Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 39   Maris 2003
NEMAN MAFITA


BABBAN SHAFI
GASKIYA DAYA CE
FADI SONKA
Wasiku
NEMAN MAFITA
DUNIYAR FINAFINAI
RAHOTO
Malam Zurke
RA'YIN FIM
Bukukuwa
Sauran Labarai
SABUWAR FUSKA
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka

Bangon Fim ta 35. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 34. Danna nan ka gani!

Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM MAI FITOWA!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
FADI SONKAr sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da tunanin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: Wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, ta da jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Sababbin Daraktoci sun yi wa Baba Ali caa
Saboda ya kira ku shashashai

A CI-GABA da bayanan da muke kawo maku kan tabarbarewar kasuwar finafinan Hausa, a wannan karon mun kawo maku ra'ayin wasu sababbin daraktoci ne kan sukarsu da darakta kuma mai kwalliya Baba Ali Yakasai ya yi, inda har ya ce shashashai ne. Baba Ali ya yi magana ne kan yadda sababbin daraktoci suke shigo da wadansu tsare-tsare cikin finafinai, misali aiki da komfuta don tsara wani abu kamar a nuno aljani da makamantansu. Sakamakon furucinsa, daraktocin sun yi masa caa, suna cewa nai kamata a ce babban mutum a wannan harka kamarsa ya fadi haka ba. Ga yadda suke cewa, a tattaunawarsu da SANI MOHAMMED MAIKATANGA:

Sauyin zamani ne ya kawo sababbin daraktoci

SABON darakta kuma fitaccen dan wasa Aminu Ali Zango ya kalubalanci kalmar da tsohon darakta Baba Ali Yakasai ya jefi sababbin darakkatoci da ita da ce wa babban kuskure ne. Aminu wanda aka fi sani da suna 'Kwai-A- Baka', ya nuna matukar mamakinsa kan yadda Baba Ali ya kira su da suna shashashai a cikin Fim ta watan jiya.

Cikin wani nuni da 'Kwai-A-Baka' ya yi wa Baba Ali, ya ce shi bai ga dililin da zai sa tsofaffin daraktoci su fi ka yin nukura da sababbi ba, musamman idan aka yi tunanin cewa wata rana su sababbin ne za su iya maye gurbin da tsofaffin za su bari ko ba-dade ko ba-jima.

"Baba Ali ya sake tunani. Ya tuna dan birni na zaune bakauye zai shigo birni, zai waye, zai murmure zai kuma ya tara abin duniya sama da dan birnin," cewar Aminu.

An kuma tambayi Aminu ko ya yarda da cewa aikin darakkta sai mutum ya karanta. A nan sai ya ce shi dai bai karanci aikin ba amma cikin ikon Allah ya iya sosai, "kuma ba a samun cikas ko wata tangarda tsakanina da wadanda ke ba ni kwangilar yin fim."

Ya ci gaba da karin bayani kamar haka: "Ni ban taba cinye wa kowa kudinsa ba kuma ba na yi wa mutane 'kan-ta-waye'; don idan mutum ya je wani wuri aka ce ya zo wurina zan yi masa a N450,000."

Da aka tambaye shi yadda ya shiga aikin darakta duk da cewa bai karanci abin ba, Aminu ya ce shi ai tsohon dan wasa ne tun tuni, ya goge kuma ya samu shawarwari daga daraktoci irin su Zulkifilu Muhammad, Ishaq Sidi Ishaq da kuma marigayi Tijjani Ibraheem.

Sai dai kuma bai yarda da cewa sababbin daraktoci sun yunkuro ba ne sanadiyyar zargin cin kudi da kuma 'kan-ta-waye'da ake yi wa tsofaffin daraktocin. Shi a nasa ra'ayin, sababbin daraktaci sun yunkuro ne saboda sauyin zamani da lokacinsa. Ya kara yin nuni da cewa, "Idan Allah ya sa a nan haryar abinci ko arzikin mutum take , to babu makawa sai ya ci."

Wasu daga cikin finafinan da Aminu 'Kwai-A-Baka' ya yi wa aikin darakta sun hada da Gadara, Iko, Zara, Azama, da Al'umma. A karshe ya nuna cewa shi da wanda bai karanta ba " ai tun daga screenplay ake fara shi idan daraktan da ya yi karatun abin daga can zai baro bida s-baya."

An haifi Aminu Ali a cikin 1972 a unguwar Zango, bayan Asibitin Murtala cikin birnin Kano. Ya gama karatun firamare cikin 1986, daga nan kuma bayan ya kammala karatun karamar sakandire, sai ya shiga Kwalejin Koyon Fasaha, Nassarawa Technical College a Kano inda ya kammala cikin 1992. Ya gama karatun difloma a 'Kano State Polytechnic' inda ya karanci fasahar gine-gine ('Building Technology) cikin 1995.

Ya kuma yi kasuwanci iri daban-daban tun lokacin da yake karatu. Daga cikin sana'o'in da ya yi akwai harkar gilashi da kuma kere-kere, sana'o'in da aka san mazauna unguwar Zango da su. Aminu ya kuma yi difloma a fannin mulki, wato 'Public Administration.'

Aminu ya ce ya fito cikin finafinai sama da dari daya. Fim din farko da ya fara fitowa a ciki shi ne Sa'adatu Sa'ar Mata, daga nan sai Kwai A Baka, Ni'ima da Hanzari. Na baya bayan nan kuma akwai su Kudira, Alkibla, Jumurda, da Kauna. Yawanci yakan fito a munafiki, mai murdiya, jami'in tsaro ko wani mai wani gurbataccen hali. Koda yake kwai aBake da su. "Ni halina na kwarai ne, ba za ka sani ba sai ka yi hulda da ni," inji shi.

Su Baba Ali 'yan 'Cut-Action!' ne kawai
Cewar Aminu Bala

Aminu Bala, wanda ake yi wa lakabi da 'Makashinka' saboda wani fim da ya taba shiryawa, yana daga cikin matasan furodusoshi da ake ji da su yanzu a Kano. Ya shirya finafinai da dama, wadanda suka hada da Lawisa, inda ake nuno mutum yana tafiya babu kai ko kuma ka ga kan mutum yana kumbura yana sacewa. Shi ma ya yi nasa bayanin kamar haka:

ABIN da ya sa zan ce wani abu kan maganar Baba Ali, kai su tsofaffin daraktocin nan da furodusoshi suna bakin ciki ne, don sababbin furodusoshi sun gane 'kan-ta-waye' kawai ake yi masu. Maimakon ka kashe naira dubu dari a fim iinka, sai a yi ma lissafin dubu dari biyu, daga karshe su je suna yi ma dariya-domin da ma ba kudinsu ba ne, na matan aure ne ko irin masu zaman kansu din nan. Duk yanzu babu wani kamfani babba da yake da kudin yin fim na kanshi, duk na kwangila ne!

Kuma da (Baba Ali) yake cewa sabbin ba su iya komai ba, shi ma din me ya iya? Ya yi karatun ne? Ai duk working experience ne. Kawai don sun ga sabbin suna kawo sabbin abubuwa ne a harkar suke jin haushi. Kuma wallahi ba abin da suka iya; karya ne wannan zancen nashi da yake fada. Ai wani abin kunya ma wani fim da suka taba yi wa irin nasu effect din inda wani dodo yake wasa da wuta, suka je suka kona kan dodon. Shi effect na komfuta ai ko Turawa ma suna aiki da shi, musamman ma irin wanda Bala Anas ya kawo, suna ganin su ba za su iya ba ne shi ya sa suke yi mana bakin ciki a harkar. Kuma suna ganin an zo da sabon salon da ba su iya ba shi ya sa. Har a mujallar Fim aka ba da labarin wannan fim din da suka kona wa wani fuska, wanda babban abin kunya ne a gare su ba har ma mu.

Duk wani abu da yake cewa ni kuma na fada karya yake, musamman a kan fim din Salma-Salma da yake magana. Mutum ya je ya kalla mana; ai ba karamin ci-gaba ba ne wannan.

To kuma da yake maganar practical effect ai ba su da ilimin shi practical effect din, domin ga shi sun je garin practical effect sun kona wa mutum fuska. Amma in da mutum zai tsaya ya yi nashi abu practically ai ya fi ma. Haka ma wani fim da dadewa wanda cinna wa wata wuta aka so a kashe ta a wani fim. Abin mamaki, duk irinsu ne suka yi wannan. Kuma shi na komfuta din da yake magana da sannu za mu kara fadada shi. To wai da ya ke cewa "sabbin daraktoci", shi ma ai a wajen Tijjanin ya koya, su Hafizu Bello, Ali Nuhu da sauransu. Ashe kenan ma su ne ba su iya ba, shashashun kenan. Kuma ai ba sai an fada ba yanzu su kansu masu kallon sun ga sabbin abubuwa a kan wannan harkar, ba kamar yadda finafinansu suke ba, su tara finafinai da yawa kawai su je su yi ma camamar fim wai sunan kuma ka kashe kudi.

Kuma da yake maganar ba a san maye komfuta ba sai ya gaya mana, Alhaji Lawan Abba mai CBC, bai karanci aikin ba ne? Ai yana gani, kuma ya sani yanzu ma akwai wani fim dina mai irin wannan effect din. Za mu yi shi kuma zai yi mamaki. Kai, duk wannan fa don sun dai samu wadanda za su yi wa zakin baki ne su tsara su, (su ce) "Ai za ka saida fim dinka, za a sai kwali kamar kaza..." - yi ta yi ma dadin baki a karbe ma kudi! Shi ne 'kan-ta-waye', daga karshe kuma a bar ka da kayan jaket fim ba kasuwa kuma an ki biyan mutane hakkinsu. Ka ji suna cewa, "Ai wane ma mu muka koya masa, ka kawo kaza." Kawai da ka saki jikinka shi kenan, sai a bar ka da cizon yatsa. Yanzu ka duba, wadanda suke ba shi aiki mutum goma yanzu ko daya babu, saboda sun an cuce shi. To da suka ga sabbin sun shigo sun fara karbar harkar sai wasunsu ciwon zuciya ya fara kamasu. Ta nan ne su sabbin suka fara aiwatar da komai da kansu.

Ita kungiyar da suke ce wa ta manyan daraktoci ce, mu wannan ba wani abu da muke tunani. Su waye furodusoshin? Ai mu ne! Ba sai mu daina ba su fim din ba, mu ga su wa za su shugabanta! Haka kuma akwai wani fim da suka yi wanda wani dodo yake fitar da wata wuta ta ka, aka samu laita da sheltos in a aka kunna laita sai a danna shi heltos din, sai wutar ta tashi. Ana yin haka dai da tafiya ta yi ta fiya ashe wannan sheltos din yana zubowa kan dodon nan, ba a ankara ba sai kawai suka bar dodon da konanniyar fuska. Kuma shi wannan tsohon daraktan shi ne ya yi wannan pratical effect din. Wanda wannan ko a tarihi in aka ji shi wallahi a dai harkar fim abin kunya ne. In bai san yadda zai yi a komfuta ba ya je ya yi tambaya mana; ai akwai masana, ba wai ya soke ta ba da kuma su wadanda suke dan kokartawa. Ya fa sani wannan ba wai kwaba hoda a yi wa budurwa ko tsohuwa kwalliya ba ne. E, mun san ya iya wannan babu wani tantama. Da irin wannan handamar da su suka handami wani fim na yaki, inda ya zo yaki ya zama kokawa. Ba zan fadi sunan fim din ba, amma dai wannan ma ai abin kunya ne ga irin yadda suke tunkahon su wasu ne a harkar. Kuma ai sai mun ga kai ya za ka samar mana abin da muke so sannan mu ba ka fim dinmu. Kuma wannan kungiyar ba ta isa ta dakusar da mu ba, Kuma ma ai duk yaran Tijjani Ibraheem ne marigayi; duk shi ya koya masu, daga baya kuma suka koma suna cewa wai su ma daraktoci ne, suna munafinci, dukkansu ba wanda ya karanci abin. Wai ya je waje-karya ne, duk 'yan "Cut! Action!' ne, ba su iya komai ba, babu wani maganar su ne za su zama wani abu. Sannan sabbin daraktocin da furodusoshi su ci gaba da rike gaskiya, kar a cuci 'yan kwangila, musamman mata, kamar yadda sauran suka yi masu (da sunan) cewa su ne wane.

Ban tsokani Baba Ali ba
Cewar Mudassir

Mudassir Haladu (Barkeke) yana daga cikin matasan 'yan wasa da suka rikide suka zama daraktoci. Lokacin da Baba Ali ya kira sababbin daraktoci shashashai, ya ambaci Mudassir da cewa shi Mudassir, wanda ake kira 'Mudan' a fagen shirin fim, ya taba furta cewa "harka ta koma hannun yara" a gaban Baba Ali din, wanda hakan na nuna kamar dai Baba Ali ya dauka tsokanarsa Mudassir din ke yi. A nan, Mudassir ya bayyana nasa ra'ayin kan ra'ayin Baba Ali Yakasai: Me kake son ka fada kan abin da Baba Ali ya ce?

MUDAN: Ni ba martani zan mayar ba, tunda duk mutumin da ya girme ka ya fi ka. Amma duk mutumin da shekara hamsin a haife ya haife ni, in ma jika ne ya yi da ni. Amma ni ba martani zan mayar ba a kan ci-gaban harkar fim, tunda ban ji ba ban gani ba ne, a mujallar Fim ta January na ga abin da ban ji ba ban gani ba an rubuta an ce na fada. Kuma ba wai ina kalubalantar Fim ba ne, a'a wanda ya yi maganar (baba Ali) shi ya fadi "Yanzu nan Mudassiru a bakin Kwality ya wuce ya yi masa shewa cewa "harka ta koma hannun yara." Ina tabbatar masa da cewa ni respecting dinshi ma yanzu na fara ban ce zan daina ba. Kuma lokacin da na shigo harkar fim kafin in daga a san ni babu hannun wadanda na fada sai hannunsa shi da marigayi Tijjani Ibraheem. Saboda haka duk wanda ya yi maka abin alkhairi, in dai kai ba butulu ba ne, ba za ka taba mantawa ba.

FIM: In da ka karanta sosai za ka ga cewa ba ka dai nuna cewa da shi kake ba amma shi a tunaninsa saboda shi ka fadin hakan.

MUDAN: Ni ba zan iya cewa da shi nake ba ko ba da shi nake ba, tunda akwai lokuta a cikin industiri za ka ga akwai wani abu da yake tashe. Lokacin da ake wannan abubuwan lokaci ne da yara suke samun ayyuka suke ji da kansu ko wani abu, kuma ka san hankalin yaro da babba ba zai taba zuwa daya ba. Ko da gaya masa na yi, bai kamata a cikin mu da ni da wani abu ba, a ce ni kadai ya kirawo sunana ya ce ni na fada. Lokacin yara ne muke ji da kanmu saboda aiki a hannunmu yake. Shi ya sa muke wannan ihu-ihun muke cewa "harka ta koma hannun yara". Kuma in muka gan su ko fada muke yi dole mu ba su respect dinsu. Ni ban ce da shi nake ba.

Fim: Shin lokacin da ka gaida shi, ka wuce ka furta wannan maganar?

MUDAN: Ai a wannan lokacin safe da rana da dare kowane lokaci, ina tabbatar maka iya ya mu yana da muka fito da harka ta koma hannun yana, mun kai kusan mu a shirin da biyar amma kuma wani zubin sai mu kwana a bakin Kwality, saboda sakewa da muke yi a gurin, da kuma hadin kai da mai wajen ya ba mu. Shi ya sa wani zubin ma sai mu kwana muna yi, sai washegari kowa ya kona gidansu ya rama barci.

Fim: To, wace kalma mai karfi yanzu za ka furta ta nuna cewa kai ba da Baba Ali kake wannan maganar ba, a'a acikin irin hayaniyarku ta yara ce ka fada?

MUDAN: To abin da zan iya ce wa shi ne wannan magana da muke yi ba zan iya cewa ba Baba Ali nake ba, kuma ba zan iya cewa da shi nake ba. Tunda kalma ce muke cewa harka ta koma hannun yara, a lokacin da muke wannan muna nufin da manyan muke dukkansu. A lokacin da muke fada muke yin nishadi da manyan muke. Allah ya jikan Tijjani Ibraheem, lokacin da muke nishadi da annashuwa in ya gani sai ya ce, "Ta yara kyau take ba ta karko." To ni ba da shi nake ba, saboda na fahimci ko ya kullace ni da wani abu. Don Allah yadda ya fada ta mujallar Fim bai kirawo ni ya gaya min ba ni ma na fada ta Fim ya yi hakuri.

Mu kada mu yi 'kan-ta-waye'
Cewar Dandukusuru

YUSHA'U IDRIS UMAR, wanda ake kira Dankusuru saboda wani fim da ya taba shiryawa mai wannan sunan, yana daga cikin sababbin daraktoci da ake ji da su a Kano. Fim din da ya fara bada umurni a cikinsa, mai suna Lawisa, ya ja hankalin jama'a musamman saboda siddabarun da aka yi a cikinsa inda akan nuno mutum yana tafiya babu kai ko kuma kan mutum yana kumbura. Ban da Lawisa, ya yi wasu finafinan. Shi ma dai a nan ya fadi nasa ra'ayin kan alkalancin da Baba Ali ya yi a kan mutane irinsa:

DA farko abin da zan ce (shi ne) ita wannan harka yadda ake yi mata tunani ba haka ba ne: wai sai ka zauna tare da wanda ya karanci abin ba ko yake cikin harkar tun tun tuni, ba a danganta damin basirar ka da kwakwalwarka. Tunda ni dai duk aikin da na yi tun lokacin da na fara haduwa da mai kamfanin Sarauniya zu zuwa su Mohammed Garba Kabara wanda mun yi ayyuka da dama da shi, kamar ni na rubuta labarin Mishkila, Ludufi, Kasaita, sannan kuma ni ne na yi masa matamakin darakta. Sannan bayan ganin irin abubuwan da ake yi kai ma ka yi kokarin kawo naka a ciki, ka hada da na wancan. Kuma ni da ma na fi son kallon finafinai irin na Turawa na siddabaru; da irin wadannan finafinan ne nake ganin yadda wasu abubuwansu suke har ni ma na rubuta nawa labarin wanda nake tunanin zai burge mai kallo. Labarin fim din ma daga mafarki yake farawa. Duk irin wadannan su ne za su kawo mana sauyi kan irin labaranmu na "ba na son 'yar talaka" ko "ba na son dan talaka," da dai makamantansu. Su wadanda ke kiran kansu manyan (daraktoci) su ne suke irin wadannan finafinan, ko ka ga ana sare-sare. Wani abu kuma fa su mutane ba gajiya ko daina kallon finafinan suke ba, a'a wasu ma yanzu suke sayen kayan kallon. To me ya sa ba za mu inganta harkar ba?

Shi wannan labarin na Lawisa, bayan mun gama screenplay sai muka samu wanda zai sarrafa mana hotuna, wato mai C.B.C. Alhaji Abba Lawan, kuma ya gaya mana yadda za mu yi in munj e wajen daukar shirin. Shi ne ya yi aiki a Salma Salma da Aisha 2, tare da maigidanmu Bala Anas Babinlata.

Na karanta a mujalla inda wani yake cewa sabbin daraktoci shashashai ne, abin ya ban kunya. Ai da ba don makoyi ba da gwani ya ji kunya. Shi da yake maganar sabbin daraktoci sabbin daraktoci, to wai harkarma daga farko zuwa yanzu wa ke jagorancinta? Tsofaffin daraktoci ne! Don haka duk halin da harkar ta shiga su ne. Akwai abubuwa da dama daya kassara harkar fim a yau, kuma mu da ake cewa wai ba mu da rijista da Kungiyar Daraktoci kuma suke ganin za su iya dakatar da mu a gwamnatance, to duk da haka sai mun kawo gyaran da gwamnati da 'yan kallo za su san cewa e, wasu sun tallafa wa harkar nan.

Abin da nake son gaya wa sabbin daraktoci dai shi ne mu ci gaba da rike gaskiya. Kar mu yadda mu koyi yadda daraktoci masu tunkaho da kansu suke yi, wato 'kan-ta-waye' da suke yi wa wasu furodusoshin. Tunda yanzu wannan 'kan-ta-waye' din da furodusoshin suka gane ana yi masu shi ne ya sa suke tsoron zuba kudinsu a wannan harkar, gudun kar a yi masu abin da ya faru a baya. Yanzu ya kai ga tsofaffin daraktocin suna zaman takaicin da har ma kasancewa sabbin daraktoci da furodusoshi sun karbi ragamar, domin su ba gaskiya suke kullawa ba. Sai mu sabbin daraktoci ina so ya zamanto ba kowane fim in an kawo maka karbe hayan, kai ka iya ba; a'a, ya kamata mu yi amfani da yadda daraktoci manya na waje suke: kowane darakta da pattern dinsa; irin su John Woo wanda shi ko a gidan sinima da an nuno sunanshi za ka ji ana ihu domin sun san irin fim dinsa. Kai ko da wani fim ya samu ba irin nashi ba da ya saba yi sai ya san yadda zai kawo wani abu irin na pattern dinsa a ciki. Ba kamar mu nan ba ina an ba ka action film -hayam; love film - hayam; adventure film - hayam, a'a za ka ga su wani bangarensa action ne, wani fantasy irin na siddaba ru da mu muke son amfani da shi yanzu, ba wai kawai fim na 'yan daba ka je ka samu wata gada ka dauka ka kai wa furodusa ba ba ruwanka ko yaya za su kare a kasuwa. Kuma ma sai ka kalli fim ka rasa gane wanene ma darakta domin ka rasa gane kangadon fim din, don haka sai a rasa gane waye ya iya ma a ciki. Kuma shi Bala Anas Babinlata maigidanmu wanda irin finafinansa da yake amfani da patterm dinsa ya iya kuma mu ma mun san ya iya masu kallo ma sun san ya iya; da ka so shi da kar ka so shi shi dai ya iya kuma ya huta.

Wani abu kuma wanda wani kamfani ya kwace daga hannun tsohon daraktan ya koma yin daraktin da kanshi wanda duk da cewa sabo ne kuma yana yin abin da shi wancan din yake yi, har ma an samu wani canji sabanin aikin wancan. Ba komai ba ne ya sa hakan (sai) kin tsayawa a pattern daya. Yanzu kamar Izu (Ojukwu) - wani darakta da ke Jos - ya zama wani abu a Legas a dalilin iyawarsa. Amma duk wani sauran darakta da yake kiran kansa ko suke kiran kansu waye-waye, wallahi duk soki-burutsu ne, ta ci barkatai. Tabbas shekarun baya su wadannan manyan ne suka yi kokarin juyo ra'ayoyin mutane kan harkar, amma yanzu... to, ga su nan dai! Har wani tsohon darakta da yake ambato cewa ba a san meye komfuta ba.

To wannan effect din da yake magana ai an yi shi ne tun wasu shekaru baya, da kuma wasu abubuwa da ake yi na natural ko reality. An ce akwai wani fim da ya yi wanda mu wannan abin kunya ne. Abin da zan ce wa Baba Ali in dai shi ne bai san komfuta ba ya yi bincike kar ya kara kona wa mutane fuska. Ta irin handamarsu ya handami wani fim na yaki (Burin Zuciya), wanda yakin ya koma kokawa, kuma wai suna tunkaho su ne daraktoci. Wannan ai babban abin kunya ne in abokan sana'armu 'yan Kudu suka gani.

Siddabarun zamani ci-gaba ne
Cewar Brown

FARUK ASHU BROWN ne daraktan wani sabon fim da bai fito ba mai suna Masoyiyata, wanda shahararren fim din nan na Amerika mai suna Titanic aka mayar da Hausa. Shi ne fim na farko na Hausa da ya bada umurni cikinsa. Don haka furucin Baba Ali ya shafe shi kenan? Ga yadda ya maida martani a takaice:

BABA Ali yana da damar fadin abin da yake so. Abin da na sani kawai shi ne an sami ci-gaba a fagen finafinai a tsakanin lokacin da na shiga wajen 1999 da kuma lokacin da Iyke Moore ya shirya fim din Dan'adam Butulu kashi na farko. Idan za ka hada da da yanzu za ka san an samu ci-gaba sosai. A da zan iya tunawa, Baba Ali na matsayin make-up artist. Siddabaru wajen shirya fim (visual effect) ci-gaba ne sosai a wannan harkar. Idan ka duba finafinan Turai kamar su The Matrix, Scary Movies, duk za ka tarar da su cike da irin wannan siddabarun na badda-bami don ganin an sami damar an burge. Saboda haka amfani da komfuta gurin wannan shirin ya danganta ga yadda kai ka tsara. Domin abin da ka sa wa komfuta shi za ta ba ka: idan ka sa shirme ka karbi shirme, idan ka sa abin kirki ka samu abin kirki. Ka kara yarda da ni a kan maganar shirin fim shiri ne da ke debe kewa, karantarwa da kuma sanarwa ga mai kallo. Haka zalika mafi akasarin finafinan shekarar da ta wuce, finafinai da sababbin masu bada umarni suka shirya ne, irin su Umar Jalo wanda ya yi finafinai da yawa na Ibro wadanda ke sa mutane farin ciki a gidajensu. Ya dai rage ga mai kallo ya zabi wanda yake bukata.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin