Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 33   Satumba 2002


BABBAN SHAFI
MU LEKA MU GANI
HIRAR MUSAMMAN
Wasiku
KU TAMBAYE SU
Rahoton Musamman
Rahoto
Malam Zurke
RA'AYIN MUJALLAR FIM
Bukukuwa
Sauran Labarai
Fitattun Taurari
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka Bangon Fim ta 31
Bangon Fim ta 30
Bangon FIM ta 29
Bangon FIM ta 28
Bangon FIM ta 27
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da MU LEKA MU GANIn yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Akwai fa'idodi mutum ya shirya fim a Legas

-MUHAMMAD Balarabe Sango II

MUHAMMAD Balarabe Sango II shi ne shugaban kungiyar shirya wasan kwaikwayo ta Janzaki, wadda ita ce kungiyar 'yan dirama mafi girma a Kano. Ya dade yana yi wa wannan kungiya shugabanci. A tsawon lokacin jagorancinsa kungiyar ta shirya finafinai masu dimbin yawa.

Sango dai, kamar wasu 'yan fim din, ma'aikaci ne. Yana aiki a wani kamfanin inshora. A da, a Kano yake zaune, to amma sai kamfanin ya yi masa sauyin wurin aiki, ya maida shi Legas. Shin yaya kenan? Tun komawarsa can, wanda yanzu an dan dade, ya watsar da harkar fim kenan? To, bayani dai shi ne ko a Legas din M.B. Sango II bai watsar da dirama ba, domin yana shiga ana damawa da shi. Kuma idan ya zo Arewa ma, yakan shiga harkar fim a yi tare da shi.

IBRAHIM SHEME ya so ji daga Sango yadda harkar wasan kwaikwayo take a Legas. Shin akwai 'yan wasa a can? Yaya suke wasansu? Menene ra'ayinsu kan finafinan Hausa da ake antaya masu daga nan? Malam M.B. Sango II ya amsa wadannan tambayoyin a kwanan baya lokacin da ya kawo ziyara a ofishinmu na Kano.

FIM: Malam Sango, yaya yanayin wasan kwaikwayo yake a Legas?

SANGO: Akwai 'yan wasa da dama a can. Suna yin stage drama (wasan kan dabe) sosai a unguwanni kamar Agbo Malu (a Apapa), Mile 12, da Agege. Suna yin kidan koroso da kuma dirama sau biyu a rana: su yi da yamma da kuma da dare. Kudin shiga yakan kama daga N30 zuwa N40. Idan an yi baki, misali idan su Ibro sun je, kudin yana kaiwa N100 duk mutum daya. Za ka ga samari da 'yanmata suna zuwa kallon wasannin da ake yi.

Da ka isa can suka gane kai ma dan fim ne daga Arewa, yaya suka karbe ka?

SANGO: Farkon zuwana sun yi murna da suka gane ni. Suna neman shawarata a kan wasanninsu, kuma nakan yi masu directing (aikin ba da umurni) jefi-jefi.

Yaya suke kallon 'yan wasanmu na Hausa?

SANGO: E, suna son su ga wane kaza ya zo. Ba su damu kullum a zo ba. To amma 'yan wasanmu ba su cika zuwa ba.

Me ya sa ba su zuwa sosai?

SANGO: 'Yan wasanmu ba su fahimci wannan sana'a tamu sosai ba. Wasa kan dabe ya fi samo kudi. Idan mutum uku daga nan suka tafi can suka hadu da na can, za ka ga har tafiya yawon yin wasa suke yi gari-gari - har Fatakwal da Inugu da Shagamu da Ibadan sukan je.

Yanzu idan mutum daga nan yana son ya je Legas ya shirya fim dinsa, wadanne fa'idoji zai iya samu a can?

SANGO: Na farko dai yanayin Legas mai kyau ne a kowane lokaci a shekara, tunda garin a gefen teku yake. Ba mai aibu ba ne. Ya yi daidai ta yadda kyamara za ta iya daukar hoto ko da babu haske mai yawa. Na biyu, batun kashe kudi, za ka iya samun supporting astistes (wato 'yan wasan da za su fito maka a wasu bangarori) a can Legas din, kuma kwararru ne matuka. Kuma ba sai mutum ya tafi da ma'aikatan daukar fim din masu yawa ba tunda akwai kwararru a can. Ka dubi Nigerin films mana. Kai, ko da aikin daukar fim din zai ci kudi fiye da na nan, gwamma ka yi hakan domin fim din zai fi ingantuwa. Abu na uku shi ne akwai kayan aikin hada hotuna (editing) birjik a can. Na hudu, akwai hukumar tace finafinai, tunda da ma can a can ake yi kafin a fara a Abuja; ka ga za ka iya gyara fim dinka ka gama komai a can. Na biyar, bayan ka gama fim dinka, za ka iya haska shi a 'National Theatre' da ke Iganmu da kuma sauran gidajen sinima da ke akwai a duk Kudu.

To, kai kanka yaya aka daina jin duriyarka tun da ka koma Legas?

SANGO: Ba haka ba ne. Lokacin da nake nan din ma, yin wasan bai dame ni sosai ba. Har yanzu ni ne shugaban Janzaki, amma zan sauka a watan Oktoba na bana. Yin wasa a fim abu ne da na dauka na baya-baya a harkokina. Kuma ko da ina can Legas din ma an kira ni na zo na yi wasa a shirin Samodara 2 na 'Fatima Production,' na gama na tafi. Kuma har yanzu nakan rubuta labarin fim in tsara shi screenplay). Na karshen da na yi shi ne na fim din Kawata Kishiyata na kungiyar Janzaki, wanda bai fito ba tukuna, kuma daga can na zo muka yi shi.

Sa'annan a Legas din, masu sha'awar finafinai suna kawo min ziyara su ji labaran 'yan fim ko in raba masu wata gardama. Kwanan nan ma a Legas din zan yi wani fim. Bayan haka, idan wani abu ya taso na 'yan fim baki daya, ni ne nakan je a matsayin dan wasan Hausa. Akwai wani taron kara wa juna sani na kwana uku wanda kungiyar MOPPAN ta shirya a bara a Legas, ni kadai ne daga Arewa da ya je wurin. Kuma na karu, har ma na aiko wa Kungiyar Masu Shirya Fim ta Jihar Kano takardun da aka bayar a taron.

To yaya ba ka shiga cikin finafinan 'yan Kudu ba har yanzu?

SANGO: A gaskiya na so in shiga harkar. To, ka san sha'anin 'yan'uwan namu ('yan Kudu): sai ka fahimce su sosai, tunda yawanci addininsu suke sawa a finafinan nasu. Dole ka tabbatar ba a sa ka inda za a tsinka ka ba.

Shin ko masu-hannu-da-shuni 'yan Arewa suna taimaka wa 'yan wasa 'yan Arewa da ke can kuwa?

SANGO: Matsalar da ake fuskanta a nan Arewa ita ake fuskanta a can din ma. Ita kungiyar 'yan dirama da ke Agbo Malu sun yi kokarin su fara shirya fim, amma sai ba su bi ka'idoji da tsari ba, suka yi kuskure. Na ba su shawara, suka ce sai sun sake tsari. Yanzu na fara yi ma wasu masu kudin magana. To, duk wanda zai ba ka kudi a can sai ya duba sosai.

Me za ka gaya wa furodusoshinmu masu son su je Legas su shirya fim, musamman wane taimako za ka iya yi masu a can tunda an ce da dan gari kan ci gari? SANGO: Duk wanda ke son yin fim a Legas, ya tuntube ni ko ta hanyar ofishin mujallar Fim ne. In kuma na Legas ne yake son ya zo Kano ya yi fim, to ya tuntube ni. Wani abu da nake son ka gane shi ne a gaskiya Hausawa ne suka mamaye harkar fim a Nijeriya.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin