Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 27   Maris 2002
RA'AYIN MUJJALAR FIM


BABBAN SHAFI
Mu Leka Mu Gani
Zuwa Ga Masu Karatunmu
Wasiku
Ku Tambaye Su
Abokanmu
Rayuwarmu
Holywood
Malam Zurke
Ra'ayin Mujallar Fim
Rahoto
Sauran Labarai
Shirin Fim A Kaduna
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.
JE KA TA NAN

 
 


Balaraba: Rana ta fadi da rana tsaka!

"Wai gaskiya ne Balaraba ta rasu?"

WANNAN furuci za ka ji jama'a da dama ya ke neman jin hakikanin gaskiyarsa lokacin da labarin mutuwarta ya fara bazuwa. Mutum ba zai ce ga iyakar mutanen da suka kidime ko hankalinsu ya tashi ba bayan sun tabbatar da cewa Allah Madaukakin Sarki wanda ya halicci Balaraba, ya karbi abinsa lokacin da take kan hanyarta ta zuwa Kano inda aka shirya mata walima kafin a kai ta gidan miji daidai lokacin da ita da angonta Shu'aibu da sauran dubban jama'a ke cike da farin cikin auren wannan fitacciyar 'yar wasan fim.

Misalin Balaraba kamar misalin Iman ce. Iman wata yarinya ce, budurwa, 'yar kabilar Bororon daji. Wata rana tana kiwon shanu a cikin dajin kasar Kenya, sai wasu Turawa 'yan yawon bude ido suka gan ta a fefen titi da shanu tana kiwo. Da suka ga surar jikinta, sai suka fahimci tana da sifar da kamfanonin tallar kayan sawa na zamani ke nema domin tallata hajarsu. Nan da nan suka nemi iyayenta da hukumar gundumarsu, suka bai wa iyayen Iman makudan daloli. Kawai sai suka rankaya da ita Amerika.

Cikin kankanen lokaci aka sa ta a makaranta ta yaki jahilci, ta goge, ta koma mace sambaleliya, kyakkyawa. Yanzu Iman tare da fitattun matan tallace-tallace na duniya take gogawa (Super Models). Ta yi kudi, ta yi suna, ta kuma mallaki kadarori na miliyoyin daloli.

To haka ita ma Balaraba. Bafilatana ce wadda da rana tsaka ta yi sha'awar shiga finafinan Hausa. Haka ta je ta kai kanta Kano, ta shiga cikin birnin Dabo babu wanda ya san ta sai Bala Makosa, editan mujallar Nishadi. Cikin shekara daya ta yi fice da suna. Finafinanta da sunanta da hotunanta suka game arewacin kasar nan. Kowane gida idan babu fim dinta, to akwai hotonta, idan babu hoton kuwa, to ba za a rasa yawan fadar sunanta ba. Haka dai ta zama kamar gishiri ko ashana -gidan kowa akwai.

Mutuwar Balaraba ta zauna daram cikin zukatan jama'a, musamman masu sha'awar kallon finafinanta da wadanda ba su sha'awar finafinai da suka ji labarin cewa wannan kyakkyawar yarinya ta auri Shu'aibu Lawan bayan jama'a da dama har da attajrai sun neme ta da aure - ita kuma ta ce sai Shu'aibu za ta aura ko a rami zai saka ta.

Mutuwa dai daya ce; kowa ya san tana kansa kamar yadda ta fada kan Balaraba. Abin da kawai ya dugunzuma jama'a shi ne yadda Balaraba ta bar duniya ta hanyar mummunan hadarin mota kuma kan hanyar zuwa bikin auren. Allah ya jikan Balaraba!

Tilas iyayenta da masoyanta su gigita. Ba kuma za su taba mantawa da wannan rana ba ta 16 ga Maris. Su ma 'yan fim za su dade suna bakin cikin mutuwarta. Ta taka rawa sosai don ciyar da finafinan Hausa gaba. Ko shakka babu, rabuwa ko mutuwarta zai kara gigita su. Kamar yadda masu shirin fim na kasar Caina suka gigice sanadiyyar mutuwar Bruce Lee a hadarin mota a cikin 1965, nan mu ma abin ya same mu a 2001 lokacin da su Aminu Hassan suka rasu a hanyar Katsina. Ta sake aukuwa a Caina din dai sa'adda dan Bruce Lee mai suna Brandon Lee ya mutu cikin mota lokacin da ake daukar wani fim mai suna The Crow a Jihar North Carolina da ke Amerika a cikin 993. Wannan bala'i da ya auka cikin gidan Bruce Lee ya sa matar da ya mutu ya bari da 'yarsu Linda da kuma Shannon sun bazu cikin duniya neman taimakon addu'ar rokon kada Allah ya maimaita.

Nan 'yan fim na Hausa, tun da Balaraba ta bi sahun su Aminu Hassan, ya kamata mu mike tsaye da addu'a da rokon Allah ya kiyaye gaba. Halin kunci, gigita da rashin walwala da ango Shu'aibu Lawan ya tsintsi kansa a ciki abin tausayi ne. Mujallar Fim na yi masa ta'aziyya. Allah ya ba shi hakuri da juriya tare da shi da iyayen Balaraba.

Sai dai Shu'aibu da iyayen Balaraba, kai, da ma sauran 'yan fim da jama'a baki daya, mun hakkake cewa da ma a rubuce yake kwanan Balaraba ya kare daga wannan rana. Babban abin bakin ciki kawai shi ne ta bar duniya a kan titin da shugabannin da muka zaba suka ki su gyara duk da mutuwar da daruruwan jama'a ke yi a kansa. Talakawan da ake mulka ba da son ransu ake kashe biliyan da doriya ba don yin katin zama dan kasa. Ina amfanin wadata 'yan kasa da katin dan kasa a cikin kasar da danta ba shi da sukunin yin tafiya a kan titi, kullum yana cikin jimamin ko-ya-dawo ko kuma ba-ya-dawo ba - kamar yadda Balaraba ta hau titin ta tafi inda ba a batun ranar dawowa! Allah ya ba ki ladar auren da kika yi, duk kuwa da cewa ba ki kai ga shiga dakin miji ba.

Ku kuma abokan sana'ar Balaraba, zai kyautu ku sani cewa mutuwa dai ishara. Bayan ka yi wa mamaci addu'a, to kuma sai ka sani cewa kai ma taka tana zuwa, ko ba-jima ko ba-dade. Sai ka dubi rayuwarka, ka kara kyautata ta. Idan aikin alkhairi kake yi, to ka kara azama, in kuma kana yin kuskure ne sai ka nemi gafara daga gun Ubangiji, kuma ka yi kokarin gyara. Duniya ba gidan zama ba ce.

Bayan haka, ya dace mu yi kira ga jama'a don Allah a daina baza ji-ta-ji-ta a kan mutuwar Balaraba da danginta, domin ko me mutum zai ce, wadannan bayin Allah sun rasu ne a kan kyakkyawar niyyar da ke zukatansu. Babban abin da ya dace mu yi masu shi ne addu'ar Allah ya ba su Aljanna Firdausi, amin.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin