ya fadi shi bakin gaskiyarsa kenan. A lokacin da aka kira shi ya yi jawabi bayan an karrama shi a taron ne ya yi furucin, yana cewa wai 'yan mujalla, musamman Ibrahim Sheme na Fim da Dr. Ibrahim Malumfashi da Kabir Assada na Garkuwa, su ji tsoron Allah su daina yi wa 'yan fim kazafi. Shugaban na kungiyar furodusoshin Jihar Kano ya ce a maimakon haka, yana son mujallun su rika yin koyi da sahabban Manzon Allah (s.a.w.) wadanda ya ce su ne farkon wadanda suka fara aikin jarida ta hanyar ruwaito hadisan Manzo amma ba su taba kauce wa gaskiyar abin da ya faru a zamanin Manzo ba. Mandawari ya ce abin yana ba shi mamaki yadda ake amfani da mujallu ana bata sunayen mutanen da da sunayensu ne ake sayar da mujallun. Daga karshe ya yi roko ga hukumomin mujallun da su rika rubuta labaran ci-gaba a kan dan wasa maimakon buga mugun labarinsa. Ya kuma yi tsokaci da cewa hakika Fim da Garkuwa suna samun ci-gaba, to amma wannan, a cewarsa, yana da nasaba ne da sunaye da kuma hotunan 'yan fim da ake amfani da su.
Idan karamin yaro ko wani mai raunin fahimta ya ji wannan maganar, sai ya dauka kila haka take. To amma duk mai hankali ya san cewa lallai Mandawari ya yi bambarma a nan. Ni na fahimci cewa Mandawari yana kwatanta 'yan fim irinsa da annabawa ne, su kuma 'yan mujallun Film Industry kamar sahabbansu ne kenan. Wato dai su 'yan jarida sahabbai ne wadanda ya kamata su rika ruwaito labaran ayyuka da kalaman 'yan fim (su Mandawari) - wadanda suke kamar annabawa ne?
Mu dubi wannan furuci da idon basira. Shin 'yan fim suna koyi da Annabi kamar yadda Mandawari yake so a fahimta? Amsa ita ce ba za a rasa 'yan fim da dama da suke kwatanta koyi da Annabi ba. To amma fa su ba annabawa ba ne. Sauran fa? Wato wadanda ba sa koyi da Annabi fa? Annabi bai yi karya ba. Bai aikata zunubi ko daya ba. Bai ci naman wani ba. Bai yi sama-da-fadi da kudin amana ba. Bai karya dokar Allah (s.w.t.) ba. Shi ko dan fim, ajizi ne; ko da ya yi kokarin tsare mutuncin Shari'a za a sami wurare da dama da ya keta haddinta. A kan batun yin amfani da sunayen 'yan fim ana buga mujalla ana samun ci-gaba, sam bai kamata mutum mai hankali kamar Mandawari ya yi tunani irin wannan ba ballantana har a ji ya fito daga bakinsa. Shin ya san matsayin aikin jarida a kasa kuwa? Idan bai sani ba, bari a gurguje in gaya masa. Su kafafen yada labarai, kamar madubi suke. Wani marubuci ya taba cewa kafafen yada labarai suna nuna yadda al'ummar da suke cikinta take; idan al'umma mai nagari ce, to idan ka karanta jaridunta za ka gane; idan lalatacciya ce ma, za ka gane. Duk al'ummar da ta waye (kuma ina jin 'yan fim ai wayayyu ne ko?), to ba za ta so zama haka nan babu kafar da ke yada labaranta ba. Ko banza dai labaran za su kara wa al'umma haske a kan abin da take ciki. Wani shugaban Amerika ya taba cewa in da za a ba shi zabi tsakanin a ce kasa ta zauna babu jarida ko babu gwamnati, to shi a zabinsa gwamma a ce akwai jaridu babu gwamnatin. Gwamnati fa na nufin doka da oda! Dalili shi ne ya san cewa su jaridun za su iya zama tamkar majalisar kasa inda jama'a za su rika tattauna matsalolinsu kuma su amince kan yadda za su warware su. Wannan kenan!
Mu kuma dubi aikin da su Mandawari suke yi. Shin ba wata aniya suke watsawa cikin kasa ba cikin kasakasai? Shin suna ganin al'ummar da ake watso wa finafinan ba ta da wani hakki a kan mutane irin su Mandawari? Shin haka nan suke so a kyale su suna yin yadda suka ga dama ba tare da wani yana gadinsu ko kula da su ba ta yadda da ya ga an yi fawul sai ya busa usur? Ni a ganina, mujallun Film Industry suna yin bakin kokarinsu wajen kula da 'yan fim. Kuma sun yi amanna da harkar shirya fim, da yadda za a iya amfani da ita a gyara al'umma. Haka kuma sun san cewa za a iya amfani da harkar a lalata al'umma. To me muka zaba? Shin mu zabi yin gum da bakinmu (wato babu mujalla ko jarida) ta yadda duk wanda ya ga damar yin abin da ya ga dama sai kawai ya je ya yi? Ai ko Allah da ya halicce mu bai bar mu mu je mu yi abin da muka ga dama ba! Ya kafa mana dokoki! Wannan kenan!
Batun yin rahotanni na ci-gaba, tun tuni muka kyaro wannan wayon-a-cin, wai an kori kare daga gindin dinya. Shin menene rahoton kawo ci-gaba wanda ba na kawo ci-baya ba ne? Me Mandawari ya fahimta da rahotannin kawo "ci-gaba"? Mun yi sa'a ya fadi wani abu, inda ya ce a fadi kyakkyawan abu game da dan wasa, a boye mummunan abu na dan wasan. A takaice, shi dai yana son a bar 'yan fim sakaka: idan wani ya zambaci wani, kada a fadi; idan wata da wata sun yi fada a kan wani saurayi kada a fadi; idan wani ya karbe kudin wata bakuwar furodusa ya yi gaba, kada a fadi; idan wani ya fito a wani fim da ya saba wa addini, kada a fadi; idan an samu "furodusa madandani" kada a fadi; idan... Wannan kenan!
Ni a ganina, yawancin bil'adama suna da nakasu, sai dai na wani ya fi na wani. Wata sa'a nakasun nan hudubar Shedan ke haifar da shi. Dole ne a yi wa mutum matashiya a kan ya rika gyara halayyarsa. Kafafen yada labarai suna da alhakin farkar da mutum daga barci ko su sanya shi a hanya idan ya kauce. Irin wannan aikin, an dade ana yinsa, kuma tun kafin zamanin sahabban Annabi (s.a.w.) ake yinsa, tun a zamunnan annabawan da suka gabaci Manzo. Saboda haka kuskure ne Mandawari ya ce ya fi son a rika yi masa bambadanci, kada a "tona" kowa, a bar kowa ya yi abin da ransa ke so.
Kuma ga wani garaje ba gudu ba; shin sau nawa mujallun nan suka buga "mugun" abu a game da wani dan wasa? Shin ko Mandawari ya dauka duk abin da suka sani shi ne yake gani a mujalla? Ai kashi 95 cikin dari na labaransu da sharhin da suke bugawa na "ci-gaba" ne, irin wadanda Mandawarin yake cewa yana so su buga - ga shi kuwa tun da aka fara suke yin hakan ba tare da ya roke su su yi ba. A ganina, dalilin da ya sa suke yin hakan shi ne saboda harkar jaririya ce har yanzu; ya je ya duba mujallun ya duba abubuwan da suka yi a shekaru uku da suka wuce, ya gani.
Za mu ci gaba a Fim ta watan gobe insha Allah.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin