Ba za mu yi abin da za a ce assha ba
-Sani Bello Gusau
Daga ABUBAKAR MAIHOTO a Gusau
MALAM Sani Bello haifaffen garin Gusau cikin Jihar Zamfara ne. Ya yi makarantun firamare da sakandare dinsa a Gusau kafin ya wuce makarantar koyon aikin gona inda ya yi shekara biyu, ya samo satifiket.
Bakin gwargwado Sani dai ni masani ne game da harkar wasannin Hausa. Na same shi a harabar kungiyar 'Peyori Film Production' a Gusau yana koyar da yadda ake yin wasan kwaikwayo, kuma shi ne zai zama daraktan shirin.
Sani dan wasa ne da ya dade ana damawa da shi a harkar. A cewarsa, tun yana firamare yake da ra'ayin wasan kwaikwayo. Ana yi da shi tun lokacin, da ya zo sakandare nan ma ana yi da shi. Har zuwa yau a Gusau dai ba a yi sai da shi game da harkar wasannin kwaikwayo. Har aikin gwamnati da yake yi duk bai sa ya bar wannan sana'a ba.
To kila wasu su ce me ya sa Sani bai yi fice ba? "Abin da ya sa ban yi wani fice can ba," inji shi, "shi ne shirya fim kamar wanda yake na sayarwa ne da sauransu to wanda zan ce na yi finafinan sayarwa har duniya ta fara gani daga cikinsu shi ne Babu Maraya Sai Raggo sai kuma Ki Yafe Ni na daga bayan nan. To duk wadannan finafinan matsayin da aka ba ni da sauransu na buga su fiye da yadda aka ce in yi, saboda su kansu (masu finafinan) ba su yi tsammanin zan yi shi kamar yadda aka ce in yi ba."
Ya fada wa wakilinmu dalilin kafa wannan kungiyar tasu, "Makasudin kafa ta shi ne muna son mu yi kalubale ga wasu kungiyoyi na masu shirya finafinai wadanda suka aro al'adun wasu kasashe can daban suna kawo mana ana yin finafinai da su matasanmu suna gani suna koyi da abin da mutanen waje suke yi, suna barin al'adarmu. Saboda wannan shirin da ka ga muna yi da sauransu abu ne wanda ya shafi al'adarmu mu 'yan Arewa kuma Hausawa. Sannan kuma mu rike al'adun nan namu na kwarai, kada mu yi watsi da su. Sannan na uku ya kasance tunda lokacin Shari'a ne to duk abin da za mu yi na rayuwarmu ya yi daidai da yadda Allah ya ce.
"Bayan mun raya al'adummu mu kara sa zuciyoyin matasa da kowa su gane cewa Shari'a ita ce komai gare mu a rayuwarmu ta duniya da lahira."
Lokacin da wakilinmu ya isa wurin da ake rihazal din sabon wasan na su Sani, ya tarar da wurin cike da samari da 'yanmata. Wannan ya ba shi mamaki da yake Zamfara dai jiha ce ta Shari'a. Ya yi tunanin cewa tunda an hana karuwanci a jihar, to su wadannan 'yanmatan akwai izini daga gwamnati an ba su damar su zo su yi wannan harka ko suna samun izini daga wajen iyayensu ne?
Sani Bello ya amsa wannan tambayar: "Da farko duk wanda ka gani nan wurin tun farkon tsarin za ka ga tsarin layin mata daban na maza daban. Ai ka lura ko? Sannan duk mafi yawancin matan nan suna aikin gwamnati ne; akwai na Ma'aikatar Fasaha da Al'adu cikinsu. Abin da yake ka'idarmu a nan (shi ne) duk wata mata wadda ta san ba ta da 'yanci ko aikin yi ba za mu dauke ta ba. Abin da nake nufi da 'yanci shi ne sai mun san matsayinta kowace iri ce sannan za mu yarda mu dauke ta, saboda mun san jiharmu jihar Musulunci ce. Ba za mu yi abin da za a ce assha ba.
"To wadannan mata da kake gani ma'aikata ne kamar yadda na ce maka, sannan akwai zawarawa. Bayan haka ba mu daukar mace fim sai mun bi daddagi mun ji menene matsayinta domin gudun wani abu daya: sau da yawa ana shirin fim da wata matar aure ba a sani ba. Mun sha ganin haka. Don guje wa wannan matsalar muke bincike mai zurfi kafin mu dauki mace. Kuma ba mu hulda da 'yanmata; ka'idarmu sai mace ta kai shekara goma sha takwas, mafi karanci kenan, sannan ba mu hulda da masu zaman kansu in har akwai su."
A matsayinsa na darakta, me zai ce kan ko akwai wata ka'ida da Gwamnatin Jihar Zamfara ta shimfida inda duk wani fim wanda za a shirya sai an kai wa malamai ko Ma'aikatar Addini sun duba sun ga bai saba wa Islama ba? Ga amsar Sani Bello: "Kamar yadda na riga na sanar da kai can baya, muna son mu nuna al'adunmu masu kyau da kuma Shari'a da muke ciki tana da muhimmanci. Wannan fim din da za mu shirya shi ne a kan wadannan abubuwa guda biyu wadanda na gaya maka: fim wanda zai karantar da dabi'u masu kyau da babu waka babu nuna tsiraici. Saboda haka idan muka shirya shi a kan tafarki mai kyau, watau Shari'a tare da al'adunmu masu kyau, babu shakka za mu ba gwamnatin jiha da duk wani wanda yake da hakki a nan jihar don su duba su yi gyara in akwai. Saboda ba mu son duk wani abin da zai fito a Jihar Zamfara a ce Allah wadarai da shi ganin ya saba ma Shari'a. Saboda haka muke son gwamnati su fara duba fim din su ga cancantarshi, duk inda suka ga akwai wani gyara sai a gyara kafin a fitar da shi kasuwa."
Sani ya yi maganar yin fim babu waka yana daga cikin kudurorinsa. mun tuna masa maganar da wasu ke yi cewa wasu masu shirin fim suna cewa fim ba ya karbuwa ga jama'a sai an sa waka. To yaya wannan na su Sani zai kasance? Daraktan ya ce, "Duk wani wanda ya ce fim bai karbuwa sai an yi waka karya yake yi. Zan ba ka misali. Mafi yawancin finafinan Ibro da su Dan Wanzan wakoki suke yi? Ka ga ai al'adarsu ce suke kawowa su sa. Kuma ai ba wasu kudi suke kashewa sosai ba. Ga su sun karbu sosai kuma babu waka. To yaya aka yi suka samu karbuwa sosai? Saboda haka mu ba sai da waka ba fim zai samu karbuwa, a'a ma'ana ake so ga fim. Saboda shi dan wasa mai karantarwa ne. Saboda haka za mu nuna masu ba sai da waka fim zai samu karbuwa ba."
To, Sani Bello, sai mun gani.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin