ZUWA GA MUJALLAR FIM,
DON Allah ku isar mani da sakon ta'aziyyata ga mahaifin Balaraba, Malam Muhammadu Kaura, da mijinta Shu'aibu Lawan (Kumurci), da dukkan danginta, da ''yan fim baki daya, da ku mujallar Fim. Ubangiji ya gafarta mata zunubbanta, ya sa ta a Aljanna, amin summa amin.
Ku kuma da na lissafa a sama, Allah ya ba ku hakurin rashinta. Ni dai na zo Kano mun sadu da Shu'aibu a Sabon Titi daidai kofar shagon Ishaq Sidi Ishaq, muka yi hotuna, har yake gaya mani in zo bikinsa bayan Sallah. Na ce da shi insha Allahu zan zo bikin. Ya ce da ni, "Ba ji!" Allah ya ce, "Kulli nafsin za'ikatul mauti."
A karshe, ina so in tambaye ku: ainihin wace 'yar wasa ce ta yi sata a gidan su Balaraba kamar yadda kuka bayyana a Filin Malam Zurke a Fim ta watan Mayu? Kun san Hadiza da yawa a Kano; ni akwai wata ma da nake son wasanta har na same ta a gida muka dau hoto. Ku fayyace mana don kau da waswasi. Na biyu, Zurke ya ce N20,000 ta sata, amma a wani wajen na ga kun rubuta N2,000 ne ta sata. Ku wayar mani da kai.
TK Mohammed Sulaiman,
Sakataren Garkuwa Drama Club, P.O. Box 98, Akwanga, Jihar Nasarawa. Tel.: 047-20738
...SHU'AIBU, KA SO TA HAR ABADA!
INA fata wannan mujalla mai farin jini za ta ba ni dama in mika ta'aziyyata zuwa ga Shu'aibu Lawan (Kumurci) a kan rasuwar masoyiyarsa Balaraba. Allah ya jikanta, ya gafarta mata, amin.
Ga wata 'yar magana da nake so na fada wa Shu'aibu. Shu'aibu, tunda dai Balaraba tana sonka dari bisa dari, to sai ka buda zuciyarka ka shirya wata irin rayuwa ta har abadan abadin tare da ita, daga nan har iyakar ranka. Za ka iya yin tambaya ka ce, ko me ya sa na fadi haka? Na fadi haka ne saboda ita mutuwa ba ta yanke kauna ta hakika, sai dai ta kara dankonta. Kuma idan ka yi tsawon rai za ka ce hakika Amina Abdulmaik ta fadi gaskiya.
Saura da me? Shu'aibu, ka fa tauna goro cikin turare. Sai ka tambaye ni makari! Wassalam.
Amina Abdulmalik.
(Marubuciyar littafin Ruwan Raina), Abuja.
...ALLAH YA BA SU HAKURI
INA son in mika sakon ta'aziyyata ga iyayen Balaraba da Shu'aibu. Allah ya ba su hakurin wannan rashi. Da fatan duk wani Musulmi zai yi mata addu'a. Ku kuma Allah ya kara maku karfn aiki da fadin gaskiya.
Aliyu Mohammed, P.R.O., Garkuwa Drama Club, P.O. Box 98, Akwanga, Jihar Nasarawa.
... YA DACE A YI MATA GIDAUNIYA
INA so in nuna goyon baya ga shawarar da Ibrahim Sheme ya kawo ta a kafa gidauniya saboda Balaraba. Idan 'yan fim suka yi haka sun taimaka wa iyayenta, sun kuma kara wa harkarsu martaba. Hakika wannan kalubale ne ga dukkan shugabannin kungiyoyin masu shirya finafinan Hausa da kuma dukkan 'yan wasa.
Idan aka sa wannan asusu a hannun amintattu, za a iya samun wadanda za su ba da tasu gudunmawar, har ma da ni a ciki. Domin muhalli ba karamin muhimmanci yake da shi ba a rayuwa. Duk wannan ya nuna cewa Sheme yana kishin harkar fim kwarai.
Al-Mustapha Idris Mohammed Koko,
P.O. Box 11335, Kano. Tel.: 064-649293, 632297; GSM: 080-23047611
...KUMURCI KA YI TAWAKKALI
NA rubuto wannan wasikar ne domin na mika ta'aziyyata ga 'yan'uwan Balaraba. Ina mai fatan Allah ya jikanta, ya kuma gafarta mata, ya sa Aljanna ce makomarta, amin.
Zan yi amfani da wannan dama in yi kira ga Shu'aibu a kan faruwar wannan al'amari. Kumurci, ka sani Allah (SWT) shi ya sanya soyayya tsakaninka da Balaraba, kuma ya yi nufin kulluwar aure a tsakaninku. Amma Allah bai yi nufin ku yi zaman auren ba. Saboda haka ka yi hakuri da faruwar hakan, kuma ka yi addu'a ga Allah (SWT) da ya saka maka da mafi alheri. Domin kuwa haka Annabi (SAW) ya yi mana horo da umarni da cewa idan wani abin damuwa ko na bakin ciki ya faru gare ka, to ka yi tawakkali kuma ka yarda da kaddara, sa'annan ka yi fatan da addu'a Allah ya saka maka da mafi alheri.
Daga karshe ina taya zabiyar 'yan fim Rabi Mustapha murnar samun miji. Allah ya ba da zaman lafiya, amin.
Kabiru Adamu Iliyasu (Kaicy),
Unguwar Fulani, Wudil LGA, Jihar Kano.
...ALLAH YA YI MATA RAHAMA
ZA mu so mu yi amfani da wannan dama domin yin ta'aziyya ga iyaye, 'yan'uuwa da dukkan abokan sana'ar Shu'aibu dangane da rashin da aka yi na Balaraba. Da fatan Allah ya yi mata rahama da gidan Aljana Firdausi, amin.
Aminu Rabiu TaIlor (Fege)
Malumfashi Ventures, M9 Ibrahim Taiwo Road, Kasuwar Barchi T/Wada, Kaduna.
... KUMURCI KA DAU HAKURI
INA isar da sakon ta'aziyyata ga iyayen Balaraba da kuma mijinta. Allah ya jikanta, ya yafe mata. Kumurci, na san dole ne ka damu sabo da wannan babban rashi da ka yi. Amma ka daure, ka kwantar da hankalinka. Don kuwa wannan ya nuna Ubangiji yana sonta da rahamarsa. Ubangiji ya yi mata rahama. Kai kuma Allah ya ba ka dauriyar rashi. Allah ya ba ka wata, amin.
Aliyu Matazu,
CC.6 Dabban Road, U/Sanusi, Kaduna.
...ALLAH YA FI MU SON TA
ALLAH ya gaya mana cewa dukkan rai zai dandana mutuwa. To Allah ya fi mu son Balaraba kuma ta mutu a kan hanyar raya sunnar Annabi (S.A.W.). Don haka muna fatan Allah ya gafarta mata, ya sa Aljana makoma ce a gare mu baki daya.
Shu'aibu, ka yi hakuri. Allah kuma ya ba ka misalinta. Kuma iyayenta da ke nan Kaduna Allah ya kara muku dogarar Musulunci, kuma Allah ya ba kawaye da masoyanta irinmu hakurin rashinta, Allah ya jikan dukkan 'yan'uwa Musulami tun daga zamanin Annabi Adam (A.S.) zuwa yau, amin.
Aunty Shaw, Adama Halima Abdulkarim,
No. B13 Yola Road by Ibrahim Taiwo Road, T/Wada, Kaduna.
ALLAH JIKAN DUKKAN MUSULMI
INA so in yi amfani da wannan dama domin in mika gaisuwar ta'aziyyata ga Shu'aibu da iyayen Balaraba da kuma dukkan masoyan Balaraba a kan wanan rashi da muka yi nata. Allah ya jikanta ya gafarta mata. Kuma dukkan wadanda suka riga mu gidan gaskiya tun daga zamanin Annabi Adam har ya zuwa yanzu, Allah ya jikansu, idan kuma tamu ta zo, Allah ya sa mu cika da imani, amin.
Muhammad Sunusi Abdulmalik,
No2/12 Kankiya Road, U/Shanu, Kaduna.
ALLAH YA BA SHU'AIBU WATA
A MADADIN 'yan'uwa da abokai, ina mika sakon ta'aziyyata ga iyaye, 'yan'uwa da kuma angon Balaraba, Shu'aibu. Allah ya jikan Balaraba kuma ya rahamshe ta, ya ba 'yan'uwanta hakurin rashinta. Shi kuma Allah ya ba shi wata mafi alkhairi, amin.
Muhammed Rabi'u Usman,
AM 3, Abuja Road, Kaduna.
... INA CIKIN BAKIN CIKI DA ALHINI
INA matukar nuna bakin cikina da kuma alhini zuwa ga Shu'aibu, iyayen Balaraba, masu shirin fim, da kuma duk masoyan Balaraba da 'yan'uwanta da suka rasu. Allah ya jikansu, ya kuma sa su a Aljanna Firdausi domin alfarmar Manzon Allah (S.A.W.).
Shu'aibu sai ka dau hakuri, Allah kuma ya musanya ma da wata kamarta, amin.
Kabiru L. Chiranchi,
P.O. Box 14408, Gwale L.G.A., Kano.
...KARSHEN WAHALARSU KENAN
A MADADINA da dukkan mutanen gidanmu, ina mika sakon ta'aziyya ga dukkan 'yan diramar Hausa a kan rashin da muka yi. Allah ya jikanta, ya gafarta mata, ya haskaka kabarinta, amin. Ina so in yi amfani da wannan damar domin in mika sakon ta'aziyyata ga mijin wannan jaruma da kuma iyayenta da dukkan masoya da abokan arziki. Allah ya sa karshen wahalarsu kenan, amin. Mu kuma Allah ya ba mu hakurin jure wannan rashi da muka yi, ya ba iyaye da mijinta da dukkan 'yan wasan Hausa hakurin wannan rashi.
Halimat Bintu Muhammed,
Daliba a makarantar Salamatu Kabir da ke Sardauna Crescent, Bashama Road, Kaduna.
...ADDU'A CE BABBAR KAUNARTA
GA gaisuwarmu ga iyayen Balaraba da mijinta Shu'aibu. Allah ya mayar masa da alherinsa. A gaskiya rasuwar Balaraba akwai alamun samun rahama Allah tare da ita. Domin Allah cikin ikonsa bai karbi ran ta ba sai da ya nufe ta da yin aure. Don haka ina kiran masu kaunarta da cewar yanzu addu'a ita ce babbar kaunar Balaraba. Allah ya jikanta, amin. Ina so a mika ta'aziyyata ga Ibrahim Mandawari da Ishaq S. Ishaq da sauran 'yan wasa maza da mata. Allah ya jikanta tare da 'yan'uwanta da suka rasu. Allah ya kyauta namu zuwan, amin!
Labaran Mustapha Mohd Dan Kari,
No. 25 Ciranchi Quarters, along Gwale Road, Kano City.
... ALLAH YA SAKA SU A ALJANNA
MUNA mika ta'aziyyarmu ga dukkan ma'aikatan mujallar Fim, da kuma dukkan 'yan wasan fim din Hausa, musamman Kano da Kaduna, a kan rasuwar 'yar'uwarmu kuma kanwarmu, kuma matar dan'uwanmu, masoyinmu, Shu'aibu Lawan (Kumurci), Malama Balaraba Mohammad Kaduna. Allah ya jikanta da duk 'yan'uwa da wannan hadarin ya rutsa da su, ya gafarta masu kurakuransu, ya sa Aljanna ce makomarsu. Sannan muna mika ta'aziyyarmu ga iyayenmu (watau mahaifanta). Allah ya kara mana hankurin rashin, mu kuma ya sa mu yi kyakkyawan karshe, amin.
Ciyaman da Sakatare,
Gamji Drama Group, c/o Muhammadu Awwal Umar, P.O. Box 203, Kontagora, Jihar Neja.
... GAISUWA GA SHU'AIBU
NA rubuto muku wannan wasikar ne domin in mika gaisuwar ta'aziyya ga Shu'aibu a kan rasuwar matarsa. Allah ya jikanta, ya gafarta mata, amin.
Abdullahi Hassan,
School of Soccer, P.O. Box 58, Middlesex Street, London.
...ALLAH BA SHU'AIBU JURIYA
INA mika sakon ta'aziyyata ga iyayen Balaraba da angonta Shu'aibu. Allah ya sa ta huta, amin. Shi kuma angon Allah ya ba shi hakurin juriya. Mu ma Allah ya sa in tamu ta zo mu cika da imani. A karshe ina mika sakon ta'aziyya ga ma'aikatan wannan mujallar mai farin jini, wato Fim.
Musa Bello Jada Adamawa,
Okigwe, Jihar Imo.
...Allah ya rahamshe su
ALLAH ya yi wa wadannan mamatan rahama, ya jikansu, ya ba iyalansu hakurin juriya da wannan babban rashi da muka yi baki daya. Mu kuma in tamu ta zo Allah ya sa mu cika da imani, amin.
Ina mika gaisuwa ga Shu'aibu. Allah ya ba shi dangana, ya mayar masa da mafi alkhairi.
Balaraba Datti Abubakar,
Rijiyar Lemo, Kano; Tel.: 064-644872 ko 646596
... A BA SHU'AIBU KANWARTA
SANNUNMU fa! Sannunmu fa!! Sannunmu fa!!! Wannan rashi da muka yi ba rashin mutum biyu ko uku ba ne, har ma da mu masu kallo. Allah ya gafarta mata, ya sa Aljanna ce makomarta, amin summa amin. Allah ya bai wa Shu'aibu hakurin jure wannan rashin.
Ga shawara ga iyayen Balaraba: Don Allah in Balaraba tana da kanwa wadda ta kai aure, a ba Shu'aibu ya aura.
Malam Kawu Jalingo,
Tudun Wada Ward, Jalingo, Jihar Taraba.
ALLAH YA HADA SU A ALJANNA
MUN rubuto maku wannan wasikar ne domin rashin masoyiyarmu Balaraba Mohammed, ko mu ce Balaraba Shu'aibu domin Allah ya sa ta cika da igiyar auren dan'uwanmu Shu'aibu. Da muka sami labarin mutuwarta wallahi daya daga cikinmu kuka kawai ta dinga yi. Yaranmu kuwa ga baki dayansu suka tafi gidan makwabcinmu Ashafa (editan mujallar Fim) domin sun fi son su ji daga bakinsa.
Wallahi mun fi tsawon kwana uku ba mu da aiki sai zancen Balaraba da kuma yi mata addu'ar Allah ya jikanta, ya sa ta yi dace da rahamarsa, kuma ya jikan sauran 'yan'uwanta da al'ummar Musulmi amin.
Muna yi wa iyayenta gaisuwa. Allah ya ba su dangana. Gaisuwa ga Shu'aibu. Duk mai rai dai yana tare da mutuwa. Allah ya ce, "Kulli nafsin za'ikatul mauti." To, Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi tsakaninsu, amin. Allah ya hada su a gidan Aljanna, kuma ya ba shi wadda za ta kwantar masa da hankali. "Innal laha ma'as
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin