Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 35   Nuwamba 2002
RAHOTO


BABBAN SHAFI
MU LEKA MU GANI
TALLA
Wasiku
KU TAMBAYE SU
Duniyar Finafinai
Rahoto
Malam Zurke
Rayuwarmu
Bukukuwa
Sauran Labarai
Fitattun Taurari
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka
Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM MAI FITOWA!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da MU LEKA MU GANIn yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection


'Yan fim sun je ta'aziyyar Adamu Halilu

Karkashin jagorancin Iyan-Tama

Daga ALIYU ABDULLAHI GORA II a Kaduna

SHUGABAN Kungiyar Furodusoshi ta Arewa, Alhaji Hamisu Lamido Iyan-Tama tare sakataren kungiyar, Malam Abdullahi Maikano Usman, sun jagoranci wata tawaga ta 'ya'yan Kungiyar Furodusoshi ta Jihar Kaduna suka kai gaisuwar ta'aziyyar rasuwar shahararren darakta Alhaji Adamu Halilu, wanda ya rasu ran 1 ga Satumba 2002.

Tawagar, wadda ta kunshi sabon zababben shugaban Kungiyar Furodusoshi ta Jihar Kaduna, Malam Ashiru Sani Bazanga, ta isa gidan marigayin da ke layin 'Kagoro Close' a Tudun Wada, Kaduna, da misalin karfe biyar na ranar Asabar, 29 ga Satumba, 2002.

Bayan Maikano ya gabatar da furodusoshi ga iyalan mamacin, tare da jaddada juyayin rasuwarsa, sai furodusoshin suka yi wa mamacin addu'ar neman gafara da kuma rahamar Ubangiji.

Furodusoshin sun hada da Iyan-Tama, Maikano, Bazanga, Aliyu Abdullahi, Magaji Suleiman, Ahmed Alkanawy, Abubakar Ishaq, Nasiru Dan Bisallah, Murtala Aniya, Dr. Sani, da kuma wakilin mujallar Fim Aliyu Abdullahi Gora II.

A jawabinsa na karshe, Abdullahi Maikano Usman ya ce babu shakka rasuwar Alh. Adamu Halilu babbar asara ce ga dukkan masu shirin fim, musamman idan aka yi la'akari da gagarumar gudunmuwar da ya bayar wajen kyawawan shawarwari da ya bada wajen habaka darajar shirin fim. Maikano ya yi kira ga dukkan mai sana'ar shirin fim da ke arewacin kasar nan da ya ci gaba da yi wa marigayin addu'ar neman rahamar Allah.

Ta'aziyyar ta biyo bayan sanar da furodusoshin da wani furodusa ya yi cewa Allah ya yi wa Alhaji Adamu Halilu rasuwa. Da yawa sun bayyana mamaki, suka ce sam ba su san cewa ya rasu kusan wata daya da ya gabata ba.

Anya za a yi gasar finafinai ta Arewa a bana?

Daga WAKILINMU a Kano

A BISA dukkan alamu fitacciyar gasar finafinai din nan ta Hausa, wato 'Arewa Films Award' ta shekara ta 2002 za ta sami tangarda. Wannan kalami kuwa ya fito ne daga bakin babban jami'in masu shirya gasar, fitaccen daraktan nan Alhaji Abdulkareem Mohammed.

Da yake amsa tambayoyin mujallar Fim a a ofishinsa da ke kan titin 'Zoo' a Kano, shugaban na kamfanin editin na 'Moving Image' ya tabbatar da cewa a bana ba za a gudanar da gasar ba sai fa idan su masu shirya gasar sun sami wasu kamfanoni ko wani kamfani da zai iya daukar nauyin gudanar da bikin.

Ya yi nuni da irin kudin da kamfanin shirya gasar nasu mai suna 'Arewa Films Promotion' ya kashe a wajen shirya bikin na 2001, amma ya kasance abin bai yi wa aljihun kamfanin dadi ba.

An tambaye shi ko sun fara fafutikar neman mai daukar nauyin gasar, sai ya amsa: "Sosai kuwa. A yanzu din nan muna nan muna tattaunawa da kamfanin NASCO da kuma gwamnatin Jihar Bauchi". Ya kara cewa kuma muddin abin ya kankama daga daya daga cikin wadannan, to za a ji son buga tambarin shiri.

A karshe da aka tabo masa batun taron kara wa juna sani na kasa da kasa da za a yi kan finafinan Hausa, sai Alhaji Abdulkareem ya toge ya ki cewa komai bisa dalilin cewa shi dan kwamiti ne kawai. Duk da haka dai ya tabbatar da cewa a taron baya-bayan nan da aka gudanar, 'yan kwamitin taron sun cimma kudiri daya cewa za a rika yin taron a duk bayan shekara biyu.

Za a fara taron a cikin 2003, a tsakiyar shekarar ko kuma can wajen gabatowar karshenta, "ba don komai ba kuwa sai don mu yi wa taron kyakkyawan shiri," inji Malam Abdulkareem wanda har ila yau shi ne mawallafin mujallar Duniyar Fim.

Mahaifiyar Tsigai ta rasu

Daga SANI AHMED SASA, a Gombe

ALLAH ya yi wa mahaifiyar shaharriyar 'yar wasan nan Hajiya Hussaina Gombe (Tsigai) rasuwa. Mahaifiyar, mai suna Hadiza Wulaye, ta rasu a ranar Lahadi, 15 ga Satumba, 2002 bayan ta yi fama da rashin lafiya inda aka kwantar da ita a asibitin kwararru na Gombe.

Marigayiyar mai shekaru 65 a duniya ta bar 'ya'ya da dama, daga ciki har da ita Tsigai wacce ke yawan fitowa a fim tare da Rabilu Musa Danlasan (Ibro).

'Yan fim da dama sun halarci wurin karbar ta'aziyya. Daga cikinsu akwai Ibro da tawagarsa, sai Alhaji Damamusau da tasa tawagar, da furodusoshi da 'yan wasan fim na Gombe da dama.

Allah ya jikan marigayiyar, kuma ya ba magadanta jimirin jure wannan rashin, amin.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin