MUN riga mun dan ba da labarin yanayin soyayyar da ke tsakanin marigayiya Balaraba da Kumurci tun a Fim ta watan jiya.
Za ka iya kiran Shu'aibu da Balaraba da lakabin Laila da Majnun, ko Romiyo da Julet. Dalili kuwa shi ne matasan biyu sun shaku da juna sosai, har ta kai barci kadai ke raba su. Balaraba takan je gidan su Shu'aibu ta rika taya mutanen gidan wasu 'yan aikace-aikacen gida. Duk mutanen kusa da gidan sun san ta. Hakanan a cikin gari tare ake ganinsu a koda yaushe a cikin tasi da sukan yi shata tana yin zirga-zirga da su.
Mafi yawan finafinan da Kumurci ke ciki akan gayyaci Balaraba; hakanan ita ma a nata akan gayyace shi. Inda babu shi a ciki yakan raka ta. Ita ma takan je ta sa shi a gaba a wurin shirin fim din da babu ita, sai an gama su taho tare. Akwai wani daukar fim da suka je har Shu'aibu ya so tafiya ita kuma ta hana shi. Da ta fuskanci kamar zai sulale idan ta je yin scene, sai ta kulle shi. Haka Kumurci ya kasance a rufe har sai da ta gama daukar fim din a ranar. Wani da aka yi abin a gabansa ya shaida wa Fim cewa, "Wallahi ko abinci ma sai dai ta taga aka mika wa Shu'aibu ya ci."
Wata rana kuma ana daukar fim din Kacibus na 2, Balaraba ta rika yin magiya cewa don Allah a yi sauri a kammala domin lokacin haduwarsu da Kumurci ya yi. Ranta ya baci matuka ganin an dan bata lokaci. Ana cikin haka ne kuwa sai ga Shu'aibu ya dira wurin har ya gaji da jira ya biyo sawunta.
Ba a taba ganin soyayya irin ta Laila da Majnun, da kuma Romiyo da Julet ba a tarihi. Haka a shirin fim namu na Hausa, ba a taba ganin soyayya irin ta su Kumurci ba. An yi korafin cewa wai Laila da Majnun, da kuma Romiyo da Julet "ba su dace ba." Haka ma su Kumurci. Su duk wadancan masoyan ba su auri junansu ba suka mutu. Su ko su Kumurci sun yi aure, to amma amaryar ta rasu kafin ta tare.
Allah ya jikanta, amin summa amin.