Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 34   Oktoba 2002
WASIKU


BABBAN SHAFI
MU LEKA MU GANI
HIRAR MUSAMMAN
Wasiku
KU TAMBAYE SU
Rahoton Musamman
Rahoto
Malam Zurke
RA'AYIN MUJALLAR FIM
Bukukuwa
Sauran Labarai
Fitattun Taurari
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka
Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM MAI FITOWA!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da MU LEKA MU GANIn yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Wasikun masu karatu

INA SO A YI DABI'A NA 2

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA son ku ba ni fili cikin mujallarmu mai farin jini domin in bayyana ra'ayina game da shirin Dabi'a. Sani SK ya fito a matsayin Nasir a cikin shirin. Ya so a ce ya yi kudi,amma har fim din ya kare bai yi kudin ba. To ya kamata a ce ya yi kudin. Saboda haka mu na so a yi mana kashi na 2 domin mu ga yadda zai yi da tsohuwar matarsa; ya ya zai yi da amarya?, da sauransu. Na gode.

Hon. Ahmad Hashim Sashen koyon aikin gona(Agric), Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.PMB 2346, Sakkwato.

KU TSARKAKE FINAFINANKU

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

LALLAI ina daga cikin masu kallon finafinan Hausa domin suna da fa'ida, ilimantarwa, kuma ta wani bangaren suna zama guba wanda zai iya bata tarbiyya musamman ta matasa ('yan kasa da shekara 22).

Amma ina yi wa 'yan fim kyakkyawan zaton cewa yunkurinsu shi ne kawo gyara da fadakarwa ga al'umma. Wannan kyakkyawar niyyar ce za ta sanya duk mai adalci ya yaba muku wajen wannan yunkuri, kuma ya ba ku hanzari a wajen da kuka yi kuskure, bisa la'akari da cewa mutum fa mai kuskure ne ba ya iya tsarkake gabarin kurakurai. Ba na bukatar yin tankade da rairaya ga finafinan da na gani, da manufar nusar da ku abin da ya dace da shari'a da wanda bai dace ba, wannan kun fi ni sani tunda harkarku ce. Shawarata a nan ita ce kawai ku ji tsoron Allah kada wajen neman gira ku rasa ido.

Lallai kwadayin samun karbuwar fim a gurin masu kallonsa, ba zai zamana ya janyo muku fadawa rikici da Allah ba, manufata ita ce ku yi taka-tsantsan wajen kokarin burge 'yan kallo, da abin da zai janyo muku fushin Allah. Ni ba malami ba ne amma na ji a wajen malamai cewar Manzon Allah SAW ya yi fadakarwar " wanda duk ya nemi karbuwa gurin mutane da saba wa Allah, to Allah zai ... Haka wanda ya nemi yardar Allah da saba wa mutane to Allah..." . Na bar malamai su cike wadannan guraben!

Na ga finafinai masu yawa wadanda suka dace da shari'a, irin su Wasiyya. Haka na ga wadanda suke kalubalantar al'adarmu da addinimmu. Zai fi dacewa idan aka yi kokarin saita tunanin 'yan kallo na shirya fim kawai wanda yake bayyana irin hakikanin rayuwarmu da halin kasancewarta, ba tare da aron wata rayuwar wadda ba irin ta al'ummarmu ba ce. Raye-raye da wake-wake a cikin fim yana kayatar da shi tare da bayyana sako, amma illar da ke cikinsa tana da yawa, in aka yi kokarin sitirtawar jiki gwargwadon iko da nisantar amfani da kalmomin batsa (musamman na soyayya), zai fi samun karbuwa a gurin Allah, kuma in an yi hakan saboda neman yardar Allah to zai yarda kuma ya albarkaci sana'ar (bisa la'akari da abokan gasarku wadanda ba za su kula da wadannan dokokin ba, tare da tsoron watakila za su fi ku jan hankalin 'yan kallo). Duk abin da aka nufi Allah a cikinsa, to za a yi mamakin kyakkyawan sakamako, duk da cewa dai yakan jarrabi mai neman yardar tasa ya ga irin dauriyarsa.

Tsarkake finafinan Hausa daga barin tsiraici, batsa, wakoki masu motsa jarraba (na soyayya), yasasshen zance, rantsuwa da Allah, ashar da sauransu, zai sanya finafinan su zama makaranta mai kwazo da inganci irin wadda ake amfani da ita wajen kafa al'umma tagari. Allah ya yi muku jagoranci, amin.

Magashi Auwal Ibrahim, Dept. of Genetics and Plant Breeding, People's Friendship University of Russia, Moscow -117198, Russia.

MUN JI DADI DA FILINKU A INTANET

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

ASSALAMU alaikum. Gaisuwa mai yawa ga mujallar Fim. Bayan haka ina son shaida maku cewa mun ji dadi sosai da kuka bude fili a intanet, kuma muna fatan filin zai dore.

Muhammad Sani Umar Mafara muhsan1400@yahoo.co.uk

INA SON FINAFINAI A BULGERIYA

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

NA kasance mai sha'awar shirye-shiryenku da kuke sawa a intanet, kuma mai sha'awar kallon fim na Hausa a lokacin da ina gida Nijeriya, don yanzu na kasance ina karatu a Bulgeriya.

To a gaskiya yanzu ina da bukatar finafinan Hausa da ake yi kamar irin su Gagarabadau. Don haka in akwai yadda za a yi ku aiko min su in biya ko ta post office ne su kawo min to a gaskiya ina da bukata. Sai na ga amsarku. Wassalam.

Abusufyan Attahiru

KU KARA KOKARTAWA

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA mai rubuto maku wannan wasika ne don na kara yi wa masu shirya finafinan Hausa jinjina. A gaskiya yadda kuke fim din ku yana matukar burge ni, kuma ina rokon Allah ya sa ku kara kokartawa ta fannin fim da kuma buga mujallu. Ina mika gaisuwata ga dukkan masu yin fim. Allah ya sa ku ci gaba a hakan. Bissalam.

Sadiya Yakubu

AINA'U KI BUGO MANI WAYA

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

DON Allah ku taimake ni ku isar da gaisuwata zuwa ga wadannan mutanen: Ali Nuhu, Ahed S. Nuhu, Ibrahim Mandawari, Tahir Mohammed Fagge, Maryam Aliyu, Hadiza Kabara, Ishaq Sidi Ishaq da kuma masoyiyata wadda nake jin ta a zuciyata, take faranta mani raina a duk lokacin da na gan ta a fim, wato Aina'u Ade. Kuma don Allah ku sama mani lambar tarho nata, ga na wajen aikina: (072-223907/222285). Don Allah tana samun wannan lambar ta buga mani waya. Na gode. Allah ya sa mu dace, amin.

Miss Mary Paul, c/o Ruth Malum, ECWA Church, Bogo, P.O. Box 511, Gombe.

SHAWARA KAN SHIRIN FIM

ZUWA GA IBRAHIM SHEME,

NA rubuto domin in nuna maka jin dadinmu wato mu ma'abota kallon finafinan Hausa, a kan yadda kake taimakawa wurin yada al'adun Hausa ta hanyar Fim.

To amma wani hanzari ba gudu ba, don Allah muna son a yi 'yan gyare-gyare a kan harkokin fim. Daga ciki har da irin wasan da 'yan wasa suke yi. Bari inyi misali da fim dinka na Gagarabadau. A gaskiya wasan ya yi ma'ana saboda an canza salo daga kan soyayya, aure da mutuwarsa, zuwa wani abu na nishadi da rayuwar yau da kullum. A Gagarabadau yadda Hindatu Bashir ta yi wasa, gaskiya ta zake sosai a matsayinta na matar attajiri, tunda an nuna cewa za ta iya shatar jirgi to bai kamata a ce saboda ta shiga motar kasuwa tai ta hayaniya ba. Sannan ma'abota kallo sun dauka za a bai wa Dan Yarbawa isasshiyar dama ya nuna tasa fasahar amma sai 'Liyu Liyu" (Gidigo) ya yi gaje-gaje bai bari muka ji dadin kyakkyawar hausar Dan Yarbawa da abubuwan ban dariyarsa ba.

Zan yi amfani da wannan damar domin in isar da sakona ga masu shirya fim da kuma daraktoci, kamar masu fim din Abdulmalik, Nukura,Fa'ida, Sammatsi, da sauransu, da su rinka kokarin nuna abin da hankali zai dauka, su rage bai wa 'yan wasa damar yin abin da zai canza salo da ma'anar wasan.Wasu abubuwan ba sa cikin al'adun Hausa kamar yadda aka nuna a fim din Abdulmalik,wato yadda iyayen A'isha suke amsa wa surkinsu waya, da kuma yadda suke kiranta a gabansu kan sai ta yi hira da shi.

Ta wajen kwalliyar 'yan wasa kuma don Allah a rinka la'akari da al'ada , wuri, yanayi da shekaru. Don sau da yawa za ka ga kayan da dan wasa ya sa a farkon fim wai bayan shekara daya zuwa sama wannan kayan zai maimaita, sannan yanayin da za a nuna dan wasa a matsayin wanda ya mallaki miliyoyi sai ka ga sutura da muhalli da aka mallaka masa bai kai haka ba .

A karshe ina muku fatan alhairi. Allah ya kara maku fahimta da juriyar ci gaba da abubuwan alhairi da kuka faro.

Maimuna S. Bello

YABO GA KAMFANIN H.R.B.

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

DON Allah ku ba ni fili a mujallarku mai farin jini in mika godiyata da yabo ga kamfanin H.R.B. Productions, domin an ce yabon gwani ya zama dole. Na ruboto wannan wasika ne a kan wani fim dinsu mai suna Mashi. Hakika, fim din ya burge mu ya yi ma'ana kuma an yi zaben hazikai kuma fitattun 'yan wasa. Allah ya saka muku da mafificin alherinsa, amin. A karshe ga gaisuwata nan ga edita Ibrahim Sheme. Allah ya ja zamanin kamfanin mujallar Fim da H.R.B. Productions. Gaisuwa ga Ali Nuhu, Hadiza Kabara, Saratu Gidado, Hajjo, da dukkan sauran 'yan wasa.

Ibrahim Khaleel Babura,

Sauki Democratic Chemist, Hospital Road Babura, Jihar Jigawa.

ALLAH BADA ZAMAN LAFIYA

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

GAISUWA ga Fati Mohammed tare da Abida da A'isha Musa. Allah ya ba da zaman lafiya.

Jamila bin Othman

JAHILAI A BIKIN ABIDA

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

DA farko mu yi wa Annabi (s.a.w.) salati. Kuma ina yi wa ma'aikatan mujallar Fim fatan alheri. Na biyu maganata zan yi ta ne a kan abin da ya faru a wurin bikin walimar auren Abida da Hamza. A gaskiya na ji kunya kwarai da gaske a kan abin da ya faru a wurin bikin shirya liyafar da aka yi da yamma. A gaskiya furodusoshi da daraktoci wadanda akwai sa hannunsu a cikin wannan wautar da aka tafka, yanzu ransu ya yi musu dadi da suka bata sunansu a idan duniya da kuma masu kaunarsu? Kash! Allah wadaran naka ya lalace.

To a gaskiya kun ji kunya sosai domin muna ganinku a matsayin masu kishin ci-gaban Arewa har muna murna, ashe abin ba haka yake ba, ashe an fake ne da guzuma ana harbin karsana. In ban da wautar jahilci, wanene zai so ya rufe kofar da ta ke kare masa mutuncinsa da 'yan'uwansa? Wannan ai ya zama wauta, domin dan jarida ai mai kare mutuncin kowa ne a duniya ga baki daya. In ban da jahilci wai har ya tashi yana wasu maganganu marasa dadi saboda ya sami sararin sheke ayarsa.

Kuma a gaskiya na yi bakin ciki da har wasu daga cikin furodusoshi za su fito suna cewa su suna gaba da mujallar Fim, wanda ina ganin suna bata wa kansu lokaci ne domin ina ganin wannan ai jahilci ne da kuma wauta. A Musulunci babu gaba. Maimakon su da za su tsaya su ga cewa Allah ya bunkasa mujallar Fim ko ta yaya ta kara samun karbuwa a wurin jama'a da ma kasa ga baki daya! Ina fatan za ku hada kai domin a kori jahilci da ma kuma shaidan, domin ku da kanku kun san mujallar Fim dashen da Allah ke so ne.

Magana ta ta karshe ita ce shawara ga 'yan mujallar Fim. Ina mai ba ku shawara da ku riki salatin Annabi (s.a.w.) ya isar maku a kan komai na duniya da lahira. Ina so ku taimake ni ku mika min gaisuwa ga Ahmed Mohammed Amge furodusa. Haza Wassalam.

Sani Zubairu Adamu Plot 1636, Oko Awo Street, Victoria Island, Lagos.

KU BA NI HOTON ABIDA DA ALI

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

ASSALAMU alaikum. Ina fatan komai lafiya, Allah ya sa haka, amin. Na rubuto don in jinjina maku bisa kokarin da kuke yi, Allah ya taimake ku. Sa'annan ina so ku aiko mani da hoton Abida da Ali Nuhu ta mail box dina. A karshe nake muku fatan alheri a dukkan al'amuranku. Wassalam.

Asmau Abubakar

Tudun Wada, Kaduna.

Hajiya, kafin mu aiko maki da hotunan, za ki iya kwafar wasu hotunan na 'yan wasa, cikinsu har da Abida da Ali Nuhu, a gidan yanarmu na intanet, wato a www.fim.tvheaven.com

KU AIKO MIN DA MUJALLA

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

DA fatan kuna lafiya. Don Allah ina so ku aiko min da mujallarku ta wannan wata. Bissalam.

Aminu Muhammad

Za ka iya samun mujallar a wurin masu sayar da ita ko kuma idan kyauta kake so, to, ka shiga cikin intanet, ka duba adireshinmu, wato www.fim.tvheaven.com, za ka same ta. Mun gode.

F.K.D. MUN GAJI DA INDIYA

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

NA rubuto wannan wasika ne domin in yi magana a kan finafinan FKD. A gaskiya mun gaji da ganin finafian Indiya a Hausa.Don Allah Ali Nuhu idan kana son ka yi fim din soyayya to ka duba irin soyayyarmu ta kasar Hausa ko in ce ta Nijeriya. A kullum muna zakuwa fim ya fito daga FKD amma sai ya kasance in mun saya sai mu ga wani fim din Indiya kawai aka yi da Hausa. Mun ga So (Mohabbatein), Sharadi (Dilwale Dulhania Le Jayenge), Mujadala (Dillagi). To don Allah ya isa haka. Kai dai Ali ba jahili ba ne, kana da ilimin da za ka kago labari da kanka tunda kuwa kana rubuta ma wasu. Don Allah ku canza tsari.

Jummai Jamilu

SHAWARA GA 'YAN MUJALLA

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA son ku ba ni fili a mujalla mai farin jini da albarka don in isar da sako gare ku ku 'yan mujallu. Hausawa sun ce wake daya ke bata iri. Gaskiya akwai wadansu mujallu da suke rubuto wasu abubuwan da bai dace ba a kan 'yan fim, wadanda mu makaranta ba ma jin dadinsu. Ni ina fadar wannan ne a matsayina na Musulma da kuma abin da Musulunci ya fada. A Musulunci fa aka ce duk wanda ya rufa wa wani asiri Allah zai rufa masa nasa asirin, haka kuma wanda ya tona wa wani asiri shi ma Allah zai tona masa nasa asirin.

A Musulunci ba kyau bincike, ana aiki da abin da aka gani zahiri ne. Akwai wata mujalla da ta rubuta labarin Ali Nuhu a watan Maris mai taken "Ali Nuhu da tufafin arna," har aka hada da iyayensu. Sai kuma watan Yuli inda aka sake buga labarin Ali Nuhu da dai sauran abubuwa a ciki. Gaskiya abin da suka yi ba su kyauta ba, mu kuma haka ba zai sa mu tsani Ali Nuhu ba. Wannan abin alfahari ne a gare mu, mu Musulumai. Mutumin da ya yi firamare a Saint Thomas amma kuma yana cikin Musulunci. Soboda haka don Allah 'yan mujallu a san irin labarin da za a dinga bugawa a kan tarihin mutum. Ai tunda yace shi dan Barno ne, ya san abin da ya sa ya fadi hakan; sai a bar shi a hakan, duk abin da aka ga mutum ba ya so a sani to a daina ya masa bi-ta-da-kulli sai an tona rufin asirinsa, domin kowa in cewa aka yi za a binciko asalinsa za a samu abin aibi a ciki. Saboda haka rufin asiri yana da kyau don haka Musulunci da zahirin abin da mutum yake amfani ba da badini ba.

A inda aka rubuta Ali Nuhu ya yi amfani da kayan arna har aka hada da iyayensa, a nan bai dace su sa iyayensa a ciki ba. Tunda dai shi ya yi laifin ba iyayensa ba, kamata ya yi a rubuta masa a yi masa nasiha. Ko kuma a kira shi a yi mashi nasiha baki da baki tunda bai fi karfin a yi masa magana ba. Kuma na tabbata zai dauka. Kuma duk dan'adam ba wanda ba ya kuskure, wani abin za ka yi shi sai daga baya ka gane kuskurenka. Shawarata gare ku 'yan mujalla don Allah a hada kai a dinga yin abin da zai kawo ci-gaba cikin sana'arku da kuma al'adun Hausa, kar a yi abin da zai sabawa Musulunci kuma kada a ja da wanda Allah ya daukaka shi bai kamata harka ta bakin ta shiga tsakaninsu ba.

Don Allah Ibrahim Sheme a samo mana wakili a Jihar Adamawa, sannan kuma muna da matsalar samun mujallar Fim a Adamawa. Kamar ni yanzu kowane wata sai na aika Kano a saya mani domin ni na fi karanta mujallar Fim a kan kallon fim.

Gaisuwa ta musamman ga Dandugaji, Ahmed S.Nuhu, Hauwa Ali Dodo, Ashafa Murnai Barkiya da Ibrahim Sheme.

Ummu Tukur Raji. P.O. box 749, Yola, Jihar Adamawa

KU DAINA ZAGIN HALITTARKU

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

DON Allah 'yan wasan fim ku daina zagin halittar junanku. Ku tuna fa, kuna fadakarwa ne. Idan ku bai maku zafi ba, mu 'yan kallo yana damunmu.

Ba ina nufin dukkan 'yan wasa ba, amma sau tari ana zagi kai tsaye na halittar Allah wanda ya yi wa abokin sana'arku. Misali, sau da yawa kamar Dumbaru da sauransu, ana zagin bakinta. To yin haka ba fadakarwa ba ne. A yi misali da kalmar da ta dace, ba ambaton halittar mutum ba. Allah ya sa an gane.

Mohammed Awwal

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin