ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA so in ba wani makarancinku amsa game da tambayar da ya yi na cewa Ali Nuhu wane yare ne? Mutumin, mai suna Mohammed Bukar Habib Danborno, ina so ka nemi mujallar Garkuwa ta watan Afrilu/Mayu 2002, za ka ga tarihin Ali Nuhu, wanda shi kansa Alin yake boyewa. An yi hira da wani mutum mai suna Nuhu Poloma, dan asalin garin Gelengu cikin Karamar Hukumar Balanga ta Jihar Gombe. Mutumin yana mai fadin cewa Ali dansa ne, shi ne na hudu a jerin 'ya'yansa.
Ya auri uwar Alin a nan Kano wacce ita Babarbariya ce shi kuma Nuhu Poloma, Bawaje ne. In ka duba za ka san cewa shi Ali Bawaje ne, dan Jihar Gombe, tunda uba ake bi.
Mutumin a halin yanzu shi ne shugaban jam'iyyar PDP a nan Jihar Gombe. Don haka ku ma mujallar Fim kun yi kuskuren cewa shi Ali Babarbare ne. Domin na tabbata dattijon ba zai yi karya ba. Ku huta lafiya.
A'ishatu Y. Imam.
I.R.S., P.M.B. 022, Gombe.
FATAN ALHERI GA HINDATU
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA son in mika gaisuwata tare da fatan alheri zuwa ga Hindatu
Bashir a kan aurenta da ta yi. Muna matukar farin ciki. Allah ya sanya alheri amin summa amin. Allah ya kare ki daga sharrin makiyanki. Sannan kuma sai fatan alheri zuwa ga Rukayya Umar Santa da Misbahu M. Ahmad. Allah ya kawo mana ranar auren naku, ya kuma tabbatar ya sa a yi a sa'a. To Rukayya yau dai Misbahu ya ce shi din ga naki ne, sai a yi masa kwalliya da gazal har da tozali! Dawayya ya yi daidai; haka muke so sauran 'yan wasa su yi koyi da ku. Allah ya sanya alheri. Gaisuwa ta musamman zuwa Zahra'u Shata.
Hajiya Aisha Gaidana
Gidan Hakimi, Galadanci, Kano.
KU BA NI TARIHIN RABI'U H.R.B.
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
DALILIN da ya sa na rubuto maku wannan wasika shi ne, ina
so don Allah ku taimaka ku ba ni tarihin furodusan nan Rabi'u Ibrahim mai kamfanin H.R.B. kuma idan da hali ku buga hotonsa, sanin kwarewarsa wurin shirya fim; kuma ina jin dadin ganin finafinansa saboda wadansu kalmamin Hausa da yake sakawa a dukkanin fim din da ya shirya. Ku huta lafiya.
Ibrahim Maidada Mai Faci,
Bakin Tashar Motar Mutum Biyu, Gassal LGA, Jihar Taraba.
INA SON TARIHIN DAN WANZAN
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
NA rubuto wannan wannan wasika ne musamman a kan Malam Zurke. Ni din nan a cikin wannan mujalla shafin Malam Zurke yana daga cikin abin da nake matukar so na karanta, domin har wani suna na saka wa Malam Zurke na musamman-wato 'Shanshani'. Saboda a bisa dukkan alamu Fim ba ta so a san wanene takamaiman Malam Zurke saboda bayanan sarri. To amma ina so in har ba a damu dangane kowaye shi ba, ina so a bayyana mani kowaye shi soboda burge ni da yake matuka da gaske.
Bayan haka ina so kamar yadda kuka yi hira da yawancin fitattun 'yan wasa ina so ku yi hira da Dan Wanzam wanda suke yin fim da Ibro domin mu ji dalilin da ya sa suke fim da Ibro saboda mun ga a yanzu duk fina finan Ibro ba ya yi da shi, sannan kuma mu ji tarihinsa gaba daya.
Daga karashe don Allah ina so a mika gaisuwata ga Ibrahim Sheme, Ashafa Murnai, sai Ibro domin na ba shi Gwarzon shekara ta 2002 saboda saboda ba a yi kamarsa ba a fagen fim.
Abba Atiku,
Tsamiyar Boka Bus Stop, Hotoro, Kano.
NA YI MAKU LAIFI NE?
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA so ku ba ni dama in mika sakon gaisuwa ga ma'aikatan wannan mujallar mai farin jini. Ba yabon kai ba, zan iya cewa ina daga ciki mutanen da suke karanta wannan mujallar a kowane wata. Sai dai kash! ban sani ba ko na yi maku laifi ne, domin na rubuto wasika sau hudu, amma har yanzu ba a buga ko da daya ba. Amma ban yi fushi ba. Kuma don Allah ina so ku ba ni cikakken adireshin kamfaninku da ke Kano.
Adamu Muhammad Babankuka,
M.H 12 Badagi, Lapai Road, Kabala West Junction, Kaduna.
Ofishinmu a Kano yana nan kusa da gadar nan da ake bi a tsallake titi a 'Yandusa, Gyadi-Gyadi.
ASHAFA ZA KA SA NI A FIM?
ZUWA GA ASHAFA MURNAI BARKIYA,
ASHAFA, da kai nake so in kama kafa wajen shiga harkar fim, domin ganina da kai daya, amma sai na fahimci kai mutum ne mai mutunci. To a gaskiya tunda kuka bude ofis a Kano, ina son in rika kawo maku ziyara to amma ina gudun wulakanci. Don haka da kai zan kama kafa kuma ina son ka yi mani hanyar da zan fara fim a kamfanin FKD da HB da HRB da kuma 'Northern Star Films, wato kamfanin mujallar Fim. Hakika na ji dadin yadda ka karbe ni da fara'a muka gaisa na ba ka wasikata. Ina fata ba za a watsa mani kasa a ido ba.
Gaisuwa ga dukkan 'yan fim.
Murjanatu T. Adam,
Block 'K' 98, Kundila Housing Estate, near Masjudus Sahaba Friday Mosque, Maiduguri Road, Kano.
INA YAKUBU LERE NE?
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
NA rubuto maku wannan wasika ne domin neman karin bayani game da fitaccen furodusan nan El-Saeed Yakubu Lere wanda ya yi suna wajen fada ko in ce hayaniya da abokan sana'a. Wani abin da ya ba ni mamaki shi ne, a da, da wuya ka ga mujallar Fim ba tare da maganar Yakubu Lere ba wanda sanin kowa ne ya kara da mutane da yawa, amma a yau sai ka ga an yi wata uku babu ko da sunansa a cikin mujallar.
A nan dai na fahimta cewa mai laya kiyayi mai zamani. Don haka ina kira ga Lere cewa ya kara fitowa a dama da shi mana.
Gaisuwa ta musamman ga 'yan fim.
Jamilu Bello Dogarawa.
c/o Muhammed Sani Bello, Faculty of Administration, A. B.U. Kongo Campus, Zariya, Jihar Kaduna. Telephone, 069-333971
INA KAUNAR FARIDA JALAL
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA son don Allah ku ba ni fili a cikin wannan mujalla mai farin jini don in nuna kaunar da nake yi ma Farida Jalal, jaruma mai haskawa. Farida, ina fatan kina lafiya, kuma ina maki barka da sabuwar shekara. A karshe ina mika gaisuwa ga Ibrahim Sheme, Alh. Garba Dangida, da Ashafa Murnai Barkiya.
Alh. Samaila Lawal Kwashi
No. 2 Mamman Zugau Road, Jibiya, Jihar Katsina.
INA TAYA SU MAIKATANGA MURNA
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
GAISUWA ta musamman ga dukkan 'yan'uwana ma'abota karanta mujallar Fim. Kuma ina mika gaisuwa ga Malam Ibrahm Sheme, kuma ina taya murna ga Malam Sani Muhammad Maikatanga da Malama Salaha Muhammed Suleiman Gumel bisa auren da suka yi. Allah ya bada zaman lafiya, amin.
Yusuf Suleiman Musa Gyadi-Gyadi,
Department of Accountancy, University of Maiduguri.
MUNA MURNAR SU MISBAHU
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
DON Allah ina so a ba ni fili a cikin wannan mujalla mai farin jini domin in nuna farin cikina game da auren Misbahu da Rukayya wanda aka ce za a yi. A gaskiya aurensu ya cancanta, kuma ya yi daidai. Allah ya bar su tare. Daga karshe nake cewa gaisuwata ta musamman ga jarumata Aina'u Ade da Ishaq Sidi Ishaq, Nura Husaini, da kuma Shu'aibu Lilisco.
Abubakar Garba Jibia,
No. 3, Mamman Zugau Road, c/o Hamalu Video Cassette B/Tasha, Jibiya, Jihar Katsina.
HAFIZU YA BURGE NI DA RUHI
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA so in mika sakon gaisuwata ga kamfanin H.B. saboda fim
din da suka yi mai suna Ruhi. A gaskiya fim din ya burge jama'a, ya yi ma'ana, kuma darakta Hafizu Bello da Maje El-Hajeej sun cancanci yabo, da jarumar fim din wato Zahra'u Shata. Da fatan Allah ya kara maku basira. Allah ya kare ku daga sharin masheranta. Gaisuwa ta musamman ga Yakubu Lere, Ibrahim Sheme, Hafizu Bello, da kuma sabuwar tauraruwa Farida Jalal.
Nafi'u Abdullahi Liman,
F.P. 9, Alkalawa Road, T/Wada, Kaduna.
KU AUNA KAFIN KU AIKATA
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
JAN hankalin da zan yi wa furodusoshi shi ne, idan za su yi finafinai su rika dora labarin a kan mizani su auna su ga cancantarsa kafin su yi shi. Haka kuma 'yan wasa kuma idan aka ba ku sin wanda za ku yi, ku auna shi ku ga cancantar, da dacewarsa kafin ku aikata. Haka kai ma darakta idan furodusa ya kawo maka fim ka auna shi akan mizani tukunna, kaga cancantarsa da dacewa. Ku ma mawaka idan aka kawo maku waka to ku dora ta a kan mizani tukun. Sai kuma ku 'yan kallo idan kun kalli fim ku tsaya ku fahimce shi. Kar ku yi zagi, ku aika wa mujallar Fim da nasiholinku.
Salisu (Sidiya)
Alfijir Sound Centre, No. 10, Muhammad Dikko Road, Dutsin-ma, Jihar Katsina.
Wasiku na i-mel
Muna so masu aiko da wasika ta hanyar Intanet su rika sa cikakken sunansu da adireshinsu, ba adireshinsu na 'e-mail' kurum ba. Muna da damar mu ki buga duk wasikar da ba mu yarda da ita ba ko don ba ta dauke da cikakken suna da adireshi. Kuma a rubuto da Hausa.
KU CI GABA DA AUREN JUNA DON...
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
DA fatan kuna lafiya. Don Allah ina dada ba 'yan fim din Hausa
shawara da su ci gaba da auren junansu. Domin ta haka ne zai sa sauran jama'a da su daina kyamar auren 'yar fim. Hakan zai zama misali babba a gare su.
A gaskiya na ji dadin wannan ci-gaba da kuka samu na canza website daga www.kanoonline.com zuwa www.fim.tvheaven.com. Wannan canji yana nuna ci-gaban Hausa fim a duniyar fim. Kuma wannan site ya fi dacewa da mujallar Fim domin samun damar ganin hotunan 'yan fim da makamantansu. Hakan ya dada min jin dadin karanta mujallar a intanet.
Dalilin da ya sa kuka ga na fi son karanta mujallar a Intanet, domin a ko da yaushe ta fi kusa da ni. Sannan, a matsayina na ma'abocin son ganin fim din Hausa da kuma son jin labarin 'yan wasan kamata ya yi da in yi amfani da hanya mafi sauki a gare ni wadda za ta kusanta ni da su.
Mustapha Mu'azu
Webmaster, Weekly and Daily Trust newspapers
22, Lusaka Street, Wuse Zone 6, Abuja.
WANENE YA RASU CIKIN 'YAN FIM?
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
DON Allah ina so in san ko wane dan fim ne ya mutu a cikin
watan nan, ko watan da ya wuce. Mun ji dai an ce wani ya mutu a cikin 'yan harkar fim na Hausa. To Allah ya jikan Musulmi, amin.
Hajiya Hasiya Ali B. Magashi,
Embassy of Nigeria, Dakar, Senegal.
Darakta Tijjani Ibraheem ne Allah ya yi wa rasuwa a ran 25 ga Disamba, 2002. Allah ya jikansa, amin.
TAMBAYOYI GAME DA AINA'U ADE
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
ASSALAMU alaikum. Da fatan kananan lafiya ameen. Bayan
haka ina son in samu wadansu abubuwa kamar haka: adireshin i-mel na Aina'u Ade; shin Aina'u ta taba yin aure? Kuma 'yar wane gari ce? Za ku aiko mani da hotonta? Na gode kwarai.
Buhari Muhammed
Ba mu da adireshin i-mel na Aina'u. Aina'u ba ta taba yin aure ba. Asalinta Bayarabiya ce, amma dao 'yar Kano ce-domin a nan aka haife ta kuma a nan ta tashi kuma a nan take zaune tare da iyayenta. Mun daina aika wa mutane hotunan 'yan wasa domin su ba su so saboda wasu sun buga kalanda da hotunan ba tare da izini ba. Mun gode.
ZAN IYA BIYAN KUDIN SHEKARA?
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA son in ji ko zai yiwu na biya subcription na shekara daya don ku rinka aiko mani da mujallarku kai tsaye, in yana yiwuwa ina son ku sanar da ni kudin da kuma ta hanyar da zan biya.
Ubale Randy,
Information Office, Ganjuwa L.G.A., Kafin-Madaki,
Jihar Bauchi.
ubaleaazeez@yahoo.com
Malam Ubale, mun taba jaraba wannan tsarin, amma ba mu ji da dadi ba saboda rashin ci-gban kasarmu ta wannan fuskar: ko dai ka ji mujallar da muka aika wa mutum ba ta isa gare shi ba (wani ya dauke ta a hanya) ko kuma tsadar aikawar ta fi farshin mujallar. Shi ya sa muka hakura tare da ba jama'a irinka hakuri. Edita
INA JIN DADIN FINAFINAN HAUSA
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
DA fatan kuna lafiya. Allah ya sa haka amin. Don Allah ina son
ku rika aiko mini mujallar Fim saboda ina matukar kaunar fim din Hausa kuma ni bako ne wajen aiko maku wasika amma ba bako ba ne wajen kallon fim din Hausa. Wassalam. Na gode.
Alhaji Abdoulmoumin Abdousamad
SANARWA:
Wasiku na GSM
Ba mu buga duk wata wasikar GSM wadda ba ta dauke da cikakken suna da adireshin wanda ya rubuto ta. Kuma muna sanar da masu rubutowa cewa za mu buga lambar GSM dinsu tare da wasikunsu. Amma idan mutum ba ya son a buga lambar wayarsa sai ya gaya mana bayan ya sa cikakken suna da adireshi. Haka kuma tilas a rubuto wasikar da Hausa.
INA TAYA HINDATU MURNA, AMMA...
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA taya Hindatu Bashir murna da ta yi aure amma kuma ni ban
yarda shekarunta 28 ba. Ni a nawa hasashe, ga Hindatu can ina gani a cikin shekaru 35.
Sai kuma tambaya kan Ali Nuhu da Rukayya Dawayya. Me ya sa ba su da wani aiki sai rawa kamar a cikin Kauli da Dhalal ba su da wani rol sai kawai aka nuno su cikin suna rawa.
Yagana Ahmed Maiduguri
08037872443 (mazauniyar Kano ce)
KU BA NI LAMBAR ALI NUHU
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
ASSALAMU alaikum. Don Allah ina so ku ba ni lambar wayar
GSM ta Ali Nuhu.
Halima, NAF Base, KD
(08037022470)
Lambar Ali ita ce: 08037861210
INA SON LAMBAR ISHAQ
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
DON Allah lambar Ishaq Sidi Ishaq nake so ku ba ni ta GSM ko ta gida.
Aisha Dangote,
Sokoto Road, Kano. (08023273172)
Lambar Ishaq ita ce: 08037876235
TA'AZIYYA GA IYALAN TIJJANI
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA so a mika min gaisuwata ga iyalan Tijjani Ibraheem kuma a ba ni wayar Farida Jalal. Na gode.
Farida Moh'd Yola, Kano. 08023353306
Lambar Farida Jalal ita ce: 08034523556
... ALLAH YA RAHAMSHE SHI
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
NA samu labarin rasuwar Tijjani Ibraheem a gun abokina Yakubu Muhammad na 'Two Effects'. Allah ya ji kansa ya rahamshe shi, amin.
Isma'il Inuwa Darzo, Bauchi.
080 23531799
FATAN ALHERI A GARE KU DUKA
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA taya mujallar Fim da ma'aikatanta da dukkan masu karanta ta fatan alheri a wannan shekarar tare da ta'aziyya a bisa dukkan rashe-rashen da aka yi a cikin 2002. Na gode.
Alh. Kabiru Ado
Minjibir, Jihar Kano. 08033334201
ALLAH JIKAN TIJJANI
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA fatan Allah ya jikan Tijjani Ibraheem kuma Allah ba Kumurci da amaryarsa zaman lafiya. Na gode.
Sarki Muktar, Dabo Films, Kano. 080 35881365
FATAN ALHERI HRB, NAKWANGO
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
INA jinjina wa HRB da Nakwango game da nasihar da ya yi wa 'yarsa Saima a Rawani-2. Ba ita kadai ya gyara wa zaman aure ba, har da sauran mata masu wasa da aure. Na gode.
Najlah Iya 08033492386
INA FILINKU NA INTANET?
ZUWA GA MUJALLAR FIM,
ME ya sami filinku na hira ta intanet? Wassalam.
Ibrahim Dankano, Lamingo Prison PMB 2024 Jos. 08037030954
Rashin isasshen fili ya kawo haka, amma muna kokarin ganin mun dawo da filin. Mun gode.
Sauran wasika sai watan gobe. Mun gode. Edita
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin