Wulakanci a bikin Abida
YANZU dai ta tabbata cewa akwai wadansu 'yan fim wadanda suka daura gaba wurjanjan da 'yan jarida wadanda ke ba da labarai a kan harkar shirya finafinan Hausa. Wannan ya fito fili karara musamman a bikin fitacciyar jaruma Abida Mohammed, wadda ta auri furodusa kuma mai kamfanin 'Home Alone Production,' Hamza Mohammed Danzaki, kwanan nan. Tun kafin a daura auren abokan ango suka yi taro inda suka yanke shawarar cewa a yi duk yadda za a yi a hana 'yan mujalla (kamar dai yadda suke kiran 'yan jaridun Industry) buga labari kan auren, ta hanyar hana su yin hira da ma'auratan da kuma daukar hotunan abubuwan da za su faru a lokacin shagalin auren. A cikin jahilcinsu, wannan zai taimaka wajen durkusar da mujallun, ta yadda wata rana za a wayi gari a ga babu mujalla ko daya a fagen shirin fim. Abin dariya kenan, wai yaro ya tsinci hakori!
Da farko, tun a gidan daurin aure an hana a yi hira da Abida. Kokarin da 'yan mujalla suka yi don su tattauna da amaryar bai yi nasara ba, domin a cewarta an hana ta ta yi magana ba tare da izini ba. Shi ko Hamza da zaran ya ga wani dan mujalla sai ka ga ya murtuke fuska kamar an aiko masa da labarin mutuwa. Sa'annan da aka zo yin walima a otal din Ni'ima, nan ma an so a nuna wa 'yan jarida iyakarsu. Ga su sun zo da kayan aiki, amma aka yi kulle-kullen hana su shiga zauren da ake bikin. Sai da kyar aka bar 'yan wasu mujallu biyu suka shiga, su din ma don an san mujallun sun daina fitowa a tsawon watanni. A cikin zauren kuma an binciki kowane mai daukar hoto don a tabbatar babu dan mujalla a cikinsu, musamman mujallar da ke jagorantar sauran, wato Fim.
To, kamar yadda al'amura suka wakana dai, duk wannan yunkuri ya ci tura. 'Yan mujalla (ciki har da ita kanta Fim) sun ci kasuwar bikin auren Abida. Da su aka yi komai. Duk da yake jahilan da ke ganin sun hana 'yan mujalla shiga zauren bikin suna tunanin sun ci nasara, a banza, domin kuwa duk abin da ya faru a kan idon 'yan mujallar ya faru. Babu wani abu da aka yi ko wata kalma da aka furta a wurin wanda 'yan jarida ba su gani ko suka ji ba. Haka kuma sun daddauki hotuna son ransu.
Sakamakon wannan yunkuri na abokan ango da iyayen gidansa, ya kamata mu ilimantar da Hamza da wadannan 'yan zugar a kan aikin jarida, musamman matsayinsa a harkar shirya fim. Da farko dai, muna taya Hamza da Abida murnar aurensu, murna kuma ta fisabilillahi. Muna murnar ganin yadda 'yan fim din suka rufe ido suka auri junansu, kamar dai yadda Fati Mohammed da Sani Musa suka yi a bara. Idan angwayen sun tuna, 'yan mujalla suna daga cikin dalilan da suka sa aka san Abida da Hamza, ta hanyar labaransu da aka rika bugawa. Mujallar Fim, musamman, ta fi kowace mujalla ba da labaran Abida, kuma labarai ne da suka kara wa 'yar wasan kwarjini. Mujallar ce ta fara buga Abida a bangonta, har ta yi ayar tambaya: "Me Ya Sa Ake Rububinta?" A lokacin, so mujallar ke yi 'yan kallon finafinai su san Abida da farin jinin da ta shigo Industry da shi. Duk wanda ya karanta labarin ya san ciyar da ita gaba aka yi. Kuma lokacin da Abida ta zama Jarumar Jarumai Mata a gasar Arewa, an bugo ta a bangon mujallar Fim tare da taya ta murna ita da Hamza. A nan, ba ma sai mun ambaci tarin wasikun da mutane masu kallo suke rubutowa ba a kan 'yar wasan, ana bugawa. Muna sane da cewa mujallu da dama sun yi wa Abida irin wannan karramawar.
A nazarin da muka yi, duk mugun yunkurin hana ba da labarin auren a mujallu ba laifin Abida ba ne. Domin wakilan mujallu da dama sun ga Abida kafin auren da kuma lokacin da aka sa ta a lalle, suka bukaci su tattauna da ita. Ta gaya masu cewa tana so ta yi, amma an hana ta. Wannan ya nuna kenan ango da abokansa ne suka yi kullin. Ga shi yanzu an bar wasu da tunanin cewa wani mugun abu aka yi a cikin zauren bikin, musamman da yake akwai dimbin masoyan Abida da su ma aka hana su shiga zauren, aka sa sojoji suna bin su da bulalar dorina suna caula masu. Kamar yadda wani ya ce, ba a taba wulakanta jama'a a bikin auren wani dan fim ba irin yadda aka yi a bikin Abida Mohammed. Abu dai bai yi dadi ba! Shin ko da ma irin tarihin da abokan ango suke so Abida ta bari kenan?
Mu a mujallar Fim mun san cewa mutum yana da ikon ya shirya bikinsa yadda ya ga dama. A wasu kasashen, musamman Amerika, har wata duniya 'yan fim suke tafiya (musamman tsibirai masu nisa) su yi aure a boye saboda wasu dalilai. Amma ko su din ma, idan 'yan jarida suka ji labari, sukan yi hayar jirage helikofta su je tsibiran da kyamarori masu dauko nesa, ana ganinsu su dauki hotuna daga sama kuma su sanar da duniya. To, a inda kai ya waye kenan. Mu a nan da yake har yanzu a dawa muke, shi ya sa har ake kulle kofar dakin otal, a ce ba a son 'yan jarida. Har a bari wasu ballagazun 'yan fim suna wage baki a zauren biki suna fadin muggan kalamai game da su kansu a bainar jama'a, suna fadin abin da zai rikita tunanin jama'ar gari, har jama'ar garin su tafi suna cewa, "Au, ana yin abu kaza da abu kaza ne a cikin harkar fim?" To wa ya tozarta wani a nan in ba su masu irin wadannan surutan banzan ba?
MU LEKA MU GANInmu shi ne an yi wa Hamza da Abida ingiza-mai-kantu-ruwa kawai. An hada su husuma da mutane masu kaunarsu ('yan jarida). Su lura mana, idan 'yan mujalla ba su da amfani ga 'yan fim, ya aka yi aka bar su suka ba da cikakkun labaran duk wani aure na 'yan fim da aka yi, kamar auren su Bashir Bala (Ciroki), Jamila Moh'd Sabo da Fati Abubakar, Aminu Moh'd Sabo, Maijidda Abdulkadir, Fati Mohammed, Halima Adamu Yahaya, marigayiya Balaraba, da sauransu? Ya ba a hana ba? Sai na wata wai Abida?
Su fa 'yan jarida, suna adana tarihi ne. Ko bayan shekaru aru-aru 'ya'ya da jikokin Abida za su so su ga yadda aka yi auren uwarsu/kakarsu a lokacin da ta yi wata sana'a mai jawo wa mutum tashe da farin jini. Kuma su angwaye su sani, babu wanda ya isa ya hana a rika buga jaridu da mujallu a kan harkar fim a duk kasar da harkar ta bunkasa. Dokar kasa da ta duniya ta bai wa manema labarai wannan damar, shi ya sa duk wanda ya bushi iska sai ka ji ya ce shi ma bari ya kafa mujalla ko jarida kan abin da ya ga dama.
Shawararmu ga 'yan fim baki daya ita ce su kyale 'yan jarida su yi aikinsu, domin ko su kansu masu kallo suna son aikin. Shawaraki ne kadai zai ce mujallu ba su da amfani. Kuma ku kwatanta abin da namu 'yan mujallar suke rubutawa da wanda na Kudu ke yi mana, ai sai ma ku gode Allah cewa ka'idojin addini da al'adarmu suna da tasiri a kan aikin 'yan mujallunmu. Su kuma masu yin zuga, su sani cewa aikin wofi suke yi; suna bata wa kansu lokaci ne. Ga matsalolin gaske nan birjik cunkushe a gabansu, su tafi su warware su mana, sun tsaya suna dukan iska. Su sani cewa dashen da Allah ke so babu mai iya hana shi ya girma.
Mu kuma 'yan mujalla baki daya, mu farka.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin