Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 39   Maris 2003
RA'YIN FIM


BABBAN SHAFI
GASKIYA DAYA CE
FADI SONKA
Wasiku
NEMAN MAFITA
DUNIYAR FINAFINAI
RAHOTO
Malam Zurke
RA'YIN FIM
Bukukuwa
Sauran Labarai
SABUWAR FUSKA
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka

Bangon Fim ta 35. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 34. Danna nan ka gani!

Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM MAI FITOWA!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
FADI SONKAr sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da tunanin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: Wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, ta da jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Mun cika shekara 4!

GODIYA ta tabbata ga Allah, Madaukakin Sarki. Allah ya yi tsira ga Manzonsa Muhammadu dan Amina (s.a.w.) da sahabbansa da alayensa.

Wannan watan da muka shigo na miladiyya, wato Maris 2003, wata ne na farin ciki a gare mu a ofishin mujallar Fim. Dalili shi ne a wannan watan ne mujallarmu mai farin jini, Fim, ta shekara hudu da kafawa. Wadanda suka san tarihinta za su tuna da cewa ta fara fitowa ne a cikin watan Maris 1999, a daidai lokacin da harkar fim ta fara bunkasa.

Abin farin ciki ne a gare mu cewa mujallar ta kawo wannan lokacin duk da dimbin kalubalen da ta fuskanta daga bangarori daban-daban. Amma maimakon mu shirya gagarumin bikin taya kanmu murna, sai muka ga ya dace mu yi addu'o'i a kebance na godiya ga Allah (s.w.t.) saboda arzikin da ya yi mana, tare da bukatarsa kan ya ci gaba da agaza mana a wannan aikin mai wahala.

Wahala! E, wannan aiki ne mai matukar wahala. A cikiin wadannan shekaru hudu na hakilon fito maku da mujalla a duk wata, mun sha tasku kwarai. Mun sha wahala wajen neman irin labaran da muke ganin sun dace masu karatunmu, wadanda babu shakka sun nuna cewa suna yarda da abin da muke rubuta masu, su karanta. Irin wadannan labaran, masu inganci ne, wadanda ake rubutawa a cikin lafazi mai dadi da hikimar harshe. Idan an same su kuma sai matsalar buga su-tace su da tsara su a komfuta da kai su madaba'a inda ake buga mujallar. Akwai kuma matsala ta rarraba mujallar a garuruwan da muke iya kai ta, sai matsalar sayar da ita, sai kuma matsalar karbo kudi. A duk lokacin da muke fafutika kan aiwatar da abu daya, muna kuma shirin fitowar mujalla ta gaba! A cikin kowane aiki da na zayyana a nan, akwai wadansu manyan matsalolin a kwance.

Duk da haka, ba matsaloli kawai ba ne muka sha; mun sha dadin aikin, musamman ma mu ga cewa mun samu wani labari da muke nema kuma mun buga shi. Idan aka tambaye ni in fadi babbar nasarar da muka samu wajen buga Fim cikin shekarun nan hudu, zan ce shi ne dorewar mujallar. Domin kuwa mun ci karo da kalubale da suka yi barazana ga dorewarta. An yi mana jan ido, an ce za a halaka mu (har ma wani furodusa ya yi kudirin kashe mu din a aikace!), an yi yekuwar a daina karanta mu ko yin hulda da mu, an ci namanmu ba bisa hakkinmu ba, an cinye mana kudi bayan an sayar da mujallar, an kai mu kara kotu (a yanzu haka muna shari'a da wani da yake son mu biya shi diyyar naira miliyan 50 don mun buga hoton matarsa da ta rasu!), an shiga an fita don a karya mu. Bugu da kari, kudin kayan aiki irin su takarda da ladar dab'i duk sun yi tashin gwauron zabo. Duk wadannan matsaloli ne, amma ba su hana mu ci gaba da aikinmu ba. Sara da sassaka ba ya hana gamji toho. Kamar yadda na taba fadi, a bisa akida muke yin wannan aikin-ba kawai don neman kudi ba; akidar nan kuma ita ce mu ga mun taimaka wa masu kokarin ganin an habaka harshen Hausa da al'adun Hausa. Shi ya sa ma muke saka mujallar a intanet don kowa ya gan ta a ko'ina yake a duniya. Shi kuwa mutum mai akida, ba ya tsoron barazana kowace iri ce.

Wani babban abin da ke faranta mana rai shi ne cikakken goyon bayan da masu karatunmu da 'yan kasuwa masu sayar da mujallar da kuma dimbin 'yan fim suke ba mu. Da yawa sun ba mu shawarwari, a rubuce ko ta-baki, kan yadda za mu gyara aikinmu; wasu sun fahimce mu kan kurakuranmu, wasu sun sa mu a hanya a inda suke ganin mun baude. Wannan ya sa a koyaushe guyawunmu suke kara karfi, aniyarmu take kara daskarewa, muke ci gaba da aiki babu kama hannun yaro. Mun gode, mun gode, mun gode! Jama'a, goyon bayanku gare mu ne fa ya sa kuke ganin Fim ba ta taba yin fashin fitowa ba komai ruwa ko zafin rana tun daga lokacin da ta koma wata-wata yau shekara uku! Kuma shi ya sa, idan kun lura, tsarinta ya kara ingantuwa, musamman fitar hotuna da kyan dab'i. A kan haka, mun kudiri aniyar ganin aikinmu ya ci gaba da gyaruwa har ya kai koluluwar inganci a fagen aikin jarida na Hausa.

Ya Allah, muna rokonka, ka ci gaba da agaza mana; ka sanya mu a kan hanya tagari; ka kautar da dukkan kuskure daga faruwa a gare mu; ka tsare mu daga sharrin masharranta daga cikin bayinka wadanda suke bidarmu da sharri; ka sa mu kasance taurari a cikin samaniyar aikinmu; ka yafe mana kurakuranmu; ka ba mu koshin lafiya da hikima da karfin imani, ka kawo ci-gaba tare da natsuwa a harkar shirin fim na Hausa ta yadda harkar za ta amfani mai yin ta da kuma wadanda ake yin ta dominsu, kuma ka sa yadda muka ga cikon shekarar nan ta hudu da fara wannan aiki, mu ga cikon shekaru hudu nan gaba a aikin. Fatiha!

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin