Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 35   Nuwamba 2002
Rayuwarmu Daga Balaraba Ramat YakubuMalama Balaraba Ramat


BABBAN SHAFI
MU LEKA MU GANI
TALLA
Wasiku
KU TAMBAYE SU
Duniyar Finafinai
Rahoto
Malam Zurke
Rayuwarmu
Bukukuwa
Sauran Labarai
Fitattun Taurari
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka
Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM MAI FITOWA!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da MU LEKA MU GANIn yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Amsoshin tambayoyinku

Mata masu azabtar da marayu

Zuwa ga Anti Balaraba,

BAYAN gaisuwa yaya aiki da fama da jama'a? Da fatan Allah ya saka da alheri, amin. Dalilin wannan wasika tawa shi ne ina so ki shawo mana kan irin matan nan da ke bai wa 'ya'yan kishiyoyinsu azaba saboda iyayensu ba sa gidan ko don rashin cikakken hankali ko Allah ya yi masu rasuwa ko makamancin haka. Anti, wallahi in kika duba akwai irin wadannan mata a zamanin da muke ciki kuma a garinmu ma muna tare da su. Akwai wata mace wadda Allah bai ba ta haihuwa ba sai kudi amma wajen goyo ba 'yar arziki ba ce, wato in an ba ta yaro ko yarinya ya shiga uku ko maraya ne ko da iyayensa a duniya, don babu ruwanta. Wallahi in ta kama yaro ya yi laifi har tsine mata ake yi. Ko don ba ta san dadin haihuwa ba ne? Da ta san dadinta da ba ta yi haka ba. Bissalam.

Yayani Popular Guy Isawa,

P.O. Box 279, Isawa L.G.A., Jihar Bauchi.

Yayani,

Zuri'ar 'ya'ya aba ce wacce komin kudinka ba ka sayenta a kasuwa, Allah shi ke badawa ga wanda ya so. Kuma Allah ba kin maraya yaake ba don iyayensa sun mutu. Maraya ba bawa ba ne kuma amana ce. Allah madaukakin Sarki kan danka a hannun wanda ya so yi wa rahama. Duk mutumin da ya zalunci wani Allah zai saka masa balle maraya. Ina kira ga iyaye mata don Allah don Annabi su dinga saukaka wa rayuwarsu wajen zama da 'ya'yan kishiya ko tana da rai ko ta mutu ta bari ko aurenta ya mutu, ki dauka a ranki cewar wannan matakin uku za su iya samunki; za ki ji dadi in an azubtar da naki 'ya'yan? Ba ki sani ba ko dan da kika wulakanta kika azabtar ya zama shi ne za ki mora, ba yadda Allah bai iya ba.

NA KASA ZANTAWA DA MASOYINA

Anti Ramat,

GAISUWA mai yawa tare da fatan alheri. Ina kara jinjina maki kan kokari da kike yi na magance matsalolin rayuwarmu na yau da kullum. Allah ya kara taimakawa, amin.

Bayan haka na rubuto ne domin neman shawara game da da wata matsala da ke damuna. Matsalar kuwa ita ce na je Kasa Mai Tsarki ne a shekara ta 2002. A ranar da za mu dawo ne bai fi kamar saura sa'a daya ba mu taso sai na hadu da wani Balarabe wanda nan take Allah ya sa son juna a cikin zukatanmu, inda ya nuna mani matukar kaunarsa har ya kara da cewa idan har zan amince shi yana son ya aure ni. Kasancewar mun hadu a kurarren lokaci sai ya ba ni lambar wayarsa a kan alkawarin cewa idan mun iso gida lafiya in buga masa. To bayan mun dawo, na yi kokarin samunsa, amma lokacin da duk na buga sai Larabawa su dauka, ni kuma ba na jin Larabci su kuma ba sa jin Turanci. Na rasa abin da zan yi. Kuma wallahi Anti Balaraba kullum sonsa karuwa yake yi a zuciyata. Don Allah ki taimake ni da shawarwari masu gamsarwa. Allah ya taimaka. Wassalam.

Aisha Aliyu Hassan,

Usman Danfodio University, P.M.B. 23461, Sokoto.

Aisha,

A gaskiya kina cikin halin dimauta wanda sha'awa kan haifar da shi. Shawarata a nan mai kyau ce, amma sai na fara gargadinki tukunna. Jinsinku ba daya ba ne ke da sha'awa daya kika yi da shi, ba kasa daya kuke zaune ba. Ya kamata A'isha ki kara tunani mai zurfi: anya ba sha'awa ce ta zarme miki zuciya ba? In kin yarda cewar kaunarsa kike yi to ga shawara biyu: (1) Tunda ba ki jin Larabci to nemi wanda yake ji a nan U.D.U. wanda zai zama tafinta tsakaninki da wanda kike yi wa wayar don su gane a nemo miki shi ku yi magana; (2) ko kuma ki daure ki biya Umara ki koma Saudiyya ki neme shi a adireshin da ya ba ki, watakila ki yi dacen samunsa. Amma da hatsari zuwanki nemansa, A'isha. Wayar ta fi tsafta.

ME YARINYAR TAKE NUFI NE?

DON Allah ina son Hajiya ta fayyace mani dalilin wannan matsala da nake ciki. Wato akwai yarinya da nake so kwarai da gaske. Amma ita ta ki amsa mani bukatata. Amman a kullum tana zuwa wurina mu yi hira. Amman duk lokaci da za ni furta mata zancen soyayya sai ta nuna mani ita ba ta amince ba. Kuma duk da haka nan wannan zancen ba za shi hana ta dawowa wurina gobe ba. Wai don Allah me ya kawo haka ne?

Auwal Rabilu,

c/o Govt. Science Sec. School, Dansadau, P.M.B. 1030 Gusau, Jihar Zamfara.

Auwalu,

Anya kuwa yarinyar nan tana kaunarka? Don zai yi wuya a yadda na fahimci bayaninka. Auwalu, tana bata maka lokaci ne kawai, ta maida kai abokin hira, in har wanda take so ya fito ta gama da kai. Tun yanzu ka sallame ta, kafin ta sa sallame ka. In kuma ta ki to, kai in ta zo kar ka zauna, bar mata gurin. In tana sonka za ka gane.

WA KE CIN ARZIKIN WANI DAI?

GAISUWA da fata alheri a gare ku. A gaskiya ban gamsu da bayanin da Hajiya Balaraba ta yi ba a cikin mujallar watan Satumba 2002 dangane da "hakuri maganin zama da uwar miji."

Da farko ta fara da fatawa mai kyau amma cikin bayaninta akwai inda ta ci wa matan aure fuska da wulakanta darajar mata a idon duniya. Kalmomin da ta fadi ba shi da asali bare fa'ida ko fadakarwa face cin fuska da raini da take niyyar jawo wa mata. Idan kuka duba inda ta ce "kar ki manta cin arziki ne ya kawo ki gidan, kuma arzikin wannan tsohuwar kike ci, domin da ba ta haifa ba da ke ba ki gan shi kin aure shi ba. Ki tuna zai iya canja ki, don zai iya auren mace goma amma fa karya yake yi ya sauya uwarsa."

To ya zama auri-saki kenan kuma ita dadinta ne a ce danta bai iya ajiye mata? Kuma a addinance ban taba jin inda aka ce wai mace in ta yi aure ta je cin arziki ne ba. Kuma ina son ta sani cewa ai ita uwar tasa ba a halatta mata shi ba ta aure shi. Kuma kowace mace tana da gatanta a gidansu. In da ba don darajar aure ba da ba wata mace da za tai aure don ta je cin arziki gidan wasu. Maganar "cin arziki" ba ta taso ba!

In ma haka ne ai shi ke cin arzikinta don da ya aure ta ya samu zuri'a da ita, don kuwa ta haifa masa 'ya'ya kuma in Allah ya sa suka ba 'ya'yan tarbiyya irin ta Musulunci sai ka ga 'ya'ya sun koma suna kulawa da uwar da uban har ma da kaka (uwar miji). To ashe kenan da uwar ba ta haife ta ba, kuma ita matar ta nace da cewa sai shi za ta aura ba da ko bai samu zuri'a ba.

Bugu da kari, Balaraba ta ambaci cewa, "Arzikin tsohuwa take ci." Ina so Hajiya ta sani cewa ita ma uwar mijin ta ci arzikin surukanta ta ci da suka bar ta ta zauna ta haife shi har take tunkaho da cewa danta ne. Don haka ita ma ta bar wannan matar dan ta ta sake, ta kuma dauka cewa ita matar dan 'yar ta ce kamar yadda ta haife shi, shi zai sa zaman lafiya a tsakaninsu. Kuma babu raini bare wulakanci ko makamancinsa. Ta yi la'akari da arzikin danta, kar ta ce duk abin da ya sai wa matarsa sai ya sai mata, ko kuma a gutsuran mata. Yawan sa ido a abin da danta ke yi wa matarsa shi zai jawo wa danta wahala saboda hakkin matarsa ya rataya a wuyansa. Ba ta da wani wanda zai wadatar da ita face shi, domin a addinance ya kamata ya kula da su gabaki daya. Amma idan ya kasance ita mai 'ya'ya ce da yawa, watau kenan kowane danta za ta sa rai zai kawo mata abu ko kulawa da ita. To ita matar dan ta ba ta da wani sai shi fa? Kin ga ita uwar za ta fi ta samun kulawa da yawa, haka abubuwan da za ta samu ya fi na matar danta guda daya.

A karshe ina kira ga Ramat Yakubu da ta rika nazari sosai kafin ta yi wata fadakarwa ga jama'a, ba wai kawai dadin rubutu ya kwashe ta ta rika bata wa mata rai ba. Haza wassalam.

Ni ce taku,

Rahmatu Al-Mustapha (Gwamma) Mrs.

National Board for Community Banks, The Presidency, Minna Zonal Office, No. 13 Shiroro Hotel Road, Minna, P.M.B. 167, Minna, Jihar Neja. Tel.: Res. 066-222194; 221559; off.: 066-220931.

Rahmatu,

Ina ga kamar kin fi son kanki a nan uwata, domin duk matar da ta auri danki, Rahmatu, to tana cin albarkacinki ne. Har shi mijin da ta aura din, don shi ma albarkacin tasa uwar yake ci. Amma bari mu ji abin da jama'a za su ce. Masu karatu, gare ku.

SANARWA:

Don Allah masu rubuto wa filin "Rayuwarmu" wasiku su rika takaita bayanansu saboda sauran jama'a ma su samu filin fadin albarkacin bakinsu. Mun gode.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin