Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 34   Oktoba 2002
MU LEKA MU GANI TARE DA IBRAHIM SHEME


BABBAN SHAFI
MU LEKA MU GANI
HIRAR MUSAMMAN
Wasiku
KU TAMBAYE SU
Rahoton Musamman
Rahoto
Malam Zurke
RA'AYIN MUJALLAR FIM
Bukukuwa
Sauran Labarai
Fitattun Taurari
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka
Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM MAI FITOWA!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da MU LEKA MU GANIn yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Alh. Adamu Halilu (1936-2002)

Inna Lillahi wa inna ilaihi raji'un!

A RANAR Lahadi, 1 ga watan jiya, wani abin bakin ciki da jimami ya faru a kasar nan. Wannan ko shi ne rasuwar Alhaji Adamu Halilu a gidansa da ke 'Kagoro Close', Sabon Garin Tudun Wada, Kaduna. Rasuwarsa ta biyo bayan dadewar da ya yi yana fama da rashin lafiya; ya dade barin jikinsa ba ya aiki tun lokacin da ya shanye shekaru da dama da suka gabata. Allah ya jikansa, ya yafe masa kurakuransa, amin summa amin!

Alhaji Adamu, ko Baba kamar yadda ake kiransa (domin fa ko da ba shi ne ya haife mu ba, mun san ya haife mu, domin shekarunsa 66 a duniya), ba karamin mutum ba ne a kasar nan. Musamman ma ga masu harkar nan ta shirya finafinai, shi ba Baba ba ne kurum, a'a Kaka ne ga yawancinsu. Duk wani mai hankoron shi shugaba ne a harkar, ya-Allah zabensa aka yi ko shi ya nada kansa shugaba, marigayin yana gabansa. Alhaji Adamu Halilu yana daga cikin jerin gaba na mutanen da suka assasa sana'ar shirya fim a nan nahiyar Afrika, ba nan kasar ko kuma yankin Arewa kurum ba. A takaice, marubucin wasannin fim din Hausa da Turanci ne kuma gogaggen furodusa, sa'annan shahararren daraktan finafinai ne. Ya ba da umurni a matsayin darakta a finafinai sama da 70 na gwamnati. Sun hada da Mama Learn the Lesson (1971), Shehu Umar (1975), da Kanta of Kebbi (1976). Hasali ma dai fim din Hausa na farko da aka shirya a duniyar nan, mai suna Baban Larai, tare da Adamu Halilu aka yi shi; ya fito a matsayin dan wasa a fim din, kuma shi ne ya je ya zauna aka yi editin fim din da shi.

Adamu Halilu ne dan Arewa na farko da ya je Ingila domin yin kwas a kan ilimin shirya fim, a cikin 1959. A lokacin, daliban Arewa da ke zuwa waje sukan karanto wasu abubuwan ne, kamar aikin koyarwa ko aikin likita wadanda ake ganin sun fi ci. Ana ganin aikin shirin fim shirme ne. Hasali ma dai lokacin da ya nemi tallafin gwamnati don yin karatun sinima ko fim, sai marigayi Alhaji Abubakar Imam (Allah ya jikansa), marubucin Magana Jari Ce, ya yi matukar mamaki, ya ce masa, "Sinima? Haba, sinima ai maganar banza ce!" Da Adamu ya nace, sai su Imam suka kyale shi tilas. Abin sha'awa, da ya komo daga Ingila a cikin 1961, Turawan mulkin mallaka suka zo za su shirya fim din Baban Larai, wanda shi ne fim din farko da aka shirya da wani harshen Nijeriya, Imam da kansa ne ma ya rubuta labarin, kuma suka yi aiki tare da Adamu Halilu a kan fim din!

A 1954 Alhaji Adamu ya fara aikin fim. Duk rayuwarsa a fagen shirin fim ya yi ta. Shi ne daraktan farko na Sashen Majigi na gwamnatin tarayya (Federal Film Unit) a Legas. Da Sashen ya zama Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya kuma (Nigerian Film Corporation), shi Alhaji din ne aka nada Manajan Daraktanta na farko. Ya sadaukar da kansa ga aikin, yana ta hakilon ganin cewa harkar ta kafu sosai a kasar nan. A ganinsa, idan Nijeriya ta jagoranci sana'ar shirya fim a Afrika, to duniya duka za ta san yadda al'adun bakar fata suke kuma ta girmama su. Shi ya sa ya dingi yin aiki ba hutawa har zuwa lokacin da ya yi ritaya a cikin 1985.

Abin bakin ciki ne, amma kuma kaddara, da Adamu Halilu ya samu rashin lafiyar da ta hana shi ci gaba da ba da gudunmawa ga harkar fim. Har ya rasu yana da burin ganin cewa shi ma ya shirya fim nasa na kansa, musamman ta hanyar zamani da ake ciki. Yana da labarai da ya rubuta yana son ya mayar da su fim, amma ina! Kaddara ta riga fata.

Mutum ne mai goyon bayan finafinan bidiyo da ake shiryawa a yanzu, ga shi kuwa wasu hamshakan tsofaffin 'yan fim suna kyamar tsarin, har suna cewa su ba za su yi fim na bidiyo ba sai na seluloyid duk da yake hakan ya gagare su. Shi a ganinsa, duk abin da zamani ya kawo da shi za ka yi aiki.

An sha karrama Adamu Halilu saboda gudunmawar da ya bayar ga adabin Arewa. Karramawa ta karshe - kuma ta takwas - da nake jin an yi masa ita ce wadda Cibiyar Adana Al'adun Arewa ('Arewa House') ta yi masa a cikin Maris 2001. A wurin har sai da hawaye suka barke masa lokacin da Janar Buhari ya mika masa lamabar yabo da kuma kudi N60,000. Su kansu mahalarta, da yawa sun yi kuka da hawayensu ganin halin rashin lafiyar da yake ciki ta yadda bai iya tashi sai an kama masa.

Idan ka yi la'akari da aikin da mutum kamar Adamu Halilu ya yi, abin zai ba ka mamaki in na ce maka shugabannin shirin fim na Hausa ba su je ko da gaisuwar ta'aziyya a gidansa ba. Da yawa ma suna nuna wai ba su san ya rasu ba, ga shi kuwa an fadi a rediyo da talbijin. Wannan abin kunya ne, domin fa duk wani mai hankoron shi babba ne a wannan harka, mace ko namiji, da bazar su Adamu Halilu yake rawa. To, duk da haka ina kira ga dukkan wanda ya karanta wannan sharhin ya yi addu'ar Allah ya jikan marigayin.

Haka kuma ya kamata shugabannin shirin fim da gwamnatocin tarayya da Arewa su gaggauta yin wani abu na karrama shi bayan ransa. Iyalinsa suna nan (matarsa da 'ya'ya kamar goma da jikoki); a taimaka masu da wani agaji mana. Wannan zai ba da kwarin gwiwa ga duk wani mai son shiga harkar, ko kuma yana ciki, ya ci gaba da yin azama a kan aikinsa. Bugu da kari, Kungiyar Furodusoshi ta Arewa za ta iya ware wata rana a duk shekara a matsayin Ranar Tunawa Da Marigayi Adamu Halilu domin a yi juyayin ayyukansa, kuma a yi masa addu'o'i. Su kuma gwamnatoci suna iya rada wa wasu hukumomi ko tituna sunansa. A Kaduna, ina kira ga gwamnati ta rada wa zauren bikin al'adu da ke cikin Hukumar Al'adun Gargajiya (Arts Council) sunan Adamu Halilu (wato kamar a ce 'Adamu Halilu Theatre'), da sauransu. Duk da yake dai shi haifaffen Garkida cikin Jihar Adamawa ne, tun yana yaro ya maida Kaduna ta zama garinsa a dalilin zuwa aiki. Sa'annan ya kamata a fito da finafinansa kasuwa kowa ya kalla, domin shi din ma ya bukaci hakan a lokacin da yake raye.

Wani abu da marigayi yake so shi ne a yayin da Yarabawa da Inyamirai ke yin finafinan tsafe-tsafensu, duk fim na Arewa in za a yi shi, to ya kasance yana ciyar da al'adunmu gaba ne. Don haka ya dace dukkan furodusoshi da daraktoci su sa wannan a ransu idan za su yi fim. Yin wannan ba karamar darajtawa ce ga rayuwar Alhaji Adamu Halilu ba.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin