|
Mu mara wa mujallunmu baya
-Dr. Rasheed a bikin cikar Garkuwa shekara 2
Jagororin GARKUWA: Malam Kabir Assada da Dr. Malumfashi
|
Daga A ALIYU A. GORA II a Kaduna
AN yi kira ga daukacin al'ummar Arewa su ba da cikakken hadin kai da goyon baya ga ci-gaban kafafen yada labarai masu zaman kansu na yankin. Shugaban Tsangayar Fasaha da Addinin Musulunci ta Jami'ar Bayero, Kano, Dr. Abubakar A. Rasheed, shi ne ya yi wannan kiran a wurin taron bikin cika shekara biyu da kafuwar mujallar Garkuwa kwanan nan.
A bikin, wanda aka yi a dakin taro na Gidan Arewa da ke Kaduna a ranar Asabar, 8 ga Yuni, 2002, an kuma karrama wadansu muhimman mutane na arewacin kasar nan, ciki har da wasu fitattun 'yan wasan fim.
Dr. Rasheed, wanda ke magana a matsayinsa na babban bako mai jawabi a taron, ya ce, "Ya wajaba a gare mu mu sake tunani idan dai har muna so Arewa ta bunkasa ta kuma ci gaba. Jaridu da mujallu na daga cikin hanyoyin bunkasa al'umma, don haka ya zama wajibi ga 'yan bokon Arewa da masu kudin Arewa su agaza wa jaridun Arewa ta hanyar ba su tallace-tallace da kuma bude gidajen jaridu da mujallu da niyyar kare kai, ba da niyyar cin riba ta nan kurkusa ba."
Dr. Rasheed, wanda shi ne tsohon manajan-darakta na kamfanin buga jaridun New Nigerian da Gaskiya Ta Fi Kwabo, ya kuma yi kira ga marubuta da su dage wajen taimakon jaridu da mujallun Arewa da rubuce-rubuce masu ma'ana da wayar da kai. Ya ce su kuma masu karatu su jure wajen saye da karanta mujallu da jaridun da ake yi a Arewa a matsayin gudunmuwarsu don dorewar jaridu da mujallun.
Tun da farko sai da mawallafin Garkuwa, Dr. Ibrahim Malumfashi, ya karanto jawabin maraba inda ya yi amfani da wannan damar ya jawo hankalin 'yan Arewa a kan sanin muhimmancin karanta jaridu da mujallun Arewa. Ya ce ginshikin ginuwar kowace jarida ko mujalla yana samuwa ne kawai ta hanyar tallace-tallace. Ya kuma nuna takaici a kan yadda masu kudinmu suka fi son ba da talla ga jaridun Kudu, maimakon su ba na Arewa. Hakan, inji shi, yana ba da gagarumar gudunmuwa wajen rugujewar jaridu da mujallun Arewa.
A nasa jawabin, Alhaji Mustapha Idris, wanda ya wakilci shugaban taron, Manjo-Janar Muhammadu Buhari, ya amince da jawabin Dr. Malumfashi, inda ya yi kira ga 'yan jarida da cewa kamata ya yi su kira wani taro inda za a tattauna kan yadda za a shawo kan matsalolin da ke addabar jaridu da mujallun Arewa. A karshe kuma ya jawo hankalin 'yan Arewa a kan bai wa karanta mujallu da jaridun Arewa muhimmanci, ya ce kin yin hakan yana daya daga cikin abubuwan da suka sa 'yan Kudu suka tsere mana.
Da yake jawabi a taron, Shugaban Kungiyar Furodusoshi ta Jihar Kano, Alh. Ibrahim Mandawari, ya yi kira ga masu mujallun Hausa, musamman Ibrahim Malumfashi da Ibrahim Sheme, da su yi wa Allah su rika sa kishin addini a aikinsu na jarida. Ya ce sahabban Manzon Allah (s.a.w.) su ne farkon wadanda suka fara aikin jarida ta haryar ruwaito hadisai kuma ba su taba kauce wa gaskiyar abin da ya faru a zamanin Manzo ba. Mandawari ya yi roko ga hukumomin mujallun da su rika rubuta labaran ci-gaba a kan dan wasa maimakon buga mugun labari.
Taron ya samu halartar manyan baki daga sassa daban-daban na arewacin kasar nan, ciki har da Alhaji Abdullahi Gambo, wanda ya wakilci Gwamnan Jihar Kaduna. Daga cikin 'yan wasan da suka samu halarta akwai Ibrahim Mandawari, Aminu A. Shariff (Momo) da kuma wakilin Abida Mohammed, Adamu Sani. A karshen bikin an karrama wadansu mutane da suka hada da Shugaban Majalisar Dokoki ta Tarayya, Alhaji Gali Umar Na'abba, da gwamnonin jihohin Kaduna, Gombe, Neja, Zamfara, da Sokoto, sa'annan da 'yan wasa uku: Mandawari, Abida da kuma Momo. Haka kuma mujallar ta karrama wasu wakilanta: Zainab Muhammad Siddam, Kallamu Rugar Waje, da Umar Bandi Kofar Kware.
An tashi lafiya daga taron da misalin karfe 2:27 na rana.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin
|
|