Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 31   Yuli 2002
RA'AYI BA GABA BANE


BABBAN SHAFI
RA'AYI
Zuwa Ga Masu Karatu
Wasiku
Balaraba Muhammad (1983-2002) 
Rahoton Musamman
Rahoto
Malam Zurke
Ra'ayin Mujallar Fim
Bukukuwa
Sauran Labarai
Fitattun Taurari
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka Bangon FIM ta 29
Bangon FIM ta 28
Bangon FIM ta 27
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da ra'ayin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


Mutunci Madara Ne...

Daga HALIMA UMAR GIADE

ALAL hakika a duniya mutum ba shi da wata daraja idan har ba shi da mutunci. Kuma duk wanda ya yi wasa da mutuncinsa har ya zube, to fa ba shi da sauran wata kima a idon al'umma ko da kuwa ya mallaki dukkan abin da yake cikin duniya ne. Kowa ya san cewa kunya, natsuwa, kamun kai da kuma rashin kwadayin abin duniya su ne manyan ginshikan da mutum zai gina ya samar wa kansa mutunci. Idan kuma har ya yi wasa da shi ya zube, to fa ya rabu da shi kenan don kuwa shi mutunci madara ne, idan ya zube ba ya kwasuwa.

Ba wani abu ne ya sa na fara da wannan shimfidar ba sai don ina son a fahimci inda na dosa. To a warware dai ina so na yi sharhi ne a kan halayyar da wasu mata 'yan fim suke yi wadda kan jawo mutane da yawa suke zargin cewa 'yan fim duka battatu ne. A hakikanin gaskiya, ina yawan ganina finafinan Hausa wadanda ake rawa da waka a ciki, amma guda hudu ne suka fi bata min rai har ya sa na fara raina wayon 'yanmatan da suka yi raye-rayen. Na farko na kalli wata waka mai taken "Don Allah Share Babu Damuwa" a cikin wani fim mai suna Kauna wadda Abida Mohammed tare da Aminu A. Shariff suka rera. A gaskiya duk Musulmi mai kishin addini, da Bahaushe mai kishin al'ada, da mata masu kishin baiwa da Allah ya yi wa mata, za su ji takaici idan sun ga yadda Abida, cikakkiyar Musulma kuma Bahaushiya wadda Allah ya yi wa kyakkyawar kira, maimakon ta zama mai kishin baiwarta, sai ga ta a gaban jama'a tana faman gantsarewa da karya kugu da jijjiga, ta manta cewa kaset din zai iya zagaye duniya kuma masu la'antarta sai sun fi yawa. Na tabbata ko da tantirin dan iska ne kuma fajiri idan ya gani sai ya raina mata wayo a zuciyarsa ko da kuwa ya yabe ta a fili.

Fim na biyu da na kalla shi ne Zubaida, inda aka sa wakar da Hadiza Kabara da Ali Nuhu suka cashe mai take "Bokiti". Dubi fa yadda Hadiza ta dinga girgiza kirji da tsalle-tsalle kuma ba tare da ta suturta kirjin ba. Haba Hadiza, kada fa ki manta har duniya ta nade wannan kaset din yana nan, kuma idan ba ki manta ba akwai haihuwa, akwai tsufa, akwai mutuwa!

A karo na uku na kalli fim shirin Taqidi na 2 inda na ga wata waka da Aina'u Ade ta yi tana ta faman rawa, rawa kuma irin ta wulakanta kai. A da na dauki Aina'u yarinya mai aji kuma mai daraja kanta, amma sai ga shi tun tafiya ba ta yi nisa ba ta fara dagula wa kanta lissafi. Na san cewa wakar Larabawa ce, to hakika ta yi kuskure don kuwa su ba haka suke yi ba; sai ta koma ta sake sabon koyo.

'Yar'autar masu laifi daga cikin 'yanmata hudu masu ban takaici ita ce Rukayya Umar Santa (Dawayya), wacce ta samo inkiyar sunanta daga shahararriyar wakar nan mai ratsa zukata amma kuma rawar wakar mai sanya zuciya kuna, wato "Dawayya". A gaskiya ba wani burgewa a ga mace tana faman girgiza kamar wani reshe don kuwa abin ba zai yi mata kyau ba ko kadan. A ganina yin hakan ba shi da wani amfani.

To babban abin da yake daure mani kai a nan shi ne, a duk lokacin da za a yi hira da 'yan fim za ka ji sun ce su fadakarwa suke yi, kuma su kara da cewa addini bai hana ba, ko su ce akwai wakoki na fadakarwa. To don Allah wannan rawar ce ta fadakarwa? Ku fa yi nazari da kyau. Wai shin me kuke nema ne a wannan harkar? Idan suna kuke nema, ai wanda kuka yi ma ya isa ku yi wa Allah godiya. Idan kuwa don burgewa kuke yi, wallahi ku sani bata kanku kawai kuke yi a idon duniya. Idan kuwa kudi ne, ina mai tabbatar maku da cewa mutunci ya fi kudi. Idan kuma kuna ganin kamar ci-gaba ne, to a zahiri irin na mai haka rijiya ne kuma zubar da mutunci ne da daraja irin taku ta 'ya'ya mata kuma 'yan'adam masu cikakken 'yanci. Idan ba ku farga ba, to da sannu za ku yi nadama, nadama mara amfani, don kuwa wata rana za ta haifar maku da mara ido.

Abu na gaba da na yi nazari a kansa shi ne su kansu furodusoshi da daraktocin suna da laifi. Da a ce 'ya'yansu ne ko kannensu, na tabbata za su kwabe su, su hana su. To su ma wadannan din ya kamata a dinga tsawata masu; ko da kuwa yarinya ta yin ne to a goge wajen. Idan kuma ta dage a kan sai ta yi to sai a fidda ita daga cikin shirin duk dai don a kare martabarta da ta addini da kuma al'ada.

Shawarata a nan ita ce ku yi kokari ku dinga kare mutuncinku da martabarku, kuma ku rika kama kanku. Ita dai mace komai na jikinta al'aura ne. To ina kuma ga idan tana girgizawa tare da gantsarewa komai yana bayyana a fili kuru-kuru? Kuma duk mutum mai suna na usuli kokari yake ya kwatanta halayyar mai wannan suna. Misali, Hadiza da Rukayya sunaye ne na usuli kuma na mata da kuma 'yar Annabin Rahama; Abida da Aina'u ma sunaye ne masu daraja. Amma maimakon a gado takwaran sai aka bige da gadon su Karishma Kapoor, Kareena, Juhi, Madhuri Dixit, Janet Jackson, TLC, Destiny's Child, da sauransu. Allah ya kiyashe mu, amin! Don haka don Allah 'yanmata ku daina irin wannan abu, ku yi kokari ku kare mana mutuncimu, kada ya kasance mun shiga sahun sauran matan duniya masu son tabbatar da 'yancin mata wanda Turawa suka kirkira a kokarinsu na ruguza addinin Musulunci. Yin hakan kuwa na iya sawa mu fada fushin Ubangiji tare da azabarsa mai radadi. Ku kuma daraktoci ku sa ido a kan lamarin. Mu masu kallo da ma aikinmu ne mu kalla mu fadi na gyara don a gyara, mu kuma yabi na yabo don a ci gaba.

Na yi wannan tsokoci ne ba don cin mutuncin 'yan fim ba, sai domin an ce gyara kayanka ba ya zama sauke mu raba, saboda yadda ko da yaushe suke cewa su malamai ne masu son kawo gyara a al'umma. To ya kamata a ce malami ya bai wa dalibinsa darasi mai amfani a nan duniya da ranar kiyama. Komai kudin mutum, ko kyansa, ko iliminsa, to idan ba shi da mutunci bai zama cikakken mutum ba. ·

Malama Halima Umar Giade daliba ce a Sashen Koyon Aikin Jarida (Dept. of Mass Communication) a Jami'ar Bayero, Kano.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin