Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 45   Disamba 2003
NEMAN MAFITA


BABBAN SHAFI
GASKIYA DAYA CE
HIRA DA DARAKTOCI
Wasiku
NEMAN MAFITA
SHARHI KAN FINAFINAI
RAHOTO
Malam Zurke
RA'YIN FIM
Bukukuwa
ADABI
SABUWAR FUSKA
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka

Bangon FIM TA 45. Danna nan ka gani!
Bangon FIM TA 44. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 43. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 42. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 41. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 40. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 39. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 35. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 34. Danna nan ka gani!

Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM YA FITO!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
Sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

KASH! Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

'Yan wasa: Farida Jalal, A.A. Shariff (Momo), Kasimu Yero, Bashir Nayaya, Abubakar Yusuf Ladan, Hajara Usman, Sani Idris Moda, Sani Garba S.K, da Rashida Bello.

Darakta: Aminu A. Shariff

BABU IRINSA!

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

'Yan fim suna tsinka kansu

Cewar A.S. MOHAMMED

FITACCEN dan wasan nan da ke Kaduna, A. S. Mohammed, ya yi kakkausar suka a kan wadansu munanan halaye da wasu 'yan fim ke nunawa, musamman ga masoyansu 'yan kallo. Jarumin na shirin Maina ya ce kamata ya yi duk wata dabi'a mai kyau a same ta wajen dan fim, amma maimakon haka sai wasu su rika amfani da daukakar da Allah ya yi musu su rika zubar da mutuncinsu. Dalilin da ya ba da na yin wannan tsokaci shi ne, da yawa sai ka ga dan fim da bakinsa yana rokon masoyansa wani abu, musamman katin G.S.M., ko wurin kwana, ko ka ji dan fim yana cewa, "To yau dai muna wuri kaza, Allah ya sa a kawo mana abinci!" A cewar A.S., wannan ba karamin abin kunya ba ne da zubar da mutunci, musamman ga su 'yan kallo masoyan finafinai.

A wannan tattaunawar ce kuma, Fim ta yi amfani da wannan dama ta yi wa jarumin tsokaci a kan abin da ya hana kashi na biyu na fim din Maina fitowa. Amsar kawai da ya iya bayarwa ita ce, "E, to rashin yin fim din Maina kashi na biyu, zan ce ya bata mani rai, saboda ba haka aka so ba, wai kanin miji ya fi miji kyau. In da so samu ne, a yi shi na daya da na biyu gaba daya. To amma kuma idan har akwai takura, to shikenan. Saboda ai bayan fim din Maina na yi finafinai da yawa ga su nan, wadansunsu ma duk ba su fito ba."

Mun tambayi A.S. a matsayinsa na babban aminin furodusan fim din na Maina, wato Nasiru Garba Dan Funtuwa, shin ko rashin kudi ne ya sa furodusan ya kasa shirya na biyun? Sai ya amsa da cewa, "To a gaskiya na yi masa wannan tambaya ni kaina, sai ya ce mani kawai in saurare shi, akwai abin da yake jira, to har yanzu dai shiru."

A kan rashin jin duriyar Nasiru, A.S. ya kada baki ya ce, "Ai ya ma bar garin, wai ya koma Funtua da iyalinsa baki daya. Kuma har yanzu ba wanda ya tuntuba game da fim din. Kai, mu ko labarinshi ma ba mu ji!"

To idan haka ne kuwa, za a iya cewa Nasiru ya gudu ya bar ladarsa. Domin kuwa binciken mu ya nuna cewa 'yan kallo da yawa suna jiran fitowar Maina 2. Sai dai ko da shi furodusan bai yi ba, mun ji ana rade-radin cewa jarumar fim din, wato Hauwa Maina, da kuma shi A.S. a shirya suke idan furodusan zai ba su dama su ci gaba da shirin na biyu.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin