Yadda aka yi fitaccen mai daukar hoton bidiyon nan ya rikide ya koma darakta
IDAN ba yau ba da za a fadi tarihinsa, masu kallon fim ba su san Mohammed Garba Kabara ba, sai dai sunansa suke gani a akwatunan talbijin ko kuma jin sunansa. Sunan Kabara dai ya yi nisa sai fa inda finafinan Hausa ba su karasa ba. Ko tantama kuma babu Mohammed ya aje tarihi na dimbin gudunmuwar da ya yi a boye. Ba kida ko waka yake yi ba; mai daukar hoto ne na finafinai (cameraman).
Babban dalilin da ya sa aka ce ya aje tarihi shi ne: Kabara ne ya dauki mafi yawan manyan finafinan da suka fi shahara. Shi ya dauki Tawakkali na 1 & 2, Badali 1 & 2, Mujadala 1 & 2 Kudiri 1 & 2, Furuci 1 & 2, kai da duk wani fim da ya yi fice dama wanda bai yi ba wanda darakta Tijjani Ibraheem ya tsara.
Tun a cikin 1990 ya fara daukar na'urar hoton bidiyo inda suka yi Tsausayin Takaba tare da Tijjanin. Tun daga lokacin kuwa ya zarce da aikin nasa har yanzu daga baya ya rikide ya koma darakta. Sai dai kuma tun tafiya ba ta yi nisa ba Kabara ya yarda da cewa akwai bambanci sosai tsakanin mai daukar hoto da kuma darakta. Kai ko mu'amalarsa da jama'a ita kanta ta nuna haka don kuwa a ranar 18 ga Fabrairu cewa ya yi "a wannan ranar wallahi sai da na yi attending mutum 42." Shi ya sa a ranar ya ce kansa kamar zai buga. To a unguwarsu ma da yawa sun dauka ko siyasa ya koma zai iya ci ganin yadda ake ta yi masa sallama a gida.
A cikin wannan hira da ya yi tare da MOHAMMED NASIR za ku ji dalilan da suka sa Kabara ya ce akwai bambanci tsakanin darakta da kuma mai daukar hoto (cameraman). Shin daga lokacin da yafara darakta zuwa yau finafinai nawa ya jagoranta? Wadanne ne kuma ke kan hanya? Wane sirri ne a gare shi har jama'a sun fara yi masa yawa tun bai yi nisa da zama darakta ba? Ga Kabara:
Fim: To kafin mu ji yadda ka shigo harkar fim, bari mu fara jin tarihinka.
Kabara: An haife ni a unguwar Kabara Kano) a 1970. A can na yi firamare ta Jarkasa. Daga nan na tafi sakandare ta Gwale. Kafin nan kuwa sai da na yi karatun Islamiyya har na sauke. Bayan na yi sakandare ta Gwale sai na fara aiki a CTV a 1989 inda nake yin cameraman. Da na shekara uku sai na tafi Jami'ar Bayero ta Kano na yi Professionall Diploma a kan aikin jarida (mass communication).
Fim: Da ka gama ina ka nufa?
Kabara: (dariya) E, to ai ka san lokacin harka ta bude muna samun kasuwa inda akan rika kirana ina yin aikin daukar hoton bidiyo na aure ko suna ko walima. A hankula har Allah ya kawo na shiga cikin wannan harka.
Fim: A wace shekara ka shiga harkar fim?
Kabara: Ina jin a 1990 lokacin da muka yi Tsautsayin Takaba.
Fim: Da me ka soma?
Kabara: Da cameraman. Don Tijjani Ibraheem ya jawo ni ya ce mu zo mu yi Tsautsayin Takaba wanda (Umar Bawa) Dukku ya ba shi aiki.
Fim: Ashe ka dade kana sarrafa kyamara.
Kabara: Kwarai, saboda ni ita ce layina, abin da na karanta kenan.
Fim: To bari mu dan ji wasu daga cikin finafinan da ka yi wa aiki.
Kabara: Gaskiya suna da yawa. Don yawanci duk finafinan da Tijjani Ibraheem ke darakta, to ni ne mai kyamara. Ga su nan barkatai.
Fim: Me ya ba ka sha'awa ka bar aikin kyamara ka koma darakta?
Kabara: Tun farko ban taba yin tunanin zan yi aikin darakta ba. Sai da yawa mutane na kawo min aiki su ce in yi darakta na fim dinsu. To tun ina janyewa har dai na daure na fara karba.
Fim: Yaya aka yi har suke nema ka yi masu darakta alhali ba ka taba yi ba?
Kabara: Yadda aka yi suka sa ni, shi ne sai da yawa suna gani idan muna aiki, za su ga ina aikin ni kadai ko da da darakta ko ba su. Shi ne ya sa suka yi tunani ko za ni iya.
Fim: Da wane fim ka fara?
Kabara: Da jimawa bayan mun gama Tsautsayin Takaba sai Alasan Kwalle ya kawo min wani fim mai suna Rashin Mafadi na yi masa darakta. Daga nan ban kara yi ba sai da aka dan tura ni na je na yi wani fim, Dace.
Fim: Daga lokacin da ka yi Rashin Mafadi ka ce ka dauki tsawon lokaci daga baya ka yi Dace. To rashin mafadi ne ya sa ba ka samu mai fada maka gaskiya ka ci gaba da yi ba, ko kuwa dace ne ba ka yi ana kiranka ka yi?
Kabara: (dariya) Sau da dama ba ni da lokacin da zan je in yi saboda duk aikin da Tijjani zai yi ni ne mai kyamara. Idan babu ni, to ba ya jin dadin aikin sosai. Sai ga shi yanzu dai ka ga yadda Allah ya yi.
Fim: Daga wane loaci ka jefar da kyamara ka koma kana ba da umarni?
Kabara: Ai ni har yanzu ban yada kyamara ba. Dole ne, ita wannan kyamara ai ita ce kashin bayan kowane fim. Saboda haka ni ko yaushe ina kyamara, ko gobe ina kyamara.
Fim: A baya bayan nan wadanne ne finafinai ne ka yi wa darakta?
Kabara:Yanzu wadanda na yi wa darakta ba su fita ba akalla za su kai guda bakwai. Akwai C.I.D., Fa'ida, Murdiya, Mu'amala, Ka'ida, da sauransu.
Fim: Wane irin bambanci ka samu tsakanin aikin kyamara da na ba da umarni?
Kabara: Gaskiya kalubale ne babba. Saboda idan kana aikin kyamara babu ruwanka da tension (zafin kwakwalwa). Idan kana darakta kuwa za a kawo maka labari mara kyau dole sai ka maida shi mai kyau. 'Yan wasa akwai wanda ya san abin da yake akwai kuma wanda bai san abin da yake ba. Dole ka maida wanda bai san abin da yake ba ya san abin da yake. Haka furodusa, kowa ya taso sai ya dirar maka. Amma idan kana aikin kyamara babu ruwanka. Kai dai kawai aikinka ka sani. Amma darakta akwai wahala sosai.
Fim: Lokacin da ka fara ba da umarni ko ka samu matsala tare da Kungiyar Daraktoci ta Jihar Kano?
Kabara: Babu wata matsala da na samu. Don tun kafin in fara sun san I can be a director (zan iya aikin darakta). Wannan dalili ne ya sa lokacin da aka yi taro suka fada min cewa an saka sunana a cikin kungiyar.
Fim: To yanzu wane kalubale ne a kanka?
Kabara: Kawai in ga wannan harka tamu ta gyaru sosai.
Fim: Wai kai har yanzu kana cikin mutanen boye ko ka tafa fitowa a fim?
Kabara: Ni har yanzu mutanen boye ne; sau daya ne, lokacin da ake yin Abin Sirri Ne, aka rasa wanda zai yi wani scene a makaranta, aka rasa likita, sai na sa kaya na fito. Kuma ni ne daraktan fim din.
Fim: Yanzu wadanne finafinai ne gabanka?
Kabara: Akwai Kuskure, Shakuwa, Rinjaye, Baiwa, Du'a'i, Mubaya'a...
Fim: Kabara, ka tara finafinai da yawa, ba ka gudun shiga sanadiyyar tara finafinan jama'a jingim a hannunsu?
Kabara: Su suka jera kansu. Idan furodusa ya same ni sai in ce ina da wani a hannuna. Amma wani lakaci laifin furodusa ne; wani zai zo ya ce maka shi dai don Allah ko farawa ne a je a yi. To idan an fara an tsaya ka ci gaba da na hannunka ai ba laifinka ba ne.
Fim: A cikin fim din Kuskure an ce kun tura 'yar mutane Katsina ta auri wani mutum alhali tana da miji….
Kabara: (dariya) Ai mutum ya tsaya kuma zai ga yadda muka gyara Kuskure a cikin kuskure!
Fim: Allah ya kara gyarawa.
Kabara: Amin.
Fim: Shin menene tsakaninka da 'yar wasa Hadiza Mohammed Kabara? An ce sunanka ne take amfani da shi.
Kabara: E, haka ne. Mun hadu daita tun lokacin da za a yi wani fim mai suna Malam Karkata.Ta zo tana bakuwa, to ka san Allah kan hada jinin wasu. Daga nan muke tare da ita har yanzu.
Fim: Kun dade tare. To akwai maganar aure tsakaninku kamar yadda ake ta yadawa?
Kabara: Gaskiya ji-ta-ji-ta ce kawai, babu maganar aure a tsakaninmu.
Fim: Lokacin da mujallar Fim ta kira sunanka a filin Malam Zurke cewa kai tazuru ne, an yi ta surutun wai kana da iyali. Mecece gaskiyar maganar?
Kabara: (dariya) Ni har yanzu tazuru ne; ba ni da mata balle da.
Fim: Darakta, mun gode.
Kabara: Ni ma na gode.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin