RANAR Asabar, 6 ga Afrilu, 2002 an yi taron kaddamar da wani fim wanda fitacciyar 'yar wasan nan Hindatu Bashir ta shirya mai suna Maula. A taron, wanda aka yi a otal din 'Tahir Guest Palace' da ke Kano, jama'a daga sassan daban-daban na al'umma sun halarta: 'yan fim ne, 'yan siyasa, 'yan kasuwa, ma'aikata, 'yan jarida, da jami'an gwamnati. Babban abin burgewa game da taron shi ne halartar da Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Dr. Umar Ganduje, ya yi tare da mukarrabansa. Ya je ne a madadin Gwamna Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso, wanda a lokacin ya yi balaguro. Wato kenan in da Kwankwaso yana nan, to da da kansa zai halarta.
Bayan wannan, a watan jiya wani gungun 'yan fim (shugabanni da mabiya kungiyoyin 'yan fim) ya kai ziyara ga Gwamna Kwankwaso a Gidan Gwamnati. A ziyarar, an tattauna da Gwamna bayan an gabatar da 'yan fim gare shi. Gwamna ya nuna jin dadi da ziyarar, kuma ya bayyana goyon bayan gwamnatinsa ga shirin fim na Hausa.
A gaskiya, duka wadannan gagarumar nasara ce. Kaddamar da Maula, musamman shi ne karo na farko a Kano da babban jami'i irin Mataimakin Gwamna ya halarci wani taro na 'yan fim. A da, sai dai ka ga wasu malamai, ko 'yan kasuwa ko sarakai ko 'yan majalisa a taron 'yan fim. Kuma kai wa Gwamna ziyara shi ne karo na farko da aka yi hakan. Dalili shi ne duk da yake akwai yunkurin a fahimci juna tsakanin 'yan fim da gwamanati, zaman-doya-da-manja ake yi. Amma halartar Mataimakin Gwamna wurin kaddamar da fim, da kuma karbar da Gwamna ya yi wa maziyartansa, tare da kalaman kara karfin gwiwa da shugabannin gwamnatin suka furta a wuraren, alamu ne da ke nuna an shiga matakin gaba ko wani yanayi na kara dankon zumunta a tsakanin bangarorin biyu.
Mun fahimci cewa kafin yanzu, gwamnati, musammman 'yan Gidan Gwamna, suna dar dar da rungumar 'yan fim ne saboda siyasa. Sun ji wasu mutanen gari (musamman malamai) suna yawan sukar 'yan fim. Don haka tunda su suna la'akari ne da inda bakin malaman da manyan jama'a ya karkata, sai suna janye jiki daga gare su. To, mun kuma fahimci cewa su kansu malamai da sauran manya tuni sun soma sauya tunaninsu game da 'yan fim. Sun fahimci cewa shirin fim bai saba wa addini ba shi kansa tunda za a iya amfani da hanyar fim din a gyara dabi'a.
Duk wannan ya sa muke farin ciki da har Mataimakin Gwamna ya zo taron 'yan fim, shi kuma Gwamna ya karbe su hannu bibiyu. Allah ya sa abin ya ci gaba har su kansu Gwamna da Mai Martaba Sarki a gan su a wani taro ko al'amari na 'yan fim wata rana.
Mun tuno cewa a wasu jihohin, sam abin ba haka yake ba. Lokacin da aka kaddamar da Rigar 'Yanci a Gombe, Mataimakin Gwamnan jihar da Mai Martaba Sarkin Gombe da mukarrabansu duk sun halarta. Sa'annan ko a jihar da batun Shari'a ya fi zafi, wato Zamfara, Gwamna ya ba da taimako na kudi da mota lokacin da aka kaddamar da fim din Babu Maraya… a can Gusau. Kuma mun ji cewa a yunkurin da ake yi na kaddamar da fim din Kaddara a Kaduna, Gwamna Ahmed Mohammed Makarfi ya ba da agaji.
A ganinmu, ya kamata su kansu shugabannin shirin fim, musamman ma dai na Jihar Kano, su tashi tsaye wajen inganta dangantakar 'yan fim da gwamnati da sauran jama'a. Bai kamata su rika nokewa ba. Abin kunya ne a ce ba su taba ziyartar Gwamna ko Sarki ba a kungiyance sai a bana. Sai dai idan taronsu ya tashi su kira hakimai da wasu malamai da suke da alaka da su. Ya kamata daga yanzu su rika shirya kai ziyara ga Gwamna da mataimakinsa da Sarki da manyan malamai. Zai kyautu a rika kai ziyarar shan ruwa a karshen Ramadan ko ta Barka Da Sallah ko ban-gajiya ko ta ta'aziyya (idan wani abu na bakin ciki ya faru, misali fadowar jirgi da ya faru a Gwammaja), da sauransu. Mun ji dadi da muka ji cewa kwanan baya wasu shugabannin shirin fim sun kai ziyara ga shehin malami Dokta Yusuf Ali a gidansa a Kano. Sai dai kuma ita wannan ziyarar ba da sanin sauran 'yan fim aka yi ta ba, a'a a asirce aka yi ta kuma ba tare da wata bayyananniyar manufa ba. Ya dace idan har za a yi irin wannan ziyarar, a sanar da membobin kungiya, ba a yi wani 'sunkuru' ko tuwona-maina ba.
A nan, muna kira ga Kungiyar Furodusoshi ta Arewa da ta shirya kai ziyara can kololuwar gwamnati, wato Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja. Ko dai a rubuta takardar neman ganin Obasanjo kansa, ko a ga mataimakinsa Atiku Abubakar, ko shugabannin majalisun tarayya biyu din nan, wato Cif Pius Anyim da Alhaji Gali Umar Na'abba (wanda dan Kano ne), ko kuma ma a gan su baki daya. A ziyarar, a tsara ganin wasu shugabannin, kamar su Shugabar Hukumar Tace Finafinai ta Nijeriya, Madam Roseline Odeh, da Ministan Yada Labarai, Furofesa Jerry Gana, da shugaban Hukumar Kiyaye Hakkin Mallaka, da Babban Daraktan Hukumar Fasaha da Al'adu ta Kasa, da Darakta-Janar na Hukumar Talbijin ta Nijeriya (NTA). Dukkansu suna da alaka da shirin fim. Idan an gan su a sanar da su ci-gaban da aka samu a harkar fim na Hausa, a gabatar da wasu bukatu (misali a nemi a kafa ofishin Hukumar Tace Finafinai ta Nijeriya a Kaduna ko Kano, kamar yadda aka yi a Legas, musamman tunda yunkurin yin hakan da aka faro yanzu ya ci tura).
Shirya irin wannan ziyarar ba ya bukatar wani siddabaru. Akwai 'yan fim a Majalisar Tarayya, 'yan Arewa, idon sani, wato irin su Alhaji Abdu Haro Mashi (Sardaunan Furodusoshin Arewa) da Alhaji Abubakar Sadiq Yar'Adua (furodusan shirin Tajir wanda zai fito a bana), da Alhaji Ibrahim Ganyama (shugaban kamfanin hada hotunan fim da shirya fim na Mu'azat da ke Kano), da sauransu.
Irin wannan hobbasan ne ya sa takwarorinmu 'yan Kudu suke zuwa Abuja su ga duk wanda suka ga dama, kuma su yi tasiri wajen tsare-tsaren gwamnati kan shirin fim. Mu kuwa yawanmu ya zama na yuyuyu, nauyinmu ya zama na buhun kaikai. Wannan ko yana faruwa ne ba don komai ba sai don shugabannin shirin fim na Hausa suna muku-muku kan rungumar malamai da jami'an gwamnati, kuma suna tafiyar da shugabanci kamar suna jin tsoro.
To, don Allah dai muku-mukun ya isa haka nan. Lokacin farkawa ya yi. Motsi ya fi labewa.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin