Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 31   Yuli 2002
WASIKU


BABBAN SHAFI
RA'AYI
Zuwa Ga Masu Karatu
Wasiku
Balaraba Muhammad (1983-2002) 
Rahoton Musamman
Rahoto
Malam Zurke
Ra'ayin Mujallar Fim
Bukukuwa
Sauran Labarai
Fitattun Taurari
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka Bangon Fim ta 30
Bangon FIM ta 29
Bangon FIM ta 28
Bangon FIM ta 27
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da ra'ayin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


Wasikun masu karatu

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

NA rubuto takarda domin in taya manyan 'yan wasa da suka yi aure murna. Da farko ina mai taya murna ga Aminu A. Shariff (Momo) da amaryarsa Maryam Mohammed, Abida Mohammed da angonta Hamza, anty na Halima Adamu Yahaya da Comrade Auwalu, gami da Alh. Dan'azumi Usman tare da amaryarsa Hajiya Rabi dukkansu. Allah ya zaunarda su lafiya.

Daga karshe ina yaba ma su Abida da Momo game da yadda suka yarda suka auri abokan sana'arsu. In da yawancin 'yan fim suna yin haka da mutuncinsu ya fi haka.

Mohammed Nazifi A. Imam,

No. 9, Imam House, Kwarau, Birnin Yero-Kwarau, Igabi L.G.A., Jihar Kaduna.

GAISUWA GA 'YAN WASA

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

BABBAN dalilin rubuto wannan wasika shi ne domin ku isar mani da gaisuwa ta musamman zuwa ga wadannan 'yan wasan: Ibrahim Mandawari, Tahir Fagge, Shehu Hassan, Alhassan Kwalle, Ibrahim Maishinku, Sani Musa Mai Iska, Sani Danja, Ashiru Sani Bazanga, Nura Imam, Nura Husaini, Musbahu M. Ahmad, Abida Mohammed, Fatima Mohammed, Wasila Isma'il, Hafsatu Sharada, Amina Garba, Hajara Usman, da Jamila Haruna.

Sai gaisuwa ta musamman zuwa ga Ahmed S. Nuhu, Ali Nuhu, Ladi Jamila Salisu, Talatu Adamu (Yabi). Da fatan duk suna lafiya.

Moh'd Zuladaini Sani da Musa Abba

Rahama Umsu Provision Store, Bakari Dandali, R/Tsamiya, Sandamu LGA, Jihar Katsina.

ALI DA SANI DANJA NA BURGE NI

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

NA rubuto muku wannan wasika ne don in nuna farin cikina game da yadda gwanayena Ali Nuhu da Sani Danja suke yi a fim. A gaskiya suna burge ni. Daga karshe, ina so in mika gaisuwa zuwa ga Ahmed S. Nuhu, Shu'aibu Lawan, da Abida Mohammed. Ina masu fatan alheri tare da sauran 'yan wasan Hausa. Shehu Abdullahi, Yaron Malam Audu, No. 19 Tudun Kofa, c/o Post Master, NIPOST Lafia, Jihar Nassarawa.

SHIRIN DABI'A BAI TSARU BA

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

ZAN yi kira ga daraktan fim din Dabi'a, Mohammed Garba Kabara, kan yadda ya gurgunta fim din, wanda yake mun yi bakin ciki lalacewar da ya yi da kuma rashin tsaruwa. Akwai kurakurai da dama.

Na farko, a siyasar Sani S.K., kamata ya yi su yi amfani da irin kokarin dare daya. Ba faduwar girma ba ne, amma a ce an yi siyasa babu abokin takara, sannan an fadi sakamako daga shi sai maidakinsa suke sauraron rediyo, babu 'yan tawaga. Na biyu, wanda yake da burin samun naira ko ta halin kaka ya salwantar da kayansa da na matarsa ya fadi zabe? Ai kamata ya yi a ce ya samu tabin hankali ko wani abu daidai wannan. Na uku, sannan fim din ya cika a yi nan a yi nan, ana cikin wannan sai kawai mu ga can, babu bin daya bayan daya, sannan ga yawan tunani.

Kirana a nan shi ne Mohammed Garba Kabara ya gyara, da shi da takwarorinsa irin su Zilkiflu Muhammad a fim din Maqabuli. Ina gaida Hadiza Moh'd Kabara da kuma Hafsat Iliyasu.

Sir Dauda Suleman Zurmi

Ex. STVdent (ZACAS), Zurmi Local Govt., P.M.B. 1107, Gusau

Jihar Zamfara.

ALLAH YA TSARE MUJALLAR FIM

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

NA dade ina ta jinjina maku a kan aikin da kuke yi wurjanjan game da bayanai da kuke bayarwa filla-filla a kan duniyar finafinan Hausa. Sannan kuma ga shi uwa-uba kuna ciyar da adabin Hausa gaba. Wannan mujallar tana debe mani kewar littattafan adabin Hausa kamar Magana Jari Ce, Gogan Naka, Kulba Na Barna, da sauransu, da yake yanzu ana matukar kamfar ire-iren wadannan littattafan. Babu abin da zan ce da wannan mujalla sai sambarka da tubarkalla. Allah ya kara wa ma'aikatanta basira da kwazo, ya kuma tsare ta daga sharrin masu sharri da 'yan a-mutu-kowa-ya-rasa, da yake ba sa son a fadi gaskiya.

Gaisuwa ga sabon edita Ashafa Murnai Barkiya. Bissalam.

Shaffa'u Lawali Juniyo.

c/o Zuwaira Falalu Lawali Kaura, P.O. Box 1869, Sokoto.

IBRAHIM DIN WEEKLY TRUST NE?

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

KU sa ni a hanya wadannan tambayoyin:

1. Shin Ibrahim Sheme da nake gani a jaridun Weekly Trust da New Nigerian shi ne babban editan mujallar Fim?

2. Na daina ganin rahotannin wakilinku Kallamu Shu'aibu; ko me ya faru?

3. Da yawa ina ganin kuna rubuta 'Take Two' a wasu larabanku, meye ma'anar wannan?

A gaida Ibrahim Sheme da madugu uban tafiya Mandawari.

Asma'u Aminu Manja.

(Babu adireshi)

AMSOSHI: 1. Ibrahim Sheme, wanda ke gabatar da filin 'Bookshelf' a jaridar Weekly Trust, kuma yana rubutu a New Nigerian, shi ne mawallafi kuma babban editan mujallar Fim; 2. Allah ya yi wa Musa Gambo Sheme (Kallamu Shu'aibu) rasuwa, kamar yadda muka bayyana wata biyu da suka wuce; 3. 'Take Two' da ke fitowa a filinmu na Rahoton Musamman wani kira ne (na bayar da umarni ga 'yan wasa) wanda daraktan shirya fim kan yi idan ana daukar fim; akan yi 'take one' (wato dauka ta daya) sannan a yi dauka ta biyu (take 2) har zuwa yawan daukar da aka ga ta wadatar.

BA KU SON BUGA WASIKUNA?

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

ZAN yi matukar farin ciki idan har na ga wasikata a cikin wannan mujalla taku mai farin jini. Na aiko muku da wasiku da dama amma har yanzu ban ga ko da guda daya ba. Kai hatta i-mel na aiko amma har yanzu ban ga kun buga ba. Kuma ina so ku mika min gaisuwata ga 'yan wasan irin su Rabilu Musa (Ibro), da Kulu Saminaka da Ibrahim Mandawari.

Auwalu Muhammed Gayawa,

Karamar hukumar Ungogo, Jihar Kano.

INA KAUNAR DUMBARU

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA son in shaida maku cewan ina son Dumbaru. Ina mai kaunarta, kuma ina son ta aiko mini hotonta.

Adamu A.D. Lager,

Kwadan, Yamaltu Deba LGA, Jihar Gombe.

A RAGE BA BOKAYE MUHIMMANCI

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA so in mika shawarata ga daraktoci a kan su rage bai wa bokaye muhimmanci a fim, mu samman idan an je neman magani wajensu. Domin kada muttane su dauka cewa bokaye na da wani muhimmanci a kan biyan bukatun jama'a maimakon dogaro ga Allah (SWT).

M. Kasimu Yusuf Jibia,

Jibia, Jihar Katsina.

LAIFIN ME NA YI MAKU?

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

DON Allah muna so ku ba mu fili a cikin wannan mujalla mai farin jini domin mu yi wadansu yan tambayoyi guda biyu. Na farko, muna rubuta maku wasika da dama amma ba ma ganin ko daya. Ko akwai wani laifi da na yi maku ne? Domin da hannuna nake kawo maku har ofishinku, ba wai aikowa nake ba.

Kuma ina son a mika gaisuwata ta musamman ga amarya wato Halima Adamu Yahaya. Allah ya ba da zaman lafiya da zuri'a tagari, amin.

A'isha da Safiya Bello Umar,

CW 10, Kubau Road, T/wada, Kaduna. Tel. 062-412355.

Malama A'isha, babu laifin da kika yi mana. Abin ne da yawa, wai mutuwa ta je kasuwa. Amma daga yanzu za ki ga canji.

A TSAIDA KALLO LOKACIN SALLA

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

NA rubuto wannan takarda in yi maku jinjina tare da jawo hankalinku a kan wata matsala. Ina mai bukatar don Allah cikin fadakarwar da kuke yi, ku rika nuna ma masu kallo muhimmancin tashi zuwa salla. Masu kallo ku rika tashi zuwa salla idan lokaci ya yi.

Nura Umar Manya Manya,

Nigerian Prison Services, Medium Security Prison, Zamfara State Command, P.M.B. 1027, Gusau.

MAI ISKA KA MAIDA TALATUNKA

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA son in yi amfani da wannan dama in ba Sani Mai Iska hakuri a kan ya maida matarsa, saboda a gaskiya mu masoyan Fati muna gudun irin hakan ya faru ga Fati, kuma wasu za su ce saboda Fati ya saki Talatu. Duk da yake Talatu ta fadi a cikin mujallar Fim cewa ba ruwan Fati, wannan bai kare Fati ba. Sani, mu dai masoyanta abin da muka ga ya fi shi ne ka mayar da matarka ka yi hakurin nan da ka saba yi da ita kafin ka auri Fati. Kuma idan ka duba, ita rayuwa guda nawa ce? In mu ne yau ba mu ne gobe ba. Shi kansa wanda ya halicce mu hakuri yake yi da mu. Da fatan Allah ya kara mana hakuri baki daya.

Rabiat Mohammed Ladan,

c/o Alh. Sabi'u K.K., Nagwamatse Crescent, Sabon Gari, P.O. Box 160, Kontagora, Jihar Neja.

FURODUSOSHI NA BA MU KUNYA

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

A GASKIYA furodusoshi kuna neman ku ba mu kunya. Domin muna alfahari da ku, amma koyaushe sai ka ga wannan furodusa yana rikici da wannan. Mu muna murna cewa mun samu 'yancin kanmu a finafinan Hausa, sai kuke nema ku sa a yi mana dariya. Don Allah ku hada kanku zama daya. A karshe ina mika gaisuwata ga Ibrahim Mandawari, Hadiza Kabara, Zik, Ishaq Sidi Ishaq, Rukayya Umar Santa, Shehu Hassan Kano, Tahir Fagge da babbar masoyiyata, Abida Mohammed.

Hadiza Yusuf,

Workers Village, Block 10B, Doma Road, Lafia, Jihar Nasarawa.

A GAIDA SU SHU'AIBU LILISCO

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA mika gaisuwata ga 'yan wasa kamar su Idris Shu'aibu Lilisco, Aminu Shehu Dambazau,Ali Nuhu, Ahmed S. Nuhu, Ibrahim Mandawari, Musbahu M. Ahmad, Abida Mohammed, hadiza kabara. Hajara Usman, Tahir Fagge, Halima Adamu Yahaya, Aina'u Ade da sauransu.

Jummai Ibrahim Muhammad

Unguwar Sarkin Gabas, No. 234,

Tsohon Layi, Jahun Jihar Jigawa.

SHEME YA FADI GASKIYA

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA son ku ba ni fili a wannan mujalla mai farin jini a kan wasu furodusoshi da ba su da tunani. Wai har za su ce a hana mujallar Fim fita! Ku sani fa, mujallar Fim garkuwa ce ga masu shirya finafinai, in ba don mujallar ba, da Hausawa ba za su kai labari ba.

In ban da ku ai shi Ibrahim Sheme gaskiya ya fada! Saboda wallahi in ya ce zai fadi sirrin masu harkar fim, da ba haka ba. Saboda mu kanmu abin da muka sani ne. Wai har za ku ce a kafa abokiyar adawar mujallar Fim. To ai tun kafin a fara yin fim Sheme yana da sana'a, babu mai hana shi abin da Allah ya ce zai zama. Sai mu ga mai tugewa.

Ai akwai 'yan wasa da suke zuwa nan Jalingo; in mun ce za mu fadi abin da suke yi, wallahi da ba mai sake kallon fim. Da ma an ce ka bi abin da malam ya fada, kar ka bi abin da ya aikata. To ku yi hattara.

Mallam Kawu Jalingo.

Tudun Wada Ward, Jalingo, Jihar Taraba.

MUNA CIGIYAR YAKUBU LERE

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA so don Allah ku fada wa Yakubu Lere cewa akwai wani mutum wanda ya bugo mani waya wai in gaya mashi inda Lere yake. Ni kuma ban san inda yake ba. Saboda haka Lere ina so ka rubuta adireshinka a cikin mujalla tare da lambar wayarka. Shi dai wannan mutum da yake bugo min waya daga kasar Nijar yake bugowa.

Bayan haka, ina so in ce wani abu kan kin halartar daurin auren Rabi Mustapha da 'yan fim suka yi. Abin kunya ne a ce kamar Rabi ta yi aure amma su ki zuwa. To, wallahi mu dai Rabi ta burge mu. Saboda ta yi aure, in haushi kuka yi da ita, ita dai ta yi gaba. Allah ya zaunar da ita lafiya, ya daukaka ta, amin.

A karshe ina mika sakon ta'aziyyata ga iyayen Balaraba Mohammed da mijinta Shu'aibu Lawan. Allah ya ba su hakurinjure wannan rashi. Kuma ina ba iyayen marigayiyar shawara su yi tunani su ba Shu'aibu kanwarta. Allah ya sa su amsa wannan rokon, amin.

Hajiya Gambo Muhammad Gidado Tsiga,

No. 11, Tudun Wada, Zaria, Jihar Kaduna. Tel.: 069-335156

Hajiya, lambar wayar Lere dai ita ce 062-318318, kuma yana zaune a Badarawa, Kaduna.

FINAFINAN 'FKD' SUNA DA INGANCI

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

IDAN rana ta fito tafin hannu ba ya kare ta. Wannan magana haka take idan muka yi la'akari da irin yunkurin da kamfanin 'FKD Production' na Ali Nuhu suke yi. A gaskiya Ali ya cancanci yabo kan irin wannan hazakar da yake nunawa wajen fitar da ingantattun finafinai don ci-gaban harkar fim a Arewa. Ana amfani da motoci, gidaje, da sutura masu dacewa cikin fim dinsa. Wannan yana nuni da cewa Hausawa suna ta ci-gaba a duniya. Allah ya taimaka da budi, ya kuma kara basira kan abin da ake yi amin.

Daga karshe ga gaisuwata ga Ahmed S. Nuhu, Kumurci, A.A. Shariff, Isma'il Koli, Aleebaba, da sauransu.

Habulle Usman India,

c/o Alhaji Usman Abdu, P.O. Box 15, Maiduguri, Jihar Borno.

MUNA YABA MAKU KAMAR KOWA

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

HAKIKA mu masu karatun mujallarku ne sosai. Muna yabawa kamar yadda kowa ke yaba maku. Amma kash! sai ya kasance duk unguwarmu babu wanda ya taba rubuto muku wasika ko sau daya ne. Ni na ce zan fara domin mu ma mu rubuta namu ra'ayoyin. Daga karshe muna yi maku fatan alheri, Allah ya kara yi muku budi na alkhairi, amin.

Muhammad Zayyana A. Sakkwato

Manaja, New Zaiyana Fashion Design, Shehu Shagari Way, Sokoto.

IDAN BABU DUMBARU A FIM...

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

GA sakona nan ga uwargida Dumbaru, da fatan za a isar min da shi. Don Allah Dumbaru ta ci gaba da fitowa a fim kamar da domin idan babu Dumbaru a fim, sai dai in kalla kawai ba don sha'awa ba. Da fatan idan Hajara Dumbaru ta karanta wannan wasika, za ta ci gaba da fitowa a fim kamar da.

Nafisa Halilu,

No. 1 Nagogo Street by Kwanar Chanchangi, Tudun Wada, Kaduna.

FILIN WASIKU ANA BIYA NE?

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

MUNA masu jinjina maku bisa ga kokarin da kuke yi na wayar mana da kai a kan 'yan wasa, da fatan za ku kara himma.

Sannan kuma a matsayinmu na 'yan kungiyar masu karanta mujallar Fim, mun sha aiko da wasiku na yabo da shawarwari, amma har yau ba ko daya. Shi ne muka yanke shawarar mu turo shugabanmu ya bincika in ana biya ne mu sani, in kuma akwai abin da ya dace a yi, sai mu yi, don mu ji karfin kare mujallarmu, don ta zama tamu mu duka. Da fatan za mu samu cikakkiyar amsa.

Gaisuwa ta musamman ga Rukayya Umar Santa.

Sa hannun shugaban kungiya, Mustapha Sani Dirin Daji, da Sakatare Ma'aruf Jafar Ko-Ka-Yi-Gaskiya -Ba-Su-Sani, Kungiyar Makaranta Mujallar Fim ta yankin Zuru Emirate, P.O. Box 29, Dirin Daji, Sakaba LGA, Jihar Kebbi.

Malamai, a gaskiya ba biya ake ba kafin a sa wasikar mutum a mujalla. Idan kun ga wasikarku ba ta fito ba, to ko dai ba ta iso gare mu ba, ko ba mu gane rubutun ba, ko ma'anar ba ta kai ba, ko kuma tana kan layin fitowa. Mun gode da wannan wasikar taku. Edita

KU CIRE FILIN HOLLYWOOD MANA

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

DA farko ina nuna matukar farin cikina game da samun sabon edita da muka yi. Bayan haka, a mujallar watan Maris shafi na 3 kun yi maganar matsalar samun yawan wasiku, kuma shafukan wasikun sun yi karanci. Me ya sa ba za a rage shafukan filin Hollywood ko ma a kashe filin ba domin ba shi da muhimmanci sosai a gare mu? Na uku, ya kamata a dinga duba nisan wurin da wasiku suka zo domin masu rubutowa daga nesa su ji dadi kuma su san mujallar Fim ta kowa ce.

Fadila Zanna,

G.F.C. Monguno, Jihar Borno.

Fadila, mun gode da wannan shawarar. Za mu duba ta.

KANAWA A DAINA YABON KAI

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

NA rubuto wannan wasika ne zuwa ga mujallar Fim, mujalla mai farin jini, gagara-gasar-masu-gasa, domin in gabatar da gaisuwata da jinjina ga dukkan jami'an wannan mujallar a kan kokarin da suke yi na sada zumunci tsakanin makallata, makaranta, da kuma masu shirya finafinan Hausa.

Bayan haka in son in yi amfani da wannan dama in jawo hankalin wasu daga cikin furodusoshi a kan yabon kai da suka fara sawa a cikin finafinansu, wanda yake a gaskiya da ba haka muka saniba. Misali, kamar cikin fim din Tasiri, ko wa ya kalli wakar da Ishaq Sidi Ishaq, Ali Nuhu, Balaraba Mohammed da Aina'u Ade suka rera, zai fahimci akwai yabon kai a ciki. To wannan bai kai kamar cikin fim din Taqidi ba inda Ahmad S. Nuhu da Fati Mohammed ke rera wata waka, suna cewar wai su 'yan Kano akwaisu da nairori. Abin da kunya! Shin Kanawa kawai ne ke da kudi? Me wakar ke nufi? Kudi kawai ne baiwa?

Ina kira ga irin wadannan mutane da cewa su daina. Don ko a Kano duk mai hankali da ilimi ba zai yi sha'awar ji ko ganin irin wannan ba. Akwai wadanda Allah ya ba baiwa ko mu'ujiza da ta fi ta kudi, amma ba su yi gori ba.

Da fan wadanda na yi dominsu za su ji kuma su gyara.

Muna yi ma dan'uwanmu Shu'aibu Lawan (Kumurci) ta'aziyyar rashin mata da ya yi. Ma'assalam.

Suleiman Attahiru Gusau,

Gusau Hotel Limited, Zaria Road, P.M.B. 1093, Gusau, Jihar Zamfara. Tel.: off: 063-200396, 200727; residence: 063-200959.

INA SON RUKAYYA FIYE DA MISALI

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA son in yi amfani da mujallarku in isar da sakona ga Rukayya Umar Santa (Dawayya). Ni wani masoyinta ne mazaunin Gusau. Sanadiyyar kaunar da nake mata ya sa duk wani kaset da ba ta a ciki to mai rauni ne a gurina. Idan har da hali ku yi ma wannan takarda iso gare ta domin in samu wasu dadadan kalmomi daga bakinta. Son da nake mata ya wuce tsammani! Na gode.

Abubakar Aliyu Gusau,

c/o Aliyu Abdullahi Gusau, Zamfara Video Mark Production, P.O. Box 18, Gusau, Jihar Zamfara.

KIRA GA MATA MASU RUBUTOWA

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

NA rubuta wannan wasika ne domin in bayar da shawara ga masu rubuto wasika a wannan fili, musamman mata daga cikinsu. Don Allah a duk lokacin da wata mace za ta rubuta wasika ga wannan fili, su rika nuna matsayinsu, watau mai aure ce ko ko marar aure. Domin sau da yawa za ka ga mace ta rubuto wasika ta sanya adireshinta, wasu har ma da lambar tarho amma babu matsayin aure. Saboda haka nake kira ga 'yan'uwanmu mata da su rika bambantawa ta hanyar sa 'Miss' (mara aure) ko 'Mrs' (mai aure) don a gane. Dalili shi ne wannan fili na wasiku fili ne na bayyana ra'ayoyi a kan harkar finafinai da kuma sada zumunci. Wani zai so ya rubuta ma wata takarda domin neman karin bayani kan wani ra'ayi nata da ta rubuta amma rashin sanin matsayinta zai iya hana shi yin hakan.

Dahiru Yusuf Galadima,

Kofar Marusa Qtrs, P.O. Box 22, Katsina.

MUJALLARKU TA KORI STARDUST

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

NA rubuto wasikar nan ne domin in kara yaba maku a kan irin gudunmuwar da kuke badawa wajen kara farfado da harshen Hausa. Gaskiya wannan ba karamar taimakawa ba ce ga ainihin adabin Hausa. Mu ta hanyarku ne muke samun damar musayar wasiku da ma'aboto kallon wasannin kwaikwayo. Haka kuma a sanadiyyarku ne wasannin kwaikwayo suka kara samun karbuwa ga mutanen Arewa har ma na Kudu.

A yau an wayi gari mujallar nan ta kasar Indiya mai suna Stardust ta kaura ta koma inda ta fito. Haka su ma finafinan Indiya tuni muka yi jana'izarsu, duk a sanadiyyarku. Kun ba ma'abota karatunku damar rubuto maku wasiku na yabo ko na suka ko kuma kalubalantar wasu daga cikin ra'ayoyinku. Sannan a dalilinku ne yau wasu daga cikin 'yan wasa suka rikida suka zama furodusoshi.

Daga karshe ina mika gaisuwa ga Ibrahim Sheme.

Mustapha Abdullahi (Musty) Sokoto,

Executive producer, Tsautsayin Shagwaba, Sokoto.

MANDAWARI SAI HAMDALA

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

NA rubuto wannan wasika ne domin in nuna rashin jin dadina dangane da wata kalma da Yakubu Lere ya fada game da Ibrahim Mandawari a mujallarku ta watan Nuwamba a shafi na 28. Lere ya ce wai hassada ce ke damun Mandawari. Ni dai na san shekaru goma da suka wuce na fara ganin wani fim wai shi Aminu Mijin Bose, wanda a wancan lokacin babu wanda zai ce tauraron Mandawari bai haskaka ba. Aka zo aka yi Jamila da Jamilu. Babba da yaro ya san da zaman Isma'ila na cikin Ki Yarda Da Ni, wanda duk kasar nan ba wanda bai gan shi ba. To amma in har hassada ke damun Mandawari, lallai bai gode wa Allah (SWT) domin ya daukaka ta duniyar fim. Allah ya ba shi, mun ji kuma mun gani, sai mu ce saura a nemi na Can, kuma a rika godewa. Allah ya kare ku daga sharrin masu sharri, amin.

Hajara Yakubu Ladan,

NEPA District Office, P.M.B. 10, Bauchi.

HATTARA MASU SANYA FIM A CIDI!

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA mai matukar farin cikin rubuta wannan kasida domin in fadakar da 'yan'uwana furodusoshi da duk wani mai sha'anin finafinai, tun daga kan masu shiryawa har zuwa kan masu hada hotuna. Zan yi magana a kan wani al'amari da ya fara yaduwa a duniyar finafinan Hausa wadanda ake rikodin dinsu a faifai na CD, wanda idan ba a yi da gaske ba, to sha'anin fim zai nakasa, kuma jama'ar da ba sa son gurbatar tarbiyyar 'ya'yansu za su kaurace wa wadannan finafinai na CD. Abin da ya sa na rubuta wannan kasida shi ne wani abu da na gani da idona. Raina ya yi mummunan baci da ganin wannan abu kuma hankalina ya yi mummunan tashi. Kowa ya san an fara sanya finafinanmu a cikin faifai na CD har muna murnar an ci gaba. Ashe ci-gaban mai shiga rijiya aka yi; an yi tuka ne furodusoshi suke nema su warware da kansu. Wani abin ban haushi da ban mamaki da neman a dakushe hasken al'adun mutanen Arewa da gurbata tarbiyyarmu da neman a karyata maganar Annabi (S.A.W.) da ya ce duk wanda ya nuna tsiraicinsa da wanda ya gani dukkansu Allah ya tsine musu. Sai ga shi kafin a yi ma furodusoshinmu rikodin a cikin CD, a Legas sai an sanya rawar 'yan 'Mapoka' (ko rawar Awilo), wato wadanda suke rawa tsirara, ana gwatso ana nuna fasikanci kiri-kiri kamar yadda na gani a cikin fim din Dodanniya na 1 and na 2 da sauran wasu finafinan hausa a CD. Kash! Allah wadaran naka ya lalace. Ban ga dalilan da ya sa furodusan wannan fim ya yarda da wannan mummunan abu ba da sauran wadanda suka yarda aka saka wannan fasikanci ba. Kar ku manta, wannan al'amari ya shafi addini, da al'adun mutanen Arewa, don wannan yana daga makircin abokan zamanmu ('yan Kudu) don su gurbata tarbiyyar 'ya'yanmu, kuma su yada manufarsu a cikinmu. Allah ya sauwake, amin! Ya kamata furodusoshi su daina yarda da wannan. Tashi za ku yi tsaye ku yi wa addininku aiki, duk abin da kuka san zai taba addininku da tarbiyyarku da al'adunku, to ku tsaya sai inda karfinku ya kare. Duk abin da za a yi ma addininku izgili ku gaggauta kawar da shi. Kuma ya kamata manya masu kudi da dukkansu furodusoshi su sayi injina na yin rikodin a faifan CD da kansu, su rika yi ba sai sun kai can inda za a sanya abin da aka ga dama ba.

Yanzu kuma zan yi magan kan wasu abubuwa da ya sa ake yawan sukar finafinan Hausa.

Sanin kowa ne shirin finafinan Hausa ya samu karbuwa a kan sauran finafinai, amma ina sanar da furodusoshi a kan wani abu da ba su gane ba har yanzu. Mutane sun gaji da kallon finafinai na soyayya, domin kashi bakwai cikin goma na finafinai duk na soyayya ne, uku ne kadai ne na wasu abubuwan. Ina kira ga furodusoshi da su canza salon finafinansu. Tunda an karantar da jama'a soyayya da zaman gida, da tsoratarwa a kan kwartanci, ya kamata a koma ga tsantsar al'adun Hausa. Ya kamata furodusoshi masu kishin addininsu da al'adunsu su kara fito da al'adun Hausa. Shin ko ba ku ga wani fim da 'yan Kudu suka yi ba mai suna Oduduwa, wanda yake nuna tsantsar al'adun Yarabawa? Kuma furodusoshi me zai sa ba za ku yi wani gagurumin fim ba guda wanda za ku hada kai ku nuna tsantsar al'adun Bahaushe da mutanen Arewa? Ku daure ku yi kamar yadda aka yi su Magana Jari Ce, Shaihu Umar, Ruwan Bagaja, da sauransu.

Ya kamata a daina koyi da finafinan Canis, Amerika da Indiya, ana dauka ana fassarawa, don wadannan ba al'adunmu ba ne. Ya kamata furodusoshi su kasance suna kirkirar labari da kansu wanda ya shafi al'adunmu da addininmu, kuma su yi koyi da Ibrahim M. Mandawari da Abdullahi Maikano Usman wadanda duk finafinan da suka yi babu wanda ya saba wa al'adarmu da addininmu. Kuma ina kira gare su da su daina satar fasaha domin a dokar kasa satar fasaha ba karamin laifi ba ne. Ka kirkiri abinka ya fi dadi da ka saci fasahar wani.

Abdulkarim M. Bashir Al'Arabi,

No. K11/25, Saminaka Road, Unguwar Kanawa, Kaduna.

AFPAN DA BATUN HADIN KAI

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

IDAN aka ce furodusa a harkar shirya fim, ana nufin mai shirya fim din ko kum in ce mai daukar nauyinsa. A shirin fim akwai wani da ake kira Executive Producer, wato cikakken mai daukar nauyi, mai cire kudinsa a shirya fim.

Shin me Kungiyar Furodusoshi ta Arewa (AFPAN) take yi don ganin sun kawo canji a tsarin finafinanmu ta yadda za su yi gogayya da duk wani fim a fadin duniya? Tun da aka kafa kungiyar har zuwa yanzu ta kasa kawo wani gagarumin gyara. Shin rashinshugabanci nagari ne yake damunta ko kuma 'ya'yan kungiyar ne ba sa bai wa shuwagabanninta hadin kai?

A gaskiya, babban abin kunya ne a ce 'ya'yan kungiyar sun kasa biyan N1,000 da aka ce kowannensu zai biya bayan sun ci moriyar fim din; shi ne dai ya sa aka san akasarinsu a duniya don a da a garinsu ma wani ba a san shi ba. Aa gaskiya in dai haka ne zan iya cewa sun yi abin da Hausawa kan ce an ci moriyar ganga.

Idan fa har wadannan furodusoshi suka kasa yin wani abu na yabawa, to zan iya cewa sun ba Sardaunan Furodusoshin Arewa, Hon. Abdu Haro Mashi, kunya, tunda shi ne musabbabin kirkiro wannan kungiya.

Ya kamata a ce kungiyar ta sa ido a kan irin finafinan da ake shiryawa don kar su wuce gona da iri wajen isar da sakon da suke son isarwa.

In ba don mujallar Fim ba da watakila ba wanda zai san akwai wata Kungiyar Furodusoshi ta Arewa. Na karanta wata hira da aka yi da sakatare na wannan kungiya inda yake cewa wai 'ya'yan kungiyar ne ba sa kawo musu korafi balle su dau wani mataki da har za a gane kungiyar tana aiki. To ai su ne wakilan jama'a, ma'ana 'ya'yan kungiyar da sai su kira taro su bayyana wa membobinsu ga irin tsarin da suke yi. In ana haka sai a ga an cimma nasarori masu yawa.

A gaskiya in har ba a samu hadin kai a tsakanin furodusoshin Kano ba, to da wuya a ce furodusoshin sun kulla wani abu da 'yan baya za su zo su yaba musu tunda ita Kano ita ce kanwa-uwar-gami a shirin fim a Arewa gaba daya. Amma har yanzu akwai hassada da gaba a tsakanin wasunsu tare da sa ido a kan abin da wani ya samu da ya yi fim din shi.

Ya kamata a samu cikakken hadin kai tsakanin furodusoshi da dillalan kaset domin ganin wannan sana'a ta samu ci-gaba mai yawa. Har yanzu kasakasan da ake nadar (recording) za ka samu tsakiyarsa ya zana layi ko yana rawa ko kuma ka sayi kaset sai ka je gida ka tad da ba komai cikinsa gaba daya ko wani bangarensa.

To furodusoshi, in har ba ku motsa ba to tarihi ba zai mance da ku ba kuma ba zai yafe maku ba. Domin lokaci zai zo da ku ba ku nan, kun tafi, ko dai kun tsua ko Maiduka ta yi ta gama. Don haka sai yabon Allah wadarai za su yi maku. Don Allah a gaggauta kawo gyara tare da kiran taron kungiyar na kasa da gayyatar manyan mutane, domin wannan sana'a ba karama ba ce a rayuwar al'ummarmu da 'ya'yanmu, musamman ma matasa, tunda su ne za su kasance manyan 'yan fim a gobe.

Shu'aibu A. Umar (Ruqash) Fatori,

Shu'aibu ya rubuto ne daga Sashen Darussan Musulunci, Jami'ar Bayero, Kano.

ALLAH YA SAKA MAKU DA ALHERI

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

DALILIN rubuta muku wannnan wasika shi ne don in gode muku tare da yi muku addu'a a kan ayyakan da kuke yi ma jama'a na wayar musu da kai a kan harkokin finafinan Hausa da na Indiya da Amerika. Allah ya saka maku da alherinsa, amin.

Gaisuwa zuwa ga Ibrahim Sheme, Kabiru Nakwango, Bashir Nayaya, Isa Bello Ja, Kabiru Maikaba, Abdullahi Zakari (Ligidi), Tijjani Asase, Damisa, Sani Musa (Mai Iska), da Ishaq Sidi Ishaq.

Faruk Mohammed,

W. 17, Gamagira Road, Sabon Gari, T/Wada, Kaduna.

JUYAYI KAN RASUWAR BALARABA

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA fatan zan dan samu fili a cikin wannan mujallar tamu don in isar da sakon ta'aziyyata ga iyayen Balaraba, Shu'aibu Lawan, da kuma dimbin masoyanta. Hakika in akwai wani mutun guda da zai fi jin zafin rasuwar Balaraba, to kuwa ba kamar Malam Muhammadu Kaura ( mahaifinta ), musamman ganin cewa ba ita kadai ce ta rasu ba har ma da wasu 'yan'uwanta. A hirar da wannan mujallar ta yi da shi ne a fitowarta ta 27, mahaifin nata ya bayyana karara cewa a duk cikin 'ya'yansa tara, ba wadda ya fi ji da ita kamar Balaraba. Ikon Allah, ashe ma bai sani ba cewa rabuwarsu ta zo! Allahu Akbar! Allah ya ji kanta da rahamarsa, amin.

Tabbas, rashin Balaraba ga iyayenta da mijinta Shu'aibu da ma duniyar shirin fim din Hausa, ba karamin rashi ba ne, musamman in aka yi la'akari da irin dimbin gudunmawar da ta bayar ga wannan harka da kuma wadda take kan bayarwa har zuwa lokacin da Ubangiji ya karbi ranta. Ba shakka Balaraba ta bar gurabu masu wuyar cikewa a zuciyoyin dimbin masoyanta.

Wani abin lura game da Balaraba shi ne kusan akasarin rayuwarta a kan kaddara take gudanar da su, domin in za a iya tunawa ita ce yarinyar da a kwanakin baya wasu Katsinawa suka yi yunkurin tafiya da ita Katsina, a fadarsu wai 'yarsu ce da ta bace tun tana kankanuwa. Ba a jima ba kuma wasu bayin Allah suka yi nufin tafiya da ita kasar Saudiyya, amma Allah cikin ikonsa duk ta tsallake wadannan hadurran.

Balaraba na sahun gaba-gaba na jerin 'yanmata masu shirin fim da suka bayar da babban misali a cikin wannan harka, domin kuwa ta tsiri yin aure a daidai lokacin da tauraruwarta ke kan ganiyar haskawa sannan kuma kowa yana kwadayin ganin fuskarta. Amma saboda tunanin abin da kan je ya komo, yarinyar ta yanke shawarar hakura da harkar. Face gidan mijinta za ta tafi don ta bauta wa mahaliccinta - sabanin su o'o!

Ina iya tunawa, akwai inda Balaraba ke amsa wata tambaya da wannan mujallar ta yi mata inda take bayar da amsa da cewa, "Kawai ni na ga aure shi ne martabar 'ya mace, saboda diya mace ba aure ai shirme ne, diya mace da aure shi ne take da martaba. Kuma kowa zai dinga dubanta da daraja". Wannan batu nata haka yake. La shakka, Balaraba ta raya sunnar Manzo (S.A.W).

Haka kuma wani abin yabawa ga ma'auratan shi ne irin yadda suka dinga bayar da amsoshin tambayoyin da wannan mujallar ta yi masu, sai ga shi akasarin kalaman da suka yi amfani da su duk tauhidi ne, wato danganta lamurransu ga Ubangiji maimakon cika baki da fariya duk kuwa da sanin cewa suna da dimbin mahassada game da lamarin auren nasu.

Hakika, Shu'aibu ka yi rashin mata, domin ba samun mata ne matsala ba, amma samun mace shi ne matsala.

Haka kuma Malam Muhammadu Kaura ka yi rashin 'ya. Mu kuwa 'yan kallo mun yi rashin babbar mai wa'azi. To amma dukkanmu ya muka iya da abin da Ubangiji ya kaddara mana tun fil'azal? Abin da kawai ya rage mana yanzu shi ne mu yi ta kwarara mata du'a'i da fatan Ubangiji ya yafe mata kurakuranta. Allah ya haskaka kabarinta. Allah ya kyautata makomarta. Mu kuma Allah ya ba mu guzurin ishe ta, amin!

Alhaji Sahab Saminu Mohammed,

The Director, Bali Drama Club & Films Production, Area 1 Sec. 2 Behind Area 1 Central Mosque, Garki, Abuja.F.C.T. Tel.: 0803-7865831; 080-3787195

... MU CIKA MATA BURINTA

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

KASANCEWAR mu ma mutuwa tana kanmu don Allah mu yi kokari mu cika wa Balaraba wasiyyar da ta bar mana. A hirarta ta karshe da mujallar Fim ta ce mu gafarce ta, kuma mu ci gaba da yi mata addu'a.

Shugaban masu karanta mujallun Fim da Bidiyo na Jihar Kano,

Yusuf Suleman Musa Gyadi-Gyadi, Kano,

Dept of Accountancy, University of Maiduguri, Jihar Borno.

FINAFINAN HAUSA NA DA ALFANU

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

IDAN za a lissafa abubuwan da suke bayyana mana halayen mutane ko nuna al'adarsu, in dai aka fadi abu daya ko kuma biyu, na uku za a sa fim. Finafinan Hausa suna kokori wajen share wa mutane hawayensu. Har ila yau su ne a kan gaba ta wajen isarda sakonni zuwa ga al'ummar birane da kauyuka. Yanzu mu duba mu ga yadda aka samu ci-gaba, ko yadda mutane ma'abota kallon finafinan Hausa suke nuna goyon bayansu ta wajen aiko da wasiku zuwa ga mujallar Fim ko mawaka da jarumai maza da mata. To nan ma mai karatu za ka gane gamsuwar mutane da samun saukin fahimtar da suke samu a cikin finafinanmu.

Bari in ba da misali da fim din Akasi, inda Kabiru Nakwango ya nuna mana akwai alkalai wadanda suke yin hukunci na gaskiya ga duk wani mutumin da hukuncin ya hau kansa. Irin wadannan alkalan su ne masu nuna gaskiya a wajen aikinsu. Kuma su ne wadanda ba ruwansu da karbar rashawa da cin hanci, kamar shi Nakwango ya yi wa Shu'aibuLawan Kumurci a kotu. Na yi farin da na ji mutane suna yaba wannan shari'ar da aka yi a fim din.

Kuma sai na tuna, kwanakin baya lokacin da ina kauye wajen wani kawuna, na je hutu, na ji wasu samari suna yin hira a kan finafinan Hausa. Wani daga cikinsu yana cewa halin da Bashir Bala (Chirlki) ya aikata a cikin fim din Samodara, wai kamar an sani don akwai shugabanni wadanda suke aikata irin wannan halin a zahiri. To ka ga muhimmancin finafinai na Hausa yana kewayawa lungu-lugu yana wayar da kan jama'a game da al'amarin da ya shige masu duhu.

Dole in amince da zamanin nan namu na yanzu da kuma yadda ake samun ci-gaba sosai fiye da da. Ga kuma yanzu ana samun sababbin na'urori da ake amfani da su wajen inganta wannan harka.

AURE YANA HANNUN MAZA

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA so in yi wani dan tsokaci ga wasikar Hajiya Hadiza Mohamed Bawa da aka buga a cikin mujallar Fim ta watan Mayu 2002 inda ta ce rasuwar Balaraba "kalubale ne ga mata 'yan fim".

Abin da ban fahimta ba shi ne, shin idan 'yar wasan kwaikwayo ta rasu ba ta da aure ta yi mutuwa kenan mai muni? Kalmar 'kalubale' a nan ta zama wani irin gargadi mai razanaswa. Ni kuwa na fahimta cewa aure ba a hannun mace yake ba, a hannun namiji yake. Akwai mata bila'adadin da na san suna ta jiran miji amma bai samu ba. To shin ita 'yar wasa akwai wani wuri ne na musamman da aka ajiye mata mazan aure sai dai kawai ta zaba sadda ta ga dama? Maimakon kalmar 'kalubale', kamata ya yi H. Hadiza ta yi musu addu'ar Allah ya ba su maza nagari domin su aura, kasancewar aure ibada ce babba. Kuma yana da kyau a rika yi musu kyakkyawan zato, domin sana'arsu gyara mutane take a cikin annashuwa ba da bulala ba. Sana'arsu ta fi sana'o'i da dama da mata ke yi kyau. Wassalam.

Amina Abdulmalik,

Marubuciyar littafin Ruwan Raina, Farid Ventures, Wuse Abuja.

GAISUWA DAGA KASAR KAMARU

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

ASSALAMU alaikum warahmatul lahi wabarkatuhu. Bayan sallama ina fatar kuna nan lafiya inda muke nan lafiya a nan Yaounde Cameroon. Muna murna da gaske da irin burgue mu da irin shirye-shiryeku na Hausa. Ina bukatar kulla abokantaka da ku.

Bukatana shi ne ku turo mini hotunan 'yan wasa mata da maza ta komfuta ko kuma ta akwatin gidan waya (bp.760 Yaounde Cameroun). Madalla, mun bar ku lafiya.

Bako Abdoulaye

Malam Bako, zai kyautu ka zabi 'yan wasan da kake bukatar hotunansu, sai mu aiko maka. Ka san suna da dimbin yawa! Edita

KU BA NI ADIRESHINSU

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

BUKATA nake yi da ku turo mini da adireshin 'yan wasa na Hausa domin na rubuto ma kowa da wasikar shi. Ina fara gode muku. Allah ya ba ku lafiya, amin.

Idrissou Mohaman

Malam Idrissou, idan ka aiko wa da kowane dan wasa wasika ta adireshin wannan mujallar, za mu ba shi hannu da hannu.

SAURAN IBRO DANFODIYO KO?!

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA so don Allah ku ba ni fili a wannan mujalla tamu mai farin jini domin na ce wani abu game da Rabilu Musa (Ibro).

Ibro, hakika duk wanda ke kallon wasanka a halin yanzu ya san tuni tusa ta kare wa bodari. Yanzu don girman Allah idan dai an ce ana yin wasan Hausa ne domin fadakarwa, to wanne irin sako ne ke cikin fim din Ibro Dan Chana da Ibro Shehu Jaha? Kodayake ga shi ma yanzu ka yi Ibro Dan Daudu da Ibro Usama.To kuma kenan sai mu jira fim din Ibro Dan Iska, Ibro Dan Giya, da kuma Ibro Usman Danfodiyo, ko? Tunda kuwa Shehu Usman Danfodiyo (R.T.A.) da Osama bin Laden duk waliyyan Allah ne, masu jihadi bisa tafarkin Allah. Ibro! Ba girin-girin ba dai...!

Danladi Zakariyya Haruna

No. 1 Isa Waziri Road, after NITEL Office, P.M.B. 3164 Kano.

ME YA FARU DA KU A INTANET?

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

YAYA harkoki? Na yi kokarin karanta labarun da ke cikin mujallarku a intanet. Bayan na bude adireshin da kuka ba da amma sam babu abin da na gani. Me ya sa haka? Ko ba ku zuba labaran daidai ba ne?

Kabiru Anka

Malam Kabiru, muna jin dai lokacin da ka bude shafin namu muna cikin gina website din ne. Amma dai yanzu ka jaraba ka gani, komai ya yi daidai. Edita

KU NEMO FURODUSAN NA'IMA

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA son in yi amfani da wannan damar don in roke ku don girman Allah ku nema mana furodusan fim din Na'ima daga Bauchi don ku yi hira da shi. Dalili kuwa shi ne na karanta hirar da kuka yi da wani furodusa daga Bauchi, Dokta Hassan Yarima, kuma gaskiya yadda ya yi bayanai bai yi adalci ba domin yana cewa wai akwai sabbin furodusa masu tasowa daga wasu kananan hukumomi da sababbin finafinai, kuma gani na yi har yau babu fim din da 'yan Bauchi suka yi ya kai fim din Na'ima kyau balle har ya fi shi, amman sai Dokta Bello ya gwada bai ma san shi ba balle ya fade shi. Don haka muna rokon Fim ta sama mana furodusan Na'ima don mu ji labarinsa, kuma yaya ya yi shiru? Ko shi ma iyayensa sun hana shi shirin fim din ne? Daga karshe ina muku addu'ar Allah ya ja zamanin mujallar Fim, amin. Na gode.

Zainab Musa,

Maxgrade Nigeria Limited Bauchi, Airport Road, G.R.A. Bauchi.

Don Allah wakilinmu na Bauchi ka nemo furodusan Na'ima ku tattauna. Edita

KU KYALE AL'ADUN INDIYA

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA so in ba masu shirin fim shawara da su bar al'adun Indiya don Allah. Daga karshe zan mika gaisuwata ga uwar magana Zinaru da uban magana Ibrahim Mandawari. Masoyiyarku ce daga Jos. Wassalam.

Maimuna Galla

IBRO KA YI I-MEL MANA

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA so in ba da shawara a kan finafinan da ake yi na zamani. Abin da na ke so in fadi kuwa shi ne dan Allah a bar al'adun Indiya tunda ba al'adun Hausawa ba ne. In an lura finafinan da ake yi a da sun fi na yanzu koyar da al'adunmu. A karshe ina mika gaisuwa ga Ibro kuma don Allah ya bude i-mel. Wassalam.

Mohammed Shugaba

Msquare Home Vide, No. 5, Dogon Karfe, beside A.B. Galla's House, Jos, Jihar Filato.

MUN GAJI DA LABARAN LERE

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

NA rubuto wannan wasikar domin in bayyana damuwata da ta mutane da dama masoyan mujallarku. Damuwar ita ce yadda kuke ta ba da labarai da suka shafi furodusan nan Yakubu Lere, koyaushe kuna so ku nuna cewa shi wani waliyyi ne. Domin yau sama da shekara daya da wuya mutum ya sayi mujallarku bai ga wani labari ba inda ko dai Lere yana bobotansa ko kuma ku da kanku kuna wanke shi. Ko kun dauka ba a ganewa ne? To, mu dai mun gaji da wannan furofagandar. Shin babu wani furodusa ne sai Lere? Ko kuwa ya riga ya saye ku ne, ba ku iya wani katabus in babu shi? Ku daina ba mu kunya.

Habiba Umar,

Plot 3, Zakin Close, off Dodoma Street, Zone 6, Wuse, Abuja.

LERE, KA DAINA JA DA MANYANKA

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA so a mika sakona ga Yakubu Lere, a ja mashi kunne, saboda rigimarsa ta yi yawa; ya gama da 'yan wasa, ya koma kan manya. Ina so ya sani cewa su Mandawari sun fi karfinsa, ba ya iya ja da su, iyayensa ne ba abokan rigimarsa ba. Ya yi hatara, masu zuga shi za su kai shi su baro shi. Wassalam.

Asmau Lawal Wowo,

Wuse, Zone 6, FCT, Abuja.

LERE YANA WAYAR MANA DA KAI

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

DALILIN rubuto wannan takarda tawa shi ne domin na jinjina muku a kan wannan aiki, da fatan Allah ya taimake ku, amin. Bayan haka, zan yi amfani da wannan dama tawa domin na yi jinjina ga babban furodusa, Alhaji Yakubu Lere, domin ya cancanci a yaba masa bisa ga kokarin da yake na wayar da kanmu ta hanyar shirya mana finafinai masu ma'ana da kuma inganci. Da fatan Allah ya kara taimakonsa, amin.

Yisa Yusif,

Jeddah, Bab Sheriff, Saudi Arabia. Mobile: 053615278.

S.K. YA DACE DA KOWANE WASA

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

NA gani a mujalla wata Hafsa Abdulhamid tana cewa wai Sani S.K. bai dace da wani bangare ba a fim. Haba Hajiya! ki kara tunani a kan S.K. sosai. Ni na san duk inda aka kai Sani S.K. zai dace da matsayin. Ai Hajiya dole ne a yaba wa masa dari bisa dari, kuma ina rokon S.K. da duk wanda ya sa shi a bangaren 'yan daba, idan ya yi shegantaka sosai ya yi nadama sosai, domin tsoron hukuma. Idan kuma babu hukuma to ai Allah yana gani, saboda haka wannan aiki bai dace ba. Domin wanda duk bai daina mummunan aiki ba zai doku a ranar gobe alkiyama.

Bako Sakatare,

Bab Sharif, Jeddah, Saudi Arabia, mobile.054650519 Tel: 02 6433562.

A DAINA YIN 'KASHI NA 2'

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

BABBAN dalilin rubuto maku wannan wasikar shi ne domin in yi tsokaci kan batun yin kashi na 2 da ake yi a finafinanmu na Hausa. Yin haka yana rage mana son kallon finafinan. Dalili shi ne za ka kalli fim, amma bayan duk an gama nuna mana muhimman abubuwan da labarin ya kunsa, kammalawa kurum ya rage, sai ka ga an ce maka wai sai a kashi na 2 za a gama. Don Allah masu shirya fim ku daina yin haka. Ku rika gama kowane fim a kashi na 1, ba sai an je kashi na 2 ba. Na gode.

Ibrahim Haruna Dankofa Mun fassaro wannan wasikar ne daga Turanci. Edita

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin