TUN lokacin da Allah (SWT) ya dauki ran shahararriyar 'yar wasa Balaraba Mohammed da wasu danginta, dubban mutane suke ta yin addu'ar Allah ya jikanta, kuma ya bai wa magadanta da masoyanta jimirin jure rashin. Mujallar Fim ta kasance fagen da mutane ke mika sakon gaisuwarsu a kan rasuwar; an bugo waya, an rubuto wasiku, an yo aike, an zo da kai...
A Fim ta watan jiya mun ba da filin wasikun masu karatu ga dimbin masu yin ta'aziyyar su Balaraba. Kadan kenan muka buga. Akwai daruruwan wasikun ta'aziyya wadanda in muka ce za mu ci gaba da buga su, to za a shafe watanni ba su kare ba. Haka kuma mun yi la'akari da cewa akwai yawan maimaitawa na kalaman da wasikun suke dauke da su, domin dai duk magana daya ce: wato rasuwar Balaraba. Saboda haka muka yanke shawarar mu buga sunayen wasu daga cikin mutanen da suka aiko da sakwannin ta'aziyyarsu ga magada da masoyan marigayiyar. Mun lura cewa wasu wasikun suna dauke da shawarwari na musamman ko goyon baya kan wani batu, to amma kuma mun lura cewa yawancin shawarwarin mun mun buga su a wasu wasikun a watan jiya. Misali ita ce shawara tare da goyon baya da wasu masu karatu suka bayar kan a kaddamar da Gidauniyar Tunawa Da Marigayiya Balaraba. To, mun gode da wannan goyon bayan da jama'a suka bayar, kuma za mu mika shawarwarinsu ga Kwamitin Tunawa Da Balaraba wanda har ya fara aikinsa.
A nan kasa ga jerin sunaye da adireshin wasu da suka aiko da wasikun ta'aziyya wadanda ba mu buga a watan jiya ba. Muna godiya ga duk wanda ya aiko da sakon ta'aziyya, tare da ba da hakuri ga duk wanda bai ga sunansa a jerin da ke kasa ba.
Sauran shafukan wasiku mun ba da su ga masu rubutowa kan wasu al'amuran na shirin fim. Ahmed Yakubu, Muhammed Sani da Ahmed Rufai No. 93, Hassan Gwani Street, badarawa Kaduna.
*
Shehu Garba Iyaye Kwadon,
c/o Gare A.D Laga, P.M.B 79 Kwadon, Yameltu Debu L.G.A Jihar Gombe
*
Jummai Ibrahim Muhammad
No. 234, Unguwar Sarkin Gabas, Jahun, Jihar Jigawa
*
A'isha Husaini Bakori, da Jummai Disina Muhammad
Block, 11 flat 4, Shandam Close, Area 11, Garki, Abuja
*
Yahaya Usman Dangora,
Unguwar Cashew Kwali Area Council, F.C.T. Abuja
*
Armaya'u aminu 'Yandaki,
P.O. Box 2020, Kaita L.G.E.A. Kaita, Jihar Katsina
*
Danjuma Bala Sarkin Kasuwa, Jalingo, Jihar Taraba
*
Bayatu Muflahu, da Sa'idu Danladi Malamin Daji
P.M.B. 0073, Forest Section, Bauchi L.G.A., Jihar Bauchi
*
Muhammmed Surajo 2 Ssiekh Ibrahim Adamu,
P.O. Box 20, Akuba, Lafiya, Jihar Nasarawa
*
Muhammad Mustapha B.
No 5, LGW, Shandam L.G.A. Jihar Plateau
*
Nasir Suleman (Madade)
P.M.B. 4002, G.D.S.S Malunfashi, Jihar Katsina
*
Muhammad Alh. Ali,
Damaturu L.G.E.A. Damaturu, Jihar Yobe
*
Abdullahi Bello Uban Dawaki,
Sultan Atiku Sec. Sch., P.M.B. 2277, Kano Rd, Sokoto
*
Yamo Musa Muhammad (manager)
M.M. Belo Nig. Ltd, Kankara, Jihar Katsina
*
Aminu Gidado,
Fed. Ministry of Works & Housing
*
Umar Abba El'Nafati,
c/o Abba A. Ibrahim, Secretary Section, Ashaka Cement Plc, P.M.B. 3276 Kano
*
Adam Yusuf (Doctor) Yadin Lere, Lere L.G.A., Jihar Kaduna
*
Zainab Baita Muhammed,
Gyadi Gyadi, Kano
*
Alh. Sama'ila Kwal Kwashi,
Hammalu Video and CD, Disk Centre, No. 2 Mamman Zugau Road, Jibia, Jihar Katsina
*
Usman Adamu Imam Lushi,
No. 30 Palace Way, P.O. Box 149, Jalingo, Jihar Taraba
*
Muhammed Bashir BK,
Independent National Electoral Commission, Jihar Katsina
*
Ahmad I. Babanliya,
Sardauna Sacks Limited, No. 77 Bello Dandago Rd., Kano
*
Ummi da A'isha Ibrahim Nikau,
Maiduguri Rd., Near New Motor Park, Potiskum, Jihar Yobe
*
Shu'aibu Ahmed N.,
Tsohon Layi Quarters, Jahun, Jihar Jigawa
*
Dan yawa, aff, abba karami daumar, Tsohon Layi Quarters, Jahun, Jihar Jigawa
*
Alh. Babba sa'adu kallah Jibia
Wasian Patent & Med. Store, No. 1, Maikudi Road, Bakin Kasuwa, Jibia, Jihar Katsina
*
Mustapha Yusuf Zugau,
c/o District Head Office, P.O. Box 1, Jibia, Jihar Katsina
*
Laraba Yusuf,
Yar Wagana, Inuwa Lamido Quarters, P.O. Box 1274 Gombe, Jihar Gombe
*
Abubakar Garba Jibia,
No.3, Mamman Zugau Road, Jibia, Jihar Katsina
*
Nasiru Attahiru Gusau,
P.C.C., P.M.B. 01061 Gusau, Jihar Zamfara
*
Rabi'at Moh'd Ladan,
c/o Alh. Sabiru K.K, Nagwamatse, Sabon Gari, Kontagora, Jihar Neja
*
Malam Abdullahi Danjuma,
Haske Int. Paint, Jibia, Jihar Katsina.
*
Anas Hamisu Lawal,
c/o Aliyu Abdullahi Gusau, P.O. Box 18, Gusau, Jihar Zamfara.
*
Bello Agwada mai kanwa, da Hamza Adamu mai 'yankunne,
P.O. Box 78, Bakin Kasuwar Yauri, Yelwa-Yauri, Jihar Kebbi.
*
Awal A. Jihar (Sec. T.P.A.)
c/o Halilu Abubakar, No 2, Faru Memorial Shopping Complex, Market Rd, P.O.Box 88 Billiri, Jihar Gombe.
*
Shu'aibu A. Muhammed (Senator)
Agric. Dept. Sabon Garti L.G.A., Zaria, Jihar Kaduna.
*
Zainab Isyaku Kajuru,
G.G.S.S. T/Balewa Way, P.M.B. 1273, Kaduna.
*
Inuwa Abubakar,
Auditor, G/Gora Drivers Association, Chukun L.G.A., Jihar Kaduna.
*
Malam Aliyu Yakubu (Master)
No. 64, U/Fatika, Kofar Jatau, Zaria, K.S.T.V. Kaduna.
*
Jamila Badamasi Usman
Block 1,Gambia Street, Malali Low-Cost, Kaduna.
*
Hafsat Muhammad,
No. 228, U/Alakli, Zaria, Jihar Kaduna.
*
Ibrahim Rimi, Jamila, da Hadiza,
NurRim@aol.com
KURAKURAI A SHIRIN TASIRI 1
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA da shawara ga furodusoshi ne dangane da yadda suke shirya finafinansu. Mafi yawancin lokuta sai ka ga ba su tsayawa su fitar da labari da kyau ko kuma idan sun yi sai ka ga kurakurai da dama. Alal misali, a cikin fim din Tasiri 1, mutane da dama sun yi mamakin ganin cewar mahaukaci na waka kuma mai ma'ana. Sannan kuma wani babban kuskure da suka yi shi ne a inda aka nuna cewar Ali Nuhu ya bayyana wa abokinsa Ishaq cewar yana jin yunwa sosai amma abin mamaki sai kawai aka nuno shi yana juyewa mahaukaci abincin, wanda hakan bai yi daidai ba. Kamata ya yi a nuna Ali yana kokarin cin abincin amma sai wani abu ya ratso da zai hana shi cin abinci, kuma sai a nuna shi mahaukacin ya zo gidan Ali yana barar abincin, wanda hakan zai sa ya ba shi sadakar wannan abincin.
Duk da haka 'yan fim suna kokari wajen fadakar da jama'a. Amma sai dai su rinka amfani da na'urori irin na zamani. Daga karshe ina mika gaisuwata ga Ibrahim Mandawari da Saima Mohammed wadanda a cikin shirin fim ba ni da gwarzaye da suka fi su.
Asma'u Adamu
ASHAFA YA CANCANCI ZAMA EDITA
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
NA yi matukar farin ciki a lokacin da nake karanta mujallar Fim ta watan Maris na yi kicibis da labarin cewa Ashafa ya zama sabon Editan Fim. Na yi murna sosai, domin kuwa idan muka yi la akari da yadda Ashafa ya shahara wajen rubuto mana labarai masu dadi cikin sabuwar mujallar nan Bidiyo, to za mu ga ashe Ashafa ya cancanci zama editan Fim. Daga karshe ina gaida Ibrahim Mandawari, Hamisu Lamido Iyan-Tama, Ahmed S. Nuhu, Isa A. Isa, A.A. Sharif (Momo), Aina'u Ade, Maryam Umar, Hadiza Kabara da Rukayya Umar.
Bashir Ahmed Sasa
Fatima Binta Investment, Gombe.
NA YI MAKU LAIFI NE?
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
Don Allah ina so ku ba ni fili cikin wannan mujallar taku mai farin jini domin na yi wadansu tambayoyi guda biyu. Ina fata za ku taimaka ku amsa min su. Na farko, yaya na rubuto maku wasiku da dama amma har yanzu ban ga ko da guda daya ba? Ko akwai wani laifi da muka yi muku? Ko kuwa samunku ne ba ta yi ba? Bayan haka kuma ina son ku ba ni adreshin shahararren dan wasan nan kuma furodusa, wato Rabilu Musa (Ibro). Kuma idan kuna da lambar wayarsa ku ba ni.
Auwalu Turawa Gayawa
Malam Auwalu, babu laifin da ka yi mana. Ko dai wasikarka ba ta iso gare mu ba, ko kuma ba ta cancanci bugawa ba, ko kuma tana cikin taskarmu wadda ke cike da daruruwan wasikun jama'a. Shi kuma Ibro, mun sha ba da tarihinsa da labaransa. Sai dai kash! ba mu da lambar wayarsa. Mun gode. Edita
GAISUWA GA GWANAYENA
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
DON Allah ku ba ni fili in gaishe da wadanda suke burge ni a fim din Hausa: Nura Hussaini, Ibrahim Maishunku, Hafsat Iliyasu, Aina'u Ade, Isma'il Ishaq Koli, Saminu Moh'd, Abdullahi Maikano, da kuma uwa-uba Aminu Shehu Dambazau.
Tasiu Musa Dankanjiba
No. 13A Mai'unguwa Road, Kabala Costain, Kaduna.
TAMBAYA KAN GAGARABADAU
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
DALILIN wannan wasika shi ne, a kan fim dinku Gagarabadau. Shin sababbin 'yan wasan da kuka sa a ciki, cancanta ce ko son kai? Ina maganar Sadiya Abdu Rano da Aliyu Gora II. Ina fatan dai fim din ba zai tsaya ga nishadantarwa kawai ba, zai ilimintar da jama'a, kuma ya zama abin koyi ga masu shirya finafinai.
Nuraddeen Abdullahi Bagwai
Bagwai Bookshop/Video Centre, No 7, A.G.B. Shopping Complex, Bichi, Jihar Kano.
nurelbagwai@yahoo.com
Ba son kai ya sa muka sa Sadiya da Aliyu a Gagarabadau ba. Shi Aliyu, ba sabon dan wasa ba ne kamar yadda ka dauka (misali, ka kalli fim din Ana Bikin Duniya..., za ka gan shi). Ita kuma Sadiya, ta yi sha'awar yin wasan ne ta shiga. Mun gode.
WACE MUHAWARAR ZA MU YI?
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
KUN ce a zo a yi muhawara a intanet (filin http://groups.yahoo.com/group/Finafinan_Hausa/join). To a kan me za a yi? Ina neman haske a kai. Ya kamata ku rubuta a mujallarku, saboda mutane su sani a kan abin da za a yi. Wassalam.
Jamila Bala Sirajo
Haba Hajiya! Ai kuwa mun yi cikakken bayani! To, idan har ba ki fahimta ba, ki duba daga shafi na 48 zuwa na 51 na wannan mujallar, a duk fitowa muna kawo irin muhawar da mutane ke yi a dandalin intanet din a kan shirin fim. Ke kanki tunda kina da adireshin i-mel, za ki iya shiga ki fadi ra'ayinki ga duniya. Edita
FINAFINAN HAUSA BA SA BURGE NI
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
NI a gaskiya ina son kallon fim amma finafinan Hausa na yanzu ba sa ba ni sha'awa, domin suna saka kade-kade har ma suna barin 'yanmata su rinka kada jikinsu fiye da yadda ya kamata.
A rinka shirya wasanni wadanda za su wa'azantar da jama'a .
Bayan haka, gaskiya ina jin dadin yadda kuke kawo labarai na 'yan wasan fim. Amma akwai wani abu guda daya da yake bakanta mani rai. Shi ne: me ya sa a dukkan kwalayen finafinai da littattafai na Hausa a wannan zamanin da haruffan boko ake rubuta su? Mu tuna fa, a zamanin da duk kasar nan babu masu rubutu sai mu Hausawa, kuma da ajami muke rubutun. Ma'assalam.
Auwal Ahmad
2, Yekini Str., Lagos.
HASSAN BELLO BA DOKTA BA NE
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
NA karanta hirar da kuka yi da Dokta Hassan Bello inda yake fadin cewar wai har yana da ilimin dokta. To wallahi ba gaskiya ba ne. Domin na gan shi ma har a kauye yana ce wa Sulani shi likitan shanu ne. To in gaskiya ne ku dubi wuraren da yake ikirarin ya yi aiki; ya ce yayi aiki a British Encyclopaedia. Me ya hada aikin likitan shanu da wannan? Ya ce ya yi aiki a babban asibitin Azare; to me ya hada shanu da mutane? Ko ko duk likitan shanu zai iya duba mutane? Kuma ina son Hassan Bello ya sani cewar mu fa mun san shi ba sanin shanu ba, don haka don Allah ya rika kula.
Ahmed S. Garba, No. 108, Gwallaga Qtrs, Bauchi.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin