Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 32   Agusta 2002
RAHOTO


BABBAN SHAFI
MU LEKA MU GANI
HIRAR MUSAMMAN
Wasiku
MU LEKA HOLLYWOOD
Rahoton Musamman
Rahoto
Malam Zurke
RA'AYIN MUJALLAR FIM
Bukukuwa
Sauran Labarai
Fitattun Taurari
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka Bangon Fim ta 31
Bangon Fim ta 30
Bangon FIM ta 29
Bangon FIM ta 28
Bangon FIM ta 27
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da MU LEKA MU GANIn yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Masu shirya fim su rika kusantar Malamai

-Sakataren Izala

Daga SHAFI'U MAGAJI USMAN a Kaduna

MANAZARTA da masu kallon abubuwan da suke faruwa a fagen shirya finafinan Hausa, musamman masu kallon harkar a addinance, sun sha yin suka kan yadda ake shirya finafinan da kuma su kansu 'yan wasan. Kan haka ne muke ta yin hira da malamai domin samun gudunmawarsu ga harkar. Idan kun tuna, malaman da muka zanta da su ya zuwa yanzu sun yi ta cewa Musulunci dai bai haramta fim ba illa wasu gyare-gyare da harkar take bukata. A wannan karon mun sake zakulo wani mashahurin malami mazaunin Kaduna kuma sakatare na Majalisar Malami ta Kasa (karkashin kungiyar Izalatul Bidi'a wa Ikamatus Sunnah), Sheikh Umar Hassan, wanda shi ne limamin masallacin 'Rimi College' da ke Kaduna. Bismilla:

FIM: Allah ya gafarta malam, ganin cewa harkar fim tana yawan samun soke-soke musamman daga malaman addinin Musulunci, shin fim yana da wani matsayi ko asali a Musulunci ko kuwa bai da shi?

SHEIKH UMAR HASSAN (ya fara da bismilla da addu'a): Duk abin da Musulmi zai yi, daga wasa da doki zuwa wasan gudu, zuwa wasan tsalle ko ketare wasu abubuwa da sojoji kan yi, domin shirin ko-ta-kwana akwai shi a Musulunci, amma shi tamsiliya kuwa wani abu ne wanda a cikin Alkur'ani an ambaci "watilkal amsalu-watilkal amsalu ko masalullazina kaza - Masalullazina kaza, har Kausawa sun mai da shi ya zama hausarsu, sai ka ji an ce misalin kaza ko misalin wane. Wato dai kamar hannunka-mai-sanda, ko irin tsarin tatsunniyar da da ake yi. In ka ji a hira kafirai suna cewa Annabi (SAW) abin da yake fada talsuniya ce ko abubuwan da yake yi sihiri ne ko bokanci. Nan ba suka ba ce, don shi Annabi ya zo ya tarar da wadannan mutane ne kan irin wadannan dabi'u kuma Alkur'ani yana bayanin abubuwan da suke boye ko tsinkayar abubuwan da za su faru a gaba, kawai sai su ce ai wanan bokanci ne, duba ne, don duban kawai suka sani a wancan lokacin.

In muka koma kan batun tamsiliya da ka yi mani tambaya a kai kuwa, duk abin da mutum zai yi in ba zai fid da shi cikin Musulunci ba tamsiliya ne. misali, kamar 'ya'yan Annabi Yakub, wato Annabi Yusuf da 'yan'uwansa, duk abin da suka yi din nan kamar siga ce ta tamsiliya. Domin in ka lura a karshe Allah ya gafarta masu gaba daya. Ka ga kenan wannan an yi ne domin a nuna wa mutane yadda sharrin 'yan'uwa yake musamman idan ka nuna masu yadda wani alheri ya same ka ko zai same ka. A takaice dai tamsiliya shi ne a yi abu mummuna, da nufin nuna wa wani sakamakon wanan abu a karshe don za yi koyi.

FIM: A takaice dai fim yana da asali a Musulunci kenan.

SHEIKH UMAR: Kwarai da gaske kuwa, asaloli kuwa masu yawa! Amma abubuwan da suke dai bata al'amarin har a kasa gane asalin nasa shi ne, rashin yinsa da sigar Islama. Ko zamanin Annabi (SAW) akwai munafukai da za su zo gare shi a matsayin mutanen kirki alhali ba haka ba ne. To ka ga a nan masu boye barna su bayyana abin arziki, wanda ko mutum bai karanci Suratul Munafikuna ba tamsiliya zai fayyace masa sakamakon munafiki.

FIM: To ga irin finafinan da ake shiryawa na Hausa a yanzu wadanda muna tsammanin ka kalli wasu. Malam, mecece fahimtarka kan tasiri ko illarsu ga al'umama a Musulunce?

SHEIKH UMAR: Ni a gaskiyar magana Allah bai sa na yi karo da wanda zan yi suka hakikatu ba, amma yawancin wadanda na gani sun dace da addini da kuma al'adar Hausawa.

FIM: Amma kuma yawancin malamai suna sukar al'amarin nan har wasu suna fassara shi da cewa laifi ne. In kuwa ba laifin ba ne menene ra'ayin Malam kan masu ra'ayin cewa ya dace malamai su shigo cikin harkar tsindum domin yin gyara?

SHEIKH UMAR: A karantar da mutum ai shi ne malanta, ba wai sai ya rike littafi ba. Ka ga kamar kai da muke magana da kai yanzu, dan abin da na sani na dada maka ka dauka, ai ka malantu da abin kenan. Haka kai ma in ka sanar da wani. Abin da ban ambata ba a baya shi ne labarin hankakin da Allah ya turo daya ya kashe daya ya kwakule kasa ya rufe shi saboda a ilimantar da Kabila yadda zai yi da gawar Habila. Ka ga wannan ma tamkar tamsiliya ne, don hankakin nan mala'ika ne amma inda mutane suke sukar cewa malamai ba su shigo ba, ba nan ne abin suka ba, su masu yin ne ya kamata a kowane lokaci su rika kusantar malamai kan ayyukan nasu. Sai a nuna masu yadda abin yake.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin