ZUWA GA MUJALLAR FIM,
DALILIN wannan wasika shi ne na kalli Burin Zuciya na ga
gyara a ciki, na ga ya dace in yi wa furodusan gyara, wato Ibrahim Mohammed Mandawari. Gyara na farko shi ne na farko sun nuna cewa Sarki Abdurrahman ya bai wa Gimbiya kyautar bayi; na biyu shi ne wurin da shi Mandawari ya ba Gimbiya tarihinshi, ka ga wannan tarihin rayuwarsa bai nuna inda ya fito ba; na uku, Gimbiya ta ji wakarshi san da aka fitar da shi gari aka kai shi daji dogarai suka doke shi, da ya farfado sai ya fara waka, da ta ji wakar sai ta fita ta gudu, sai ga ta a garin Sarki Abdurrahman. Idan za a tuna, da farko sun ce Sarki Abdurrahman ya aiko mata bayi amma da ta yi batan kai sai garin Sarki Abdurrahman amma ya ce bai san ta ba! Kuma ga shi sun ce Mandawari na cikin bayin da Sarki Abdurrahman ya aika mata da su. Sannan ga shi shi ma Mandawari ya zo garin Sarki Abdurrahman inda shike a da can. Amma da ya zo ba wanda ya san shi.
Daga karshe ina mai sauraron Mandawari. Kuma ya ce shi ne 'baban soyayya.' To baban soyayya ka yi nazari mana.
Hamza Adamu mai saida 'yan kunne,
Bakin kasuwar Yauri, P. O. Box 78, Yauri, Jihar Kebbi.
GYARA A FIM DIN BURI
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA mika sakon gaisuwa da jinjinawa zuwa ga dukkan jami'an
wannan mashahurin kamfani, watau mujallar Fim, a kan kokarin da suke yi na fahimtar da jama'a da kuma samar da labarai a kan harkokin fim. Bayan haka, zan yi amfani da wannan dama in gabatar da wata kasida a kan fim din Buri da na kalla.
A gaskiya Buri ya kayatar da ni, kasancewar abubuwan da yake karantarwa suna faruwa. Sai dai kash! Ni a wurin wannan fim ya samu rabuwar Albinla kuma daga wurin mutum guda, wato jarumin wannan fim Alhaji Hamisu Iyan-Tama a inda a rayuwarsa ta duniyar farko kamar yanda ake ba da labari ya kasance yana karantarwa ne, wanda cikin ikon Allah ya samu karin girma. To a gaskiya kamata ya yi ya ci gaba da kasancewa malami ko da ko zai kasance shi ne shugaban makaranta, idan kuma ya bar harkar malanta ne to kamata ya yi a nuna wa mutane, don babu malamin da ke barin makarantar da yake karantarwa ya koma kasashen waje a kan harkar kasuwanci kuma kasaitaccen da ba ma za a taba hada shi da wancan tsohon malami ba. To wannan shi ne kuskuren da na fahimta a fim din.
Suleiman Attahiru Gusau,
Gusau Hotel Limited, Zaria Road, PMB 1093, Gusau, Jihar Zamfara. Tel: Office 063 200396 - 200727
HAR AN FARA NUNA TSIRAICI!
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
MUNA so mu fadakar da wasu 'yan fim da suka dauki akidar
nuna yara tsirara a fim. Mun ga haka a finafinai kamar darasi, Mariyatu, da kuma Tangaran 2. Wannan ai jahilci ne da kuma wai da sunan fadakarwa. Babu addinin da ya yarda a nuna tsiraici ballantana kuma addinin Musulunci.
Daga karshe muna gaida Yakubu Muhammad, Ibrahim Sheme, Mandawari, Maishunku, Ahmad, Ali, da kuma Ishaq Sidi Ishaq.
A'isha Bello Sadiq, Amina Isa Sheshe da Jamila Abubakar,
B.U.K. Staff Secondary School, B.U.K., Kano.
MUNA CIN MORIYAR MUJALLA
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA mai mika gaisuwa ga masoyana kamar su Ibrahim Sheme,
Alhaji Garba Dangida, Ashafa Murnai Barkiya da sauran ma'aikatansu, ganin yadda kuke namijin kokarin aikin wasikunmu. Sannan kuma muna cin amfanin mujalla sosai, tana wayar mana da kai a kan abin da ba mu sani ba.
Alhaji Sama'ila Lawal Kwashi Jibia,
Hamalu Vedio & CD Disc Centre, No. 2 Mamman Zugau Road, Jibia, Jihar Katsina.
NASIHA KAN MATA MASU GUDOWA
ZUWA GA 'YAN FIM,
KAMAR yadda muka san aikinku shi ne ilimantarwa tare da
tarbiyyantarwa, saboda haka duk 'yar wasan da kuka sami labarin cewa gudowa ta yi daga gidan iyayenta ba tare da son ransu ba, don Allah ku da kuke a matsayin abokan sana arta ku yi mata nasiha ta koma ga iyayenta, idan kuna neman albarka a cikin sana'arku. Ku yi irin na marigayiya Balaraba, Allah ya jikanta ta da rahamarsa. Domin ita ba ta shiga wannan harka ta fim ba sai da izinin iyayenta. aboda haka duk wadda kuka yi wa nasiha idan ta ki komawa gida sai ku kore ta kawai tunda ku kuna da mutuncinku. Amma idan ba haka ba yara suna shiga duniya suna lalacewa a sanadiyyarku. Wadansu kuma suna kashe aurensu. Mu mun riga mun san niyyarku ta alheri ce.
Nasiru Sabo,
No. 17, Anguwar Malamai, T/Wada, Zariya, Jihar Kaduna.
A KARRAMA 'YAN MUJALAR FIM
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
DALILIN rubuto wannan takarda shi ne domin in yi jinjina ga
mawallafin wannan mujallar, watau Malam Ibrahim Sheme, a kan namijin kokarin da yake yi na ciyar da harshen Hausa da Hausawa gaba a duk duniya.
Sannan kuma ina fatan yadda mujallar ta karrama su Alee Baba Yakasai, to a wannan shekarar sai ta karrama ma'aikatanta irin su Ashafa, Aliyu A. Gora II, Ibro Mammam, Sadiya Abdu Rano, Bashir Yahuza, da sauransu.
Gaisuwa mai yawa ga Furofesa Abdalla Uba Adamu da kuma 'yan wasa irin su Ali Nuhu, Ahmed S. Nuhu, Abida, Hindatu, Momo, Sir Hafizu Bello, Yakubu Lere, Tijjani Ibraheem, Tsigai, Zik, Bashir Nayaya, da Sani Garba S.K. (Suya).
Safiyanu Ibrahim Musawa,
c/o Mani Ibrahim Musawa, Gen. Hospital, Katsina, PMB 2918 Katsina.
YABO GA CIBIYAR HAUSA
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA roko ku dan ba ni fili in mika sakon gaisuwata da nuna farin
cikina a kan taron da Cibiyar Nazarin Hausa ta Jami'ar Usmanu Danfodiyo ta Sokoto ta shirya kuma kuka ba da labarinsa a Fim ta Satumba. Cibiyar ta gayyato manyan malamai masana harshen Hausa da malaman addini, 'yan wasan finafinai, da dai sauransu. Wallahi wannan cibiya ta yi abin yabo kuma ya kamata a yaba mata, domin a gaskiya yanzu ne na san cewa muna da iyaye a nan Arewa.
Sannan wajen fannin mata kuwa a gaskiya a duba yadda suke sanya suturarsu da kuma yadda suke barin kansu a bude kamar 'ya'yan arna. Nan ma akwai gyara. Kuma wajen yawaita soyayya nan ma a yi gyara don gaskiya ya kamata a fi kwadaita wa masoya yadda za su yi aure a tsari irin yadda Musulunci ya shimfida.
Daga karshe ina son in mika gaisuwa ga shugabanmu na kungiyar wasan kwaikwaiyo da taimakon kai da kai ta Kabala Costain, Alhaji Saminu M. Mahmoud, da Yusuf Barau, Sani Moda, Hauwa Ali Dodo, Wasila Isma'il, Ali Nuhu, Ahmed S. Nuhu, Ibrahim Mandawari, Shu'aibu Lawan, daraktoci da kuma furodusoshi gaba daya.
Aminu Gidado Kaduna,
Fed. Min. of Works & Housing,
Field Headquaters, Lafia, P.M.B. 43, Jihar Nassarawa.
... KU YI AIKI DA SHAWARWARIN
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
DON Allah ku ba ni fili a cikin mujalla mai farin jini domin in
bayar da shawara ga furodusoshi da daraktaci. Don Allah su yi kokari su nemi 'yan'uwansu da suka samu halartar taron da aka gudanar a Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, a kan "Sabon salon tafiyar Adabin Hausa: Ci-gaba ko Ci-baya?"
A gaskiya an gabatar da kasidu da shawarwari masu ma'ana da kuma gamsarwa, wadanda za su gyara harkar fim da kuma kyautata al'ada da addinin Bahaushe. Ina ba su shawara da cewa su yi hakuri, su jure, su yi amfani da wadannan kasidu, kada su yi kwadayin riba da kuma dan abin duniyar da za su samu, su yi dubi kan kiyaye hakkin Musulunci da Musulmi, domin Ubangiji zai saka wa kowa kan abin da ya aikata.
Abdul Mumin Abdul Fatah,
Anguwar Malam Dahiru, Gidan Limamin Jumma'a, Suleja, Jihar Neja.
TIJJANI IBRAHEEM BAI DA LAIFI
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA so in yi amfani wannan damar in yi magana a kan wani mai
karatunku Nasiru Attahiru Gusau, wanda wai yake so ya ba darakta Tijjani Ibraheem shawara a kan martanin da ya mayar wa Halima Adamu Yahaya babu wata maganar "yabon kai jahilci" yara nawa ya nema ai bai taba fada ba, ita ma kamawa ta yi. In an yi maka abin kirki bai kamata ya bar ta a ransa ba. Laifi ta yi. Don an yi mata fada ai ba wani abu ba ne, gyara mata kuskure ya yi a matsayinsa na babba.
Kuma ina so in kara game tabbatar da maganar da Tijjani Ibraheem ya yi game da gulmace-gulmacen da ake a kan su Ali Nuhu; to ai yabon gwani ya zama dole, Ali ya zama ciwon ido, babu yadda za a yi da shi sai hakuri, kuma wanda ya dace ai da shi za a yi kyau da biyayya. Ina masu fatan alkhairi, Allah ya kara dankon zumunci, Allah ya sa su dade suna yi. Gaisuwa ga babban baba Tijjani Ibraheem.
Fauziyya I. Sheshe,
Faculty of Law, Bayero University, Kano.
WA KE RUBUTA FILIN M. ZURKE?
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
NA rubuto maku wannan wasika ne don in tambaye ku wani abu
da yake daure mani da kai. Ni dai kowane wata idan mujallarku ta fito, idan ina da zarafi ba ta wuce ni, kuma da zaran na saya na barke ledar filin Malam Zurke nake karantawa kafin in karanta kowane labari.
To tambayata a nan ita ce don Allah wa ke rubuta wannan fili; ko wanene ba karamin ilimi gare shi ba. Ina fatan za ku share ma masu karanta filin hawaye da wannan tambaya tawa.
Daga karshe ina fatan za ku isar mani da gaisuwata zuwa ga Ibrahim Maishunku, Sanusi Burhan, Aina'u Ade, Ishaq Sidi Ishaq, Yakubu Muhammad, Sani Danja da kuma Hamisu Iyan-Tama.
Hajiya Hannatu Ibrahim Omar,
Emir's Palace, Kaltungo, Jihar Gombe.
Hajiya, filin Malam Zurke fili ne na nuni-cikin-nishadi, kuma Malam Zurke ya ce a gaya maki cewa shi ne yake rubuta filinsa!
ALLAH YA JIKAN MASOYIYATA
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA son ku isar mani da ta'aziyyata dangane da rasuwar babbar
masoyiyata, kuma matar Shu'aibu Lawan Kumurci, wato Balaraba. Allah ya jikanta, ya sa aljanna ce makomarta, ya yi ma Shu'aibu zabi na alheri.
A karshe, ina mika gaisuwata ga Ali Nuhu, Ahmad S. Nuhu, Ibrahim Mandawari, Hajara Usman, Hadiza Kabara, da Maryam Aliyu. Wassalam.
Hauwa'u Sani Faskari,
c/o Sani Umar Faskari, Rural Electrification Board, Musawa, Jihar Katsina.
IBRO KA DAINA CIKA BAKI
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
DON Allah ku taimaka ku isar mini da sako zuwa ga shahararren
dan wasan nan Rabilu Musa (Ibro). Ina so ya daina cika baki cewa babu wanda ya isa ya yi wani abu a duniya da zai ba shi tsoro ko kuma babu wani mutum da zai yi masa wani abu. Ni ina daga cikin masu son shirin Ibro. Ibro, ka tuna fa duniya ba ta son mutum mai cika baki. Don Allah ka rika tunani. Bayan haka inason ku mika gaisuwata ga Shu'aibu Lawan Kumurci, Hadiza Kabara, Sani Garba S.K., Ibrahim Sheme da Ashafa Murnai Barkiya.
Yayani Popular Guy Isawa, P.O.Box 279 Isawa, Giade L.G.A., Jihar Bauchi.
MUN GA WULAKANCI A GUN IBRO
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
DON Allah ina son ku yi mani kokarin tambayar mani Ibro game
da wani abin mamakin da ya yi a lokacin da ya zo Kwantagora. Wannan abin na gani da idona, ba labari aka ba ni ba, wanda idan da labari aka ba ni, sai in karyata zancen. To a ranar 7 ga watan Agusta Ibro na garin Kwantagora tare da tawagarsa, mun je masaukinsu don mu ganar ma idonmu. Har ma mun gaisa da Tsigai, Cinnaka da sauransu, sai ba mu ga Ibro da Kulu ba. Muka tambaya aka ce suna baya suna wani wasa. Sai muka je kallo. Me zai faru? Ai haka na ga sun sami bulalarsu ta danyen haki wadda muke kira "miyar tsanya", suka yi ta zabgar mutane har wasu na faduwa. Ai ko da na ga haka sai muka yi gaba kar mu ji ciwo a banza.
Sai na ga dai shi Ibro farin jini ne da son da jama'a ke masa ya sa har wasu suka aje ayyukansu suka nufi wurinsa, amma ya yi ta wulakanta mutane. To shi ne ban gane ba: wannan duk a cikin wasa ne ko kuwa ya yi don ya wulakanta mutane ne? To idan ko haka ne gaskiya bai kyauta ba. Ya tuna fa, ba shi kadai ne dan wasan da ya fara zuwa Kwantagora ba; Tahir Fage da jama'arsa sun zo, sannan kuma tun kafin a san wani wai Ibro Golobo ya zo da nasa jama'ar amma ba wanda na ga ya yi ma jama'a irin abin da Ibro ya yi. Saboda haka nake ba shi shawara da ya daina, jama'a ma ai rahama ne.
Malama Fatima Mohammed Ciroma (Mrs Abubakar),
Rimaye Primary School, Kontagora, Jihar Neja.
LAIFIN ME NA YI MAKU?
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
DON Allah ina so ku ba ni fili
cikin wannan mujallar mai farin jini domin in tambaye ku ce war shin wasikata tana zuwa ko ba ku bukatar in rika rubutowa? Na jima ina rubuto wasiku ban ga alamun kun same su ba.
Daga karshe ina mai mika gaisuwa ta ga jaruma Aina'u Ade.
Abubakar Garba Jibia,
No 3, Mamman Zugau Road, Jibia, Jihar Katsina.
Abubakar, ka binciki hanyar da kake aiko da wasikunka. Da mun same su, da ka ga mun buga.
SHAWARA GA MIJIN A'ISHA MUSA
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
NA rubuto wannan wasikar ne domin in nuna murna da farin ciki
da auren Malama A'isha Musa da Malam Ali Nayara.
Shawara ga Malam Ali Nayara ita ce don Allah ka rike matarka ka kuma lura da yadda aka yi wannan aure, kada ka ba mu kunya.
Da kuma fatan Allah ya ba da zaman lafiya da hakuri, amin.
Ramalan A. Ahmed, Abuja.
Ahmed S. Nuhu da Maryam Aliyu: An fasa auren!
WANI labari da muka samu da dumi-duminsa ya nuna cewa danyar soyayyar nan tsakanin Ahmad S. Nuhu da Maryam Aliyu (Mushaqqa) yanzu ta kare. Majiya mai tushe ta tabbatar mana da cewa Ahmed ya fasa auren Ba'abziniyar yarinyar bayan an dade ana ce-ce-ku-ce da zarge-zarge. Yayin da wasu 'yan fim suke zargin Ali Nuhu da kawo karshen soyayyar, wani abokinsa na kut da kut ya ce, "Ba ruwan Ali. Ahmed ne da kansa ya janye."
Wani mai lura da al'amuran industiri kuma ya ce, "Kai rabu da su! Ahmed ya yi sabuwar budurwa ne, karamar yarinya 'yar jika-jika, shi ya sa ya juya wa Maryam baya."
Fim ta san cewa tuni Ahmed ya yi niyyar auren Maryam, domin har kayan auren ya saisaya. Fasawar da ya yi ta girgiza Maryam da iyayenta, inji majiyarmu, har lissafinsu ya dagula. "Ka ga yanzu ai sai ta nemi daidai da ita," inji wata 'yar wasa da ta tofa albarkacin bakinta a kan wannan al'amarin.
NA JI DADINKU A INTANET
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
ASSALAMU alaikum! Na ji dadi kwarai da nake karanta mujallarku a intanet. Allah shi taimake ku, amin.
Kamaluddeen Dahiru
29 Rabah Road Kaduna, P.O. Box 5010, Kaduna.
FATI MOH'D LOKACI YA YI...
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA so in yi amfani da wannan dama taya gwanata Fati Mohammed
(Mrs. Mai Iska) murnar abin alhairin da ya same ta. Muna mata fatan Allah ya kara daukaka ta, ya sa ta fi haka. Ina kuma son in ba ta shawara a kan yanzu lokaci ya yi da za ta koma makaranta ta yi ilimi mai zurfi, yadda duk inda za ta je a duniyar nan ba za ta sami matsala ba. Kuma za ta samu daukaka da girma fiye da yanzu, cikin yardar Ubangiji. Ina kuma so fati ta dada yin hakuri da mutane masu ziyartarta; ta tuna ba ita ta kai kanta wannan matsayin ba, saboda haka ta rinka bin mutane a sannu.
A karshe gaisuwata ga Hadiza Kabara, babban yaya Ibrahim Mandawari, Hajara Usman , da Hajiya Amina Garba. Allah ya kara fahimta, amin summa amin.
Maimuna Bello (Mrs. Bello)
KUNA CIKA AIKINKU
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
BAYAN gaysua da fatan alhéri, ina gaîda Aina'u Adé da duka
jamma'a Mujallar fim. Ina mai godiya ga Allah da ya kawo mu wannan lokacin. Gaskiya ina jin dadin rahotannin da kuke yi a kan finafinan Hausa. Mujallar tana cika aikinta kuma tana taimaka wa jama'a su fahimci ma'anar fim. A karshe zan mika gaisuwata ga dukkan 'yn wasan fim na hausa. Ina so ku ba ni adireshin Sadiya Abdu Rano.
Ina meka gaysua ta'asia ga duka masu wasan Hausa.
Maman Yawale,
Reprogaphe, National Assembly of Niger, P.O. Box 12234 Niamey, Niger Republic
TSOKACI KAN GAGARABADAU
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
TUN lokacin da tallar fim din Gagarabadau ta fito na sa ido kan
fitowarsa. Lallai kun nuna kokari sai a kara zage damtse domin sauran finafinanku masu fitowa nan gaba. Sai dai matsala ta ita ce shin ba ku ne ke sukar waka da raye-raye ba? Kuma na lura wakar da Laraba (Sadiya Abdu Rano) ta yi wa shi Gagarabadau ta so ta yi kama da wata waka da aka yi a cikn wani fim na Indiya mai suna Tridev. Saboda haka ina neman karin bayani game da wa nnan .
A gaida Ashafa da baba Ibrahim Sheme.Wassalam.
Kasim Lawal Ibrahim,
P.O. Box 75, Kaura Namoda, Jihar Zamfara.
Malam Kasim, a gaskiya ba mu ne muke sukar waka da rawa a fim ba kamar yadda kake tsammani; wasu masu karatunmu ne. Kuma muna ba kowa dama ya fadi abin da ya ga dama a cikin hankali. Sa'annan batun waka ta yi kama da ta cikin Tridev, wannan gaskiya ne. Amma ba ita din ce muka kwafo muka maida ita ta Hausa ba, arashi ne kurum. Kuma kar ka manta, ai kusan kowace waka a duniyar nan za ta iya yin kama da wata wakar a wani yaren ko wata nahiyar, sai dai in ba a bincika ba. Ita wakar Tridev da kake cewa ai ainihi wakar wata zabiyar Amerika ce mai suna Gloria Estefan, wadda ke da rundunar kida mai suna "Miami Sound Machine', suka kwafa suka yi. A cikin faifan ita Estefan mai suna "Evolution" wakar take. Haka kuma ka fadi sunan kowace waka, mu kuma za mu ba ka sunan wata da suka yi kama a wajen kida ko kari, ciki kuwa har da wakokin Shata, Dankwairo ko Maidaji Sabonbirni! Mun gode.
INA AINA'U ADE?
ZUWA GA KUNGIYAR MASU SHIRYA FINAFINAI TA JIHAR KANO,
NA rubuto maku wannan wasika damin in ji yadda harkokin fim
ke gudana. Da yake mun tura maku wasiku kuma ba wani karin bayani. Wanda yake idan ba ta wannan hanya ba ba yadda za a yi mu sa mu damar tuntubarku. Idan za ka iya tunawa, lokacin da muka rubuto maku waccen wasika, mun gaya maku cewa ta hanyar (intanet ce kawai muke jin labarinku a yanar mujallar Fim (www.fim.tvheavencom).
Ga sakona ku isar mani ga Aina'u Ade cewa ta ba ni adireshinta na i-mel domin mu samu hanyar yin hulda a tsakaninmu. Kuma ina fatan ba za a samu tsaiko ba saboda a gaskiya ba na ji dadin a ce ba wani bayani. Ina fatan wannan ba za ta wuce kwana daya ba ko biyu. Na gode.
Almustapha Sidi,
Varna Medical University, Bulgaria
KADA MANDAWARI YA BIYE MASU
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
NA karanta takardar da Ibrahim Sheme ya yi game da Mandawari
mai take "Tsakanin Mandawari , Anabawa da Sahabbai". Yadda Sheme ya yi, ya yi daidai kuma wannan ya nuna mana bambancin da ke tsakanin 'yan jarida da 'yan wasan kwaikwayo. Da a ce 'yan fim ne za su maida martani da mutum ba zai iya karanta abin ba saboda bakaken maganganun da za su sa a ciki; amma Sheme ya bi abin cikin fahimata da dattijantaka. Sabod haka don Allah 'yan fim ga abin koyi nan. Sannan ina so in roki Mandawari da kar ya biye wa wadanda ba su san an shiga sabon karni ba. 'Yan fim kuma ina so su san da mujallar Fim suke rawa saboda haka kalubalensu!
Maimuna Bello (Mrs. Bello)
M.Z. FARU YA YI WA MAJE SATA?
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
KAI tsaye nake son sanar da shugaban Kungiyar Furodusoshi ta
Jihar Sokoto, M.Z. Faru, cewar ya yi abin kunya, musanman satar fasaha rana tsaka da ya yi a fim dinsa mai suna Baiwa. Sanin kowa ne an dauko wannan labari ne daga littafin shahararren marubucin nan, yaro mai farin jini Maje El-Hajeej Hotoro mai suna Gidan Kashe Ahu. Labari ne na wata yarinya mai suna Nabila wacce duk wanda ta aura mutuwa yake yi, har sai da ta yi aure sau uku mazan suna mutuwa. Daga karshe wani saurayi mai suna Salahuddeen ya dage sai ya aure ta.
M.Z. Faru, zan so sanin hujjar da za ka bai wa makaranta littattafansa na cewar kai ba satar fasaharsa ka yi ba? A gaskiya ka yi faduwar bakar tasa! Kuma saboda rashin fasaha irin taka sai ka sa wa fim din sunan marubucin, wato lakanin da ake yi masa a mujalla: " Dan Baiwa". Ka sani cewa fim din ba zai yi kasuwa ba, don zaluncin da ka yi. Da a ce Majen ka samu kuka daidaita, da fim din ya yi farin jini. Ko ba ka da labarin daukakar da mawallafin yake da ita ne? Ka bincika nan garin da kake ka sha labari. Ka kuma kara bincikawa kai yadda aka matsu da fitowar fim din Juyayi da Ruhi albarkacin sunansa.
Rukayya A.A. Lamido Buhari
No. 120, Taiwo Avenue, Sango-Otta, Jihar Ogun.
'YAN MATA KU DAINA RAWA
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA gode maku kan yadda kuke wayar da kan jama'a a kan
harkokin fim din Hausa da na Indiya da na Amerika. Abu na biyu shi ne ina nuna bakin cikina dan gane da yadda wasu 'yan matan fim suke yin wasa har suke kokarin nuna ma duniya cewa sun tashi daga fadakarwa sun koma lalatarwa, misali yadda suke raye-raye suna cin zarafin addini da al'adarmu wanda yake komi ta dade za su mutu su hadu da Allah, idan ba su tuba ba su hadu da azabarsa. Ina kira da su ji tsoron Allah su bari. Su tuna akwai tsufa kuma akwai haifuwa kuma duk abin da mutum ya shuka shi zai girba. Allah ya shirya mu baki daya.
Sidi S. Ibrahim
Kofar Atiku, Ubandoma Road, Sokoto.
SAURAN MU GA DAREN FARKO
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
NA rubuto maku wannan takarda domin in yi jinjina gare ku
kasancewar kuna fadakar da jama'a. Allah shi taimake ku shi kara daukaka wannan mujalla da mutanenta, amin. Bayan haka ina kara jinjina da yabo ga furodusa da kuma darakta na Gagarabadau. Hakika an sanya basira da hikima a ciki. Muna jiran fitowar na gaba, watau Daren Farko.
Gaisuwa ga Ibrahim Sheme, Fati Baffa Fagge, Zahara'u Shata, Ibrahim Maishunku, sannan shugaban matasa masu fim din Hausa Ali Nuhu. Na gode.
Babagida Muh'd B.
IBB Provision Store, Shop No. 4, Ubandoma Road, Sokoto.
NI MA NA SHIGO CIKIN JAMA'A
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA farin cikin sanar da ku cewa to yau ni ma na bi sahun 'yan'uwa, domin na bude i-mel domin saduwa da ku a kai a kai. Ina fata za mu amfani juna da wannan. Na gode.
Ilyasu Abdulmumini (Tantiri)
Furodusa, darakta kuma dan wasa
SHAWARA GA BASHIR NAYAYA
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA so a mika min sakon gaisuwa ga gwanina Bashir Nayaya.
Wallahi Uncle Bashir kana matukar burge ni a duk fim din da ka fito. Amma don Allah kar ka kara yin wasa mai kama da wanda ka yi a Sai A Lahira ko nawa za a biya ka. Uncle Bashir ba na son sunanka ya baci a wajen jama'a.
Amina Sulaiman Gombe
KUMURCI KA YI NAZARI TUKUNA
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
DALILIN rubuto maku wannan wasika shi ne domin in yaba
maku, in nuna maku farin cikina da jin dadi game da wasikata ta farko da na aika maku kuma ta samu buguwa a cikin watan Satumba tare da amsa tambayar da na yi. Ina so ku taimaka mani da mujallar da aka bayar da tarihin Ciroki ta adireshina.
A karshe ina so ku mika shawarata zuwa ga Shu'aibu Kumurci da ya yi nazari matukar gase game da so da yake yi wa Maryam Umar kafin ya kai shi ga zancen aure. Allah ya sa Balaraba ta huta, ya sa kabari ya zama wurin aminci ne a gare ta, mu kuma ya sa mu cika da imani. Don Allah ku isar mani da ta' aziyyata ga Kumarci da iyalan marigayiya Balaraba.
Da fatan Allah shi kara wa mujallar Fim kwazo da basira, amin.
Abubakar S. Musa
Fototek Industries Limited, P.M.B.155 Minna, Jihar Neja.
KASH! FURUCIN HADIZA KABARA
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
NA yi matukar gamsuwa game da bayanin edita a kan wasikata ta
karshe, kuma ina jiran amsar Hajiya Balaraba Ramat game da bukatar da na gabatar.
2. Abin haushi ne kalamin da Hadiza Kabara ta yi lokacin fadan da suka yi da Saratu Gidado a kan wai Saratu na zargin wani darakta yana kwana da ita Hadiza din. Idan aka yi la'akari da yadda mafi yawancin jama'a suke kallon matan industiri a matsayin marasa mutunci, to wannan zai iya tabbatar masu da gaskiyar zargin da suke yi ma duk wata mai wannan harka ko da kuwa ba hakan suke ba. Saboda haka ya zama dole su san abubuwan da ke fita a bakunasu idan ma har dole ne sai sun furta din.
Dabi'ar nan ma ta fadace- fadace a kan saurayi ko gulmace-gulmace ba a san bahaushiya, kamila, mai mutunci kuma Musulma mai ikirarin wai tana fadakarwa ba da irinta. Haba, kar ku zama 'yan Nigerian film mana! Edita, mun gode Allah ya saka da alheri, amin.
Maryam Garba Jumare
CABS, Kaduna Poytechnic, Kaduna.
ADIRESHIN BIBA DA NA HAMISU
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
DON Allah ina so ku ba ni adireshin Hauwa Ali Dodo da Hamisu
Iyan-Tama da gaggawa. Na rubuto wannan wasika ne daga kasar Burkina Faso.
Mohammed Abdullahi Yakasai
Adireshin Hamisu Iyan-Tama shi ne: Iyantama@yahoo.com. Ita kuma Hauwa ba mu da nata, amma in ka aiko mata da wasika za mu ba ta.
ANA KALLON FIM A BULGERIYA
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
DALILIN da ya sa na rubuto maku wannan wasika shi ne
ina son in shaida maku da cewa ni haifaffen Jihar Sokoto ne. An haife ni a garin karamar hukumar mulki ta Rabah a shekarar 1983. Na kare makaranta a shekarar 2000 . Ina karatu ne a makarantar koyon likitanci da ke garin Barna a Bulgaria. Kuma lokacin da ina Nijeriya ni ma'abucin kallon finafinan Hausa ne kuma ina sha'awarsu kwarai da gaske. To amma a nan Bulgaria babu finafinan, ta hanyar na'urar komfuta kacal ne muke kallo domin tunawa da gida, kada mu manta da al'adunmu na gida.
Kuma ina son in shaida muku da cewa a nan Bulgaria akwai abokanmu Turawa da yawa wadanda suka kalli fim din Hausa kuma sun yaba da shi kwarai da gaske, har ma wasu daga cikinsu sun yi kwafi wasu kasakasan namu. Daga karshe ina son ku aika mini gaisuwata ga wadannan mutane: Ibrahim Mandawari, Ibro, Ibrahimawa Production, Sani Musa Danja, Hamisu Iyan-Tama, Ishaq Sidi Ishaq, Ciroki, Zulkifilu Muhammad, Ahmed S. Nuhu, Yautai, Ali Nuhu, da sauran 'yan wasan Hausa da ke Nijeriya.
Abubakar Isah Rabah, Medical University, Barna, Bulgaria. tel.: 0035998247029.
KU RIKA SANYA MUJALLA DA WURI
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA jin dadin karatun mujallar Fim, amma me ya sa ba ku canza
website dinku a intanet sai bayan mujallar ta dade da fitowa? Ko mutum yana son ya karanta sai koda yaushe ya bude web site din ya same shi tsohuwa ce, kuma ga irinmu da ke ba ma zaune a Nijeriya balle mu saya mu karanta sai kawai a intanet muke iya karanta. Don Allah ina son idan kuka canza mujallarku ku aika mani imel.
Amina Suleman
Daga England
Hajiya, mun aika maki da amsa ta imel dinki kamar haka: Assalamu alaikum. Dalilin da ya sa muke makara wajen sanya mujallar a intanet shi ne saboda akwai wasu masu karatu da dama a nan Nijeriya da kuma Saudiyya da Nijar wadanda ba su sayen mujallar idan har za su iya karanta ta da wuri a intanet. Shi ya sa muka ce bari mu rika yin latti har sai sun sayi kwafe din sannan mu sanya ta a website. Kin san a namu tsarin (saboda rashin ci-gaba ko lattin ci-gaba ta fuskar kayan fasaha) ba za mu iya yin yadda wasu kamfanoni suke yi a kasashe kamar Ingila ko Amerika ba. Sanya mujallar da muke yi a intanet saboda kishin harshen Hausa ne, ba domin mu samu riba ta kudi ba. Ina fatan dai a sabon website dinmu kike ganin mujallar, wato www.fim.tvheaven.com.
Kuma yana da kyau ki rika duba www.kanoonline.com da kuma www.hausafulani.com domin ganin wasu al'amuran da suka shafi kasar Hausa, cikinsu har da batun shirin fim. Wassalam.
KUN BACE DAGA INTANET NE?
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
YAU wajen watanni bakwai kenan ban sake ganin mujallar Fim
a intanet ba. Tun watan Maris na shekara ta 2002, ban sake ganin wata sabuwar fitowa ta mujallar ba. Me ya sa? Ko kun sami wata matsala ne? Ko kuma kuna ganin abin ba zai dore ba ne? A gaskiya ban ji dadin haka ba! Da a kodayaushe in na tashi daga aiki ko kuma na sami wani dan lokaci nakan karanta mujallar da na yi downloading zuwa www.kanoonline.com, amma yanzu sai na ga canji. Hakan ina ganin zai iya kawo wani rashin cigaba ga ita mujallar da kuma shi kanshi shirin fim na Hausa.
Mustapha Mu'azu
Computer Unit, Media Trust Limited (Publishers of Weekly and Daily Trust newspapers), No. 22, Lusaka Street, Wuse, Zone 6, P.O. Box 6873, Abuja.
Malam Mustapha, muna jin dai kila kana cikin wadanda ba su sayen kwafen mujallar Fim a kasuwa su karanta sai dai su karanta ta a intanet kawai. Idan ba haka ba, ga shi a duk fitowa muna nuna inda mujallar take a intanet, har kuwa a jikin bangonta! To, za ka same ta a intanet a wannan adireshin: www.fim.tvheaven.com. A sha karatu lafiya!
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin