AN haifi Balaraba Mohammed a Kaduna a cikin 1981 (wato shekarunta 22 a duniya). Sunan mahaifinta Malam Muhammadu Kaura, wanda dan asalin Kaura Namoda ne a Jihar Zamfara. Shi mahaifin nata, Bafillatani ne, dan Sarkin Fulani. Mahaifiyar Balaraba, wato Malama Binta, ita ma Bafillatana ce 'yar asalin kasar Chadi. Wannan hadi na kyawawan Fulani ya haifar da 'ya kyakkyawa, fara, doguwa, mai jiki, son kowa kin wanda ya rasa. Balaraba ita ce ta biyar a dakinsu; yayyenta su ne Abdullahi (wanda aka yi hadarin motar da shi amma bai mutu ba), Jummai (wadda ta rasu tare da Balaraba), da Abubakar. Tana da kanne: Isiya, Zainab, Maryam, Ibrahim da Fatima.
Balaraba ta yi karatun firamare a 'Tudun Wada Primary School' a Kaduna, kuma ta yi karatun sakandare a 'Government Day Secondary School' da ke Rigachikun, wani karamin gari a bayan garin Kaduna kan hanyar zuwa Zariya. Daga nan gidansu da ke Unguwar Kaji, Kaduna, takan tafi makarantar, wacce ba ta da nisa daga gidan. A cikin shekarar 2000 ta kammala karatun sakandare. Karatunta na karshe kenan, koda yake kamar yadda ta gaya wa mujallar Fim (Mayu 2001, shafi na 56) "in Allah ya yarda zan ci gaba."
Marigayiyar dai ba ta ci gaba da karatun ba. Tana daga cikin irin ''yan matan nan na Arewa da suke tsananin son ''yan wasan fim da ake yayi. Hankalinsu na can gun jarumai kamar su Fati Mohammed, Hauwa Ali Dodo, Hindatu Bashir, Ali Nuhu, Ishaq Sidi Ishaq, Wasila Isma'il, da sauransu. Saboda haka da ta samu fili sai kawai ta fada cikin kogin shirin fim.
Su kansu ''yan fim sukan yi farautar ''yan wasa mata, su jawo su cikin kogin shirin fim din. Dan wasan nan da ake kira Dan Yarabawa ne ya lasa wa Balaraba mai a baki game da shirin fim. Ya je gidansu ya bukace ta ta shigo harkar, ya ce akwai wani fim da yake son ta bi shi zuwa Kano su yi. Ya yi magana da iyayenta a kan zancen. Ita Balaraba tana so ta je, to amma sai mahaifiyarta ta ce sam, Balaraba ba za ta iya yin wasan fim ba. A ganinta, da ma a ce kanwar Balaraba din ce Zainab, to ita da ta iya. Watakila ita Malama Binta, uwarsu, tana ganin Zainab ta fi Balaraba fasaha ne.
Jin haka sai Dan Yarabawa ya janye jiki daga gidan. Rannan sai suka hadu a Tudun Wada, Kaduna, ta je wani biki. Abin da Dan Yarabawa bai sani ba shi ne har Balaraba ta hadu da wasu mazauna Kano, Bala Makosa, editan mujallar Nishadi, da Idris Danzariya, furodusa kuma dillalin kaset da ke Kano, su har sun yi nasarar samun amincewar Balaraba da iyayenta kan ta je Kano ta yi masu fim. Da Dan Yarabawa ya ji haka sai ya ce to ba za ta bar shi a baya ba. Daga bisani tare suka rankaya birnin na Dabo. A nan su Danzariya suka sa ta ta yi wasanta na farko a fim din nan mai suna Maryam a matsayin jarumar shirin; daga nan kuma suka yi Matar Uba..
A Kano, Balaraba ta zauna a gidan Bala Makosa, a Goron Dutse, ya rike ta kamar kanwarsa. Adireshinta ya kasance shagon 'El-Duniya,' inda Danzariya yake. Daga bisani, da idonta ya bude a garin, sun rabu da su, ta zauna a wasu gidajen.
Zuwan Balaraba Kano ya kasance budi a gare ta a kokarinta na zama tauraruwar finafinai (superstar). Labarinta ya bazu kamar wutar bazara saboda kyawunta; da daurin gindin Bala Makosa da furodusoshi kamar su Rabi'u Harabs mai 'HRB Production' da daraktoci kamar Ishaq Sidi Ishaq da 'yan wasa kamar su Ali Nuhu, ta dinga samun kwangilar finafinai. A cikin lokaci kadan ta fito fili, kowa ya san ta. Rawarta a finafinan Kano musamman kamar su Maryam, Furuci 1 & 2, da Tawakkali 2, da wani fim da suka yi a Sokoto mai suna Zainab (inda ta fito a budurwar Auwalu Dangata) da wani fim da suka yi a Kaduna mai suna Tasiri (a matsayin budurwar Ali Nuhu) ita ta fito da ita.
Zaman da ta yi a 'HRB Production' bai hana ta yin wasu fitattun finafinai ba a wasu wurare ba, musamman Jaheed da ta yi a kamfanin 'Two Effects Empire', da kuma Rigar 'Yanci na 'Fhauzy Communication' da ke Gombe.
Kamfanin 'Mandawari Enterprises' ya matso da Balaraba kusa da shi tun daga sa'adda mai kamfanin ya yanke shawarar yin amfani da ita wurin yin fim din da shi Mandawari ya ci kuma ya sha wa alwashi,wato Burin Zuciya. Mandawari ya taba cewa a iya tunaninsa, babu yarinyar da ta kai Balaraba kyau a fagen fim din Hausa, don haka ne ma ya sa ta a matsayin gimbiya a cikin Burin Zuciya. Kafin shi, sai da ya gwada basirarta a cikin wani fim da kamfaninsa ya shirya mai suna Biyayya. Ban da su, Balaraba tana cikin Mu Shakata na 4 da Mandawari ya shirya kwanan baya wanda shi ma bai kai ga fitowa ba.
Balaraba ta dan yi zama gajere tare da Musbahu M. Ahmad a ofishinsa 'Usmaniyya Production.' A can ne Musbahu ya sanya ta a cikin wani fim mai suna Amalala. A kamfanin 'Iyan-Tama Multimedia' kuma, Balaraba ta fito a cikin fim din su mai suna Dawayya. Ganin yadda taurorinta ke haskawa sai matasan furodusoshi irin Husaini Hajin Fafa suka rika tuntubarta yin fim. Ta yi wa Hajin Fafa fim mai suna Nabila. Hakanan ta yi wani mai suna Kacibus wanda yanzu haka yana daya daga cikin finafinan da take ji da su kuma akwai na biyunsa a a kan hanyar fitowa.
A cikin mata furodusoshi, an samu wadda tasa hannu aka yi rububin Balaraba da ita. 'Yar'uwa, zabiya kuma furodusa Maryam Mohammed Danfulani (Mashahama), ta dauki Balaraba ta yi mata wani sabon fim mai suna Yayyafi.
Tun farkon shigowarta harkar fim, Balaraba tana hangen ba za ta dade a ciki ba. Da farko dai tana son ta kara karatu, na biyu kuma tana son ta yi aure idan ya samu. A wata hirarta da aka buga cikin mujallar Nishadi, ta ce ita ba ta zo ta "kori" wata ba ne. "Shekara nawa za ka yi a daina son ka a koma son wani?" inji ta.
Mujallar Fim ta taba tambayarta dalilin shigowarta kogin shirin fim, ga ta karamar yarinya. Sai Balaraba ta amsa: "Ba wani abu ba ne ya sa na shiga harkar fim ba, kuma ba wani abu ba ne na rasa har na taso daga Kaduna na zo nan Kano ba, ka gane ko? Ina jin dadi bakin gwargwado a hannun iyayena. Kuma ina da gatana fiye da yadda kowa ke zato. Ni dai tun daga kan Wasila da Al'ajabi da dai sauran makamantan finafinan nan da na fara gani sai na ji hankalina ya kwanta ina so, don na ga yadda suke fahimtar da jama'a; ni ma shi ne na ga ina da sha'awar in yi wasan Hausa."
Harkar fim na Hausa tana cike da surutai da gulmace-gulmace. Ita ma Balaraba, an yi mata irin wadannan gulmace-gulmacen, a ce wane da wane suna nemanta. Allahu a'alamu, amma kowa ya amince da cewa Balaraba yarinya ce mai kamun kai. Ita kanta ta taba gaya wa Fim cewa tun da shigo harkar fim akwai mazaje da suka yi mata caa wai suna son ta; wasu ba son Allah da Annabi suke furtawa ba, kuma ta yi kokri wajen share su. Tun lokacin da za ta bar gida ta shiga fim, sai da babanta ya ja mata kunne, ya ce, "Tunda kina so shikenan; abin da kike so shi nake so. Kuma a kama kai!"
A cewar Balaraba, "Kame kai shi ne (alheri) wurin 'ya mace. Idan ta wulakanta kanta a karshe ba za ta ga da kyau ba. Shi ya sanya ni nake bin maganar iyayena, kuma insha Allahu ba zan yi kuskure ba."
Daya daga cikin abubuwan da ta yi kaffa-kaffa da su a fagen fim shi ne irin wasan da za ta yi. Da Fim ta tambaye ta ko za ta iya yin duk wani fim da aka ba ta, sai ta kada baki ta ce, "In Allah ya yarda zan iya, in dai ba mugun acting ba ne wanda zai sa a zage ni cikin jama'a." Da aka ce za ta iya fitowa a matsayin kwartuwa, sai ta girgiza kai ta amsa, "Ba zan iya ba."
Ta yi maneman gaske tun kafin Shu'aibu Kumurci ya bullo. Daga cikinsu akwai wani Mohammed, wanda ba dan fim ba ne. Amma Allah bai sa su ne mazajen aurenta ba. Akwai ma wadanda saboda fushin an hana su aurenta har gida suke zuwa su sami babanta, su sa a kira shi, idan ya zo su zazzage shi su tafi. Shi kuwa ba ruwansa, wanda 'ya take so shi yake so. Babanta ba irin mazajen nan ba ne masu cewa dole ga wanda 'yar su za ta aura. Balaraba ce 'yar da ya fi so a cikin 'ya'yansa, saboda haka kuwa abin da take so shi yake so.
Duk da yake Balaraba ba ta son mugun matsayi a wasa, ta auri mutumin da ya yi kaurin suna a matsayin mugu, wato Shu'aibu. Kumurci suna ne da ya samu saboda iya muguntarsa a cikin shirin Ukuba. Daga bisani, da ta kara wayo a Industry, marigayiyar ta fahimci cewa wasa dai wasa ne. Shi ya sa ta gane cewa shi Shu'aibu, yadda mutane suka dauke shi, ba haka yake a fili ba.
Su mutane da ke nesa da su, cewa suka rika yi sam, Balaraba ba ta dace ta auri Kumurci ba. Dalili shi ne wai shi mugu ne a fim. Suna ganin ya za a ce wannan yarinya son kowa kin wanda ya rasa ta auri dan wasan da aka sani da riga daya da wando daya da hula daya kullum a fim? Beauty and the Beast kenan? Ita ko da ta san gaskiyar yadda masoyinta yake, cewa ta yi, "Ko a rami Shu'aibu zai saka ni na amince don ina sonsa."
Yanzu dai Balaraba tana cikin rami, bayan Allah ya yi mata cikawa kwana daya kacal da daura mata aure da Shu'aibu. Ta je Kano ta yiwo wasan Hausa kamar yadda take so, to amma da ta dawo Kaduna da niyyar komawa Kano a matsayin matar wanda take so, Allah bai yi mata izini ba, domin akwai inda yake so ta tafi a lokacin. Kuma ta tafi can din.
'Ya'yan Binta da Malam Muhammadu Kaura
1. Abdullahi (Riskuwa) Shekararsa 28
2. Jummai (A'isha) Shekararta 25
3. Abubakar (Bunari) Shekararsa 22
4. Balaraba (Amina) Shekararta 19
5. Isiya Shekararsa 16
6. Zainab Shekararta 13
7. Maryam Shekararta 10
8. Ibrahim Shekararsa 7
9. Nana Fatima Shekararta 2 da rabi
Abdullahi, da Jummai da kuma Abubakar, duk an haife su ne a barikin sojoji mai suna 'Ekwenwa Barracks' da ke garin Benin, hedikwatar Jihar Edo a yanzu. Ita Balaraba ita ce ta farko da iyayensu suka fara haifa a Kaduna.
JUMMAI MOHAMMED (1977 - 2002)
YAYAR Balaraba, marigayiya Jummai, shekarunta 25. An haife ta a birnin Benin da ke Jihar Edo, a cikin 1977. Ta yi karatunta na firamare a 'L.E.A. Primary School,' Kawo, Kaduna, kuma ta yi na sakandare a 'GDSS' Rigachikun, Kaduna, wato makarantar da Balaraba ta yi, daga 1992 zuwa 1998.
Jummai ta yi aure a cikin 1988, wato shekarar da ta kare makaranta. Tana da kishiya, ita ce amarya wurin mijinsu da ke zaune a Abuja. Ta rasu ta bar 'ya'ya biyu, Aliyu da Khadija. Ita Khadija, 'yar wata uku ce, kuma a yanzu tana kwance a asibiti sakamakon raunukan da ta yi a hadarin motar da ya dauki ran mahaifiyarta. Allah ya jikan Jummai, kuma Allah ya raya Khadija cikin koshin lafiya, amin.
MUHAMMADU SANI (1977 - 2002)
MUHAMMADU Sani shi ne direban motar da ta yi hadari, kuma ya rasu tare da su Balaraba. Shi kane ne ga mijin marigayiya Jummai. Wansa ya ba da motarsa ta shiga (Nissan Primera) a kai su Balaraba Kano. Dan shekara 25 da haihuwa, an haifi Muhammadu Sani a garin Barikin Ladi a Jihar Filato. Shi ne dan fari ga mahaifiyarsa, wadda ita ma ta rasu tun yana karami.
Kafin rasuwarsa, Muhammadu Sani dalibi ne a Jami'ar Abuja, inda yake karanta ilimin Sha'anin Mulki (Public Administration), yana kuma zaune ne a gidan babban wansu Alhaji Adamu. Allah ya jikansa.
ISIYA DATTI (1998 - 2002)
ISIYA (wato Datti) shi ne na takwas a wajen mahaifiyarsa, sannan a wajen babansa shi ne na biyar. Sunan mahaifinsa Alh. Bara'u Abdullahi. Datti ya rasu yana da shekara uku da rabi. Mahaifiyarsa Hafsat kanwa ce ga uwar Balaraba, kuma ta karye a cinya lokacin da hadarin ya ritsa da ita. A yanzu tana kwance a asibitin 'Jinya Hospital' a Kaduna. Allah ya jikan Datti, kuma ya ba mahaifiyarsa lafiya da jimirin jure wannan babban rashi, amin.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin