Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 45   Disamba 2003
RA'YIN FIM


BABBAN SHAFI
GASKIYA DAYA CE
HIRA DA DARAKTOCI
Wasiku
NEMAN MAFITA
SHARHI KAN FINAFINAI
RAHOTO
Malam Zurke
RA'YIN FIM
Bukukuwa
ADABI
SABUWAR FUSKA
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka

Bangon FIM TA 45. Danna nan ka gani!
Bangon FIM TA 44. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 43. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 42. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 41. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 40. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 39. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 35. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 34. Danna nan ka gani!

Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM YA FITO!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
Sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

KASH! Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

'Yan wasa: Farida Jalal, A.A. Shariff (Momo), Kasimu Yero, Bashir Nayaya, Abubakar Yusuf Ladan, Hajara Usman, Sani Idris Moda, Sani Garba S.K, da Rashida Bello.

Darakta: Aminu A. Shariff

BABU IRINSA!

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Haske Ya Samu A Kan Batun Auren Sani Mai Iska Da Fati Mohammed

DAGA IBRAHIM SHEME

AN dade ana baza ji-ta-ji-ta game da shahararrun 'yan fim din nan, wato Sani Musa Mai Iska da matarsa Fati Mohammed. Ba sai mun sake fadi ba, tun da aka kafa harkar fim din bidiyo na Hausa ba a taba samun 'yar wasan da ta yi farin jini, ta yi suna, kuma ta kasance ko bayan aurenta ana son jin labarinta ba, kamar Fati Mohammed. Kuma ba a taba yin ruguntsumin bikin auren wani dan fim ba irin aurenta da jarumi Sani Musa Mai Iska.

To, harkar fim aba ce da ta saba da gutsiri-tsoma. Tun kafin a yi auren nasu, an sha yada surutai a kan auren. Da aka yi biki aka gama kuma wasu surutan sun rika yaduwa a gari. Akwai ma wadanda suka ce auren ba zai yi karko ba, suka kawo dalilai barkatai. Kwatsam, sai aka samu labarin cewa Fati ta samu kwangilar yi wa wata kungiyar kare lafiyar iyali tallar fadakarwa kan cutar kanjamau (AIDS). Nan ma sai sababbin surutai suka bullo. Sani da Fati suka tafi Ingila, ta yi talla ta gama. Suka dawo. Tafiyarsu da dawowarsu suna cikin yamadidin 'yan ba-ni-na-iya, wadanda ba su ganin zarau sai sun tsinka. Aka shiga sabon fagen surutu. "Naira milyan biyu Fati ta samo, amma sun kashe kudin a Ingila da Sani," inji 'yan kwakwazo. "A'a, Sani ne ya karbe kudin, ya yi mata wayo, yanzu haka yana nan yana shirin gudu daga kasar nan." "A'a, fati ta ce tunda Allah ya sa ta samu kudi, tana son Sani ya sake ta domin ta ci gashin kanta."

Kwatsam, sai kuma sabuwar tafiya Ingila ta taso, Sani da matarsa suka tsallake ruwa. Ai fa sai 'yan surutu suka kara bude wuta. Su Sani sun gudu daga kasar. Kai, ba inda suka je, kawai suna yi wa mutane fafa ne. Ai an gan su a Nasarawa. A'a, a Legas aka gan su. An ga su a wani otal a Abuja. A'a, Sani ne shi kadai ya tafi Ingila, ya bar Fati tana boyo a gidan wata mata a Nasarawa. Ya sake ta… Wohoho!

Mujallar Fim tana sane da wadannan surutan, to amma ba kowanne ne ta ga ya dace a buga shi ba. Lokacin da ma'auratan suka tafi Ingila, mun buga wani labari inda muka nuna cewa da gaske sun tafi din, ba don komai ba sai don mu nuna wa masu cewa karya ne su Sani ba su tafi Ingila ba cewa su ne makaryatan. To, sa'ilin da aka tabbatar da cewa sun tafi din, sai muka shiga sabon shafin surutai. Aka ce sun zama 'yan gudun hijira, suna can suna kalar abinci a juji a London! (Na san London, ban taba ganin juji a can ba). Aka ce suna bin gidajen 'yan Nijeriya masu hannu da shuni suna rokon tuwo. Aka ce suna shirin barin Ingila su koma Amerika, wai Amerika ta fi sauki. Can kuma sai wata sabuwar ji-ta-ji-ta ta bullo: wai Sani ya saki Fati domin zai auri wata yarinya a Kano wadda wai ta fi fati wayewa. Kai, akwai ma wadanda suka ce da gaske har sun rabu. Can kuma sai ga wata ji-ta-ji-tar: wai Fati da kanta tana son rabuwa da Sani domin ta hadu da wani Bature da take son ta aura. (Ka ji fa, wai matar aure ta Bahaushe ce za ta rabu da mijinta ta auri wani jar fata!) Akwai ma wanda ya ce ya san Baturen.

Abin mamaki, wasu mujallu sun bubbuga wasu daga cikin wadannan surutan a matsayin dahir ne. Akwai lokuta da dama da wasu mutane suka dame mu kan mu rubuta irin wadannan labaran; babu irin shaci-fadin da ba a kawo mana ba, muka ce a'a. Ba mu yarda mu sake buga wani labari kan Sani da Fati har sai mun ga hujja muraran: ko dai su da kansu su ba mu labarin, ko kuma mu gan su da idonmu kowa ya kama gabansa ko kuma mu ga katin auren Sani da yarinyar da ake cewa zai aura ko kuma katin auren Fati da jar fata! Akwai wani furodusa da ya zo yana kumfar baki ana cewa, "Ku ba ku san aikinku ba, ga labarin mutuwar auren Sani da Fati nan kun ki bugawa! Yasin ni yayata ta ga Fati da idonta a wani gida tana kwance a falo a nan Kano."

Ni kam na yi amanna da cewa Sani da Fati ba su rabu ba. Domin kuwa a ranar 22 ga Janairu, 2003 ni da su mun yi magana a waya, inda muka fara shirya yadda za su yi hirar musamman da wannan mujallar. Mun kara tattaunawa a cikin makon. Saboda rashin daidaiton ra'ayi sai hirar ba ta yiwuwa ba, kowanenmu ya kama gabansa.

Ji-ta-ji-ta ta ci gaba da ruruwa.

Bayan watanni goma, a ranar 4 ga Nuwamba, 2003, bayan an sha ruwa, ina zaune a mota a wani kofar gida sai aka bugo min waya daga London. Sani Musa Mai Iska ne. Bayan mun gaisa, sai kuma ya gaya min yadda ji-ta-ji-tar da ake yadawa a Nijeriya game da aurensa da Fati ta dame shi, ya ce yana son ya wayar da kan mutane ta hanyar mujallar Fim. Murna ta kama ni, domin abin nema ya samu. Na ce masa ya yi kyau. Shikenan, muka aje lokaci kan cewa gobe bayan magariba za mu tattauna. Sani ya ba ni lambobin tarho guda biyu, daya ta gida, daya kuma ta tafi-da-gidanka, ya ce amma in bugo masa wayar a gida bayan an sha ruwa. Kafin mu yi sallama sai da ya ba ni Fati muka gaisa tukuna.

Washegari bayan shan ruwa sai na rubuta tambayoyin da nake ganin sun dace masu karatunmu su samu amsoshinsu daga jaruman biyu. Daga nan na tafi bakin aiki na dana rikodata a jikin tarho, sa'annan na buga wa Sani waya. Na kuwa same su suna jirana. Bayan mun gaisa, sai muka shiga tattaunawa, domin fa yin waya tsakanin Afrika da Turai abu ne mai cin kudi. Sani da Fati sun zanta da ni har tsawon minti 38 daidai a cikin farin ciki da annashuwa. A cikin tattaunawar, sun bayyana ra'ayoyinsu kan surutan da ake yi musu, da kuma kan yanayin rayuwarsu a London, sun kuma mika sako ga masoyansu. Duk da yake dai Sani ya ki amincewa ya amsa wasu tambayoyin da na shirya masa (ya ce sai ya dawo gida) kuma ya hana a yi wa Fati wasu tambayoyin da na shirya yi mata, mai karatu zai iya fahimtar abubuwa da dama game da su. Na farko, hirar ta kau da karyar da ake bazawa wai aurensu ya mutu ko kuma ya kusa mutuwa ko kuma za su auri wasu. Na biyu, ta nuna cewa da gaske suna zaune a London, cikin lumana da kwanciyar rai. Na uku, ta nuna cewa Sani da Fati suna yin makaranta ne (amma ba mu san wace iri ba ko kuma yaushe za su gama su dawo). Na hudu, suna sane da abubuwan da ke wakana a cikin da'irar shirin fim na Hausa kuma suna damuwa da wasu al'amuran, kamar su mace-mace da aka yi da kuma aure-aure-auren da aka yi a bayansu. Idan har mai karatu ya fahimci wadannan abubuwan, to burin yin hirar ta musamman ya biya, tare da fatan za a sakar wa Sani da Fati mara su sakata su wala a cikin daular aurensu.

Masu karatu, ku budo shafi na 13, ku ga yadda hirar ta kasance. A sha karatu lafiya.

Fati da Mai Iska: Karyar Makaryata Ta Kare? <

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin