Daga Balaraba Ramat YakubuA mujallar Fim ta watan Maris, a wannan filin mun buga wata wasika daga wata mai karatunmu mai suna Hauwa'u Bello Mohammed (Mrs. Abba Atiku Hotoro), wadda ta rubuto daga 'Government Day Secodary School', P.M.B. 1035, Wukari, Jihar Taraba. Ta rubuto ne a kan yadda wasu matan suke nuna matsanancin kishi a tsakaninsu da sauran matan mijinsu.
To, ina Malama Hauwa? Ki yi hakuri ban ba ki amsa ba a watan jiya kamar yadda na yi alkawari. Dalili shi ne halin jimami da muka shiga sakamakon rasuwar su Balaraba Mohammed. To, Allah ya jikansu, amin.
Hauwa, ke ce ta farko da kika fara rubuta mini takarda a wannan fili namu na "Rayuwarmu." Na gode kwarai. Allah ya sa sharhin da na yi a baya da amsoshin takardun da zan fara sawa a nan gaba su zama masu amfani ga mata 'yan'uwana, amin. Na gode.
A kan batun kishi din nan da kika yi, a gaskiya kishi kala-kala ne, Hauwa. Akwai na Musulunci irin wanda matan Annabi (SAW) suka yi. Akwai na kwatar kai, sannan akwai na hali.
Kishi irin na matan Annabi da wuya; a yanzu mazajenmu a sami wanda zai kamanta abin da ake yi wa mata a da. Kin ga wannan an share shi.
Kishin kwatar kai kuma shi ne wanda za ki ga cuta ce ta yi yawa har matar ta haukace, ta shiga malamai, ko ta dauki makami don ta kwaci hakkinta.
Kishin hali: Hali kuma wannan bai kankaruwa domin halitta ne a jikin mace. Kuma ko me za a yi mata ba za ta canja halint ba.
Da a ce mata za su yi karatun ta nutsu a harkar kishi, da sun dauki mataki daya wanda za su rike ya zama makaminsu na kai farmaki a kowane lokaci. Wannan matakin kuwa shi ne kissa. Iyayenmu mata da yawancinsu kissa suka rike suka dinga juya maza da ita. Kuma ita karuwai suka dauka ta zame musu takardar digiri a harkar sana'arsu ta karuwanci. An san kishi bala'i ne ga 'ya'ya mata. Amma kissa makami ce ga namij, in kin rike kissa za ki ga dashi mijin da kishiyar duk sai kin mallake su.