Wasikun masu karatu
KU RABA MANA GARDAMA
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA so ku taimake ni ku raba mana gardama da muke yi da abokaina. Wai shin Fati Mohammed kafin ta yi aure ne aka sata ta yi talllar kwandom (robar maza) ko kuma bayan ta yi aure ne? Domin ganin da muke mata a cikin gidan talbijin din DITV Kaduna tana tallar shi ne ya kawo mana gardamar da ta ki karewa tsakaninmu da abokaina., saboda na ce kafin ta yi aure ne, amma su sun ce bayan ta yi aure ne. Hujjarsu a nan shi ne don sun gan su tare da Sani Musa Mai Iska, wato maigidanta.
Bashir Moh. Bashir Turawa,
No. B4, Layin Dan Dambe, U/Kanawa, Kaduna.
Bayan Fati ta yi aure ne ta yi tallar domin yaki da kanjamau.
INA YABA WA HADIZA KABARA
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
A GASKIYA Hadiza Kabara ta zama abar yabo a wurina, domin ta iya wasa. A duk inda aka sa ta za ta iya, saboda haka dole mu yabe ta. Kuma ba ta da girman kai. Ga fara'a, ga kyau, ga kuma iya zama da mutane.
Buhari Bala Bado,
No. 22 Opp. Primary Education Board, Bado Area, Sokoto.
BA HAKA KAUYAWA SUKE BA
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA so in nuna wa daraktoci cewa yanzu ba lokacin Zamanin Jahiliyya muke ba. Ina magana ne kan yadda suke nunawa idan dan wasa ya fito a matsayin dan kauye a fim. Kuna fa zakewa, kuna wuce gona da iri wajen nuna yadda dan kauye yake. Sanin kowa ne cewa 'yan kauye ba yadda kuke nunawa suke ba; wani abin ma ya wuce kauyanci, ya koma jahilci. Ba bakauye kawai ba ne jahili. Kuma ku tuna duk mutumin da ba shi da kauye to ba shi da asali.
Ina yi wa Halima Adamu Yahaya da Abida Mohammed murnar aurensu. Allah ya ba su zaman lafiya a gidajen aurensu, amin.
Sakina Mohammed Sani,
No. 536, Dala Road, Bayero University, New Site, Kano.
AHMED DA ASHAFA SUN BURGE NI
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
NA fubuto wannan wasika don in jinjina wa Ahmed S. Nuhu da Ashafa Murnai Barkiya a kan irin kokarin da suke yi. A gaskiya Ahmad yana burge ni sosai a duk fim din da ya fito, haka kuma Ashafa a cikin rubutunsa na mujalla. Allah ya taimaka amin.
Gaisuwa ga Ali Nuhu, Ibrahim Maishinku, Maryam Aliyu da Shu'aibu Lawan.
Jamila Dahiru Dutse,
Faculty of Education, Bayero University, Kano.
ME YA SA BA KU YI DA NI?
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
DALILIN rubuto wannan takarda shi ne ni dai ina daya daga cikin masu karanta wannan mujalla ta Fim. Duk wata ba ta wuce ni saboda fadakarwa da ilmintarwar da nake karuwa da su a cikinta. Amma kash!, na rubuto ta'aziyyar Balaraba amma ba a buga ba. Na biyu, na shiga gasar kacici- kacici har sau biyu, da amsoshin suka fito na ga na ci amma ba a buga sunana ba a jerin wadanda suka ci. Ko me ya sa? Oho!
Musa Mohammed,
B/Dogo 'Yankaba Quarters, Zenith Bank Limited, P.O. Box 3385, Kano.
Malam Musa ka yi hakuri, kila wasikunka sun zo a makare ne, ko kuma ba su shigo hannunmu ba.
YAKUBU YA KERE MAWAKA
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
ZAN so ku ba ni fili a mujallarku domin in bayyana jin dadina ga mawakin nan Yakubu Muhammad. A gaskiya Yakubu in dai a fagen waka ne, to shi ne a kan gaba. A mawaka ba kamarsa saboda fitattun wakokin da ya yi, su suka daga finafinai da dama.
Kuma wani abin burgewa shi ne Yakubu ba ya sayen waka ya rera ko kuma a rera masa, sai dai shi ya sayar ko kuma ya rera ma masu. Abubakare Iliyasu Sansani,
G.L.D.S.S., Mutum-Biyu, Jihar Taraba.
TAYA MURNA GA MA'AURATA
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA son in yi amfani da wannan damar domin taya jarumar da ta shigar min zuciya murnar auren da ta yi, wato Halima Adamu Yahaya. Kuma ina taya Aminu A. Shariff (Momo) da amaryarsa Maryam Mohammed, da Hamza Mohammed Danzaki da amaryarsa Abida Mohammed, sai Alh. Dan'azumi Usman da amaryarsa Hajiya Rabi, murnar aurensu. Dukkansu Allah ya ba da zaman lafiya.
Umar Ibrahim Tudu, No. 2, L.E.A. Sch., Tudu, Ramin Kura II, Ramin Kura, Lere, Saminaka L.G.A., Jihar Kaduna.
TAYA MURNA GA MOMO DA HALIMA
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
DALILIN wannan wasika shi ne domin in taya Momo da Halima Adamu Yahaya murnar yin auren da suka yi. Ina rokon Allah ya ba da zaman lafiya, kuma ya ba da zuri'a daiyiba, amin. Karshe ina mika sakon gaisuwa ga ma'aikatan wannan mujallar.
Bello Agwada Mai Kanwa,
Bakin Kasuwar Yauri, P.O. BoX 18, Yauri, Yelwa-yaquri, Jihar Kebbi.
ABIDA, ALLAH YA ZAUNAR DA KE
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA son wannan mujallar ta mika sakon gaisuwata ga Abida Muhammed da mijinta. Hamza. Ina mutukar farin ciki da wannan auren nasu. Fatana gare su shi ne Allah ya ba da zaman lafiya da zuriya mai kyau. A karshe a ba ni lambar kamfanin 'Mandawari Enterprises' mai gabatar da Mu Shakata.
Mustapha Challube,
Insha Allahu Oil Nig. Ltd., P.O. Box 1661, Gamboru Road, Maiduguri, Jihar Borno.
Za ka iya buga waya kamfanin 'Mandawari Enterprises' ta wannan ambar: 064-640310
ALLAH ZAI KARE AHMAD S. NUHU
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
DON Allah ina so ku ba ni fili a cikin wannan mujallar mai farin jini domin in yi magana a kan Ahmad S. Nuhu da wasu "iyayen gidansa" da suke nema su rusa shi wai don ya yi wa mujallar Fim wasa wai ba zai sake yi masu wasa ba. To ba wanda ya isa ya rusa Ahmad sai Allah. Allah ne ya ba shi ikon ya yi musu wasa. Kenan wadannan iyayen gidan na Ahmad suna yin fushi da ikon Allah ba da Ahmad ba! Ko sun manta da kaddara ne? Allah ne yake kaddara komai ba mutum ba. Sun manta da cewar Allah yana iya daukaka Ahmad har ya zo matsayinsu. To, su yi hattara!
A nan ina kira ga mujallar Fim don Allah kar su watsa waAhmad S. Nuhu kasa a ido. A gaskiya, duk wahala ba za ta hana jarumin da Allah ke so yin tashe ba. Ahmad ya gaji dan'uwansa Ali Nuhu. To ni a nan ba abin da zan ce sai Allah ya kara daukaka mujallar Fim, ya kyautata masu niyyarsu ta alkhairi.
A karshe ina yi wa Ahmad da Ali addu'ar alheri. Allah (s.w.t.) ya kara daukaka su.
Miss Hassanat Musah Garba,
No. K79, Kundila Housing Estate, Phase II, Maiduguri Road, Kano.
MAGANIN MATSALARMU A MISAU
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
NA rubuto wannan wasika domin in gaishe ku, sannan kuma in jinjina maku saboda namijin kokarin da kuke yi wajen fahimtar da jama'a da kuma sanar da jama'a halin da duniyar finafinai hake ciki. Hakika ni ma'abuciyar karanta mujallar Fim ce domin duk wata ba ta wuce ni. Musamman nake aikowa daga Misau har Kano a sayo mani. Domin a nan Misau muna samun matsalar samunta, saboda ba ta wadatar da mu.
Saboda haka shawarata a nan ita ce, don Allah don Annabi muna so ku samu wakili a nan Misau domin mu samu saukin samun mujallar. Domin kuwa a gaskiya mujallar Fim ta shiga zuciyarmu.
Fatimah Aliyu Goshi,
c/o Ahmed M. Aliyu Goshi, P.O. Box 107, Misau, Jihar Bauchi.
Hajiya, insha Allah idan muka samu mutum wanda zai iya tsare gaskiya a huldarmu da shi, to za mu iya nada shi wakili a nan Misau.
MOMO DA ABIDA SUN YI JAHILCI
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA mika godiyata game da rahotannin da muke samu ta karanta mujallar nan mai farin jini. Allah ya kara daukaka ku, amin.
Na ga jahilcin A.A. Shariff (Momo) da Abida Mohammed a kan rashin ba da goyon baya na buga labarin bikinsu a mujalla. Wannan ai jahilci ne suka nuna. In ba su gane ba ai an taya su murna ne da kuma farin ciki.
Daga karshe ina mika gaisuwata ga Saima Mohammed da Ahmad S. Nuhu.
Asma'u 'A' Sadiq,
No. 15 Galadima Road, off Alkali Road, Kaduna.
ZAN SO IN AURI LADI, AMMA...
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA so in yi amfani da wannan dama in isar da gaisuwa ga mosoyiyata, gwanata, Ladi Mohammed (Mutu-Ka-Raba), da fatan Allah ya fito mata da miji nagari ta yi aure kamar su Fati, Abida, Maijidda, Halima Adam da sauransu.
Ita dai Ladi, duk a cikin 'yan fim ba wacce take burge ni kamarta. Saboda son ta da nake yi, da a ce na isa aure ko kuma ina da kudi, da na aure ta. Ni dan shekara 22 ne. Zan zo Kano in gan ta.
Kuma ina so idan Mujallar Fim sun san cikakken adireshe ta Ku/bani shi. Ko kuma wayar/ta.
Muhammed Two Brothers,
MV 15, Kabala Junction, Kaduna.
KU YI KOYI DA WAZIRI ZAYYANU
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
KU taimaka min da fili a cikin wannan mujalla mai farin jini da wayar da kai domin in yi kira ga furodusoshi da su yi koyi da furodusan fim din Babban Gida, wato Waziri Zayyanu. Domin fim din duk yadda ake yin fim kowane iri ne ya kai. Ga fadakarwa ga ilimantarwa, ga shi babu raye-raye da wake wake .
Ina ba furodusoshi shawarar su daina yin finafinai masu yawa, su tsaya su yi daya mai kyau da inganci. Hausawa na cewa da haihuwar yuyuyu gara da daya mai kwari.
Umar Ibrahim Tudu,
Ramin - Kura, Lere, Saminaka L.G.A., Jihar Kaduna.
KUN SHA YABO KAN BALARABA
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA son in yi amfani da wannan dama don sanar da Editan Fim kan irin yabon da ya samu daga dimbin jama'a kan yadda kuka ba da cikakken zancen marigayiya Balaraba Mohammed, tare da dukkan kawo tarihinta , rayuwarta, uwayenta, asalin yadda ta shiga harkar fim, da kuma gidauniyar ta da aka kafa. A gaskiya kun ci gaba yadda tunaninku ba zai iya karewa ba.
Na je garuruwa da dama na ga yadda suke sayen kalandar Balaraba, ku kuma a Fim kimanin wata biyu labarinta kawai kuke yi a cikin mujalla. Wannan ya yi daidai.
Ibrahim Sheme ya fi kowa kowa shan yabo a wannan lokaci; har addu'a mutane ke yi masa. Sai kuma mijinta, kuma shi ma ba wani abu ake yi masa ba illa kiran ya dau hakuri da juriya.
A karshe a madadina da rassa na wajen son mujalla, ina godiya ga edita da sauran abokan arziki, musamman shugaba Alh Hamisu Iyan-Tama.
Abdullahi Bawa Jibia,
c/o Alhaji Bawa Bawasa, No. 21 Market Road, Jibia, Jihar Katsina.
INA KAUNAR HADIZA KABARA
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
A GASKIYA ina matukar kauna da so na zahiri ga Hadiza Kabara, domin tana burge ni. Don Allah ku sada ni da ita, ta aiko mani da adireshinta.
Daga karshe, ina mika gaisuwa irin ta so da kauna ga Hadiza Kabara, da Sani S.K., da Aina'u Ade, Maryam Umar Aliyu, da Ibrahim Mandawari.
Isa Yahaya Ibrahim.
New Market Jengre, P.O. Box 1780, Jos,
Jihar Filato.
HAUSA IRI-IRI CE
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
NA karanta wata wasika a Fim ta watan Yuni inda wani ya yi magana kan a rika kula da nahawun Hausa a fim. To Malam Ahmed Mohammed Misau, zan so ka gane cewa ba wai nahawu ba ne 'yan wasan ba su da shi, a'a Hausar ce ta kasu kashi-kashi. Misali, ita A'isha Ibrahim da ka ba da misali da ita 'yar Kaduna ce, ba 'yar Kano ba. To, ka ga hausar Kano daban kuma ta Kaduna daban ta Misau ma daban. Hasali ma dai hausar Misau ta bambanta da sauran, domin kuwa na zauna a Misau na ji irin hausar can. Kuma yanzu ina zaune a Zariya ina jin hausar Zariya. Idan Bazazzagi ya ce, "Bakin alkami ta bushe," shi ko Bakano cewa zai yi, "Bakin alkalami ya bushe." Kuma ko a wata jihar guda daya za ka ga hausar garuruwa ta bambanta. Kamar Misau da Bauchi, hausarsu ba daya ba ce. Malam Ahmed, saboda haka ina so don ka fahimta ka je Jihar Kano ka ji tasu hausar sannan ka zo Jihar Kaduna ko Zariya ka ji tasu, sannan kuma ka hada su da na Bauchi, sa'annan sai ka ga idan daban-daban ne ko a'a.
Ina mika gaisuwa ga Editan Fim, da Ibrahim Mandawari, Tahir Fagge, Hajara Usman, Ladi Moh'd, Ahmed S. Nuhu, Aminu Shehu, Aminu M. Ahmad, Musbahu M. Ahmad, da Zahara'u Shata.
Hafsat Sambo,
No. 225, Unguwar Alkali, Zaria City, Jihar Kaduna.
KU SADA NI DA MARYAM ALIYU
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
KASANCEWATA mai karanta wannan mujalla a kowane wata, nake bukatar ku sada ni da jarumata, wato Maryam Aliyu, saboda ganin yadda take shirya fim dinta. A karshe ina yi mata fatan alheri, amin.
Lawal S. Ibrahimmai Kaset,
Bakin Tashar Yamma, Mai'adua Rd., Daura, Jihar Katsina.
KU SA KALANDAR MUSULUNCI
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
DON Allah ku soma rubuta kwanan watan Musulunci a cikin wannan mujalla. Kamar yadda wasu mujalla da jaridu suke yi, sai ka ga ma ga watan Nasara ga na Musulunci. Allah ya kara maku farin jiji da daukaka.
Yusuf Sulaiman Musa Gyadi-Gyadi Kano,
Dept. of Acccounting, University of Maiduguri, Jihar Borno.
Malam Yusuf, wannan shawarar taka ta shige mu, har mun fara amfani da ita daga wannan watan. Mun gode. Allah ya saka maka da alkhairi.
KO N200 FIM TA KAI TA CI KUDINTA
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA yi maku fatan Allah ya kara maku kwazo da basira, yadda za ku rike tsarinku, koma fiye da hakan. Domin a gaskiya ko da mujallar Fim ta kai N200 a halin yanzu, wallahi bisa gaskiya ba a biya ta hakkinta ba idan aka yi la'akari da irin kwazo, basira da tsarin da ke cikinta. Ba ta da ko na uku a duniyar mujallun Hausa.
Alhaji Sabi'u K.K.,
Nagwamatse Crescent, P.O. Box 160, Sabon Gari, Kontagora, Jihar Neja.
CIN GYARAN TIJJANI IBRAHEEM
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA son in ba Tijjani Ibraheem shawara a matsayina na kanen shi. Shawarar ita ce a kan maganganun da ka yi ko kuma in ce martanin da ka mayar ma Halima Adamu Yahaya a cikin mujallar watan 2 na wannan shekara. Abin nake son in shaida maka shi ne tunda har don Allah ka yi bai kamata ka fadi ma duniya cewa kai ka reni Halima ba. Tunda kusan kai ka rene ta to ka bar ta nan ba sai ka fadi ba, don Hausawa suna cewa yabon kai jahilci. Don haka a matsayinka na mai ilimi kuma wanda ya san ya-kamata, kuma mai hankali irinka, to duk yadda ranka ya baci bai kamata ka fadi wadannan maganganu ba.
Daga karshe ina maka gaisuwa ta musamman ga: Ibrahim Mandawari, Hamisu Iyan-Tama, Aminu Shehu (Acid), Tahir Fagge, Halima A. Yahaya, Fati Suleiman, Hadiza Kabara, Hauwa Ali Dodo da duk sauran 'yan wasa.
Nasiru Attahiru Gusau,
Public Complaints Commission, Gusau, Jihar Zamfara.
JINJINA GA BASHIR ABUSABE
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA fatan za ku ba ni fili a cikin wannan mujalla mai albarka, kuma mai farin jini domin in yi tsokacia kan daya daga cikin ma'aikatanku. Abin nufi dai a nan shi ne, ina son in yi jinjina ne ga wakilinku na shiyyar Sokoto, Bashir Abusabe. Hakika ina jin dadin karanta rahotannin da yake aikowa da su, duk da kasancewar bai dade sosai da tsoma kafarsa a cikin harkar ba.
Daga karshe ina yi masa addu'ar Allah ya kara daukaka shi a cikin wannan aiki, da sauran abokan aikinsa baki daya, kuma ya kiyaye su daga dukkan shari, Allahumma amin.
Muhammed Ammani Ibrahim,
c/o Salisu Yakubu, Katsina State Board of Internal Revenue, P.M.B. 2029, Katsina.
MUJALLAR FIM TANA DA AMFANI
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
GAISUWA da fatan alheri a gare ku. Mun dade muna karanta mujallarku mai farin jini mai amfani ga jama'a. Mujallar tana da muhimmanci sosai. Allah ya albarkace ta, amin.
Muna mika sakon gaisuwarmuga shahararrun 'yan wasa kamar su Hauwa Ali Dodo, Abida Mohammed, Kumurci, Rukayya Dawayya, Baballe Hayatu, da dai sauransu. Sannan muna yi wa Fati da Sani Musa (Mai Iska) murna. Allah ya kara ba su zaman lafiya.
Aisha & Ameen Isa Hamman Yero,
No. 3, Hamman Yero Road, Mayo Belwa L.G.A., Jihar Adamawa.
YAYA ZAN YI IN SHIGA INTANET?
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
DALILIN da ya sa na rubuto maku wannan wasika shi ne ina so in gaya maku cewa ina so in shiga intanet, kuma ta hanyarku nake so in mallaki adireshin i-mel nawa. Saboda ni ma ina sha'awar in fada cikin membobin da ke zauren finafinan Hausa Yahoo groups. Don haka ina son cikakken bayani daga gare ku.
Daga karshe ina gaida ga Abida Mohammed, Saima Mohammed, Asiya Mohammed, Hadiza Mohammed Gombe, Habiba Layye, Hadiza Kabara, A'ina'u Ade, Isyaku Dan Zabuwa, Sani Danja, Alhaji Garba, da Ibrahim Sheme.
Hamisu Ali (D) K,
Tudun Wada Bus Stop, Layin Dirime near Alhaji Maharazu Chemist, Dirimi, Kaduna.
Malam Hamisu, akwai 'business centres' da dama da ke jona mutum da intanet, kuma kudin da za ka biya ba su da yawa - ba su wuce N300 ba ko kasa. Za ka iya zuwa ofishinmu mu yi maka kwatancen ire-irensu. Wassalam.
KU WAYAR MANI DA KAI
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
NA kasance a kullum ina taya ku murna ganin kuma ba a bar ku a baya ba wajen shiga intanet, inda a duk inda mutum ya kasance a duniya zai iya karanta mujallarku a saukake, kuma kyauta. Wannan ba karamin ci-gaba aka samu ba, hakan zai habaka tare da daukaka finafinan Hausa da su kansu 'yan wasan.To amma wani abu da ya daure mani kai shi ne, akwai lokacin da muka kasance muna bincike a wani website sai nake cika baki a kan cewa ku ma kuna da website. Nan take aka bukace ni in bayar da adireshin site din. Na bayar kamar haka: www.kanoonline.com, muka shiga muka duba, abin da muka iske shi ne masallatai, gidajen masarauutar Kano, sai wasu hotuna guda uku wanda sunan mutum daya na iya rikewa, wato Dr. Abdalla Uba Adamu, sai kuma mujallarku mai dauke da hoton Rabi Mustapha, ita ma din ba mu samu damar sanin abin da ke cikinta ba. Shi ne nake son don Allah ku wayar mani da kai. Me ya faru?
A karshe nake mika gaisuwar jinjina da kuma fatan alkhairi ga taurarina wadanda ba ni da kamarsu a industiri, wato Abida Moh'd, Ibrahim M. Mandawari, Saima Moh'd, Aina'u Ade, Fati Baffa, Hadiza Kabara, Ibrahim Maishunku, Shu'aibu Lilisco, Momo, Ali Nuhu, Ahmed S. Nuhu, Musbahu M. Ahmed (Gentleman), Kumurci da Aminu Ali Zango.
Binta Tukur (Ta'alhazai),
Galadima Dudi Road, Kofar Fada, Malumfashi, Jihar Katsina.
Malama Binta, ai da kin yi clicking a kan hoton bangon mujallar da kika gani a intanet, to da za ki budo shafukanta ne baki daya. Duk da haka, mun samu matsala da wannan tsarin na www.kanoonline.com, saboda haka za ki iya karanta mujallar a intanet da hotuna masu kala a sabon website dinmu, wato www.fim.tvheaven.com. Ki jaraba ki gani, mun tabbatar abin zai burge ki. Mun gode.
RAMAT, TSAYA A MATSAYINKI
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA son in yi amfani da wannan dama don in sanar da Balaraba Ramat cewa tana nema ta wuce gona da iri. Ta sani fa, addinin Musulunci ba rubutun labari ba ne. Don na karanta a Fim ta Fabrairu 2002 tana sukar malamanmu. Kuma tana magana ne a kan abin da ba ta san shi ba.
Mu dai abin da muka san Balaraba Ramat da shi shine, kaga labaru. Saboda haka magana a cikin addinin Musulunci ba nata ba ne, ta bar wa malamai.
Mujtaba Yakubu Abdullahi,
No. 1, Igabi Close, Unguwar Muazu, Kaduna.
MU CI GABA DA TAIMAKA WA FIM
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA kira gare mu masu karanta mujallar Fim da mu kara ba da gudummawa ta wurin sayen kwafen mujallar tun da dumi-duminta, domin su ma su ci gaba da samar mana da mujallar, wanda ba karamin aiki ba ne. Ni mai karanta shafin nan ne na "Rayuwarmu" saboda muhimmancinsa.
Gaisuwa ga jarumina Malam Dare.
Abdul Hadi Aliyu,
Madrasatul Awladul Deen Islam, Layin Baban Ghana Nassarawa, Kaduna.
DUK IN NA GA BALARABA A FIM...!
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
NA yo wannan takarda ne domin mika sakon ta'aziyyata tare da sauran abokan aikina 'yan 'Family Support' na nan Ingawa kan rashin Balaraba da muka yi. Allah ya jikanta, ya gafarta mata, ya sa Aljanna ta zama makoma a gare ta, amin. Ni Amina, rasuwar Balaraba ta sa ni cikin damuwa sosai, yadda duk sa'ad da na gan ta a fim to zan yi kuka kamar raina zai fita. Allah ya ba mu hakurin jure wannan rashi!
Amina Yusuf,
Family Support Clinic, Ingawa, Ingawa LGA, Jihar Katsina.
GYARA A FIM DIN MASHI 1
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA son in yi gyara a fim din Mashi na 1 inda aka nuna mijinsu ya rasu ya bar Hajjo da ciki, amma sai ga shi ta daina sa gyale tun kafin ta haihu, wanda mu mun sani a Musulunci ba a gama takaba da ciki sai an haihu. Ya kamata don Allah a rinka duba fim kafin a sake shi a kasuwa. Ko da za a sami gyara sai a gyara kafin ya zo gare mu. Gaisuwa ga Ibrahim Mandawari, Ali Nuhu, Fati Baffa Fagge, Ahmed da dukkan 'yan fim.
Bilkisu Mijinyawa Bello,
No. 5, Gidan Magajin Badarawa, Badarawa, Kaduna.
GAGARABADAU YA BURGE NI
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA mika sakon gaisuwata ga kamfanin 'Northern Star Films' saboda fim da kuka yi mai inganci da ma' ana, wato Gagarabadau. A gaskiya kun nuna basira, da hazaka da kwazo. Allah ya kare ku daga sharrin mutane da mahassada masheranta, amin. Kuma don Allah ina so a rubuto mani lambar wayar Ali Nuhu.
Nafi'u Abdullahi Liman,
F.P.9, Alkalawa by Ibrahim Taiwo Road, T/Wada, Kaduna.
GAGARABADAU YA KAYATAR
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
DA farko zan mika gaisuwata ga 'Northern Star Films' wadanda suka shirya fim din Gagarabadau. Lokacin da na kalli fim din ya kayatar da ni kuma ya burge ni matuka. Allah ya kara maku basira. Kuma darakta Hafizu Bello da Al-Amin Ciroma, Allah ya taimake ku amin. Zan mika gaisuwa ga Zulai Moh'd, Ahmed S. Nuhu da masoyiyarsa Maryam Aliyu, sai Abida Moh'd.
Hajiya Aisha Moh'd,
F.C. 9 Kumashi Road, T/Wada, Kaduna.
ALLAH YA TAIMAKE KU
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
GASKIYA na yi matukar farin cikin ganin wasika ta farko da na yi muku, wadda na ga kun buga ta watan Yuli 2002. Sai dai an dan yi kuskure kadan wurin adireshina, wato W. 17, Gangara Road na rubuta, ba kamar yadda na ga kun buga ba, wato Gamagira Road.Bugu da kari kuma wannan mujalla taku, ni kadai na san irin karuwar da na samu wajen karanta ta da nake yi. In na ce zan bayyana maku za a dauki lokaci, saboda haka kawai sai dai addu'ar Allah ya taimake mu. Na gode.
Faruk Muhammed,
W. 17, Gangara Road, Sabon gari, T/Wada, Kaduna.
ALLAH DAUKAKA MUJALLAR FIM
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
GABA dai gaba dai Mujallar Fim! Maki gani ya kau da idonsa! Kullum addu'armu ita ce: Allah ya ja zamanin mujallar Fim! Allah ya daukaka ta tare da dukkan ma'aikatanta! Allah ya dora ta a kan dukkan mujallun duniya, amin! Daga karshe ina gaida Hadiza Kabara, Ibrahim Mandawari, Isa Bello Ja, Hamisu Iyan-Tama, Ali Nuhu, Ahmed S. Nuhu, Yakubu Muh'd, Sani Danja, Sani Musa, Aleebaba, Hafizu Bello, Sadi Sidi, Galin Money, da Hajara Usman.
Haruna M. Yawale Mai Gyaran Radio
P.M.B. 79 Kwadon, Yamaltu Deba LGA, Jihar Gombe.
NA YABA DA AIKINKU
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
DALILIN da ya sa na rubuto maku wannan wasika shi ne domin in yaba maku, in nuna maku farin cikina da jin dadi game da wannan mujalla taku mai farin jini. Hakika a ko da yaushe ina kokarin samun mujallar, amma muna cin wuya kafin mu samu. To amma duk lokacin da na same ta ban ma tuna abin da ya faru game da wannan wahala. Saboda sai in ji na huce.
Ina gaida Ibrahim Mandawari da Ahmed S. Nuhu da Lere da Galin Money, da Shu'aibu Kumurci.
Rabi'u Lawal Tsiga Mai Fetur,
Bakin Kasuwa, Bakori Road, Tsiga, Bakori LG Jihar Katsina.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin