Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 46   Junairu 2004
RAHOTO


BABBAN SHAFI
GASKIYA DAYA CE
HIRA DA DARAKTOCI
Wasiku
NEMAN MAFITA
SHARHI KAN FINAFINAI
RAHOTO
Malam Zurke
RA'YIN FIM
Bukukuwa
ADABI
SABUWAR FUSKA
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka

Bangon FIM TA 45. Danna nan ka gani!
Bangon FIM TA 44. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 43. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 42. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 41. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 40. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 39. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 35. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 34. Danna nan ka gani!

Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM YA FITO!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
Sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

KASH! Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

'Yan wasa: Farida Jalal, A.A. Shariff (Momo), Kasimu Yero, Bashir Nayaya, Abubakar Yusuf Ladan, Hajara Usman, Sani Idris Moda, Sani Garba S.K, da Rashida Bello.

Darakta: Aminu A. Shariff

BABU IRINSA!

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection


Ana hakon barawon da ya shiga dakin Hadiza Kabara

Daga WAKILINMU

KIMANIN mako biyu da tarewar shahararriyar jaruma Hadiza Kabara a gidan mijinta drakta Mohammed Garba Kabara a unguwar Dorayi, Kano, wani barawo ya shiga ya yi mata sata. Wata kwakkwarar majiya ta shaida wa Fim cewa barawon ya shiga gidan ne bayan fitar Hadiza zuwa gidan wasu makwafta, ya debe mata kayan sawarta guda hudu da wasu kayayaykin wadanda da take sanyawa lokacin tana harkar fim, har ta yi wadansu finafinai da su.

Jama'a da dama sun yi mamakin irin wannan barawo wanda kawai shi kayan sawa ya dauka maimakon karikitai irin su na'urar sidi, bidiyo, talbijin, rediyo da sauransu. Wata majiya ta shaida mana cewa suna nan sun zuba ido a industiri suna hakon 'Da'u fataken daren.' "Idan har muka ga kayan a jikin wata a cikin wani fim to za mu dau mataki kwakkwara," inji ta.

An tashi baram-baram daga bikin gala

Daga SANI MAIKATANGA a Kano

A IRIN bukukuwan da ake gabatarwa domin taya jama'a murnar bikin Sallah, a Sallah Karama da ta wuce shahararrun 'yan wasan Hausa na Jihar Kano sun aiwatar da nasu shagulgulan. A ranar Jumma'ar da ta biyo bayan Karamar Sallah aka yi bikin a gidan wasa na Lahai da ke kan titin zuwa gidan zoo.

Tun da misalin karfe 3 na rana 'yan kallo masoyan finafinan Hausa suka yi ta tururuwa zuwa gidan wasan. Gidan ya dinke da jama'a yadda ba a tsammani. An gabatar da 'yan wasan da suka halarci wajen kamar haka: Nura Imam, Abba Al-Mustapah, Aminu Shariff Ahlan, Ali Nuhu, Ahmed S. Nuhu, Baballe Hayatu, Farida Jalal, Fati Baffa Fagge, Sadiya Mohammed (Gyale), da dai sauransu. An yi wakokin finafinai musamman na kamfanin FKD sababbi da ba su fito ba kuma Ali da Ahmed sun taka rawa.

Jama'a 'yan kallo suna cikin yaba yadda aka aiwatar da wannan wasa, sai kwatsam gidan wasan ya kaure da hayaniya a daidai lokacin da Ali ke wakar shirin "Makamashi". Dalili shi ne 'yan kallon da ke zaune a gaba-gaba sun kare wa na bayansu, su kuma suka fara iface-iface da jefe-jefe. Amma ba wanda ya taba wani dan wasa. Nan da nan wani dansandan kwantar da tarzoma ('mobile police') ya watsa tiyagas, wanda hakan ya sa wasu suka fara haura katangar gidan suna guduwa. Haka kuma wasu 'yan mata mawaka suma sun sha da kyar inda suka rike daya daga cikinsu ranga-ranga suka kai ta gaban kamfanin editin na 'Kwality Audio-visual' suka kwantar da ita a situdiyon buga wakoki na 'Sulpha' har ta dawo hayyacinta.

Sakamakon wannan hatsaniyar, wasu masu adawa da Ali Nuhu a industiri sun rika bayyana jin dadinsu kan yadda wasan ya watse baram-baram, yayin da wasu masu kaunarsa suka nuna cewa hassada ce ake yi masa.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin