Wasikun masu karatu
ABIDA KI CIJE KI DAURE KI ZAUNA
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA mai jin dadin fitowarku a kowane wata. Allah ya albakrci mujallar Fim, amin. Don Allah ina son a dan ba ni fili don in taya Abida murnar aurenta da kuma kira a gare ta. Don Allah ta daure ta kuma cije, ta kuma hakura, ta zauna a gidan mijinta, ko dadi ko wuya, kar ta ba mu kunya. Ina mata fatan alheri.
Abdul'azeez alh. Magaji,
Karamee Electronics, Kabala Junction, Kaduna. Tel.: 062- 216238
ZUWA GA ANGON ABIDA
ZUWA GA HAMZA MOHAMMED DANZAKI,
YA kai ango, yadda ka sami mata mai fasali, hakuri da kuma addini, to don Allah ka kyautata mata. Allah ya ba da zaman lafiya, amin.
Suleiman A. Jalli Gambo
Dept. of Educational Management, Bayero University, Kano.
MOMO KA RIKE MARYAM DA KYAU
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
NA rubuto wannan wasikar ne domin in nuna murna da farin ciki da auren Aminu A. Shariff (Momo) da Maryam Mohammed. Da ma aure shi ne mutuncin 'ya mace da namiji. Shawara ga Momo ita ce don Allah ka rike matarka hannu biyu-biyu kuma ka rike alkawari, ka hada da hakuri, domin mata sai da hakuri. Na san mai suna Maryam akwai ta da hakuri da iya zama da mutane.
Abdul- 'Abdu Cake',
No. 4 Bima Road, Kaduna.
ALLAH YA ZAUNAR DA HALIMA
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA rokon editan wanna mujalla ya dan ba ni fili in mika sakon gaisuwata da nuna farin cikin abin da ya faru da Best Actress of the Year 2001, Halima Adamu Yahaya. A gaskiya ina mai matukar jin dadi kan wanna auren da ta yi domin irin fatan da ta yi a wannan mujallar na Allah ya sa wannan aure shi ne karshen auren da za ta yi a duniya, amin. Halima Allah ya ba ki zaman lafiya mai dorewa, kuma Allah ya ba ku hakurin zaman lafiya, amin.
Mustapha Challube,
Insha Allahu Oil Nig. Ltd., P.O. BOX 1061, Gamboru Road, Maiduguri. Tel.: 076 235558.
MUJALLAR FIM TANA TAIMAKAWA
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
SANIN kowa ne cewa sha'anin shirya fim na Hausa tun farko ya samu suka da korafi, amma daga baya ya samu karbuwa a kowane bangare na kasar nan da sauran kasashe inda Hausawa suke. Wannan ci-gaba ya samu ne sanadiyyar mujallar Fim, wadda Malam Ibrahim Sheme yake wallafawa. Wannan bawan Allah ba karamar gudunmuwa ya bayar ba, don da wannan mujallar ne aka haskaka wannan sana'a ta fim a duk fadin duniyar nan. Saboda muhimmancin wannan mujalla da adabin da ke cikinta, hukumar binciken al'adun gargajiya ta duniya, wato Global Instute of Culture Studies, ta yarda a ajiye mujallar Fim a dakin karatu na bincike saboda tasirinta da adabin da ke cikinta. Mawallafin ya cancanci yabo saboda kirkirar wannan mujalla don yada finafinan Hausa da kuma ba kowa 'yancin fadin ra'ayinsa game da sha'anin fim.
Abdulkarim M. Bashir Al'Arabi,
No. K11/25, Saminaka Road, Unguwar Kanawa, Kaduna.
WAI INA ZABIYA ZUWAIRA TAKE?
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
ABIN da ya sa na rubuto wannan wasika shi ne, na karanta a mujalla, inda na ga kun buga hira da mawaka mata, amma ban ga kun rubuto zabiya guda ba, wato Zuwaira. Ko babu ita ne?
Isma'ila Lawal Abubakar Saulawa,
c/o Salamah Video Centre, Sabon Layi, Katsina.
Aure dodon mata ne ya dauke zabiyar finafinai, Zuwaira Isma'il Durumin-Iya. Mun je an ce har ta samu karuwa. Wasu fitattun zabiyoyin da suka yi aure su ne: Fati Abubakar, Jamila Mohammed Sabo, Rabi Mustapha, Maryam Saleh, da Maryam Mohammed.
INA SON MUJALLARKU, SAI DAI...
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
DON Allah ku ba ni fili in isar da gaisuwata zuwa ga mujallar Fim. Wannan mujallar tana burge ni kwarai da gaske. Sai dai kuma kash!, ban san yadda zan yi domin samun wannan mujalla a kowane wata ba tare da yankewa ba. Ina fata za ku aiko mani da hanyar da zan bi domin samun wannan mujallar.
Ramalan A. Ahmed
Primary Health Care Department, Gwagwalada Area Council, P.M.B. 01, Gwagwalada, F.C.T. Abuja.
ALLAH YA BA AMINU BALA BASIRA
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA gaida mutanen ma'aikatar Fim. Ina son in yaba gwanin gwanayena, wato Aminu Bala, furodusan fim din Ludufi da Lawisa da kuma Mishkila. Gaskiya Aminu yana taimakawa da kuma wayar da kan mutane ta fannin fim; ga shi yaro amma ga basira Allah ya ba shi. Allah ya kara masa basira. Muna jiran sabon fim dinsa.
Gaisuwa ga Hadiza Kabara, Ibrahim Maishinku, da Hamisu Iyan-Tama.
Alhaji Modu Matami,
Yunusari, Yunusari LGA, Jihar Yobe.
MU RIKA YI WA 'YAN FIM ADDU'A
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
DALILIN wannan wasika tawa shi ne don ina taya wasu 'yan wasa farin ciki da jin dadi na auren da suka yi, kamar su A.A. Sharif da Halima Adamu Yahaya da Abida Mohammed. Allah ya sanya alheri amin. Allah ya kai mu na su Maryam da Ahmed su ma. Ina kira ga masoyan 'yan fim su ci gaba da yi masu addu'a don ko wacce da lokacinta na aure ya zo za ka ga ta fice sai labari. Allah ya kara taimaka maku ku ma masu mujalla da kokarinku na gaskiya.
Mukhtar Ya'u Chiranchi (Rabe),
No. 68, Chiranci Gwale L.G.A., Kano.
MAI ISKA, AI MUTANE RAHAMA NE
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA maida wa Sani Mai Iska magana ko martani a kan batunsa na cewa ana damun Fati da ziyara. Gaskiya Sani ka ba mu kunya. Ba ka san cewa mutane rahama ba ne da har kake furta cewa mutane sun zame wa Fati masifa? A hirarku ta dawowa daga London ne ka yi wadannan maganganu wadanda suka bata mani rai. Kada ka zama butulu mana, domin ai Allah ya yi maka rahama. Kada ka yi izgili da rahamar da ya yi maka!
Hajiya Na'imatu Sani Bature,
P.O. Box 95, Katsina. Tel 065 - 432417.
KIRA GA BALARABA RAMAT
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
ANTI Balaraba ina son don Allah a filinki na "Rayuwarmu" ki ba da shawara a kan irin matan nan masu yi wa kishiya karyar baka, wadda ta fi ta boka; ko me kishiya ta yi sai an gaya ma miji (karya da gaskiya). Wane mataki ya kamata ta ta dauka idan irin haka na faruwa?
Umma Gambo
No. 18, Yar'Adua Close, Batagarawa Low-Cost, Katsina.
MUJALLAR FIM MUN GODE
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
NA rubuto wannan wasika domin in bayyana matukar jin dadia, da gamsuwa, da sha'awa ga wannan aiki da kuke yi domin ku wayar da kanmu a kan abin da ya shafi harkar finafinan Hausa.
Abubakar Alh. Adam,
Finance Department, Kukawa LGA, Jihar Borno.
INA KAUNAR HAUWA MAINA
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA daga cikin masu karanta mujallarku mai farin jini saboda samun sahihan labarai game da 'yan wasan Hausa, musamman kamar su Abida Mohammed, Hauwa Maina, Ali Nuhu, Mandawari, Iyan-Tama, da dai sauransu. Zan yi matukar farin ciki idan har kuka samu zarafin isar da kaunata ga Hauwa Maina. Hakika in daga cikin masu kaunarta kuma finafinanta suna burge ni.
Ramalan A. Ahmed
Primary Health Care Department, Gwagwalada Area Council, P.M.B 01, Gwagwalada, FCT Abuja.
GAISUWA GA GWANAYENA
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
DA farko ina yi Wa Shu'aibu Lawan ta'aziyyar matarsa Balaraba Mohammed. Allah ya jikanta, amin. Na biyu don Allah edita ka aika gaisuwata ga Aminu Shariff (Momo) da Alh. Ibrahim Mandawari da kuma dattijon kirki Alh. Isa Bello (Ja).
Sanusi Tanko,
Hospital Services Management Board, P.M.B. 02266, Sokoto.
YABON ISHAQ SIDI YA ZAMA DOLE
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA son in yi amfani da wannan dammar in yaba wa shahararren daraktan nan Ishaq Sidi Ishaq, domin yabon gwani ya zama dole. Saboda na ji dadin finafinan da ya ba da umurninsu, kamar Wasila, Uzuri, Laila, da sauransu. Da fatan Allah ya kara masa kwazo da basira, amin.
Musa Judicious,
M.C. Rap, Area 1, Beach Island, Ibi , Jihar Taraba.
AYYUKAN ISHAQ SUN DACE
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
NA rubuto wannan takarda domin in mika sakon gaisuwata, jinjinawa, yabo da kuma fatan alkhairi ga darakta Ishaq Sidi Ishaq. A gaskiya, tun da dadewa na so in rubuto domin jinjina ga wannan kamili, haziki, kuma jarumin darakta wanda gudunmawarsa ga shirin finafinan Hausa ba ta misaltuwa. Babu shakka a duk finafinan da Ishaq ya yi darakta ko kuma ya fito ciki a matsayin dan wasa, to za ka taras sun hadu kuma sun tsaru, sannan kuma finafinan za su zo daidai da bukatu da kuma ra'ayin akasarin masu kallo da kuma sha'awar finafinan Hausa.
Hayatu Dan Galadima Wamako,
Shehu Shagari College of Education, P.M.B. 2129, Sokoto.
BATUN BALARABA YA RUDA MU
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
A HAKIKANIN gaskiya mutane da yawa a nan Nijar sun yi matukar girgiza a lokacin da suka tabbatar da mutuwar Balaraba. Duk sakon da ka shiga ba abin da kake ji sai maganar, saboda farko ba wanda ya tabbatar da maganar, amma ba abin da nake cewa a lokacin dalili kuwa shi ne mujallar Fim ba ta fito ba. Edita, za ka yi mamakin yadda mutanenmu a nan Nijar suka nuna alhini a kan wannan rashin. Dalilin haka kuwa shi ne muna da dimbin masu sha'awar finafinan Hausa, misali a nan Jihar Damagaram masu sha'awar finafinan sun kai kashi 80 cikin dari na jama'ar jihar.
A madadin dukkan mutanenmu a nan Jihar Damagaram ina mika ta'aziyyarmu zuwa ga iyaye, 'yan'uwa da kuma Shu'aibu Lawan wanda bayanin da ya yi maku a Fim ta watan Mayu ya sa muka zubar da kwalla a lokacin da muke karanta mujallar. Hakikanin gaskiya Shu'aibu ya nuna karfin imani wanda samun kamarsa yana da wuya. Allah ya kara ba su hakurin jure wannan rashin, su kuma Allah ya jikansu.
Hamisu Muhammed,
Zambarawa Tsatsumburum, Jihar Damagaram, Jamhuriyar Nijar.
GOLOBO YI HANKALI DA SHARI'A
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA so in bada shawara ga shahararren dan wasan nan, wato Golobo. Na ji abin da ya fada a ranar Talata, 11/06/2002, a cikin shirin safe na gidan rediyon B.B.C. Na ji yana cewa wai Shari'ar da ake yi a Jihar Zamfara ta hana shi cin abinci. To Golobo, ka fa yi hankali domin mu yanzu talakawa Musulmi ba abin da muke so irin ita wannan Shari'a. Saboda haka kada ka sake ka soki Shari'a. Idan kuma ka soke ta, to ko kai wanene za mu saba da kai. Kuma ka sani kai Musulmi ne, ai ka yi imani da cewa duk abin da zai same ka ko za ka samu an riga an rubuta tun kana cikin cikin mahaifiyarka. Kuma Musulunci ya nuna mana duk abin da ya kufce maka da ma an rubuta ba zai same ka ba, kuma duk inda rabonka yake to yana nemanka fiye da yadda ajalinka yake nemanka. Saboda haka Golobo Shari'a ba za ta hana ka cin abinci ba. Domin Shari'a wajibi ne ga dukkan Musulmi. Wajibi ne a gare ka ka san yadda ka yi ta ci gaba ba ka bata ba. Ka fa sani duk abin da kafa da an rubuta shi kuma sai an tambaye ka. Haba Golobo! kwanan duniya nawa ake yi har za ka damu da abincin cikinta fiye da lahirarka? Ka duba Manzon Allah da sahabansa an jarrabe su da yunwa lokacin da suka yi kokarin kafa Shari'a, to balle kai na baya. Kuma kana so ka shiga inda suka shiga a lahira. To ka kiyaye, wannan fadakarwa ce domin na san ka san komai, illa dai kawai aikin makiyinyinmu korarre daga rahamar Allah ne ya sa ka fadin waccan magana.
Muhammadu Aminu Bello Mani,
Kangiwa Kwatas, Mani, Mani L.G.A, Jihar Katsina.
KU BA NI TARIHIN NAKWANGO
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
DON Allah ina so ku yi mana hira da shahararren dan wasan nan Malam Kabiru Nakwango domin mu san tarihin rayuwarsa, da yadda har ya shahara wajen iya fim. Domin kuwa ni a gaskiya yana burge ni. Saboda duk bangaren da ya fito a fim to kuwa zai nuna gwaninta, ga kuma wa'azi da ilimintarwa da yake ma jama'a.
Suwaiba Shehu Idris,
No. U35, Hausa Road, D/Bauchi, S/Gari, Zariya, Jihar Kaduna.
A takaice
Adamu Umar ya yi amarya ya maye gurbin Jummai
MUNA daf da zuwa madaba'a muka samu labarin cewa mijin marigayiya yayar Balaraba Mohammed, wato Jummai, ya yi aure.
Wata kwakkwarar majiya ta shaida wa Fim cewa Adamu Umar ya auri wata mace a garin Tafa cikin Jihar Kaduna kan hanyar zuwa Abuja kimanin wata daya bayan rasuwar A'isha Jummai a hadarin da ya ritsa da kanwarta uwa daya uba daya, 'yar wasa Balaraba, da wasu 'yan'uwanta. Ya sake cike mata biyu kenan. A kwanan baya mun kawo maku sunayen wasu masu ta'aziyyar rasuwar Balaraba Mohammed, wadda Allah ya karbi ranta a cikin watan Maris na bana. Mun gaya maku cewa ba za mu buga kalaman da mutane ke yi na ta'aziyya ba domin kusan duk maimaitawa ne. To, daga lokacin da muka buga wadancan sunayen, mun kara samun wasu. A yau ga su mun kawo su. Wanda bai ga sunansa ba sai ya yi hakuri. A madadin iyalan marigayiyar muna godiya ga dukkan wanda ya aiko da sakonsa na ta'aziyya . Ita kuma Allah ya jikanta, amin.
KU RIKA BOYE WASU ASIRAN
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
NA rubuto wannan takarda ne don nuna farin cikina da murna a kan namijin kokarin da kuke yi a mujallarku mai farin jini wadda komai rintsi ba na bari ta wuce ni a duk wata. Allah shi kara mana taimako, amin summa amin.
Bayan haka ina son in yi amfani da wannan dama in ba ku wadansu shawarwari kamar haka:
a). Don Allah ku dinga yin kokari kuna dan boye wadansu asirai na masu rubuto maku takardu domin akwai abin da nake ganin bai dace ku buga ba amma kuna bugawa. Misali:
i. Kamar wani yakan rubuto maku cewa yana neman aiki a mujallarku ko a shirya fim ko makamancin haka. Ina ga kamar wannan bai kamata a tallata shi ba, kuma har ma wani yana aiki a wani wuri, to ka ga fadin wannan zai sa ko da ba ku dauke shi ba su wurin aikinsa su kyamace shi saboda jin yana son ya gudu ya bar su.
ii. Haka mutumin da zai rubuto ya ce maku yana son ku hada shi da wata 'yar fim yana son ya aure ta bai kamata ku yi wuf ku tallata wannan ba domin Manzo (S.A.W.) da kansa ya ce ku boye neman aure amma ku bayyana daura shi domin kowane abu da yake da ni'ima to yana da mahassada.
iii. Haka kamar mutum ya yo wa wani ko wata 'yar wasa wasika ta hannunku, ya kamata a ce ku bai wa wanda aka rubuto wa wasikar, kuma in yana da wata amsa ya yi amfani da adireshin mai rubutun ya aika masa da amsar. Amma sai ka ga kun rubuta wasikar a cikin mujallarku. To ka ga a nan zai rage wa wadansu kwarin gwiwa wajen aika irin wannan sakon, domin ba kowa ne yake son a tallatas hi a duniya ba.
Mal. Ahmed Usman Sufy,
Malam Ahmed, mun gode da wadannan shwaarwarin. Sai dai kuma a inda kake maganar masu rubuta wa 'yan fim wasiku muna bugawa, a gaskiya su ne suke son a yi hakan. Idan mutum ya rubuto wa dan wasa wasika, ya sa sunan dan wasan a jikin ambulon din, to ba mu ko budawa muke mika masu hannu da hannu. Idan imel ce, mukan buga ta a takarda daga intanet mu ba wanda aka rubuto mawa. Wassalam. Edita
WASIKA GA RUKAYYA DAWAYYA
ZUWA GA MASOYIYATA RUKAYYA,
GAISUWA mai yawa tare da fatan alheri. Yaya gida da kuma ayyukan yau da kullum? Ina fatan komai yana nan lafiya. A gaskiya Rukayya kina matukar burge ni da finafinanki. Allah ya sa ki ci gaba da dorewa haka, amin.
Zangina Isyaku.
Physics Dept., BUK, Kano.
KU DAINA KARA KUDI DON ZUGA!
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
NA rubuto domin in yi magana a kan wani abu da kullum ke faruwa a kan mujallar Fim da ta Bidiyo. Ina so in gaya maku cewa a gaskiya abin naku ya fara yawa. Saboda me kullum sai kun kara kudinsu? Tun Fim tana N100, kuka kara ta zama N130. Ba a dade ba kuka maida ita N150, duk ba a damu ba. To yanzu kuma kun maida Bidiyo N130.
To kar ku yi amfani da washin da wasu ke yi cewa ko Fim ta kai N500 ba ta yi tsada ba. A gurin wani haka ne, a gurin wani kuma ba haka ba ne. Saboda wani na da hali wani bai da shi. Haka ma Bidiyo kuna N100 kun maida ita N130. To ya kuke so mutane su yi? A kan mujallun Hausa guda biyu sai mutum ya ajiye kusan N300! Kuma ko wanda ake shigowa da shi daga kasar waje bai kai naku tsada ba. Kuna cewa tun hawan Obasanjo ne komai ya tashi. Amma bai kamata a ce kuna cika wa komai kudi har da Bidiyo, wadda shafinta ba su kai 30 ba. Don Allah a dinga lura
Jamila Sirajo
Hajiya Jamila, gaskiya ba zuga ce ke sa muke kara kudi ba a duk lokacin da hakan ya faru. Kamar yadda kika yi tsokaci, farashin kayan aiki ne suke tashi a nan kasar, ba kamar yadda abin yake ba a kasashen Turai ko Amerika. Ko a ranar 24 ga Yuli, 2002 sai da masu sayar mana da takarda suka yi karin farashi, ban da wanda suka yi watanni uku da suka wuce. Duk karin da aka yi a bana bai sa mun kara farashin mujalla ba don kada mutane irinki su yi kuka da mu. Amma muna son a yi hakuri da hakan domin ba laifinmu ba ne. Mu ma mun fi son kayan aikin su yi arha, ta yadda za mu iya sayar da mujalla ga kowane mai karamin karfi. In dai ba mu kara farashi ba, to sai dai mu rage yawan shafuka kenan. Game da mujallar Bidiyo, tun da ta fito a shafi 44 take, ba 30 ba. Da fatan kin lura, kuma farashinta bai kai na Fim ba. Mun gode. Edita
GAISUWA GA HAFSAT ILIYASU
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
Na rubuto maka wannan takarda domin, in sami fili a cikin mujallarka, don in nuna irin son da nake yi wa Hafsat Iliyasu, saboda ta can-canci a yaba mata wajen taka rawa a wasannin Hausa. Ina jin dadin kallon wasa matuka idan da Hafsat a ciki, kamar wasan Dabia, Garwashi, da sauransu. Kuma idan ba za ta damu ba ina son ta aiko min da adireshinta da takaitaccen tarihinta. Sannan me ya sa ba ta yawan fitowa a wasanni sosai?
Daga karshe, ina mika gaisuwa ga Editan Editoci na mujallar Fim, Ibrahim Sheme, saboda na yaba da kokarinsa wajen ilimantarwa da fadakarwa da kuma kara dankon zumunci tsakanin 'yan wasa da mu masu kallo. Allah ya bar zumunci, ya yi mana jagora, amin.
Abdu Danyaro Minjibir
Social Studies, Departmnet of Social Studies, F.C.E., Kano.
TAYA MURNA GA MOMO, HALIMA...
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
NA rubuto wannan sako ne domin na taya Aminu Shariff (Momo) murnar auren da ya yi, da fatan Allah ya ba su zaman lafiya. Haka kuma ina mika sakon taya murna ga Anti Halima Adam Yahaya a kan aurenta, da fatan Allah ya sa mutuwa ce za ta raba. Sai kuma gwanata, wato Abida Mohammed, ita ma Allah ya sanya alhairi, ya albarkanci wadannan aurarraki, amin.
Daga karshe ina fatan za ku mika min sakon gaisuwata ga yayana Sani Yusuf Ayagi, da kuma Anti Jamila Haruna.
Isa Yusif Ayagi,
Bab Sheerif. Telephone: 02-6482413. Mobile: 05 477 3049. 05 258 0590. Saudi Arabia, Jeddah.
INA TAYA ABIDA MURNA
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
ALLAH ya kara wa mujallar Fim farin jini kamar watan Sallah, amin. Dalilin rubuta wasikata shi ne don na taya Abida Mohammed farin cikin yin aurenta. Na sami labarin cewa ta yi aure ba tare da an baza a duniya ba; shi ne abin ya ba ni mamaki. To Allah ya ba da zaman lafiya ita da mijinta, ya ba su zuri'a tagari, amin, kuma sauran da ba su yi aure ba Allah ya ba su maza nagari, amin. Don Allah ina son a mika min sakon gaisuwata ga babana Tahir M. Fagge da Hamisu Iyan-Tama, Hadiza Kabara, da Alhaji Mandawari.
Yakura Sadi Baraya,
c/o Gambo Barau Potiskum.
GAISUWA GA JARUMAI
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
MUNA mika gaisuwata ga jaruman 'yan fim masu burge mu kamar su Ahmed S. Nuhu, Ali Nuhu, Abida Mohammed, Maryam Mushaqqa, Hadiza Kabara, Shu'aibu Lawan (Allah ya jikan Balaraba, amin!), da sauran 'yan fim.
Muhammed Isma'ila da Abubakar Abdulrahman
ALI, YAYA KA YI SANYI KUMA?
ZUWA GA ALI NUHU,
WAI shin don Allah Ali Nuhu yaya nake jin ka shiru ne cikin 'yan kwanakin nan? Yaya na ga ka yi coool kamar ba ka a cikin duniyar finafinan Hausa? Haba Ali! Ya kamata ka yi wani yunkuri ka yi fitar barden guza cikin wannan lokaci, saboda a gaskiya dimbin masoyanka suna nan suna zuba idon ganinka a bayyane cikin sababbin finafinan Hausa. Allah ya kara maka basira da juriyar zama da mu. Na gode.
Baba Giade
Giade L.G.A., Jihar Bauchi.
INA HUKUMAR TACE FIM TA KANO?
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
DON Allah ina hukumar da gwamnatin Jihar Kano ta kafa don tace finafinai take ake watsa wani shiri mai suna WEBS a gidan talabijin na STV? Ya kamata a dakatar da wannan shiri ba tare da bata lokaci ba. Ma'assalam.
Rabiatu Abbass Ibrahim
afrid@justice.com
INA GANIN BEKEN KASAGI
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
NAKAN yi mamaki a duk lokacin da na ji Ummaru Danjuma Katsina (Kasagi) yana korafi a kan finafinan Hausa. A nasa ra'ayin yana so a rika amfani da "professional" mawaka a kuma daina nuna samari da 'yanmata suna waka a wurare kamar lambu ko bakin rafi da sauransu. A tunaninsa hakan ya saba wa al'adun Bahaushe.
Idan yana nufin a rika sa su Sani Dan-Indo ko Dahiru Kakkabi ne, to ya sani cewa harkar ba irin tasu ba ce. Maganar an saba wa al'adar Hausa kuwa sai in ce ba haka ba ne domin kuwa (ga misali) mu a nan Katsina ba bakon abu ba ne budurwa ta wake saurayinta ko saurayi ya wasa sahibarsa musamman a rayuwa irin ta karkara. Kai, na tabbata idan aka ba Kasagi dawainiyar shirya fim a kan tatsunniyar nan mai farin jini a wannan yanki ta "Kai Musa-kai Musa, dan makaranta Musa….," dole ne sai ya hada wani saurayi da wata budurwa waka a wani muhalli mai itatuwa, da kududdufi tare da ciyayi da furanni. Mun kuma san cewa tatsunniya bangare ce ta al'adun mutane. Don haka Kasagi sai a gyara.
Muntari Lawal Tsagem
NOA, Katsina State.
c/o
KU SA KALA A FILIN ABOKAI
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
NA taba karanta wata wasika da wani yake ba ku shawara cewa ya kamata mujallar nan taku ku dinga buga ta mai kala gaba daya, to amma na ga hakan bai yiwu ba.To ni shawarata a nan ita ce wajen filin abokanku da kuke sa hotunansu ya kamata ku dinga buga su mai kala. Da fatan wannan shawara tawa za ta samu karbuwa a gare ku. Kuma don Allah ina so ku sanar da ni idan mutum zai aiko muku da hoto cikakken hoto zai aiko muku? Ko kuma ko da hafbodi ne? Kuhuta lafiya.
Auwalu Turawa Gayawa
Unguwar Yamma, Ungogo LGA, Jihar Kano.
Malam Auwalu, za ka iya aiko da hoto mai fadi ko hafbodi, to amma mun fi son mai fadin, kuma ya kasance ka fito radau a hoton. Sa'annan za mu duba shawararka. Mun gode.
MUTUWAR BALARABA KO SIHIRI?
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
SHIN wai yaya gaskiyar mutuwar Balaraba? Mutuwar ta yi ko sihiri ne? Mutane sun cika cewa Balaraba bata mutu ba kuma ni na karanta a mujalla cewa ta mutu. Misali kamar irin littafin shahararren marubucin nan Maje El-hajeej mai suna Sirrinsu, mutane suna kawo hujja da shi wai suna ganin kamar yadda ya faru a cikin wannan littafin shi ne ya faru ga Balaraba.
Bugu da kari, shin wai gaskiya ne an sace Ibro? Sannan kuma don Allah a isar min da gaisuwata ga Musbahu M. Ahmad, Zulkifilu Muhammad, Hadiza Mohammed Kabara, da Rukayya Dawayya.
Sai na ji daga gare ku ko kuma sai na karanta a mujallar wannan watan da muke ciki.
Muhassin Sani,
House No. 30 Marafa Danbaba Road, Sokoto.
Muna jin ya zuwa yanzu dai ka karanta Fim ta watan jiya inda muka karyata labarin "dawowar" Balaraba. Mutane ne kurum suka yada ji-ta-ji-tar maras tushe. Batun Ibro kuwa, ka karanta labarinsa a cikin fitowarmu ta wannan watan. Mun gode.
SHAIDANU SUKA BAZA LABARIN
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
A GAME da labarin da ya mamaye sassan wannan kasa na cewa wai Balaraba ba ta rasu ba (Fim, Yuli 2002), to ni dai abin da zan iya fada a nan shi ne kowa dai ya san mutuwa guda ce, sannan kuma Allah shi ne mai rayawa kuma ya kashe a duk lokacin da ya so ba kuma tare da ya shawarci kowa ba a lamarinsa.To saboda haka ina mai jawo hankalin mutane cewa kada su yarda Shaidan ya sa su cikin rudani. Wanene Shaidan? Wanda ya fara baza wannan labarin mai ban al'ajabi da rashin dadin ji.
Allah ya kare mu daga sharrin Shaidanu maza da mata, kuma ya kiyaye mu cikin kiyayewarsa, amin.
Baba Giade,
Giade L.G.A, Jihar Bauchi.
WAI ME KE DAMUN IBRO NE?
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
SHIN me yake rudin Rabilu Musa (Dan Ibro) har acikin shakiyancinsa yake taba addini? Shin yana zaton zai taba bayin Allah Allah ya kyale shi? Wadanda suka tara dukiya amma ba ta rude su ba suka ce sun ji sun gani ba kowa ba komai sai Allah, sai Manzonsa sai addininsa, amma wai su ne abin mayarwa wasan Hausa? In ba ku gane ba, ina nufin Ibro Usama. To wallahi in zai ci gaba da taba addini za mu roki Allah ya wulakanta shi da gaggawa!
Abubakar Aminu
KIRA GA FURODUSOSHI
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
DON Allah me ya sa ba a yin amfani da kyamara mai kyau ne wajen daukar finafinan Hausa? Saboda yanzu 'yan Nigerian films sun fi mu komai mai tsari ko da wajen bidiyo C.D. suna yi sosai yanzu don yawancin fim nasu duk da shi suke yi. Shi ne nake ba da shawara don Allah a san abin da za a yi namu ya yi kyau.
Gambo Barau Potiskum
KU BA NI ADIRESHIN SU AINA'U
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
WANNAN shi ne sakona na farko zuwa gare ku. Na rubuto domin neman sanin adireshin jarumai Aina'u Ade da Ahmed S. Nuhu, ba don komai ba kuwa sai domin burge ni da suke yi a finafinan da suke fitowa. Saboda haka na ke rokon wannan mujallar mai farin jini ta taimake ni da adireshin da zan rika turo sako zuwa ga wadannan 'yan wasa masu tashe da farin jini.
Ina so ku isar da gaisuwa da fatan alheri ga Ali Nuhu, Aminu Shariff (Momo), Abida Mohammed, Ishaq Sidi Ishaq, Sani SK, Sani Musa Danja, Shu'aibu Lawan (Kumurci), A'isha Musa, A'isha Ibrahim, Tahir Fagge, Hajara Usman, Hauwa Ali Dodo, Ibrahim Mandawari, Shehu Hassan Kano, Alhassan Kwalle, Wasila Isma'il, da darakta Hafizu Bello da daraktan daraktoci Tijjani Ibraheem.
Abdullahi Abdullahi Jr.,
Kawo New Extension, Kaduna.
Hanya mafi sauki da sakonka zai isa ga Aina'u ko Ahmed ko kuma kowane dan fim ita ce ka aiko da wasikar ta hanyar adireshinmu, mu kuma sai mu ba su.
SHIRIN C.I.D. YA YI KYAU
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
DON Allah ina son ku mika min sakon gaisuwata ga darakta Mohammed Garba Kabara da kuma furodusan fim din C.I.D. Wannan fim gaskiya ya burge ni kuma an yi kokari sosai a cikinsa. Na sami labarin cewa wani darakta aka so ya yi fim din to amma daga baya sai aka sami canji. Gaskiya C.I.D. ya yi albarka ya kuma yi kyau.
Zainab Haneef
TASLEY, USA.
KIRA GA IBRAHIM MANDAWARI
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
MUN rubuto maku wanna takarda ne don mika shawararmu ga Ibrahim Mandawari da ya sanya mana bankwana da Abida Mohammed a Mu Shakata na 5. A karshe muna mika gaisuwa ga Musbahu M. Ahmed saboda ya dade yana burge mu matuka, sai kuma Ibrahim Mandawari, Ahmed S. Nuhu, Ali Nuhu , Momo, Sani S.K. , Saima Moh'd, Abida, Fati Fagge, Aina'u Ade, da Hadiza Kabara. Kuma muna taya Abida murnar aurenta. Sannan muna mika ta'aziyya ga iyayen Balaraba da mijinta.
Fatima F. Abdullahi
No. 5b, Kamsalem Road, Malali, Kaduna.
KU BAN HOTON SU SANI DANJA
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
NA rubuto wannan wasikar ne game da hoton su Sani Musa wanda kuka sanya a mujallarku ta wani watan baya wanda suka yi su hudu a Saudiyya. Don Allah ina son ku aiko min da shi. A karshe ina kira ko bayar da shawara ga matan aure masu rubuta wasikun zuwa ga mujalla da su dinga sanya kalmar 'Mrs.' don tabbatar da cewa matan aure ne. Hakan na da amfani matuka.
Gaisuwa ga dukkan 'yan wasa, furodusoshi da daraktoci tare da mawakan finafinai baki daya.
Lawal Usman,
Sarki Abdurrahaman Way, G.R.A., Katsina.
Malam Lawal, ka duba inbox na e-mail dinka, mun aiko maka da wannan hoton da kake bukata. Edita
TA'AZIYYA DAGA BULGERIYA
ZUWA GA SHU'AIBU LAWAN (KUMURCI),
BAYAN dubun gaisuwa mai yawa, da fatan kana lafiya. Bayan haka yaya hasafi game da abin da ya faru na rasuwar amaryarka? Ina fatan Allah shi kara ba ka hankuri. Abin da ya sa ka ga wannan wasika tawa shi ne don ni ban san abin da ke faruwa ba sai yanzu da na budo website na mujallar Fim a intanet sannan na gani, don wallahi bai yiwuwa mu sani in ba tawannan hanya ba ta mujallar Fim, don muna nesa. Don ni da ke wannan magana daga Bulgaria nake wannan magana, domin ina karatuna a nan. Don Allah idan akwai yadda za a yi ina bukatar fim dinka Shu'aibu.
Nasiru Umar Wurno
Daga Bulgaria.
KABARA BA TA DA MAGAYA NE?
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
LALLAI Magana ta inganta a kan cewa Duk wanda kuka ga cewa ba ya jin kunyar mutane, to Allah ma ba zai ji kunyarsa ba. Kuma ita kunya tana daga cikin imani. Ashe kenan duk wanda kuka ga ba shi da kunya to imaninsa ragagge ne.
Dalilin da ya sa nake fadin irin wadannan maganganu kuwa shi ne, ganin yadda wasu 'yan wasa suke fitar da kunyarsu suna fakewa da fim su dinga zubar da al'adun Hausa da mutuncinsu da kuma watsa tarbiyyar yara matasa masu kallonsu. Zan buga misali da wata yar wasa mai suna Hadiza Kabara da na kasance ina matukar son wasanta amma saboda yadda take nuna rashin kunyarta a fili ya sa na dawo daga rakiyarta. To tambayata a gare ki Hadiza ita ce, shin ba ki da magaya ne? Don kuwa duk mutum mai magaya ba zai saida kunyarshi ba don neman abin duniya kamar yadda kika saida ta a fim din da kika yi na Asali 2. Don kuwa duk mutumin da ya san darajar kansa ba zai dinga irin rashin kunyar da kika yi a cikin wannan shiri da sauran irinsa ba.Kuma ki daina tunanin wannan abin da kike yi farin jini zai ja maki, wallahi babu abin da zai jawo maki face bakin jini wurin jama'a masu kallonki da kuma masu kaunarki. Don haka ina mai ba ki shawara da ke da masu dabi'a irin taki da cewa a dinga sara ana duban bakin gatari, ba don komai ba ko don tarihi yai kyau.
Muhammad Sagir Al-kasim,
No. 6, North Road U/Shanu By Abakwa Border, Kaduna.
Tel:062-240454. sagir_alkasim2000@yahoo.com
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin