SHIN yaya za mu yi mu adana adabinmu a cikin kundin tarihi? Wannan tambayar ce ta dame ni a lokacin da na nemi fim din Munkar a kantin 'Malam Kato Square' da ke Kano na rasa. Shi wannan fim, yana daga cikin wasannin bidiyo na farko da aka shirya domin sayarwa a kasuwa. Ina ma jin shi ne aka fara sawa a cikin kwali ana sayarwa. Fitaccen daraktan nan kuma marubuci, Bala Anas Babinlata, wanda ya yi daraktin din yawancin finafinan 'Iyan-Tama Multimedia,' shi ne ya shirya shi. Can kwanan baya da muka hadu da Bala ya gaya mani cewa bayan fim din ya kare a kasuwa kuma ana ta tambayarsa shi, ya sake bugo shi ya sayar (ina jin a bara ne). To ni kam ban taba kallon fim din ba, shi ya sa na je nemansa. Abin da aka gaya mani a 'Malam Kato' shi ne tuni ya kare, dan wanda ya rage din kuma an share shi daga faifai an dora wani (yanayin kasuwar kenan!).
Duk wannan hakilon ya sa na yi wani tunani: ashe haka finafinan nan na bidiyo suke karewa har wata rana su zo su bace, mutum ya neme su ya rasa? Babu shakka, in da za a yi bincike a yau, za a tarar cewa finafinai da wakokinsu da dama sun bace; mutum ba zai same su ba sai ya je wurin furodusan; don ta daraktoci ka rabu da su kawai; yawancinsu ba sa aje kwafe na kasasuwan da suka ba da umarni. Kai dai bar su da karbar ladar aikinsu, daga nan shikenan. Akwai ma daraktan da bai damu da ya kalli fim dinsa ba idan ya fito, wai sai dai ya tambayi yaransa, "Yaya, fim din ya yi kyau kuwa? Meye observation dinku?"
Gaskiya ba abin dariya ba ne a ce finafinai suna bacewa kuma babu wanda ya damu. Anya mun damu da tarihi kuwa? Idan ka dubi yadda ake nazarce-nazarcen dadaddun al'adu a yau, za ka san cewa wata rana tana zuwa da wani mai bincike zai so ya san dukkan ko yawancin finafinan da aka shirya da Hausa a wannan zamanin na finafinan bidiyo. A lokacin kila mun kau, babu wanda zai iya amsa masa tambayoyinsa sai 'ya'yanmu da jikokinmu wadanda da wuya ne su wadatar da shi. E, na san zai iya zuwa ya duba mujallun finafinai domin ya gano wasu abubuwan. Amma haka ba zai wadatar ba ko kadan, domin kuwa su wadannan mujallun ba komai suke rubutawa ba. Duk da yake suna kokari wajen adana mana tarihin shirin fim, yawancin finafinan da ake ta shekowa a kasuwa ba a ma ko ambatarsu a mujallun, sai wanda ya ci sa'a wani dalili ya sa aka ambace shi.
Sanin muhimmancin wannan al'amarin ya sa a kasashe da dama an kafa hukumomi wadanda ke adana kwafe na finafinai da wasu nau'o'in shirin fim, kamar su wakoki, hotunan 'yan fim, kundayen labarai (screenplays), takardun ofis, kayan aiki irin su kyamarori da fitilu da injinan editin, da dai makamantansu. Kai, hatta samfur na rubutun hannu na 'yan fim ana so a adana shi. Misali, ko yanzu akwai wanda ke da rubutun da marigayi darakta Aminu Hassan Yakasai ya yi da hannunsa? Kila an tattara su an kona tunda shi ya kaura! A nan gaba za mu so mu san yadda rubutun Tahir Fagge yake, mu ji yadda muryar Abida take ba ta cikin wasan dirama ba, kuma mu ji tarihin Hamisu Iyan-Tama daga bakinsa.
A shirin fim na Hausa, ba a cika damuwa da tarihi ba. Shi ya sa ma wasu ke cewa hatta wadannan mujallun ba su da amfani, duk da yake suna dan adana tarihin. Yanzu da ka dauko mujallar Majigi ta Yuli 2002 za ka ji tarihin Aleebaba Yakasai da yadda yake yin kida, kuma a Duniyar Fim ta Yuni 2002 za ka kara fahimtar ko wacece Hadiza Kabara. Akwai wasu hobbasan na tara tarihi, koda yake ba da wannan nufin ake yinsu ba; wadannan ko su ne kaset da ake ajewa a hukumomin tace fim a Kano da Abuja, da kuma tsarin shirin Mu Shakata wanda Mandawari ke yi. A tsarin Mu Shakata, za ka ga 'yan wasa suna ba da tarihinsu da kansu, ga hotunansu ga muryoyinsu, babu kyale-kyalen lokeshin. Haka kuma a can baya wani furodusa, Haidar, ya gabatar da shiri mai suna Sirrinsu, to amma ya watsar. A yanzu kuma Furofesa Abdalla na B.U.K. da mujallar Fim suna saka al'amuran fim a intanet, wanda ba za su kone ba kuma wani ba zai share su ba.
To, duk wadannan hanyoyin ba su isa ba, musamman da yake wasunsu sana'o'i ne ba wai takamaiman kokarin adana tarihi ba. Dole ne a fara yin wani abu tun yanzu domin adana tarihin shirin fim din bidiyo. Nan da shekara dari ko dubu wasu za su so su san yadda wadannan abubuwan suke, ba sai sun niki gari sun tafi jami'o'in da ke Turai ko Amerika ba don su san tarihin shirin fim na Hausa.
Na san cewa wannan gagarumin aiki zai fi yin nasara idan akwai tallafin gwamnati. Kun san cewa gwamnatin tarayya ta taba kafa Cibiyar Adana Kayan Tarihin Finafinai (wato National Film Archives) a karkashin marigayi darakta U.S.A. Galadima. To wannan hukuma dai tuni ta durkushe. Kuma da ma can babu ruwanta da 'yan fim na bidiyo sai irin na sinima, wanda an daina yinsa saboda rashin kudi. Kuma yanzu ba ruwan gwamnati da harkar fim na bidiyo in ban da ta karbi kudin shiga ta hanyar "tace" finafinai. To, saboda me za mu dogara ga gwamnati ta yi mana wannan aikin wanda yanzu-yanzu ake son a fara shi ba sai jibi ba?
Babban kalubale ne ga kungiyoyin shirin fim su fara yin wani hobbasa domin yin wannan aiki. Shugabannin kungiyoyin su ya kamata su mike tsaye wajen ganin sun fara aikin. Suna iya neman gwamnatin Jihar Kano ko ta Jihar Kaduna ta ba su wani daki wanda zai zama suto ko rumbun adana kayan tarihin. Kai, ko kafin hakan ta samu suna iya fito da tsarin cewa duk wanda ya yi fim, to ya bada kwafe guda biyu a adana; kuma a ba da sanarwar cewa kowane dan fim ya kawo hotunansa da tarihinsa a rubuce, da duk wani abu da yake ganin ya dace a adana a kansa saboda gaba, ciki kuwa har da scripts. Ana yin haka a inda kai ya waye. Mu me zai hana mu fara? Ko kuwa mu ba mu waye ba ne?