Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 35   Nuwamba 2002


BABBAN SHAFI
MU LEKA MU GANI
TALLA
Wasiku
KU TAMBAYE SU
Duniyar Finafinai
Rahoto
Malam Zurke
Rayuwarmu
Bukukuwa
Sauran Labarai
Fitattun Taurari
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka
Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM MAI FITOWA!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da MU LEKA MU GANIn yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

'Yan Hisba sun cafke 'yar wasa da Darakta saboda sun yi sumba

An maka Ali Zamani da Gohar Kheirandish a kotu da laifin bata dokar addini

Wannan ba daidai bane
Zanen Darakta da 'yar wasa suna sumba

Daga IRO MAMMAN

WANI matashi mai ba da umurni a finafinai tare da wata shahararriyar 'yar wasan fim sun shiga tsomomuwa a kasar Iran a dalilin sumbatarsa da ta yi a bisa goshi, wanda hakan ya sa gwamnati ta maka su a kotun Musulunci a kan laifin sun yi laifin taba juna bayan ba muharramai ba ne.

A karkashin dokar shari'ar Islama wadda ake gudanarwa a Jamhuriyar Musulunci ta Iran din tun bayan da aka yi juyin-juya-halin da marigayi Ayatullahi Khomeini ya jagoranta a cikin 1979, an hana maza da mata su shafi jikin juna ko da ta hanyar gaisawa ce.

Sanin hakan ya sanya mahalarta wani babban bikin bada kyaututtukan gasar finafinai a birnin Yazad duk suka yi shiru kamar ruwa ya ci su da suka ga wata jaruma da ake girmamawa mai suna Gohar Kheirandish ta kai baki ta sumbaci goshin darakta Ali Zamani kuma ta kama hannunsa suka gaisa lokacin da ta mika masa kyautar da ya ci ta Gwarzon Darakta.

Abin ya faru ne a ranar Jumma'a, 27 ga Satumba, 2002.

Da yake kare kansa, an ruwaito Ali Zamani yana gaya wa wata jarida da ke fitowa kullum-kullum mai suna Efemad cewa, "Ni aka zaba a matsayin gwarzon mai shirya fim a bikin, kuma ni dalibi ne na marigayi mijin ita Kheirandish, to jin dadin nasarata ya sa har ta sumbace ni a goshi."

Shi da ita sun ba jama'a hakuri kan kuskuren da suka tafka, suka ce su kansu ba su san lokacin da kawai suka ji sun yi wannan abu ba har sai da suka yi din, kuma sam ba sun yi hakan ne domin su bakanta wa kowa rai ba.

"Sumbar da ta yi min kwatankwacin wadda uwa ke yi wa danta ne," inji Ali.

Sai dai kash! inda Gizo ke sakar shi ne su 'yan hisba (wato dogarawan tabbatar da bin dokar Islama) da suka halarci bikin ba haka suka kalli al'amarin ba. Shugaban 'yan hisba na birnin ya bada umurnin a cafke mutanen biyu a kan laifin sun aikata alfasha a gaban jama'a.

Tuni aka maka Ali Zamani a kotu, inda aka bada belinsa a kan kudi kamar dalar Amerika 2,500, yayin da ita Kheirandish aka ce za ta dawo birnin na Yazad domin ita ma a yi mata shari'a. Ali Zamani dai dan shekara sama da ashirin ne yayin da ita 'yar wasan ta haura shekara 50.

Kamfanin dillancin labarai na Iran (wato IRNA) ya ruwaito cewa wakilin majalisar Musulunci ta kasar baki daya a nan birnin Yazad, Malam Mohsen Talebpour, ne ya shirya zanga-zangar yin Allah-wadai da sumbar da aka yi. "A yau abokan gabarmu sun kai wa addininmu na Musulunci hari," inji shi.

Kafafen yada labarai ma sun yi tir da Ali Zamani da Gohar Kheirandish. Jaridar mako-mako mai suna Ya lessaarat cewa ta yi a cikin filin ra'ayinta, "Abokan gabarmu suna kokarin bata Musulunci ta hanyar al'adunmu kuma wannan abin da ya faru shi ne babban misalin hakan."

Shi ma wani jami'in Ma'aikatar Al'adu da ke birnin an kama shi saboda ya yi sake har mutanen biyu da ake zargi suka bar birnin da farko, ana tuhumarsa da laifin "hadin baki" da su. Shi ma daga bisani an bada belinsa a kan dalar Amerika 2,250.

Wani jami'in Ma'aikatar Al'adun kuma ya ce, "Duk da yake mun yi Allah-wadai da faruwar sumbar amma ya kamata a lura da cewa abin ya faru ne a wurin da ake ta shagali, sa'annan kuma ba wai an shirya yin hakan ba ne tun da farko."

Idan aka bi tarihi, za a taras cewa shirin fim a Iran ya sha gamuwa da wahalhalu. Hukuma tana tsaurarawa wajen tace finafinai. 'Yan fim sukan yi kokarin ganin sun shallake dokokin da aka kafa masu bisa turbar addini. A kasashen duniya finafinan Iran sukan samu kyaututtukan yabo saboda tsaruwarsu.

An dan rage matsin da akan yi wa jama'a a kasar tun lokacin da Shugaba Mohammad Khatami, wanda mai sassaucin ra'ayi ne, ya dare karagar mulkin kasar bayan an yi zabe a cikin 1997. Misali an dan sakar wa mata mara a kan yadda suke sanya tufafi idan za su unguwa, yanzu akan kauda kai idan an ga mace ta sanya janbaki da kuma takalma sandal, koda yake tilas ne mace ta rufe jikinta da hijabi daga sama har kasa. To amma sam ba a yarda mace da namiji su taba jikin juna ba, wanda hakan wani abu ne da wani jami'in kasar yake ganin bai da dadi idan ya gamu da matan kasashen Turawa. Wannan ko shi ne tsohon wakilin Iran a Majalisar Dinkn Duniya, Malam Hadi Nejad Hosseinian, wanda ya gaya wa jaridar Ya lessarat lokacin da ta yi hira da shi a kan wannan al'amarin, cewa, "A lokacin walima kobukukuwa a kasar waje, nakan rike kofin gilashi a hannu daya sannan in rike jakata a daya hannun saboda kada in yi musabiha da mace. Su matan kasashen waje ba su san ka'idojin Musulunci ba, saboda haka sai su rika jin haushi idan ba ka kama hannunsu kuka gaisa ba."

Nejad Hosseinian ya ce ya taba rubuta wasika zuwa ga shugaban kare addini a Iran, wato Ayatullahi Khameini, ya tambaye shi ko an yarda a wani lokacin idan wuri ya kure (kamar a kasar waje) mutum ya yi musabiha da mace. Amsar da aka maido masa ita ce, "A kul ka kuskura!"

Tare da rahoton Parisa Hafezi.

Kash! Amerika ta hana darakta ya halarci bikin da shirinsa ya yi zarra

Gwani na gwanaye
Abbas Kiarostami na Iran

A MAKON farko na watan jiya ne aka gudanar da shahararren bikin baje-kolin finafinai din nan na birnin New York a Amerika (New York Film Festival). Daya daga cikin finafinan da suka yi zarra a bikin shi ne wani mai suna Ten, wanda labarin wata mata ne 'yar kasar Iran da kuma motarta. Shugaban bikin, Richard Pena, ya ce sau biyu ana nuna fim din a bikin, kuma a kowane lokaci sai da tikiti ya kare.

To, abin mamaki dai shi ne daraktan fim din, Abbas Kiarostami, bai samu damar halartar bikin ba duk da yake an shirya cewa zai jagoranci wani taron tattunawa a kan fim din bayan an nuna shi ga jama'a. Dalili shi ne muguwar dokar nan da Amerika ta fito da ita wadda ta ce tilas duk wani Musulmi da zai je Amerika sai ya jira kwana 90 daga ran da ya mika takardar neman izinin shiga kasar kafin a bar shi ya shiga, domin sai an binciki mutum. Wannan wani bangare ne na matakan tsaro da kasar ta dauka a dalilin harin da aka kai mata a ran 11 ga Satumba na bara.

Kiarostami ya makale a gida, wato birnin Tehran, saboda babu lokacin da za a duba takardunsa har ya halarci bikin a Amerika. Shi dai babban darakta ne a duniya, ba a gida kurum ba. Fim dinsa mai suna Taste of Cherry ne ya ci kyautar Gwarzon Fim a bikin finafinai na duniya wanda aka yi a birnin Cannes na kasar Faransa a cikin 1997. Lokacin da ya bada takardunsa ga ofishin jakadancin Amerika da ke Paris sai ya fahimci cewa kafin ma a gama duba su har ya samu izinin zuwa New York sai cikin Disamba. Kiarostami, dan shekara 62, ya ki yarda ya yi amfani da matsayinsa a duniya domin jami'an jakadancin su daga masa kafa ya halarci bikin, ya ce idan har shi yana da wannan damar, to misali wata tsohuwa fa da ke son ta ziyarci 'yan'uwanta a can? A dalilin abin da ya faru gare shi ne ma wani daraktan dan kasar Finland mai suna Aki Kaurismaki, wanda abokinsa ne, ya kaurace wa bikin.

An dauki fim din Ten da irin kyamarar nan mai suna digital camera guda biyu wadanda aka kafa a cikin gidan gaban karamar motar suna kallon direbar da sauran fasinjoji. Gaba daya labarin fim din ya faru a cikin motar ne, inda ake nuna zantuttukan da direbar, wata matashiya mace, take yi tare da fasinjoji goma yayin da take tuka su a cikin birnin Tehran. Matar tana da da dan shekara goma, wanda yana cikin motar. Yaron da ita sun rukume gardama a kan hushin da yake yi kan dalilin da ya sa don kawai tana so babansa ya sake ta sai ta ce wai shi uban yana shan miyagun kwayoyi. Daga jin yadda fasinjojin motar ke magana mutum zai iya fahimtar yanayin rayuwar kowannensu.

Kiarostami ya gogu a harkar fim. Tun a cikin 1950 ya fara aikin shirya fim, lokacin da ya fara daukar hotunan bidiyo na tallar da ake sawa a talbijin, shekaru 29 kafin a kifar da gwamnatin Shah Reza Pahlavi a kafa Jamhuriyar Musulunci karkashin Ayatullahi Khomeini. Yana daga cikin mutanen farko da aka dauka aiki a cibiyar matasa masu kula da al'adu wadda ake kira Kanun, wadda gwamnatin Pahlavi ta kafa. Ita wannan cibiya ita ce ta haifar da harkar shirin fim a Iran. Har zuwa cikin shekarun 1980 Kiarostami yana tare da Kanun, wadda ta zama hukumar shirya finafinai ta kasar. Duk da yake yakan dan jefa nau'o'in tsiwa a finafinansa na wannan lokacin, ba su jawo masa surutai ba.

A yau, an fi girmama Kiarostami a kasashen waje fiye da cikin kasarsa. A cewarsa, "Idan mutane suka je kallon fim dina a Iran, a yawancin lokuta haushi yakan kama su har su rika fita daga gidan sinima din tun kafin ya kare. Amma idan na ga yadda ake kallon wani fim dina a kasashen Yamma sai in ga ya fi burgewa fiye da yadda mutanen Iran suke kallonsa."

A kan wahalhalun sa-ido da hukuma ke jawo wa masu shirya fim a Iran, daraktan ya kada baki ya ce, "Idan na gamu da wahalhalu sukan ba ni zummar in warware su... Ina da aboki mai zana gidaje da ya ce gidajen da ya tsara mafi inganci an gina su ne a fili mai wahalarwa."

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin