Mu koma ga Allah
Da Sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai.
Al'ummar Musulmi, assalamu alaikum!
TUN a cikin 1992 aka yi fim na tarihin rayuwar da jihadin Sheikh Usmanu Danfodiyo. Kwararrun masu shirya fim har daga Amerika da Masar sun sa hannu a yin fim din, wanda kamfanin 'Mu'azat International' da ke Kano ya shirya. Sunan fim din dai Nur al-Zaman. A cikin mujallar Fim ta Janairu 2001 na yi wata budaddiyar wasika zuwa ga Gwamnan Sokoto, ina rokonsa da ya yi amfani da matsayinsa don shayar da Musulmi wannan kishi da suke ji a daidai wannan lokaci da Kiristoci ke yin finafinai suna watsa akidojinsu a garuruwan Musulmi da nufin sa masu rauni ga imaninsu; a kuma daidai lokacin da Yarabawa da Inyamurai ke ta shirya finafinai na gumakansu da al'amuransu suna yada su a duniya don tallata al'adunsu a yanayi wanda wasu daga finafinan shirme suke cike da su, kuma a zamanin da al'adar kallo ta shiga jinin Hausawa, inda ta kai yanzu kusan kowane gida babu tsarin wayarwa, fadakarwaa da sadarwa kamar fim.
A kan haka ne na ga ya dace in yi roko da kira ga Musulmi domin shiga addu'a da kamfen domin ganin wannan fim na jihadin Mujaddadi ya fito. An ce wasu jami'an gwamnatin Sakkwato, bisa son rai da rashin kishin al'ummar Musulmi, sun hau bisa fayil na fim din sun yi zaune. Don Allah duk wanda ya karanta wannan sako, to ya ba da gudunmawarsa ta hanyoyi kamar haka:
1. Addu'ar Allah ya fito da wannan fim; duk mai wata aniya ta son rai Allah ya mayar masa da abinsa;
2. Rubuta wasika ga Ma'aikatar Watsa Labaraia Jihar Sokoto zuwa ga Kwamishina da kira a gare shi ya fito da wannan fim;
3. Rubuta makala a jaridu ko magana a rediyo domin kira ga Gwamnan Sokoto ya fito da wannan fim;
4. Bin duk wata hanya wadda ta yi daidai da Musuluni domin ganin fim din ya fito;
5. Kungiyar Marubuta ta 'Writers Bureau' ta rubuta wasika ga Gwamnan Sokoto a kan ya sayar mata da fim din, ita ta kafa gidauniya a saya a sako shi ga Musulmi baki daya.
A rokon a hada da Jihar Sokoto ta sai da fim din idan ita ba a shirye take ba don fitowa da shi. Allah ya taimake mu a wannan aiki na alheri, amin.
·
Malam Danjuma shi ne Mataimakin Edita na jaridar Al-Mizan, kuma marubuci na musamman a mujallar Fim.
|
An yi taron addu'ar Balaraba a Kano
MUTANE da dama sun zubar da hawaye a wani gagarumin taron da 'yan fim suka yi a Kano don yi wa Balaraba Mohammed addu'a.
Taron, wanda aka yi ran 20 ga Maris, 2001, a dandalin 'Fagge Youth Centre', ya samu halartar yawancin 'yan fim.
Tun misalin karfe 4 saura na yamma mutane suka fata hallara a wurin.
An fara bude taro da addu'a daga bakin Malam Zubairu, sai Abdulmunafi Sani ya gabatar da addu'a da kasidar ta'aziyya. Jim kadan da farawarsa bayan ya gama ta marigayi Aminu Hassan, ya fara ta Balaraba kenan sai ga Shu'aibu Lawan ya iso. Zaman Shu'aibu ke da wuya sai hawaye suka zubo fara masa. Kai, ba ma shi ba, hatta sauran ''yan fim da yawa sun zubar da hawaye, cikinsu har da Ladi Mutu-Ka-Raba, Rukayya Umar Santa, Halima Adamu Yahaya; manyan mata Hajiya Umma Ali da Hajiya Balaraba Ramat Yakubu, su ma duk sun kidime.
Shugaban Kungiyar Furodusoshin Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Mandawari, ya yi jawabi, inda ya fadi wasu kyawawan halayen marigayiyar. Ya ce yarinya ce mai hankali da ladabi da biyayya. Ya yi addu'ar Allah ya gafarta mata.
Wasu da suka yi jawabi sun hada da Auwalu Marshal da Dan Magori.
Nura Husaini ne ya rufe taro da addu'a. Yana cikin yi bai san lokacin da ya shiga kuka ba. Kuma ya yi kamar zai fadi, sai da Tahir Fagge da Mu'azzam Boss suka rike shi. Wata yarinya ita ma ta fadi ta yi ta shure-shure saboda bakin cikin rasuwar Balaraba.
|
Editan Fim ya samu haihuwa
RANAR 28 ga Fabrairu, 2002, ne Malama Marakissiyya Ashafa, matar editan mujallar Fim, ta haifi diya mace.
Malam Ashafa a wannan rana ya zo ofishinmu cikin farin ciki, musamman domin wannan ce haihuwarsu ta farko. An yi suna ranar 7 ga Maris, editan ya sanya wa 'yarsa suna Ummu-Salimat. Ganin cewa Ashafa na mu'amala da 'yan fim, mata 'yan yinin suna sun cika gidan makil, musamman don a zatonsu zai gayyato wasu mata 'yan fim su je yinin a unguwarsu ta Rijiyar Lemo da ke Kano.
Sai dai kuma matan sun yi ta mamakin rashin ganin 'yan fim. Mai daukar hoton mujallar Fim, Bala Mohammed Bachirawa, wanda ya ga irin cinkoson matan da suka je gidan, ya tambayi Ashafa dalilin rashin zuwan matan fim. Editan ya bayyana masa cewa ba wani abu ya hana shi kirawo su ba sai don gudun husuma. "Ka ga baya ga mata, yara sun cika kofar gidan su ma don su ga 'yan fim, to idan aka hade da mata 'yan biki da kananan yara da kuma matasan unguwa aka tunkari wata yarinya, idan ba a yi hattara ba sai a ji mata ciwo."
Ashafa ya ce irin wannan yaguda da kuma sauran wasu dalilan da ya yi tunanin za su iya faruwa. "Wannan ne ya sa ban gayyato su ba," inji shi.
Duk da haka jami'ar kasuwancin mujallar a Kano, Sadiya Abdu Rano, ta je yinin suna, ta shige cikin mata 'yan biki aka yi ta daukar hoto da ita, ba su san ita ce jarumar cikin shirin Gagarabadau ba.
Jinjira Ummu-Salimat da mahaifiyarta duk suna nan cikin koshin lafiya. Malam Ashafa ya auri mahaifiyar Salimat a ranar 6 ga Fabrairu, 1999. Ita ce matarsa ta fari.
Allah ya raya Salimat, amin summa amin.
|
Daula ma ya shiga daular aure
SANANNEN dan wasan nan da ke Kano, Dailami Mustapha, ya yi aure.
An daura aurensa da Malama Rashida Mukhtar a ran 8 ga Fabrairu, 2002 a Jihar Bauchi.
Dailami, wanda aka fi sani da suna Daula, tuni suka tare da amaryarsa a Kano.
An fi sanin dan wasan a matsayin mugu a cikin fim, wato bos.
Wannan shi ne aurensa na farko.
Sai dai kash! kwana uku kacal kafin a dauro auren, gobara ta lashe gidan su Dailami da ke Gyadi-Gyadi, Kano. Allah ya mayar masa, kuma ya ba su zaman lafiya tare da Rashida, amin.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin
|
|
| |