SIYASA
Mu shiga a dama da mu
-'Sawun keke'
WASU masoyan 'yan fim da sun dade suna korafi tare da nuna damuwa a kan rashin shiga harkokin siyasa da gwanayensu ke yi. A ganinsu, akwai alamun 'yan fim dai ba su kwadayin shiga a dama da su a siyasa, musamman ma dai idan aka yi la'akari da cewa 'yan fim suna da matukar yawa, amma kadan ne suke tsundun cikin siyasa, ga shi kuwa suna da milyoyin masoya a tsakanin masu kallo. Bugu da kari, watakila ganin yadda 'yan fim ba su shiga siyasa, ko kamun kafa 'yan siyasar ba su zuwa su yi a wajensu. Ba mamaki, kin shiga siyasa ga 'yan fim yana da nasaba da ko dai rashin kudi ko kuma tsoron kada mutum ya sha kasa, tashi ma ya gagare shi.
Yanzu a majalisar tarayya, 'yan fim na Hausa ba su fi a kirga su da tafin hannu ba. A jihohi da kananan hukumomi kuma, yawanci daga bakin matsayin kansila suke tsayawa; kalilan ne suka kai matsayin dan Majalisar Dokoki ta jiha. Shin kwamishinoni nawa ne 'yan fim a jiha kamar Kano? Kila ko daya! A Kaduna ne ma za a iya ambatar Kwamishinan Yada Labarai, wato Alhaji Muhammadu Rabi'u Bako (wanda ya yi shirin Gundumi Fasa Kwanya).
ALHAJI ASHIRU SANI BAZANGA (Sawun Keke), shugaban kamfanin 'Bazanga Communicatons,' Kaduna, kuma furodusan fim din Aminan Zamani, tsohon dan wasan kwaikwayo ne a talbijin, inda ya yi suna da shirin Sawun Keke. A shirin Aminan Zamani, shi ne jarumin shirin inda ya fito a matsayin abokin Yusuf Barau, wanda ke taima ka abokin nasa ama bai sani ba uwar abokin tana zuga shi kan cewa ya bijire masa. A shirin Gagarabadau kuma wanda mujallar Fim ta shirya, shi ne jagoran ''yan sanda da ke neman rikakken dan fashin, kuma shi ne ya kama Gagarabadau lokacin da zai gudu. Kuma a shirin Daren Farko, wanda bai fito ba tukuna, shi ne abokin Hamisu Iyan-Tama wanda ke ba shi shawara kan matsalarsa da iyalinsa.
To, Ashiru dai yana daga cikin 'yan fim kalilan da suka shiga siyasa har suka ci zabe. Ya yi kansila a Karamar Hukumar Danja ta Jihar Katsina kafin a sauke su kwanan baya. Yanzu kuma yana takarar 'ta-zarce'.
Ashiru dai ya san dadi da zafin siyasa, musamman ga dan fim. Kwanan baya kafin ya sauka daga mukamin kansila, fitaccen dan wasan ya zanta da wakilinmu ALIYU ABDULLAHI GORA II a ofishinsa da ke kan titin Dutsinma a Tudun Wada, Kaduna, inda ya ari bakin 'yan fim ya ci masu albasa dangane da ra'ayinsu na shiga a dama da su a harkar siyasa. Ga yadda hirar ta kasance.
Alh. Ashiru Sani Bazanga (Sawun Keke)
|
FIM: Ashiru Sani Bazanga me za ka ce dangane da korafin da mutane ke yi cewa ku 'yan fim kuna tsoron shiga a dama da ku a harkokin siyasa?
BAZANGA: E, to, a nan ai ni sai in ga kamar cewar su dai sun matsu ne ko kuma kaunar da suke mana ce ta yi yawa a zuciyarsu. Amma ai sun san muna cikin harkar siyasa. Domin ai ita rayuwar ma gaba daya siyasa ce. Akasari yanzu kamar misali in ka dubi shugabanninmu kamar Alhaji Abdu Haro Mashi, wanda yake dan majalisa ne na tarayya, ka ko ga daya daga cikin jagororinmu ne, don shi ne Sardaunanmu na masu shirya finafinan Hausa. In ka kalli kamar irin su Bashir, wanda yana Majalisar Dattawa, ko ko majalisar wakilai, wanda yake shi ma shugaba ne a harkar fim. Akwai kuma daga shuwagabannin kananan hukumomi, misali kamar shugaban Karamar Hukumar Bakori (a Jihar Katsina), Alhaji Mansir Aminu, da ni kaina da nake maganar wanda yake kowa ya sani ni zababben kansila ne a Danja, to, da irinmu da dama, wanda yake duk muna ciki kuma a halin yanzu ma muna cikin gwamnatin kuma sannan akwai wasunmu da yawa wadanda yake suna harkar siyasa.
Wato ita siyasa bambancinta wanda mutane ba su lura da shi shi ne, mai zuwa taro da kuma mai ra'ayin yadda za a gudanar da mulkin dimokuradiyya, akwai bambanci a nan. Akasarin mu baki daya kusan dukkanmu 'yan siyasa ne, domin babu wanda bai jefa kuri'a ba, kuma babu wanda bai goyon bayan dimokuradiyya kamar yadda muke a ciki yau. Ka ko ga ashe mu duk 'yan siyasa ne.
Kana ganin halin ko-in-kula da shugabanni suke yi wa harkar fim bai ba da gudunmuwa wajen karya wa 'yan fim kwarin gwiwa ba a kan shiga harkar siyasa?
BAZANGA: E, to, ka yi magana. Kuma mu kanmu cikin wannan magana muke. Domin bakin cikin inda ya fara taso mana shi ne dai ai daga Kano inda man ne tushenmu, uwarmu da uban kai kakanninmu ma suke a game da wannan sana'a da kuma ci-gabanta. To babban abin bakin cikinmu shi ne a nan Kanon kuma shuwagabanni wadanda Allah ya dora wa jagorancinmu, mu ne muka yi masu kamfen din da suka zama abin da suka zama. To amma kuma su ne suka koma suna ci mana dudduge, ko ko su ne suka koma suna kin mu, suna kyamarmu. Domin kamar yadda a Kano ne na san cewar muka fara samun inda aka nuna cewar ma an dakatar da sana'armu, a inda daga bisani aka dawo aka ce a dawo mana da sana'armu, bisa kan su da kansu akwai kuskuren da suka yi na su ce sun hana bawan Allah neman abincinshi. Bayan kuma wadannan mutane da suka hana, su kuma ne suke ikirarin cewar suna neman kowa ya nemi madafa. To mu kuma mu ne ma muka ba wasu wuraren dafawar, fiye da su gwamnatin.
Yanzu in ka duba a Jihar Kano, ina tabbatar maka wadanda furodusoshi ke ciyarwa, suke taimaka mawa, suke sa karuwa, sun fi wadanda Gwamnatin Jihar Kano take taimaka mawa, kuma suke biyan su albashi. To, shi ya sa yanzu, mu kanmu da muke nesa, da kuma na kusan, kai har da na Kanon, mu ma mun fa canza zane. Akwai wata magana da aka yi a mujallar Bidiyo, wadda ta dan sosa mani zuciya, na so da a ce an ma bincike ni da an samu cikakken bayani. An yi bayani a kan cewa ko mu 'yan fim ba mu son shiga siyasa, har ana kawo misali da Mandawari, cewar ma yana tsoro ne. To Mandawari ya wuce ya ji tsoron wani abu wanda dan'adam zai yi a Nijeriya, don ina mai tabbatar maka a yanzu idan za a dauko bindiga a ce a fito filin yaki, Mandawari na daga cikin wadanda suke cikin sahun farko, bare kuma a harkar siyasa wanda yake da kuri'a ake aiki; kuma Mandawarin nan yana da magoya baya masoya masu kaunarsa. Kai bari in gaya maka ma, a halin gaskiya, a game da siyasar nan, kun ji Ibro ya yi ikirari, har ana dauka cewa wai saboda barkwancin shi da wasannin shi da waye, waye wannan sanar'ar shi ce, kamar Golobo ne a Jihar Sakkwato. Da yanzu Golobo na nan a matsayin nan nashi na da, ina jin shi ma duk abin da ya fada sai a ce ai barkwanci ne.
Amma Ibron nan ko da ya ce zai yi takarar gwamna a Kano, ai ba wai karya yake ba. Na san zai iya, saboda ai magana ce ta mai ilimin boko, kuma yana da shi.
Yanzu a Kungiyar Furodusoshi ta Arewa, akwai matakin da kuka dauka don ganin cewa 'yan fim sun shiga harkokin siyasa?
BAZANGA: Ai wannan ba magana ce wadda sai an zauna an tattauna ta a kungiyance ba. Domin na gaya maka duk 'yan kungiyar gaba daya 'yan biyasa ne.
A naka bangaren, me ya sa kake ganin ya dace 'yan fim su shiga siyasa?
BAZANGA: Saboda kamar maganarmu ce ta farko, wato neman maida mu saniyar ware da ake so a yi, wanda mu ne muke taimakawa, da bazarmu... ko kuma in ce da garinmu ake tuwo a ce za a lika mana a hannu. Saboda haka dole 'yan fim mu shiga a dama da mu a harkokin siyasa, kuma sai mun kama kananan hukumomi da kuma manyan mukamai a kasar nan.
To, Allah ya bada sa'a.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin
|
|