HAJIYA Laila Dogonyaro ta dade ana damawa da ita a fagen nema wa matan kasar nan 'yancinsu. Tun zamanin da ake ce wa Bature "Zaki" take kan sahun gaba na gwagwarmaya da zaluncin da ake yi wa mata. Da yake har ya zuwa yau din nan zaluncin bai gushe ba, ita ma har yanzu ba ta gaji ba; tana nan ana bugawa da ita.
Hajiya, wadda ita ce Garkuwar Garki, ta yi wani abu kwanan nan wanda ya dace mu ce wani abu a kansa. Wannan ko shi ne shigowa harkar fim da ta yi da karfinta. Ita ce ta dauki nauyin shirya fim mai suna Hannun Dama, wanda kamfanin 'Mandawari Enterprises' ya shirya a bisa yarjejeniya irin ta kwangila. Mun ji an ce an kashe makudan kudi (wai kusan naira miliyan biyu) wajen shirya fim din. A ganinmu, wannan ci-gaba ne, a ce manyan mutanen kasar nan suna zuba jari cikin harkar da ta dade manya suna kyamarta har wasu suna son su ga bayanta. Mun tuna cewa ban da Laila, akwai wadansu manyan da suka dan sa kafa daya cikin harkar, wasu kuma ma dukkan kafafun nasu. Misali, wani dan majalisar Jihar Gombe ya shirya Rigar 'Yanci, kuma wasu manyan attajiran a jihohi kamar Kano da Katsina da Zamfara da Kaduna sun mara wa shirya finafinan Hausa baya. Abin da Hajiya Laila ta yi karin ci-gaba ne na abin da mata suka yi, wato irin su Hajiya Bilkisu Salisu Ahmed Funtuwa, Hajiya Halima Dan Almajir, Hajiya Balaraba Ramat Yakubu, Hajiya Umma Ali, Hajiya Fatima Mohammed (Ana Bikin Duniya), da dimbin matan manyan mutane wadanda ba za mu iya lissafa su duka a nan ba.
Mun yi shawarar mu yi tsokaci kan shigowar ita Garkuwar Garki ne domin ita fa ajinta kusan daban yake. Su Laila su ne kasar nan; su ke fadi a ji. Tana da abin da ake kira connection, wato kamun kafa a cikin gwamnatocin jihohi da na tarayya. Don haka za ta iya ba da taimako ta fuskoki da dama. Hasali ma dai, kamar yadda ta bayyana a cikin wannan mujallar, ita ce ta yi kamun kafa ga Gwamnan Jihar Jigawa har ya ba da kudin da aka shirya fim din, kuma mun ji an ce tana nan tana shirya wani fim din na Hausa.
Kiran da za mu yi ga mutanen da mata irin su Hajiya Laila (da ma matan da ba su kai mukaminta ba) suka gaskata suka ba su amanar shirya masu fim shi ne don Allah a rika kyautata wa matan. Kada a rika cutarsu ta fuskar nawa ne ya kamata a shirya fim, ko ta wajen sayar da shi, da sauransu. Domin mun lura da cewa mata da yawa sukan zuba jari a harkar fim fiye ma da mazan, to amma yawanci sukan kare ne da bacin rai. Ko dai a yi masu shigo-shigo-ba-zurfi su zuba kudin da suka ninka abin da ya kamata su kashe, har a karshe su yi asara, ko kuma a cuce su ta hanyoyi daban-daban. Yawanci, maza ne ke zambatar tasu. Cutar mata masu zuba jari a harkar fim tana kashe masu gwiwa, kuma wannan yana sanyawa harkar ta nakasa ta hanyar raguwar masu jari a cikinta. Akwai mata da yawa da suka sa kudi suka yi fim, amma ba su ci moriya ba, bayan kuwa da fari an lasa masu zuma a baki. Daga bisani sai ka taras ko da suna son su yi wani fim din, sai su canza darakta ko furodusa. Kowa kuwa ya tuna bara bai ji dadin bana ba ne. Mun san cewa ita kwangila business ce, wato kasuwanci, to amma a yi hankali da irin ribar da ake ci daga kwangila. Gwamma ka ci riba kadan, ita mai fim ta ci nata; maimakon ka yi cin dare daya.
Muna addu'ar Allah ya sa jarin da Hajiya Laila Dogonyaro ta zuba a Hannun Dama ya yi amfani. Ta bayyana cewa kaddamar da fim din za ta yi. To hakan yana da kyau, musamman idan a Abuja za a yi taron, kuma a tabbatar dimbin masu fadi a ji a wannan gwamnatin, da manyan 'yan kasuwa da sauran jama'a, sun halarta. Wannan zai sa a san fim din, kuma a san zangon da fim na Hausa ya kai, ta yadda wasu mutanen ma za su shigo.
A karshe muna yaba wa Garkuwar Garki kan yadda ta nuna damuwa kan rigingimun da ke faruwa tsakanin 'yan fim na Hausa har tana tsawatawa. Wannan ma wani bangare ne na tsare wa jama'a hakkinsu kamar yadda ta saba yi a duk tsawon rayuwarta.