Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 34   Oktoba 2002


BABBAN SHAFI
MU LEKA MU GANI
HIRAR MUSAMMAN
Wasiku
KU TAMBAYE SU
Rahoton Musamman
Rahoto
Malam Zurke
RA'AYIN MUJALLAR FIM
Bukukuwa
Sauran Labarai
Fitattun Taurari
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka
Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM MAI FITOWA!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da MU LEKA MU GANIn yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Matsayin Shirin Fim A Katsina:
Sai sambarka, to amma…

Katsinawa suna bakin kokarinsu, amma kuma har yanzu sun bar babban gibi a harkar shirin fim. Me ya jawo haka? Kuma ina mafita?

Alhaji Haruna
Alh. Haruna Maiwada Katsina

Daga BASHIR YAHUZA, a Katsina

A 'YAN shekaru biyu ko uku da suka gabata, harkokin shirya finafinai a Katsina sun yunkuro sosai, abin babu kama hannun yaro. An samu fitowar furodusoshi masu kishi a jihar, wadanda har sun fara cirar tuta a fagen shirin fim. A garin Funtuwa akwai shahararriyar marubuciyar nan, Hajiya Bilkisu Salisu Ahmed (Anti Bilki), wacce fim dinta Ki Yarda Da Ni shi ne na farko da ya share fagen nasara a finafinan Hausa. Sa'annan kamfanin 'Alkarama Ventures' ya shirya Da Wa Zan Kuka? A birnin Katsina akwai shahararrun furodusoshi irin su Alhaji Habibu Sani Kofar Soro, da Alhaji Abdu Haro Mashi, kuma a 'yan watannin baya matasa irin su Abdu Boda sun yunkuro.

Sai dai duk da wannan yunkuri, a yanzu akwai mutanen da ke tsegumin cewa Katsina ba ta taka rawar da ya dace da ita a fagen shirin fim, musamman idan aka yi la'akari da yawan hazikan furodusoshi da daraktoci da marubuta da ke jihar. Hasali har situdiyon buga kade-kaden fim akwai. "Duka-duka fim nawa aka fitar daga Katsina? Mun san dai Damaga sun fitar da Kowa Ya Yi Da Kyau, sai Amana; tun daga nan kuma ba mu kara ganin wani fim ba," inji manajan wani katafaren shagon sayar da kaset da ke Sabon Layi, wato Yahaya Salamah.

Shin ina gaskiyar irin wannan hasashe? Idan gaskiya ne, to me ya kawo tsaikon fitowar sababbin finafinai daga birnin na Dikko? Idan matsaloli ne, wadanne iri ne, kuma wane kokari ake yi domin magance su? Tambayar da muka yi wa Muhammad Mukhtar Inwala kenan, wanda shi ne Mataimakin Shugaban Kungiyar Furodusoshin Arewa, reshen Jihar Katsina (AFPAN). Shi kuma ya ce a yanzu ne ma Katsina za ta yunkuro, musamman a harkar shirya fim. Ya ce sun karfafa kungiyarsu ta furodusoshi bisa shugabancin Habibu Sani Kofar Soro, kuma Hon. Abdu Haro Mashi, Sardaunan Furodusoshin Arewa, yana ba su goyon baya da muhimman shawarwari, kuma a koyaushe sababbin furodusoshi suna yin rijista da kungiyar. Membobinsu sun shirya wa harkar fim, domin kuwa kwanan nan wasu finafinai za su fito daga Katsina. Misali akwai Sarauniya na kamfanin Abdu Boda, da Batan Basira na Barista Ali Sa'idu, da kuma Kul! na Kabir Ahmed S/kuka. "Don haka ba gaskiya ba ne da ake cewa wai harkokin finafinai sun tsaya. A yanzu ne ma aka soma, kuma muna tare da nasara in Allah ya yarda," inji Muhammad Mukhtar.

Me'yan wasan Katsina ke ciki? Fitacciyar 'yar wasan nan Hajiya Binta Sulaiman Ola, wacce ta fito a finafinan Amana da Batan Basira, sannan kuma take fitowa a wasannin Nayalli da gidan talbijin din KTRTV Katsina ke shriyawa, ta shaida wa wakilinmu cewa harkar fim a Katsina sai godiya, saboda don neman bunkasa harkar ta sanya suka kafa Kungiyar 'Yan Wasan Kwaikwayo ta Jihar Katsina, kuma sun samu nasara har sun shirya fim mai suna In Rana ta Fito, wanda an kammala shi duka, an nuna shi a gidan sinima na Rex da ke Katsina, kuma ana nan ana shirin kaddamar da shi kafin a sake shi kasuwa.

A cikin farin ciki da kuma bugun kirji, Binta Ola ta ce, "Ai mu Katsina sai godiya, nan gaba kadan za mu shiga gogayya da Kano a harkar finafinai. Muna da fitattun furodusoshi, ga kuma 'Artistes Council' mu ma muna fim. Sannan kuma ga fitattun 'yan wasa irin su Alhaji Umaru Danjuma (Kasagi), ga Nayalli, ga Alhaji Bilis, ga Salisu Kakis... Kai, a nan Katsina har Hakimi muna da shi kuma dan wasa, wato Alhaji Sambo Idris Sambo, hakimin Funtuwa, wanda ya rika fitowa shirin Samanja a matsayin O.C. A Katsina mun ciri tuta!"

Shi ma Abdu Boda, matashin mawaki, dan wasa wanda kuma kwanan nan ya zama furodusa, ya shaida wa wakilinmu cewa ba gaskiya ba ne wai Katsina ta ci baya a harkar fim. Kwanan nan zai fidda sabon fim dinsa mai sun Sarauniya kasuwa, kuma akwai 'yan'uwansa furodusoshi da ke niyyar fitar da nasu da tuni suka gama shiryawa.

Wani abu da ke daure wa mutane kai shi ne yadda shahararren kanfanin nan 'Damaga Motion Pictures' ya yi shiru a harkar. Duk da cewa ya mallaki kayan aiki na kashin kansa, ga 'yan wasa da sauran ma'aikata, ga shugaban kamfanin mai azama da son harkar finafinai, kuma yana da hali, amma fim biyu kacal suka shirya, daga Kowa Ya Yi Da Kyau sai kuma Amana. Shin me ya ja haka? Wakilnmu ya yi kokarin ganawa da shugaban kamfanin, Hon. Alh. Abdu Haro Mashi, amma hakan ya faskara, sai dai a madadinsa ya gana da mai kula da harkokin kamfanin, wani dan wasa, darakta kuma kameraman, wato Bishir Shu'aibu Mashi, wanda ya tabbatar mana da cewa kamfanin nasu na nan zaune da gindinsa. A cewarsa, abin da ke faruwa aka ji shiru shi ne shi shugaban kamfanin harkoki sun masa yawa, sau daya yake zuwa Katsina a mako. Amma ana nan ana wasu gyare-gyare da shirye-shirye, nan gaba ka dan za a ci gaba da harkar, inji shi. "A yanzu haka akwai rubutattun wasanni kamar hudu, kuma ta kansu za a fara idan komai ya daidaita," cewar Bishir Shu'aibu, wanda aka fi sani da 'Matsala' a wasan kwaikwayo.

To idan Damaga na nan, ina 'U.K. Soro Productions' ya makale, wato kamfanin Habibu Sani Kofar Soro? Idan ba a manta ba, kamfanin ne ya yi fice daga Katsina a shekarun baya, sakamakon shirya manyan finafinai da ya yi, irin su Zakaran Gwaji Dafi, Dan'uwa, Alheri da kuma na baya-bayan nan, wato Dan Halak. Amma dai yanzu shiru kake ji kamar an aiki bawa gidansu. Ban da wannan ma, wasu 'yan wasan Katsina su koka da kamfanin suna cewa bai sanya 'yan wasan Katsina, sai dai ya yi kidansa da rawarsa duk a Kano. Suka ce wannan na kashe 'yan wasan Katsina. Kan haka ne suka ba kamfanin shawarar cewa ya dace ya rika surkawa da Katsinawa, don a samu ci-gaban harkokin wasa a jihar.

A kan haka, manajan kamfanin, Muhammad Mukhtar, ya shaida mana cewa, "'U.K. Soro Productions' ba shiru muka yi ba, kuma ba mu yi sanyi ba. A yanzu haka akwai fim dinmu da ake dauka a Kano, kuma ka ga wani nan ana gyara labarinsa (ya nuna script). Don haka nan gaba kadan za ku ji duriyarmu. Maganar 'yan wasan Katsina kuwa, tuni Alhaji Habibu ya san da wannan tsegumi da suke yi, kuma ya shirya sosai don magance hakan. Tuni U.K. Soro ke tunanin dago da 'yan wasan Katsina a idon duniya, amma ka san wani lokaci su mutane ba 'yan goyo ba ne, kana son taimakon mutum sai ya nemi durkusar da kai. Amma duk da haka, sabon fim dinmu da ake dauka a Kano, nan Katsina za a dauki wasu sassansa, kuma akwai Katsinawa da za su fito a ciki. Don haka U.K. Soro na nan zai yunkuro da karfinsa."

Harkokin cinikin kaset fa, ina aka kwana a Katsina? Kowa dai ya san yanzu al'amarin ya yi kasa a ko'ina a Nijeriya, wato kasuwa ta karye kamar yadda Fim ta ruwaito a watan jiya. Domin jin yadda ake ciki a Katsina, wannan mujalar ta gana da babban dilan kaset, Alhaji Haruna Maiwada Massanawa, wanda shi ne mai shagon 'Salamah Video Centre' a birnin Katsina. Ya warware mana bakin zaren, inda ya ce harkar kasuwancin kaset a Katsina sai godiya. "Duk furodusan da ya yi fim na zamani mai kyau, muna cinikinsa sosai," inji shi. A game da finafinan Katsina kuwa cewa ya yi: "Furodusohin Katsina ba su neman shawararmu, sai dai mu ji wai ana fim wuri kaza, amma ko talla ba su ba mu, sia munje Kano mun sawo. Haka kuma ba su tafiya da zamani, shi ya sanya finafinansu ba su shiga sosai. Don haka ina ba su shawarar cewa idan za su shirya fim, su karkata inda zamani yake. Mu ma 'Salamah' kamar yadda muka ce a mujalla nan gaba kadan za mu tsunduma."

Ko ma dai me ake ciki, harkokin fim a Jihar Katsina, sai dai mu zuba ido mu gani, domin kuwa furodusoshi suna ta azamar shiryawa da kuma niyyar fito da sababbin finafinai. Allah ya ba mai rabo sa'a.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin