Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 28   Afrilu 2002


BABBAN SHAFI
Mu Leka Mu Gani
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 1
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 2
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 3
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 4
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 5
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 6
Malam Zurke
Ra'ayin Mujallar Fim
Hajjin Bana
Sauran Labarai
Ra'ayi Ba Gaba ne
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN

 
If you had a new browser, you would be able to view this java applet. Akwai:  


Malama Binta Muhammad, Mahaifiyar Balaraba
Binta, Uwar Amarya ta yi juyayin rabuwa da 'yarta

'Rabuwa da ita ta dame ni'

Bayan an gama daura aure, wakilinmu ya kutsa kai cikin falon uwar Balaraba, MALAMA BINTA, ya samu tattaunawa da ita a kan abin farin cikin da ya same ta wanda, Allahu Akbar!, zai kasance abin bakin ciki washegari. Ga hirar tasu:

Fim: Mama, za ki iya bayyana mana farin cikinki dangane da wannan rana ta daurin Auren Balaraba?

MALAMA BINTA: Ina matukar farin ciki sosai da sosai; a yanda Allah ya nuna mana wannan rana yanzu dai mun fita kunyar mutane.

Shin akwai wata damuwa a zuciyarki ganin cewa kun shaku da Balaraba, ga shi kuma Allah ya kawo ranar daurin aurenta za ta tafi ta bar ku?

MALAMA BINTA: E, to, akwai damuwa, tunda duk cikin yarana ba wanda na shaku da shi kamar ita. Dole ne abin ya dame ni. Rabuwana da ita gaskiya ya dame ni.

Ya za ki kwatanta sauran bukukuwan da ake yi a nan gidan?

MALAMA BINTA: Alhamdu lillahi, gaskiya a nan dai ban ga bikin da ya tara jama'a kamar haka ba. Ko duk bikin da ake yi a garin nan, ban ga bikin da ya tara mutane haka ba. Alhamdu lillahi, mun gode Allah.

Kafin wannan rana ta zo, kin taba tunanin jama'ar da za su zo daurin auren za su kai haka?

MALAMA BINTA: A'a, ban zata haka ba. Ana dai fadin cewa mutane za su taru, amma ban dauka cewa mutanen za su yi yawa haka ba.

Kina da wani sako ga jama'ar arziki da suka halarci wannan daurin auren na diyarki?

MALAMA BINTA: E, ina da sako. Na gode masu kwarai da gaske a yanda suka yi farin ciki da taruwa wajen nan. (Dariya) Ban zato ba za su yi cikowa haka. Amma na gode ma jama'a sosai da sosai. Alhamdu lillahi.

Kina da sako na musamman zuwa ga Ango da Amarya 'ya'yanku?

MALAMA BINTA: Sakona shi ne Ubangiji Allah ya ba su zaman hakuri. Kuma don Allah su yi juriya da zaman duniya. Kuma su cire kunnuwansu ga mazuga.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin