Su Alee Baba Yakasai a ofishin Jakaden Nijeriya a Nijar
|
LOKACIN shagulgulan Babbar Sallah da ta wuce wasu 'yan fim daga Nijeriya sun amsa gayyatar da aka yi masu suka je kasar Nijar don sada zumunci da dimbin masoyansu da ke can. Shugabannin tafiyar su ne Alee baba Yakasai, Mudassiru Kasim, Bala ADJ, Tanko Dan Salisu, da wadda ta dauki nauyin tafiyar, Hajiya Amina Mega.
Dalilin shirya ajon na 'yan fim shi ne karrama Firayim Ministan Nijar Hamma Ahmadou bisa nasarar da jam'iyyarsa ta MNSD Nasara ta samu.
Daga cikin 'yan fim da suka je kasar akwai Alee Baba, Mudassiru Kasim, Wasila Isma'il, Abubakar Sani (Iyan-Tama), Usaina Gombe (Tsigai), Katakore, Musbahu M. Ahmad, Sadi Sidi Sharifai, Jamila A. Sadi, Umar B. Hankaka, da Dan Wanzan.
"'Yan Nijar sun nuna mana kauna sosai, kamar a gidanmu," inji mawaki Abubakar Sani. "Saboda soyayyar ne aka kai mu tashoshin yada labarai, domin yi mana wasu tambayoyi a kan wannan harka ta fim." An bukace su su ba da shawarwari kan harkar fim, kuma an yi masu tambayoyi kan wakokin fim wadanda ake matukar so a Nijar.
Jama'ar kasar sun nuna masu cewa duk wani mai harkar fim din Hausa kada ya dubi kudin da yake samu, a'a ya dubi muhimmancin sana'arsa da irin soyayyar da mutane suke yi masa.
Sun yi wasa a birnin Yamai. Suna gamawa sai 'yan birnin Damagaram ma suka ce su ma suna so a je a yi masu. Haka kuwa aka yi. Ba Hausawa kadai ba, har ma Turawan Faransa mazauna Nijar sun nuna kauna ga 'yan fim na Hausa, har suka ba da filin da aka cashe.
'Yan fim din kuma sun kai ziyara a ofishin Jakaden Nijeriya na Nijar inda aka karrama su.
"Gaskiya mun ji dadin wannan tafiya. Al'ummar Nijar sun karbe mu hannu bibiyu. Allah dai ya maimaita mana," inji wani dan wasa.