Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 30   Yuni 2002
RA'AYI BA GABA BANE


BABBAN SHAFI
RA'AYI
Zuwa Ga Masu Karatu
Wasiku
Balaraba Muhammad (1983-2002) 
Rayuwarmu
Duk Sun Yi Aure
Malam Zurke
Ra'ayin Mujallar Fim
Bukukuwa
Sauran Labarai
Ra'ayi Ba Gaba ne
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka Bangon FIM ta 29
Bangon FIM ta 28
Bangon FIM ta 27
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da ra'ayin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


Bukatar mai da littattafan Hausa zuwa finafinai

Daga HALIMA UMAR GIADE

Anti Bilki
Bilkisu S. Ahmad Funtua
BA shakka a tun lokacin da duniyar finafinan Hausa ta fara bunkasa aka samu raunin tasirin littattafan Hausa, koda yake ba wai bunkasar littattafan Hausa ta dakushe ba ne, a'a, sai dai ba kamar da ba. Ba wani abu ne ya jawo hakan ba illa ganin cewa wadannan finafinan su za a gan su ne a zahiri a kuma ji abin da ake fada, ba wai sai mai ilimi ba kawai har ma maras ilimi ya san me ake nufi. Su kuwa littattafai, in dai ba karatu mutum ya iya ba, to a gaskiya ba zai san amfaninsu da manufofinsu ba.

To tambayar a nan ita ce, me ya sa ba za a dinga kokarin maida wasu ingantattun littattafan Hausa zuwa finafinai ba?

Amsar a bayyane take karara. Na farko shi ne wasu marubutan ba su da halin daukar nauyin shirin fim din yayin da wasu kuwa ba su da damar fita ne su tsaya tsayin-daka su shirya abinsu, musamman mata, saboda ba su san kan harkar ba ko kuma igiyar aure da ke kansu ta hana su. Amma alal hakika da a ce za a dinga dauko irin littattafan da hazikan marubutanmu ke rubutawa ana maida su fim, to na tabbata da abin ya yi armashi. Abin da ya sa na ce haka kuwa shi ne a gaskiya labarun da marubuta ke sawa a cikin littattafansu sun sha bamban da wadanda furudusosi ke amfani da su wajen shirya fim. Zan ba da misalai da dama a kan haka. Farko shi ne, akwai wani littafi da fitacciyar marubuciya Bilkisu Salisu Ahmed Funtuwa (Anty Bilki) ta rubuta mai suna Ki Yarda Da Ni wanda aka maida shi fim. Karbuwar da ya samu a ko'ina cikin fadin kasar nan abin ba a magana. To amma sai aka fara yi mata kafar-Kano a fim dinta na biyu, Sa'adatu Sa'ar Mata, wanda yake shi ma littafi ne mai ma'ana, don ganin cewa na farkon ya karbu.

Muna da marubuta da dama da suke son watsa manufofinsu a ko'ina a cikin duniya, wadanda za a amfana da su, amma rashin irin wannan hanya ta watsa manufofi ta hanyar finafinai ya sa ake ganin kamar shirme suke yi. Idan ba a manta ba, muna da hazikan marubuta maza da mata wadanda idan suka tsaro maka labari sai ka san akwai ajiyar Allah a wajen. Misali ita ce Hajiya Bilkisu S. Ahmed Funtuwa, tauraruwar marubuta, hazika, kuma jaruma ta kowanne fanni. Wannan baiwar Allah tana tsayuwa tsayin-daka ta tsara labari mai tsayawa a rai wanda ya kunshi zamantakewar rayuwa ta tsarin addini da kuma al'adu masu kyau. A koda yaushe burin irin wadannan marubuta shi ne su ilimantar, su tunatar, su kuma nishadantar da jama'a hanyar wa'azi da siyasa. Marubuta suna taka muhimmiyar rawa wajen nuna yadda mata za su yi ingantacciyar rayuwar aure da mazajensu, da yadda za a bai wa 'ya'ya tarbiyya. Kai, a takaice dai suna nuna zamantakewar kyakkyawar rayuwa.

Akwai littattafai na wasu hazikan marubutanmu wadanda mu makaranta za mu so a ce an maida su fim don wadanda ba su iya karatu ba su ma su karu da abin da muke karuwa da shi a cikin littattafan. Misali daga cikin littattafan marubuciya Bilikisu S. Ahmad akwai irin su Matsala A Yau wanda yake magana a kan maza masu cin dukiyar haram ta gwamnati a yayin da suke bauta wa gwamnatin. Sai kuma aka yi dace da kamilar mata da kuma taimakon uwa tagari wadanda suka taimaka sosai wajen tunatar da wannan bawan Alhah ba tare da sun damu da yawan arzikin da yake yi masu facaka da ita ba. A gaskiya koyarwar da kuma tunatarwar da cike da wannan littafi, musamman a kan mata don su dinga kula da mu'amalolin mazajensu a wajen harkar dukiya da amana don kada su fada halaka, ba karamin taimakawa zai yi ba idan ya zama fim.

Bayan wannan akwai littafin marubuciyar mai suna Hattara Iyaye wanda yake magana a kan iyaye masu tsattsauran ra'ayi sabanin ka'idar Musulunci, da kuma illar kai yara 'yan mata karatu kasashen waje ba tare da sa ido ba. Bayan wadannan akwai rubutattun littattafan Anty Bilki da dama wadanda ba za mu iya biyanta ba sai dai mu bi ta da addu'ar Allah ya sa ta gama da duniya lafiya, Aljanna ta zama makomarta, amin.

Idan na dawo kan sauran marubutan, su ma akwai gagarumar gudunmawar da suke bayarwa. Akwai irin su Rahma Abdulmajeed, marubuciyar Ha'inci Ko Kauna, Me Ye So?, Wa Ya Fi Kishi?, da kuma Za Ta Iya wanda yake shi ma salonsa daban, wanda na tabbata idan ya rikide zuwa fim zai amsu kwarai da gaske. Akwai irin su Saliha Abubakar Zariya wadda ta rubuta Zumuncin Zamani, da kuma wata sabuwar marubuciya wato Baturiya, wacce ta yi wani littafi mai suna Hanan wanda yake magana a kan tsantsar talauci da mutanen karkara ke fuskanta da irin taimakon da ya kamata a dinga ba su. Idan ba a manta ba, gwamnati ma da kanta ta bullo da wani sabon tsari a kan irin wannan matsala, wato Poverty Alleviation Programme. To hakika shi ma wannan littafi akwai bukatar ya zama fim.

Maje
Maje El-Hajeed Hotoro
Sauran marubutan su ne Lubabatu Ya'u wadda ta yi So Shu'umi, da Sa'adatu Baba Ahmad wadda ta yi Yi Wa Kai, da dai sauransu. To alal hakika da za a taimaka wa marubuta da karfi da an kai wani mataki da ba a yi tsammanin finafinan Hausa za su kai ba. To amma sam ba a kulawa da ci-gaban da suke son kawowa a wannan harka don an ga cewa yawanci ba su san kan harkar ba, idan kuma suka ba da wuka da nama sai a cuce su. Su kuma marubuta maza irin su haziki Maje El-Hajeej, Nazir Ahmad Salih, Habib Hudu Darazo, da sauransu, ya kamata su mike a dama da su kamar yadda Bala Anas Babinlata ya mike, don a gaskiya su Maje ba za mu manta da su ba wajen bunkasa rubutun Hausa.

To ni dai ina ganin tunda sauran furodusohi ba za su iya taimaka wa hazikan marubuta don su kai gaci ba, watakila saboda kyashi ko wasu dalilai daban, to ai ga wasu shahararrun marubutan sun shigo fagen shirin fim wadanda sun san amfanin a taimaka wa wasu su ma su shigo harkar, kuma na san ba za su yi kyashi ba. Masu mujallar Fim da ku nake kuma furodusoshin Gagarabadau. Don Allah ku kam kada ku sa kyashi, ku tsaya tsayin-daka ku taimaka wa marubuta su watsa manufofinsu don mu kara samun ingantattun finafinan Hausa. ·

Malama Halima Umar Giade daliba ce a Sashen Koyon Aikin Jarida (Dept. of Mass Communication) a Jami'ar Bayero, Kano.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin