Kowa ya ji a jikinsa!
WATAKILA mai kallon finafinan Hausa kadai ne bai san cewa kasuwar finafinan ta karye ba. Amma masu shirya fim da masu sayar da shi sun san cewa ruwa ya doki babban zakara. Yau sama da wata bakwai, tun daga lokacin da shekarar nan ta 2002 ta karyo kwana, furodusoshi da dama suke shan kashin ruwan fatarar da rashin ciniki ya janyo a kasuwa. Wannan ya sa 'yan fim da dama sun shiga cikin taskun da har yanzu sun kasa fitowa daga cikinsa. Sai ka ga babban furodusa wanda a da da kyar yake amsa gaisuwar na kasa da shi, wai don isa, yanzu ya zama abin tausayi. Ya zuba kudi ya shirya fim din, ya kai kasuwa, amma kudin sun ki fita. Ya kashe N400,000, ya kasa fitar da N150,000. Kullum yana bin 'yan kasuwar kaset yana rokon su ba shi dan abin da zai yi cefanen ranar, ko wanda zai sa wa motarsa fetur. Don ta bushashar da ake yi a da kuwa, tuni furodusoshi da dama sun sauya salon rayuwarsu; 'yan na kirkin, masu yi wa dangi alheri yanzu boyewa suke yi, ta yadda idan 'yan raraka ko masu bin su bashi suka yi sallama a gidansu sai su ce wa uwargida, "Don Allah ki ce ba na nan!" Yanzu sai ka ga babban dan wasa ya shafe mako biyu zuwa uku babu wani fim a gabansa da zai yi. Haka shi ma darakta da mai kyamara da sauran masu taimakawa a shirya fim. Zaman kashe wando ya yi yawa a industiri. Ban da kuncin rayuwa da wannan ya janyo, hakan kuma ya haifar da bakin rai ga wasu 'yan fim, ta yadda da zaran ka tabo mutum sai ya nemi huce haushinsa a kanka. Gulmace-gulmace kuwa, abin ba a magana. Wani ma yakan arce ya bar garinsu saboda matsalar da shirin fim ta janyo masa.
Daga cikin manyan kamfanonin da aka san sun shahara wajen shirya fim, yanzu 'yan kalilan ne ake labarinsu. Da yawa sun durkushe, suna makyarkyatar mutuwa. Manyan furodusoshi da dama sun hakura da harkar, suna zaman warabbuka. Yawanci sun bayyana kudirinsu na daina harkar fim baki daya, har wasu sun koma wadansu sana'o'in don samun abin jefawa a bakin salati. Wadanda ba su da wurin komawa kuma, suna nan labarin nasu babu dadin ji. Yanzu fagen fim ya cika ne da finafinan sababbin furodusoshi wadanda ba su san dawan garin ba; sai bayan sun yi fim daya ne sannan za su gane; wannan shi ne sabuwar sarar 'kan-ta'waye.'
Abin da 'yan fim suka ki tambayar kansu shi ne: shin me ya janyo wannan ukubar? Kuma yaya za a yi a magance ta? Kin amsa wadannan tambayoyin guda biyu rak ya sa har yanzu harkar fim din Hausa tana cikin rami mai zurfi mai duhu. Sam, mujallar Fim ba ta goyi bayan a ci gaba da zama a haka ba, jiya-i-yau. A ganinmu, wahalar ta isa hakanan, kuma lokacin mikewa a kashe matsalar ya zo. Ba daidai ba ne a zauna kurum ana taya juna jaje. Hakan ba zai kai 'yan fim ko'ina ba in ban da wahala maras karshe.
Me ya kamata a yi? Mataki na farko dai shi ne sai an amince cewa akwai matsalar. Yin haka zai sa a fara tabukawa wajen tunanin magance ta. To, batun ko akwai matsalar dai wannan ba sai an kai ruwa rana ba. Kowa ya san akwai ta, domin kuwa kowa ya ji ta a jikinsa! To, tunda ko haka ne sai a nemi mafita.
Mecece mafitar? Wannan mujallar ta nemi jin ra'ayoyin 'yan fim, kamar yadda za a gani a wani rahoto cikin mujallar. Muna son mu ma mu ba da 'yan shawarwari wadanda idan an bi su, ko dai ba a magance matsalar ba, to lallai za a rage ta. Na daya, a tambayi shugabannin shirin fim: shin me suke yi tun da aka zabe su? A ganinmu, an zabe su ne domin su yi wa sauran jama'a aiki wanda zai taimaka a fitar da jaki daga duma. To amma har yanzu jakin nan yana cikin duman. Ya kamata membobin kungiyoyin shirin fim a kowace jiha su bukaci shugabanninsu su zauna su yi nazari, tare da sauran membobin, a kan matsalar. Kowace jiha ta dubi yanayin zamantakewar jiharta, ta ga idan yana da nasaba da halin da ake ciki. Idan an samu daidaito a kan nazarin da aka yi, sai kuma a kwatanta sakamakonsa da na sauran jihohi. Idan aka ga cewa matsalar ta shafi dukkan kasa, musamman arewaci, to sai Kungiyar Furodusoshi ta Arewa ta mike ta san abin yi. Wannan babban aiki ne a gabansu wanda ya dace a fara yinsa a yau, ba sai gobe ba.
Daya daga cikin matsalolin da muke hangen za a gano a jihohi har da sayar da basira wadda bidiyo kulob suke yi. A ganinmu, ya dace a kira 'yan bidiyo kulob 'barayin zaune', masu ci da gumin wasu. Duk inda ka leka a nan Arewa za ka ga irin wadannan shagunan, birni da karkara. Hatta matan aure yanzu bidiyo kulob suke yi daga gida, wasu kuma har karamar sinima gare su cikin gidan; mazansu sun san sata ce fa, to amma sun kau da kai domin a ganinsu wai matan sun samu sana'ar yi su ma. Bidiyo kulob ne suke ba da aron kaset a kan N20 a kacal, inda a mako daya sai su mayar da kudin kaset din da suka sawo (N250), kuma su ci gaba da ba da hayarsa. Shi furodusa ba shi da ko sisi a wannan garabasar. Me zai hana 'yan bidiyo kulob su rika biyan dan haraji ga furodusa? Duk wanda ya kalli fim ba zai je ya sawo shi ba kuma. A can baya an sha faman tsara yadda za a magance matsalar 'yan bidiyo kulob, amma a banza; ko dai an kasa aiwatar da kudirorin da aka zartar, ko kuma ba a gano bakin zaren ba yadda ya kamata.
To amma kada a dauka bidiyo kulob ne kadai matsalar. Akwai wadansu. Misali, ita kanta hanyar da ake bi ana sayar da finafinan ga dillalin kaset, tana bukatar kwaskwarima. Ya za a yi 'yan kasuwa su kara wa furodusa kudi? Ya za a yi su rika biyan furodusa a kan lokaci, kuma kudi masu kauri (ba kamar yadda ake yi yanzu ba - kana bin dan kasuwa N30,000 na kaset dinka da ya sayar, amma in ka je sai ya dauko N5,000 ya mika maka!)? Sa'annan a dubi ainihin yadda finafinan suke su kansu. Yawanci labaran soyayya ne. Labaran soyayya fa ba laifi ba ne, to amma yadda ake ba da labaran duk hanya daya ce. Wani fim din ma labari daya ne da wani wanda aka kalla, illa kawai an sauya sunansa da yadda aka dauko hotunan da 'yan wasan. Basirar masu rubuta labarai ta dakushe. Haka ita ma ta daraktoci; kullum yawancin yanayin yadda suke ba da umurni iri daya ne, babu sabon kakale. Kuma shin ko tsarin bin layi ya gamsar da kowa kuwa? Shin ana kiyaye dokar layin? Bayan haka, ga cunkushewar kasuwa da finafinai kwashi-kwaraf marasa inganci. Yawansu ya sa mai saye yakan rasa gane wanne ne mai nagari, kuma wanne ne mai rauni. Uwa-uba, duk an yi masu kudin goro: da 'camama' da wanda ya ci kudi duk jaket dinsu N45 yake. Sam, a nan ba a yi adalci ba. Hakan ya sa su kansu masu ganin wai su ne 'manya' a harkar, sun koma suna rige-rigen dauko Ibro ya shirya masu 'camama'.
To, a gaskiya wayon shirya 'camama' ko zaman dishan ko furta cewa 'Ni na daina fim' ba shi ne zai kai wannan harkar ga gaci ba. Dole ne a motsa a fuskanci matsalar da ake ciki gaba-gadi. Me ya sa muke kiran 'yan fim jarumai, masu warware matsalolin al'umma a wasan cikin kaset, amma kuma a ce sun kasa magance nasu matsalolin?
A nan bari mu yabi Kungiyar Furodusoshi ta Jihar Kano kan wani hobbasa da ta fara yi kwanan nan - wato samame a unguwanni kan masu bidiyo kulob. A samamen, an kama mutane da dama wadanda aka ba da belinsu a kan kudi N3,500 kowane mutum. Lallai ya dace a ci gaba da yin wannan aikin, kada a fara a watsar kamar yadda ake yi a da. Mun tabbatar duk wani mai harkar fim zai goyi bayan kamen da aka yi. Muna kira ga kungiyoyin furodusoshi na sauran jihohi su ma su yi irin wannan aiki. Kuma su tabbatar ba su bar matan aure da ke ba da hayar kaset ko nuna finafinan Hausa ba. Su ma gaggan barayin zaune ne wadanda ba su da bambanci da barayin da ke fasa gida suna kwashe dukiya.
A karshe, bari mu yi dan tsokaci a kan yanayin zamantakewa a tsakanin masu shirin fim. A gaskiya, masu shirin fim, musamman furodusoshi, suna ba mu kunya kan yadda suke gaba da junansu. Da wuya ka ji furodusa ko darakta kaza yana son ganin ci-gaban dan'uwansa. Kowa so yake dan'uwansa ya durkushe, wata sa'a ma har ka ga ya dauki mataki da kansa na ganin cewa wane ya samu koma-baya. A nan, mun dora laifin a kan shugabannin harkar, wadanda su ne ya kamata su rika sa baki a tsakanin membobin kungiyoyinsu wadanda ba sa jituwa. Abin mamaki, su shugabannin su ne a kan gaba wajen yin gaba da junansu. Sai ka ji shugaba ya bude baki yana sheka ashar a kan dan'uwansa furodusa, maimakon a ce shi ne yake tsawatawa. Wannan ya sa 'yan fim da dama ba su ganin shugabanninsu da gashi, domin suna kallonsu a matsayin wadanda suka kasa daukar matakan gyara harkar. Don haka muna kira ga shugabanni su rika hada kansu, su daina gaba ko nukura da juna, kuma su tashi tsaye haikan wajen ganin sun dawo da martabar shirin fim da cin ribar shirin.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin