Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 34   Oktoba 2002
RAHOTO


BABBAN SHAFI
MU LEKA MU GANI
HIRAR MUSAMMAN
Wasiku
KU TAMBAYE SU
Rahoton Musamman
Rahoto
Malam Zurke
RA'AYIN MUJALLAR FIM
Bukukuwa
Sauran Labarai
Fitattun Taurari
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka
Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM MAI FITOWA!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da MU LEKA MU GANIn yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection


Tilas fim ya tafi tare da Shari'a

Inji Sani Fodio

Daga ABUBAKAR MAIHOTO a Gusau

MALAM Sani Muhammadu Fodio yana daga cikin 'yan wasan fim fitattu da ke garin Gusau ciukin Jihar Zamfara. Asalinsa mutumin Maradun ne inda aka haife shi. Yana da shekara tara da haihuwa aka dauko shi a lokacin mahaifansa suna nan garin Gusau a 1968. Suna nan a 1968 zuwa 1973 sun samu shekara biyar suka tashi suka koma Talatar Mafara a 1973. Da zuwa sai aka maida shi makarantar Arabiyya a Zariya. Bayan ya samu shekara biyu a Zariya sai ya dawo. Yana dawowa sai aka sa shi a makarantar firamare ta J.N.I. a garin Talatar Mafara 1975. A lokacin sai aka sa shi a aji 3 daga aji 3 zuwa 4 sai ya je G.T.C. Gusau a 1978 sai ya bar G.T.C. Gusau saboda ba shi da sha'awar karatun 'Art.' A 1979 sai ya koma Sokoto, a lokacin an bude 'Special Science Secondary School'; su ne dalibanta na farko har zuwa 1984. Daga gamawarsa sai ya kama kasuwancin fata tare da wadansu Kwara a Kano.

Yna kasuwancin fata har zuwa 1986. Ya shiga siyasa a 1990, yana kasuwancin fata yana siyasa. Lokacin N.R.C. an zabe shi a matsayin Ma'aji a mukami na mazaba. Daga nan bayan lokaci ya yi ya sake tsayawa a takarar Sakatare na Unguwa (Ward) ya ci; a lokacin ana "'yar tinke," watau 'kai-da-halinka." Nan ma ya ci, domin lokacin ake siyasar gane mai jama'a.

Da muka ce Sani Fodio ya ci gaba da ba mu labarin, sai ya ce, "Daga 1990 zuwa 1992, lokacin da aka rushe siyasa, da man ina kasuwancina, sai na ci gaba da shi a takaice. Na bar kasuwancin fata a 1996 na zo na shiga cikin siyasa gaba daya. Siyasar da muka faro daukowa ita ce P.D.P. wanda yake nine sakataren P.D.P. na Karamar Hukumar Gusau, Aca yana ciyaman na Gusau. A lokacin P.D.P. tana gaba tana baya, sai muka canza sheka muka dawo A.P.P. saboda darajar mai girma Gwamna da albarkar Shari'ar nan da ya jaddada. Sai muka yi tunani a matsayinmu na Musulmi babu yadda za a yi mu ba da goyon baya sai mun dawo don ba zai yiwu ba mu ba da namu goyon baya muna wata siyasa shi ya sa muka dawo A.P.P."

To shin yaya aka yi wannan babban dan siyasar ya watsar ya koma shirin fim? Tambayar da wakilinmu ya yi masa a Gusau kwanan nan kenan. Bismilla:

Koda yake na je wajen da kuke rihasal na fim din ku na ga irin yadda abubuwa suke tafiya zan so in san matsayinka a wannan wurin?

FODIO: A takaice dai kamfani ne muka kafa; mun fara da mutum shidda mun fito daga wurare daban-daban. Daga cikinmu akwai masana harkar fim; akwai mutum guda daga 'Barewa Film Production', akwai mutum daya 'Hikima Media Film Production,' akwai mutum daya daga 'Video Mark Film Production,' bayan haka akwai wani mutum sananna ne daga cikin masu shirye-shiryen fim. Haka muka hadu mu shidda muka ce ya kamata mu hadu domin mu yi tafiya tare domin bai kamata idan an yi fim a ce sai an dauki lokaci sannan wani fim ya sake fitowa daga Jihar Zamfara ba. Saboda a lokacin da aka yi Babu Maraya Sai Raggo sai da aka dauki lokaci sannan aka yi Ki Yafe Ni wanda a wannan fim din na fito a matsayin mahaifin Wasila Isma'il. Saboda haka muka yi tunanin cewar mu hada kai domin ganin mun rika fitar da fim mai kyau a lokaci lokaci. Shi ne muka sa ma kamfanin suna 'PEYORI Film Production.' To da aka nada shugabannin sai aka ba ni Ciyaman. Ka ji matsayina a wannan wurin.

Zan so in san dalilin da ya jawo ra'ayinka bayan ka yi gwagwarmaya a fagen siyasa kuma ka dawo kana shirin fim.

FODIO: Abin da ya jawo ra'ayina kamar bayanin da na yi baya cewa goya ma shari'a baya, sannan ganin wasu sun dauki wata akida ta daban kamar masu aron al'adun wasu wadanda suka saba ma Shari'a suna amfani da ita a cikin fim. Ka ga na farko muna son duk wani fim wanda za mu yi ya kasance tsarinsa ya yi daidai da abin da Shari'a ta ce a yi, don ba za mu yarda ya saba ma tsarin Shari'a ba. Aron dabi'u marasa kyau da wake-wake din nan da raye-raye tsakanin namiji da mace to ba mu da sha'awa a gare shi. Don haka muka ga cewar ya dace mu zo mu yi abin da zai fadakar da jama'a da tarbiyantar da yaranmu masu tasowa don kada su tashi bisa wata akida ta daban. Muna son mu goge wannan al'adun da aka fara sa ma jama'a sannan mu koma al'adunmu masu kyau wadanda aka san Malam Bahaushe da ita.

Na ga abubuwan sun kankama kamar yadda na gani wajen da kuke rihazal. Finafinanku da kuke da su rubuce a kasa zas u kai kamar guda nawa?

FODIO: Muna da fim kamar guda biyar insha Allahu. Na farko shi ne wanda muke kai yanzu kuma insha Allahu ba mu son mu bata lokaci. Muna son mu gudanar da shi cikin tsari domin ya fitar da manufofinmu da jama'a za su gani.

Kamar Ki Yafe Ni irin wuraren da kuka yi amfani da su wurin fim din kun nnemi wuraren daga wurin masu kudi ne ko kuwa kun yi amfani da gidajenku ne ko otal?

FODIO: A takaice gidajen masu kudi muka yi amfani da wasu jama'a amma mun yi amfani da otal, watau 'Gusau Hotel' kawai muka biya kudi.

Ko kuna samun matsala wajen neman gidaje kasancewar wannan wani abu ne sabo a nan jihar?

FODIO: A gaskiya Ki Yafe Ni ba mu samu wata matsala ba amma yanzu da yake shari'a ta kama sosai duk da haka ba ni sa ran mu samu wata matsala. Amma lokacin da muka yi Ki Yafe Ni mun nemi aron gidaje kuma mun samu hadin kai. Ka ga sati mai zuwa muke son mu fara insha Allahu wannan fim din da ka isko muna rihazal a kanshi. Idan har ba mu samu aron gidaje ba, to sai mu je otal.

Idan za ku yi fim a nan Zamfara sai kun je kun ne mi izini daga wajen gwamnati ko kuwa yaya abin yake?

FODIO: A gaskiya a takaice na daya dai akwai rijista da ake yi a kungiyar furodusoshi ta Arewa, sannan akwai rijista da kamfani zai yi tun daga karamar hukuma har zuwa matakin jiha da matakin kasa baki daya. Kuma mu masu da'a ne da biyayya ga shugabanni tare da dokoki don gudun keta shari'ar Musulunci. Ba za mu fara gudanar abubuwanmu ba face sai mun samu shawarar hukumar shari'a da malamai don gudun saba ma shari'ar Allah.

A nan jihar masu sa ido a kan aiwatar da shari'ar Musulunci suna kuka da masu nun finafinai a gidaje suke dauko kaset marasa kyau masu bata tarbiyya ko kuma ka ga sun lika fostar finafinan kudancin kasar nan inda za ka ga mace tsirara. Me za ka ce?

FODIO: Ai wannan yana daya daga cikin abubuwan da suka sa mu yin namu don kauce wa ire-iren wadannan akidun ga yaranmu masu tasowa. Lokacin da namu ya fito insha Allahu za a ga bambanci tun daga fosta tare da sauran shirye-shiryenmu za su nuna komai irin yadda shari'a ta yarda a yi amfani. Idan Allah ya taimake mu muka yi shi kamar yadda doka ta ce, to gwmnati za ta ji dadi. Ai ka ga ko Saudiya da wasu kasashen Musulmi suna shirye-shiryen fim amma wanda bai keta ma shari'ar Musulunci ba, saboda idan ka aikata abu mai kyau ga sakamakonka marar kyau ga nashi, zabi ya rage ma mutum.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin