Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 29   Mayu 2002
RA'AYI BA GABA BANE


BABBAN SHAFI
Mu Leka Mu Gani
Zuwa Ga Masu Karatu
Wasiku
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 1
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 2
Rayuwarmu
Mu Leka Hollywood
Malam Zurke
Mutanen Boye
Bukukuwa
Sauran Labarai
Ra'ayi Ba Gaba ne
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka Akwai:
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da ra'ayin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


Alh. Magaji SulaimanMartani:
Shin Ibrahim Shemen da na sani ne kuwa?

Da ALH. MAGAJI SULEIMAN

WANI fitaccen sha'iri, wanda shekaru da dama da suka gabata ya koma ga Mahaliccinsa, ya ce, 'In za ka fadi, fadi gaskiya, komi ta ka ja maka ka biya."

Dahilin da ya sa na fara rubutun nan nawa da wannan baiti shi ne, ina sa ran duk bayanin da zan yi a nan gaba ya kasance gaskiya zan fadi, ba shaci-fadi ko gugar-zana ga wani ko wasu ba, amman zai iya zama kasanawa. Bayanin ya zama tsumangiyar kan hanya wadda take zama mai fyade babba da yaro, musamman yaron da ya zama mai kunnen kashi.

Da farko, a watan Maris 2002, na sayi mujallar Fim, da nufin in yi wa mujallar karatu tamkar yadda makauniya take cin dafaffen kwai in ya je ga hannunta. Amma sai tsautsayi ya sa na fara karo da wata kasida da a filin "Mu Leka Mu Gani." Ga dukkan alamu, fitaccen dan jaridai nan ne, kuma kwararren marubuci, ban yi kuskure ba in na kira shi da sunan fitaccen furodusa; shehin masu wallafa mujalla, wato Malam Ibrahim Sheme, ya rubuta kasidar.

Kash! da farkon rubutun da Malam Ibrahim Sheme ya yi, a shafi na biyu na wannan mujalla, ya yi dogan sharhi mai kama da abin nan da Hausawa ke ce wa "yabon kai," amma sai na fahimci cewar, kila Malam Ibrahim Sheme ya yabi kansa ne domin kila yana tunanin jama'a, musamman masu karatun mujallar, ba za su yaba masa ba. Sai na tuna da cewar Gamji Dan Kwarai, a lokacin da ya ke bikin bude kamfanin New Nigerian a Kaduna, ya ce wa 'yan Arewa, "In ba ku hura kakakinku ba to, ba wanda zai busa maku shi." In an duba wannan magana kila ba za a ce yabon kai ya zama jahilci ba.

Kwatsam, ina cikin karatu, cikin annanshuwa da amincewa da zancen da nake karantanwa, sai na yi karo da wata shedara, da na yi zaton ba ta da tsawo, na yi tunanin ba ta da tsawo ne, domin maganar da aka fara bude shedarar, wato maganar finafinan Hausa, da a yau, ban yi kuskure ba, in na ce Malam Ibrahim Sheme shi ma furodusa ne, kuma mai ba da babbar gudummuwa a wannan fage na rubutun labaran da ake mayar da su wasannin kwaikwayo, da wasu ke gani a fayau, wato cikin sauki, ba tare da sanin dimbin matsalolin da masu shirya wasannin ke fuskanta ba, daga fara wasan zuwa fitar wasan zuwa ga jama'a.

A dalilin karanta wannan kasida da na yi, a takaice, na tsaya tsafi na tambayi kaina, shin Malam Ibrahim Sheme ne da na sani ya rubuta wadannan nan kalamai kuma da zan iya kiransu da batanci mara tushe da aka yi wa Malam Ibrahim Sheme ko kuma in ce aka yi wa duk wani mai tinkaho da shirya finafinan harshen Hausa?

Kuma ina ganin ya dace in yi tambayar cewar, shin Malam Ibrahim Sheme da na sani ne, ya amince aka rubuta sunansa a wannan rubutu ko kuma ince shin Malam Ibrahim Sheme ne ya rubuta wannan kasida da kansa, wanda ya zama tamkar wadda ta dan zubar masa da burbushin mutumcin da yake da shi?

Kamar yadda Malam Ibrahim Sheme ya ce duk rubuce-rubucen da aka yi, ko ake yi a halin yanzu, ba a yin su da nufin durkusar da shirin fim ba, a'a, ana yin su ne domin habaka wannan shiri. Babu shakka, na ji duk abin da aka ce, kuma na amince, "wai in Allah ya shirya ni zan rama." Amma in an dubi wani bayani da aka fadi a gaba, za a iya cewa akwai wata boyayyar manufa da ba a fitar da ita ba, wadda a takaice take nufin yin fito-na-fito tsakanin masu shirin finafinan Hausa da wasu da suke ganin dimbin kurakuran da ake yi a fagen gudanar da shirin finafinai a yau.

Dalilin da ya sa na ce akwai zunde cikin duhu da ake yi wa masu shirin wasannin fim shi ne a inda ya ce, "... in da a ce za mu rika tona dukkan abin da muka sani yana faruwa a shirin fim, to tunda dai an daina kife kasa da babu shakka za a hana harkar baki dayanta ko kuma mutane su tsani masu yin harkar."

Mai karatu, duk wanda ya san Malam Ibrahim Sheme, ya san shi a matsayin kwararren dan jarida mai kuma sanin menene fim, kuma wasu matsaloli da hawa-da-gangara ne masu shirya finafinan Hausa ke fuskanta, amma sai ga shi za a iya cewa ya dauki wuka, ya daba wa cikinsa domin shi kansa ya fitar da fim mai suna Gagarabadau. Ashe kwamacala da dimbin kurakuran da ake tafkawa, shi ma yana ciki kenan, tunda a cikin rubutun da ya yi bai ce wasu farodusoshi ba, sai ya ce duka.

Wata shedarar da zan iya cewa ta darsu a zuciyata, ita ce da ya ce, "A cikin shekaru uku din nan tone-tonen da za a ce mun yi, ba su kai ko cikin cokali ba na kogin abubawan ashshan da ake tafkawa a shirin fim." A nan ma, yarfen da ya yi, ban yi kuskure ba in na ce kurakuran da ya ce ana yi ta shafe shi, domin ai wanda ya shirya fim, har ma ya fita jama'a suka kalla, to shi ne furodusa. To, yaya matsayin Malam Ibrahim Sheme kenan, tunda shi ma ya shiga sahun wadanda suka fitar da fim, ba sau daya kawai ba?

Ina ganin dole in tuna wa mai karatu zancen nan da aka ce "makaho bai san ana ganinsa ba, sai an taba shi." Tunda Malam Ibrahim Sheme ga dukkan alamu ya nuna ba shi cikin masu tafka asshan, amma ina sa ran yana cikin wadanda in sun ga wani dan'uwansu yana tafka aika-aika ko ashsha, zai jawo hankalin dan'uwansa kan abin da yake aikatawa. Kuma a matsayinsa na wanda ya san bambancin gabas da yamma, ya kuma san bambancin Alhamis da Juma'a, ba zai riki wani dan'uwansa a zuciya ba, kan wani aiki mara kyau da ya fahimci dan'uwansa yana aikatawa. Ai sai dai ya fito ya fadi gaskiya, in kuma an ce ya yi tonon silili ne, to shi dai tsarkake zuciyarsa ya yi.

Kuma mu dubi magana ta gaba da Sheme ya yi, cewar "masu shirin fim jahilai ne ta fuskar wayewa." Da farko ya dace mu tambayi kanmu: wanene jahili? Ina ganin mai sana'ar yin tukunya da mai sana'ar fasa dutse, duk suna daukar wanda bai iya wannan sana'ar ba, jahili ne. ballantana wanda Allah ya taimake shi, ya yi karatun zamani shi ma cewa yake yi, duk wanda ba shi da ilimin zamani, jahili ne.

To, a dan nawa kwaryar- kwaryan tunanin, duk wata sana'a ko ilimin da ba ka sani ba, za a iya kiran wanda bai sani ba jahili, a wani fagen kuwa amma ba a ce masa shi jahili ne gabansa. Tunda duk wani mutum (mace ko namiji), in ka same shi bai iya karatu da rubutu ba, to za ka same shi ya iya wata sana'ar da zai sami abin da zai sa ma bakin salati.

A dai wannan kasidar an ce, akasarin masu shirya finafinan ba su san 'Intanet' ba. To, wai ma shin, yaushe ne wannan abu 'Intanet' ta kutso kanta kasar nan? Kuma ina ganin, mutumin da yake kauyen da babu wutar lantarki, ta wace hanya ce zai san 'Intanet'? Ina ganin, in mutum ya bar garinsu da wuri, ya koma birni, ya sami wurin da ya je daga cin rani ko kabar-raba, daga nan sai ya san 'Intanet' kila ma da yadda ake amfani da shi. Amma da Allah ya yi zamansa a kauye ne, to ta wace hanya ce zai bi ya san 'Intanet'?

Kuma in mun duba akasarin wadanda suke kallon finafinan Hausa, kashi nawa ne cikin dari suka san 'Intanet'? Kila mai karatu ya ce kashi 75 cikin dari, to ashe babu mamaki in akasarin masu shirya finafinan ba su san 'Intanet' ba, domin wadanda suke nishadantar da su ko ilimantar da su ko fadakar da su, ba su san 'Intanet' ba a ido, ballantana a ce sun mallake ta.

A karshe, ina ganin lokaci ya yi da Malam Ibrahim Sheme da sauran masu hali irin nasa, na yin kutungwila ga masu shirya finafinai da su fito karara da duk wasu kura-kurai da suka gani. Ta haka, zai a gyara kurakuran da ake yi. Amma soke-soke da nuna hassada da bakin ciki, Dankwairo ya ce, "ba zai hana mai rabo ya yi ba" tunda da mai shirya wasa da mai rubuta labari domin ya sayar, duk sako suke kokarin aikawa ga jama'ar da suke kaunar abin da suke yi. Ta hanyar aikawa da sakon ne ake samun ribar da in ta taru, sai a fara tinkaho.

*Alhaji Magaji Suleiman furodusa ne kuma darakta. Shi ne shugaban kamfanin shirya finafinai na 'Sulson Films' da ke Tudun Wada, Zariya, Jihar Kaduna.

Ya aiko da wannan sharhin ta hanyar Intanet, ta yin amfani da adireshinsa na i-mel, wato sulsonfilms@yahoo.com

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin