Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 42   Agusta 2003
WASIKU


BABBAN SHAFI
GASKIYA DAYA CE
FADI SONKA
Wasiku
NEMAN MAFITA
DUNIYAR FINAFINAI
RAHOTO
Malam Zurke
RA'YIN FIM
Bukukuwa
Sauran Labarai
SABUWAR FUSKA
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka

Bangon Fim ta 35. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 34. Danna nan ka gani!

Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM MAI FITOWA!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
FADI SONKAr sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da tunanin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: Wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, ta da jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Wasikun masu karatu

SAKON TAYA MURNA
ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA in mika sakon taya muna da fatan alheri ga 'yan fimdin da Allah ya nufe su da yin aure, kamar Aminu Ilu Danbazau, Nura Hussaini, Hajara Usman, da Hasiya Ayah. Ubangiji Allah ya ba su zaman lafiya. Wadanda ba su yi ba Allah ya nuna mana lokacin nasu. Gaisuwa ta musamman ga Ibrahim Sheme bisa namijin kokarin da yake yi. Allah ya taimake shi bisa duk al'amuransa amin. Aliyu Matazu,

CC6 Dabban Road, U/Sanusi, Kaduna.

HAJJO INA MURNA

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA so ku isar mani da sakon taya murna ga Hajiya Hajara Usman (Hajjo) murnar auren da ta yi, tare da angonta Alhaji Abubakar Mohammed. Na ji dadi sosai da na ji labarin. Ina yi musu fatan Allah ya ba da zaman lafiya. Yayani Popular Guy Isawa, P.O. Box 279 Isawa, Giade L.G.A., Jihar Bauchi.

'YAN WASA BAI DACE BA

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

A GASKIYA abin da 'yan wasa suke yi wa masoyansu wallahi bai dace ba. Abin da yasa nace haka kuwa shine, duk lokacin da wani dan wasa ko 'yar wasa za su yi aure kamata ya yi a ce su sanar da masoyansu, ba sai sun riga sun yi sannan ka gani a mujallar Fim cewa sun yi aure ba. Wani auren da aka yi wanda ya tayar wa mutane da dama hankali ba don ba su son auren ba, a'a sai dai kawai ganin ya kamata a ce sun sami halartar daura auren domin nuna kauna ga wannan wadda aka daura wa auren, wato shahararriyar 'yar wasan nan mai suna Hajara Usman. A gasikiya mun yi murna da yin addu'a. Don haka muna yi masu fatan alheri, Allah ya ba da zaman lafiya, kuma wadanda ba su yi ba don Allah in lokaci ya zo su sanar kafin zuwan ranar. Salisu Ladan, No. 12 Girku Road, U/Sarki, Kaduna.

ALI: DASHEN DA ALLAH KE SO...

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

SARA da sassaka ba ya hana gamji toho." Wannan karin maganar shi ne abin da na fatimta bayan na yi dogon nazari game da kalaman batanci da nakan ji a gari da wadanda ake bugawa a mujalla a kan Ali Nuhu. Tun tuni na fuskanci cewa ya riga ya yi tashin gwauron zabo tsakanin 'yan'uwansa 'yan wasa ta fannin daukaka da kwarewa. Tun farkon fitowar finafinansa, wasu jama'a na ikirarin cewa yana da girman kai da jan aji. Bayan haka, an sha yin maganganun batanci a kan finafinansa, wanda duk idan ka lura da kalaman, ba a bukatar ya yi gyara a inda ya yi kuskure illa kawai su nuna wa duniya cewa ba shi bda basirar da zai shirya fim face ya kwafo daga finafinan Indiya. Shin mai yin screenplay na finafinai kamar Abin Sirri Ne, Juriya, Sababi da Zahiri, kuma ya yi finafinai irin su Mujadala, Juriya, So, Zubaida da sauransu, kuma ya ba da umarni a fim din Gori da Khusufi, a ce wai ba ya da basira? Bayan haka ko kun san cewa suna masu shirya finafinan Indiya sukan kwafo wadansu finafinan Amerika su mayra da yarensu?

A karshe malaman jami'a kun ba ni kunya, musanman membobinku da suka fito a intanet suka soki Ali, suka gaya masa bakaken maganganu, musamman Rabee'u Sebeji. Shin me ya kamata malami ya yi idan an yi masa kuskure? Nasiha zai yi wa mai kuskuren ko kuma zai zo kafar watsa labarai ya yi masa kacakaca? Don haka hattara. Dashen da Allah ke so … Mahmud Ibn Abubakar Mahmud, (M.I.A.M.) Sheikh Abubakar Gumi College, Kankara Road, Kaduna.

FUROFESA YA BAN MAMAKI

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA fatan wannan mujallar mai dubin masoya za ta ba ni fili in bayyana ra'ayina a kan dokokin da Furofesa Abdalla Uba Adamu ya zayyana a mujallar watan Yuni 2003 cewa wai dole sai Hausawan asali za su sami shiga gasar finafinai ta intanet ta 2003. A gaskiya na yi matukar mamaki a kan yadda Abdalla, wanda a wata wasika da na rubuto wa Fim na bayyana a matsayin jagoran yada al'adun Hausa, ya nuna tsantsar kabilanci. Babban abin da ya kara ba ni mamaki ma shi ne inda ya ce har ma da Fulani da kuma Barebari ba su cancanci shigar da finafinansu ba. Wanda hakan ke nuna cewa ba wani abu ba ne illa son rai, wanda a ko da yaushe shi ke hana mu samun ci-gaba.

Ina ba da shawara ga 'yan fim, musamman irin su Ali Nuhu, wakanda suka shiga wannan majalisar ta intanet, da su janye jikinsu tunda ba ta da amfani. Hamisu Muhammed, Zamgarawa Tsatsumburum, Jihar Damagaram, Jamhuriyar Nijar; c/o Malam Sani House, Karkarku, Sandamu L.G.A., Jihar Katsina.

BA A FAHIMCI ALI BA

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA so in fadi nawa ra'ayin a kan batun Ali Nuhu da masu kalubalantarsa a intanet. Zan fara kai tsaye da Furofesa Abdalla Uba Admau, wanda ya ce Ali ya zage su da su da dalibansu. To ni a nan ina ganin cewa furofeso bai yi adalci ba, domin ni da na karanta mujallar ta watan Fabrairu, ban ga inda Ali ya yi zagi ba, kuma ban ga inda ya ce dalibai jahilai ba ne; abin da ya ce kawai shi ne, "idan sun iya su zo su gwada". Sai wani kuma mai suna Adam Mstapha da ya ce Ali ya fito da maitarsa a fili, cewar finafinan da yake yi tsagwaron manufarsa ba ta wuce kasuwanci ba. To don Allah, Malam Adamu, me ya sa kafin ka yi wannan maganar ba ka yi wa Abdulla tambaya a kan abin da yake sawa su malaman jami'a su yi yajin aiki idan gwamnati ba ta biya su albashi da alawus ba? Ita kuma Amina Abdulmalik, cewa ta yi "Ali yaro ne". To kfin maida mata da martani bari in yi amfani da wannan damar in yi wa marigayi Abdulmalik addu'a: Allah Ubangiji ya yi masa rahama, ya sa yana cikin aljanna, ameen, ke kuma Allah ya kara maki juriyar rashinsa. Bayan haka don Allah zan yi miki tambaya a kan littafin da kika rubuta mai suna Ruwan Raina. Fisabilillahi a matsayinki na Musulma abubuwan da kika rubuta a wasu wurare cikin littafin kin yi daidai? Ke ce fa kika nuna cewa ga irin rayuwar da kuke yi da marigayi, yadda yake sumbatarki, a matsayin kazar gida ba ta gidan gona ba. To ina mai tabbatar miki, da Allah ya sa cikin da kika samu, Allah ya bar shi kin haifi da sa'an Ali Nuhu, a shekaru da hankali da kuma ilimi, to da shakka babu ko da kin rubuta littafin, ba zai bari ya fito ba mutane su karanta, ko da zai rasa ransa sai dai ki jika littafinki ki shanye, kuma ko da fim din ma ya fito ba zan bata lokacin ganinsa ba, don na san shirme ne. AbdulAziz Mohammed, No.114, Tudun Maliki, Kano.

... A TAUSAYA MASA MANA

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

DON Allah ina son a yi wa Ali afuwa kan tuntuben bakin da ya yi. Wanene ba ya kuskure? Wani in aka shimfida nasa, kare ma ba zai sunsuna ba, balle ya ci. Kuma na san duk da bai aiko da sakon ban hakuri ba, a zuciyarsa dole ya yi nadama. Amma wajen wata biyu da suka wuce, ake ta faman aika masa da bakaken maganganu. A tausaya masa mana! Yaro yana kan angoncinsa amma duk an takura masa; ai sai a sa su kasa cin abincin kirki. Tun da dai babanmu malaminmu ya mayar masa da martani ya kuma gargade shi kan ya iya bakinsa, sai a sassauta masa. Kuma masu cewa ya je ya yi aikin weather forecast ai ba dole ne abin da ka karanta da shi za ka yi aiki ba; wani sai ya karanta Catering amma sai ka gan shi a banki, to sai a ce masa ya koma kicin ya dafa abinci? Ba a haka. A yi masa rangwame ko ya sha ruwa.

Mrs. Nafisa Ali Muktar, No. 1A Tarauni Quarters, by Maiduguri Road, Kano. Tel:064-665915

ALI, AURE SAI DA HAKURI

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

NA rubuto wannan wasika ne domin in bai wa abokina Ali Nuhu shawara. Ka sani cewa rayuwar aure dai rayuwa ce ta hakuri da sanin ya-kamata. Saboda haka, a ko da yaushe ka kasance mai hakurin zama da iyalinka. Ina fatan Allah ya ba ku zaman lafiya da kwanciyar hankali. Abubakar Adam Baga, Finance Department, Kukawa Local Govt., Jihar Borno.

... KA FA RIKE AMANA

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA son wannan mujalla mai farin jini ta isar da sakon taya murna ga yaro mai tashe, dangane da aurensa da ya yi. Ali, da fatan za ka rika amana, kasancewar aure amana ne, kuma sunnar Annabi ne (s.a.w.). Saboda haka, Malam Ali Nuhu ka rike matarka da soyayya da amana. Ina maku fatan dukkan alkhairin Ubangiji a cikin wannan sabuwar rayuwa ta aure da kuka shiga. Allah ya bayar da zaman lafiya, amin.

Abdul Mumin Abdul-Fatah, Anguwar Mallam Dahiru, Gidan Limamin Juma'a, Suleja, Jihar Neja.

ALI, MISBAHU, KU YI ADALCI

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA mika sakon farin ciki da taya Ali da Misbahu murnar auren da suka yi. Ina rokonsu, don Allah su rike matansu da adalci, su san mu mata sai da hakuri. Allah ya ba su zaman lafiya, kuma ya ba su zuri'a tagari. Wassalam. Ni ce taku har abada. Laure Musa, Keffi, Nassarawa State.

UMMI, KI YI TAKA-TSANTSAN

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA so ku ba ni fili a wannan mujalla mai farin jini don in mika sakon gaisuwa ga gwanayena, kamar Ummi Nuhu, Ali Nuhu, Ahmed Sadiq Nuhu, da duk wani dan wasa baki daya. A gaskiya Ummi Nuhu kina burge ni kwarai da gaske, don ina jin dadin duk wani shirin da aka ce akwai ki a ciki. Sai ki yi taka-tsantsan da mutane, ki kuma hakura da duk abin da ya faru gare ki, ki dauka mikaddari ne. A. A. Hameed (Koryal) c/o Amas & Sons Nig. Limited, No. 65 Filling Station, Soro, Tudun Wada Ganjuwa L.G.A. Jihar Bauchi.

... DUK WANDA YA TAKA KI, TAKA SHI!

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA mika gaiwuwata ga sarauniyata Ummi Nuhu kuma ina yi mata fatan Allah ya kuma daukaka ta, ya ba ta miji nagari.

Bayan haka, Ummi na ga wata magana cewar kina da saurin fushi. To ina son in gwada maki abu daya. Duk wanda ya nemi ya daga maki hankali ban ce ki kyale shi ba ko waye. Don ba a fi ki tsumma ba, ba a gwada maki kwarkwata. Duk wanda ya taka ki, ina so ke ma ki taka shi.

Gaisuwata ga kawarki Zahra'u Shata. Kuma ina son ki ba ni adireshinki, don in Allah ya yarda zan ziyarce ki. Fatima Ishaq Tela-Ada, Kofar Baru, Daura, Jihar Katsina. Tel: 065-557005

SUNA BURGE NI, AMMA...

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

NA rubuto ne domin in nuna gamsuwata game da yadda finafinan Hausa burge ni. Sai dai kash! Duk da yadda kuke ikirarin cewa kuna koyi da al'adunmu na Hausa, e, zan iya cewa a halin yanzu ba haka abubuwan suke ba. Don haka ina fatan darektoci za su magance matsaloli. Muhammad Yahaya Gumel (Dan-hajiya) No. R3, off Abeokuta Street, Mando, Kaduna.

SHAWARA GA ASABE DANFULANI

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

AN ba mutun namiji hankali,fiye da mace, ballantana kuma aka yi sa'a namijin nan mai ilimi ne da tunani da hangen nesa, wannan kuwa ba wani ba ne illa Furofesa Abdalla Uba Adamu. Don Allah ina rokon Asabe Danfulani ta saurara, don furofesa ya fi ta hankali tunani, hangen nesa, maganganunsa da shawarwarin da yake bayarwa a kan wannan harkar ta finafinai wallahi su ne abin dauka a yi anfani da su. Don ku mata ba kowace shawara ake yi da ku ba. Ku dai a bar ku a harkokin cikin gida kawai daga daki sai kicin da sauran wasu harkokin naku na mata. Bugu da kari kuma na san shi Furofesa Abdalla ya fi ta wayewa. Faruk Mohammed, W. 17 Gangara Road, Sabon Gari T/Wada, Kaduna.

INA KAUNAR FARIDA JALAL

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA daga cikin masu karanta mujallarku saboda samun sahihan labarai game da finafinan Hausa da 'yan wasa. Allah ya kara taimako amin. Edita, zan yi matukar farin ciki in har kika ba ni sararin isar da gaisuwata ga Farida Jalal. Hakika ina daga cikin masu kaunarta kuma finafinanta suna burge ni.

Kuma don Allah ku taimaka mani da lambar wayar Sadi Sidi Sharifai idan yana da ita. Idan babu to ina zan same shi idan na zo Kano? Ina kuma gaida Misbahu Ahmed, Yakubu Muhammad, Mudassiru Kasim, Farida Jalal, Maijidda Mustapha, Ummi Nuhu, da dai sauransu. Surajo Usman Rawayya (Dan Baba), Dept of Business Administration, Federal Polytechnic, P.M.B 1012, Kaduna Namoda, Jihar Zamfara. Mun daina ba da lambar 'yan fim. Za ka iya ganin Sadi a kamfanin kada wakokin fim na Iyan-Tama, ko Sulpha (a Sabon Titi) da sauransu.

JINJINA GA ZULAI DALHAT

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA son ku ba ni fili a cikin wannan mujalla mai farin jini don in jinjina ma jaruma Zulai Dalhat, tauraruwar Kaduna. Babu shakka wannan jaruma ta fim din Salsala ta cancanci yabo, saboda irin yadda ta nuna kwarewa, gwaninta, bajinta da hazaka a cikin wasanninta. Gaskiya 'yan Kaduna, kai da ma duniyar finafinai gaba daya, kun yi sa'ar samun ha zika, kamila, kuma gwanar 'yar wasa irin Zulai. Ina fatan Allah ya kara mata hazaka da daukaka.

Gaisuwa ga Hadiza Kabara, Aina'u Ade da Shu'aibu Lawan (Kumurci). Bashar Abubakar Wamakko, Rukayya Video Centre,Wamakko, Jihar Sokoto.

ALLAH YA JIKANSU

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA so in yi amfani da wannan in mika gaisuwar ta'aziyyata ga 'yan'uwa da abokan arziki dangane da rasuwar darakta Tijjani Ibraheem. Ubangiji Allah ya jikan shi, ya yi masa rahama, ya sa ya huta, amin. Kuma ina mika gaisuwar ta'aziyyata ga Hajara Usman dangane da rasuwar mahaifinta da kuma babbar 'yarta, Allah ya jikansu, ya yi masu rahama, amin.

Gaisuwa ta musamman ga Ibarahim Mandawari, Hamisu L. Iyan-Tama, Isa Bello, Hussani Sule Koki, Misbahu M. Ahmad, Saima Mohammed, A'isha B. Umar, Hauwa Maina, da sauransu. Nasiru Attahiru Gusau, Public Complaints Commission, P.M.B. 01061, Gusau, Jihar Zamfara.

ALI, ALLAH YA DAYYABA

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA mai rokon editar wannan mujalla mai farin jini ta dan ba ni fili in mika sakon gaisuwa tare da nuna farin ciki game da auren jarumin jarumai na bana, kuma yaro mai tashe, wato Ali Nuhu. Ali, muna yi maka gaisuwa, tare da fatan Allah ya ba ku zaman lafiya tsakaninka da matarka. Allah ya ba da hakurin zama tare. Kuma Allah ya ba da zuriya dayyiba. Ni ne mai kaunarka, a madadin 'Freedon Youth Development Association,'

Mustapha Challube, Insha Allahu Oil Nig Ltd, P.O Box 1661, Gamboru Road, Maiduguri. Tel: 076-235558.

BA KU BUGA LABARINSU?

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

A KONTAGORA akwai finafinai da furodusoshinmu suka yi, amma ban ga an kula da sanya labarinsu a cikin mujalla ba. Ko ba su cimma wannan matsayin ba ne? Daga karshe ina son sanin inda zan ga wakilin ku na Kwantagora. Jinajina ga dukkan ma'aikata mujallar Fim Amina Aliyu (A.A.), Unguwar 'Yan Hausa, Kontagora, Jihar Neja.

Ai kuwa muna buga labaran Kontagora, shi ya sa muke da wakili a garin. Ko a wannan watan idan kika duba za ki ga hira da wani furodusa daga Kontagora din. Shi wakilin namu, ga lambar wayarsa: 067-220690.

BA LAIFINSU BA NE

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA son in yi kira ga masu kallon finafinan Hausa, musamman yadda wadansu ke dora karan tsana ko mummunar fahimta ga masu shirin fim wai don dan wasa ya fito a mutumin banza ko marar mutunci ko dan ta adda. Mutane su lura duk abin da suka ga dan wasa ya fito, ba halinsa ba ne, an umurce shi ne ya fito a hakan, don a nuna wa mutane ire-iren abubuwan da ke faruwa a cikin duniya, ta hanyar hikima ko gugar zana don mutane su kiyaye. Kuma irin wannan fitowa tana kara wa mutane ilimi da dama.

Babangida Dalhat (Zumudi-Master), No. 17 Shararar Pipes, Adamawa Street, kusa da gidan marigayi Bagobiri Mai Kalgo, Kofar Kaura, Katsina.

SUNA TAIMAKA WA HARKAR FIM

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

NA rubuto wannan wasikar ne domin in sada zumunci da karfafa soyayya tare da mika gaisuwa zuwa dukkan 'yan fim da 'yan mujallar Fim da dukkan wanda yake bayar da gudunmuwa ga harkar shirin finafinan Hausa. Wadannan mutane sun cancanci yabo, saboda su ne suka kai harkar fim a matsayin da take a yau.

Daga karshe nake fatan Allah ya bar mu tare. Wadanda suka riga mu gidan gaskiya Allah ya jikansu da rahamarsa, amin. Abubakar Alh. Adam, Finance Department, Baga Kauwa Local, Government Area, Jihar Borno.

LAIFIN WANENE?

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

SHIN wai kun fara gajiya da aikin mujallar ne? A mujallarku ta watan Agusta 2002 kun fito, sai dai ba irin fitowar da aka saba ba. Labarin Ibro ya fito har sau biyu inda yake cewa ba ya tsoron uban kowa, sannan kuma a labarin Hamisu Iyan-Tama kun ce a tari shafi na 36 to sai ga shi babu ma shafin kwata-kwata. Sannan labarai kusan uku duk sau biyu suka fito, amma ban ji kun ce kun yi kuskure ba. Ko ba ku karantawa idan ta fito? Kuma laifin wanene irin wannan? Sannan a fitowar Fabrairu 2003 babu rubutu a shafi har guda hudu. Kuma nan ma ban ji kun ce komai ba. Sannan ta wannan watan labarin Misbahu guda biyu ne sannan ga karancin wasiku, ga karancin sunayen wadanda suka gane kacici-kacici. Menene dalilin wannan? Da fatan za ku gyara.

Armaya'u Aminu 'Yandaki, Kaita L.G.A. Authority, P.O.Box 2020, Katsina.

Idan ka ga irin wannan ba laifin mu ba ne, laifin yana daga inda ake aikin hada mujallar ne. Idan har ka ga mujalla da shafi babu rubutu, ka mayar da ita inda ka sawo, su sake maka wata. Mu kuma su dawo mana da ita. Batun kacici-kacici, iyakar amsoshin da muka samu kenan. Mun gode.

KU RIKA BA MU KALANDA

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA son duk lokacin da karshen shekara ya yi, don Allah ku rika ba masu aiko maku da wasiku kalandunku wadanda ke dauke da hotunan 'yan fim jarumai maza da mata, ina har da hali.

Ahmed Bello, c/o Hon. Justice Hussein Mukhtar, High Court of Justice, Burundi Street, Block K. 2, Wuse Zone 5, P.O. Box 8511, Abuja.

INA KAUNAR MARYAM MUSHAQQA

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

DON Allah ku ba ni fili a cikin mujallarku mai farin jin in bayar da shawara ga abar kaunata Maryam Aliyu (Mushaqqa) dangane da abin da ya faru da ita. Maryam, ki tuna Ahmed S. Nuhu ba shi kadai ke kaunarki ba. Ni mai wannan wasika ina matukar kaunarki. Domin mu nuna wa Ahmed kasawarsa, ina kaunarki kuma da aure. In kin amince, ki rubuto mani ta wannan mujallar mai hada soyayya da zumunta. Insha Allahu zan zo domin mu sadu mu kuma shirya abin da ya kamata. Ina nan ina sauraron amsarki.

Ramalan A. Ahmed, Primary Health Care Dept., Gwagwalada Area Council, P.O. Box 01, Gwagwalada, FCT Abuja.

Kash! Malam Ramalan ka makara. Maryam dai ta yi miji, kamar yadda ka gani a cikin wannan mujallar.

KIRA GA F.K.D. DA H.R.B

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

DON Allah muna sanar da Ali Nuhu mai FKD Production da Rabi'u Ibrahim mai HRB cewa su rika sanar da mu ranar da finafinansu za su fito ta cikin mujallar Fim domin muna kaguwa da fitowar finafinansu. Gaisuwa ta musamman ga jama'ar FKD gaba dayansu da Rabi'u Ibrahim 'mai babban kamfani.' Rahima, Amina da Madin Shaua, Tsohon Layi Quarters, Jahun, Jihar Jigawa

A WARE WA MARUBUTA SHAFI

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA son in ba ku shawarar da nake ganin za ta kara wa mujallarku farin jini da kwarjini a idon masu karanta ta. Ya kamata ku ware shafi daya ko biyu a mujallarku domin yin tsokaci ga marubuta, saboda ni aikin marubuta da na 'yan fim kusan Danjuma ne da Danjummai. Ita kanta harkar fim ta samo ci-gaba ne ta hanyar wani littafi da wata shahararriyar murubuciya ta rubuta mai suna Ki Yarda Da Ni; tun lokacin da aka juya wannan littafi zuwa fim, sai harkar ta samu karbuwa. Wannan fim shi ne makasudin habakar harkar fim ta fadada ta ci gaba.

Ko ba komai, da a yi ta kame-kame gara a hada gwiwa da marubuta, saboda muna da marubuta masu kaifin hankali da basira. Idan har wannan mujallar ta karbi wannan shawara tawa, ta ba mu fili don yin tambayoyi ga marubuta game da littattafansu, ko kuma yin sharhi game da littattafai ko kuma ku rika yin hira da marubuta, to za mu yi matukar farin ciki.

Binta Tukur (Ta'alhazai), No. 61, Galadima Dudi Road, Kofar Fada, Malumfashi, Jihar Katsina. bintukscool@yahoo.co.uk

Hajiya Binta, mun gode da wannan shawarar. In Allah ya yarda za mu duba ta mu gani.

WAI BIYA AKE YI KU BUGA WASIKA?

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

SHIN don Allah kudi ake biya ne ko kuwa wata hanya ce ta sai ka san wani sa'annan za a buga takardarka a wannan mujallar? Ko kuma hotuna ake aikowa kuna zabar fuskar da ta fi kyau, kuna buga wasikunsu? Saboda abin da mamaki idan ko har ba haka ba ne, to don Allah duba cancantar wasika, ba yawan wasikun da kuke samu ba.

Jinjina tare da yaba wa jarumaina Fati Suleiman, Tahir Fage, Ibrahim Mandawari, Hamisu Iyan-Tama, Maryam Mashahama, Hauwa Ali Dodo (Biba ikon Allah), Sani Danja, don Aminu Shariff (Momo). Murtala Lawal Tafoki (Photographer), c/o Dr. Dalhat Ahmed, District Head, Tafoki, Mairuwa Local Govt., Jihar Katsina.

Malam Murtala, ka maida wukar! Ba a biyan ko sisi kafin a buga wasikar mutum. Da muka ce wasiku sun yi yawa, muna nufin su kansu wadanda muka zabe don bugawa suna da tarin yawa, don haka sai ka ga kafin a kawo kan taka an dan dauki lokaci. To amma fa mahakurci mawadaci ne. Mun gode.

GAISUWA GA GWANAYENA

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

KU dan ba ni fili a wannan mujallar mai farin jini in mika gaisuwa ga fitattun 'yan wasa irin su Misbahu M. Ahmed, Aminu Acid, Ahmed S. Nuhu, Zahra'u Shata, Rukayya Umar Santa, Hauwa Ali, Saima Mohammed, Sani Musa Danja, Abubakar Hayatu Baballe, Shu'aibu Labaran Danwanzan, da Abubakar Sabo.

Abdussalam Isma'il, Northern Nigeria Flour Mills Farm, Kaboji, P.O. Box 344 Kontagora, Jihar Neja.

A TUNA DA ADDINI DA AL'ADA

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

DON Allah daraktoci da furodusoshi, ku rika kula da sutura da kuma tsarin shiga ta 'yan fim. Idan muka duba za mu ga cewa fim din Hausa yana nuni ne ga al'adar Hausawa da kuma Musulunci, saboda haka bai kamata a dinga kwaiwayon shigar wasu ba, musamman karin gashin kanti. Kuma ina son yaba wa mujallar Fim a kan namijin kokarin da suka yi na shirya fim din Gagarabadau. A gaskiya fim din ya shiryu kwarai matuka, kuma ya hada kwararrun 'yan wasa.

Daga karshe ina mika gaisuwa ga hazikaina, kamar: Sadiya Abdu Rano, Shehu Hassan Kano, Kabiru Nakwango, Baballe Hayatu, Misbahu M. Ahmad, Fati Baffa, Ibrahim Mandawari, Ibrahim Y. Ibrahim (Dumbadus), Zahara'u Shata, da Zuwaira Isa. Fatima Abubakar Rufa'i, Federal Government College, P.M.B. 103, Minna, Jihar Neja.

INA ZAN SAMU MUJALLU?

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

NI bako ne wajen rubuto maku wasika, kuma bako ne wajen karanta mujallunku. Sai dai kuma ni ba bako bane wajen kallon finafinan Hausa. Saboda jin dadin ganinsu ya sa har na fara karanta mujallarku. Hakan kuwa ya faru ne sanadiyyar ajiye wata mujalla da daya daga cikin masoyanku kuma abokina wato Tukur Dahiru Futuk ya yi na kanga yana karanta mujallarku sai kawai wata rana na karbe bta na duba, sai na ji kawai son wannan mujallar ya shiga zuciyata. Sai na ce masa to a gasikya ni ma na koma karanta wannan mujallar. Sai ga shi Allah ya yi min zuwa gida a cikin watan Oktoba. Sai na je domin in sami tsofaffin mujallun da suka wuce domin in karanta. Na je bayan Bata na duba duka ban samu ba sai aka ce in tafi masallacin Abacha da ke cikin Sabon Gari. Na je can sai aka ce mini a gaskiya babu tsohuwa. Sai na samu sabuwa ta wannan watan na saya. Don haka in son ku gaya mani inda zan sami wadannan tsofaffin mujallun domin in faro karatun daga tushe.

Abdu Umar Shuwaki, Karamar Hukumar Kunchi, Jihar Kano; sojan Nijeriya da 6, Bataliya, garin Ibagwa, a Karamar Hukumar Abak cikin Jihar Akwa-Ibom.

Malam Abdu, za ka iya samun wasu daga cikin mujjalun da kake nema idan ka zo ofis dinmu na Kaduna.

FATAN ALHERI GA MARY CHONOKO

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

NA rubuto domin in taya Mary Isa Chonoko murnar komawarta makaranta. Da fatan Allah ya sa hakan shi ne mafi alheri a gare ta. Kuma Allah ya kara mata budi da daukaka. Daga karshe ina mika gaisuwa, ga Ibrahim Sheme, Aliyu Gora II, Maimuna Alhassan, Sadiya Abdu Rano, da sabuwar editarku Aisha Abba Ahmed, da dai sauransu.

Nazeef A. Imam, Imam House, Kwarau, Birnin Yero-Kwarau, Igabi Local Govt Area, Jihar Kaduna.

RADDI GA MOH'D DAKAYYAWA

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

NA karanta wasikarka, Jibrin Mohammed Dakayyawa, kamar yadda ka kira kanka. Kalamanka ba su yi kama da sunayenka ba.

Rashin ilimi da tarbiyya sun sa ka yi mana mummunar fahimta da fassara. To ina tabbatar maka "tarbiyya daga gida take farawa". Don haka in iyaye suka ba mutum tarbiyyar banza daga gida, to a haka zai girma. Ka ce a industiri ana hure wa matan aure kunne su kashe aurensu. To wannan na bar ka da matan aure masu mutunci su ba ka amsa, don kuwa na tabbatar su ba irin matan da ba su san darajar aure ba, har ake zuwa a hure masu kunne.

Ka ce "da, yara suna karatu ne idan suna tafiya". To, har yanzu yara masu tarbiyya haka suke kuma suna kallon fim su tsinci abubuwa masu kyau a ciki. Kuma zuwa otal ba iskanci kawai ke kai mutane ba, kamar yadda ka ce. Hatta taruttukan kara wa juna sani kan addini akan kama otal a yi su, su kuma amfani mutane. Bare kuma don za a shirya fim da ka ce ana zuwa iskanci ne. Ka ce muna kai ziyarar yaudara wajen manya, don kara mutunci a sana' armu. To mu tuni mun mutunta ita sanaar tamu da kyautatawa, don mu mun yarda da Allah da ya ce "ya rubuta kyautatawa a kan komai", kuma mun gode masa da ya kaddaro fim ce sana'armu. Muna rokonsa ya nuna mana hanya mafificiya da za mu gyara hankar. Kuma su manyan da muke kai wa ziyara masu illimi da tarbiyya ne. Sarakuna kuma da ka ce an wulakanta, su ma suna da ilimi da tarbiyya, ba za su yi wa abin mummunar fahimta kamarka ba.

Ina ba ka shawara ka koma wa neman ilimi na zamani da addini, don da jin maganganunka kana aikin abin nan da ake cewa "Jahilci a kullum ya fi hauka zama ciwo".

Usman Kabara (dan wasa), Lerawa Films Kaduna. usmankabara@yahoo.com

BAN GA WASIKUNA BA

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

NI mai karatun mujallarku ce a kowane wata, amma sai dai kash! ban sani ba ko na yi muku laifi ne, domin na rubuto wasiku da dama amma ban ga kun buga ko guda ba, amma ban yi fushi ba, ina mai shaida muku cewa mujallar ku ba ta isarmu a garin Daura, domin sai mun zo Kano sannan muke saye.

Gaisuwa ga Ibrahim Sheme, Ishaq S. Nuhu, Hajiya Fati Baffa Fagge, da fatan za ku ba ni lambar wayarta.

Salisu Ahmed Gorjo, Karkarku Palace, Karkarku, Daura, Jihar Katsina.

AHMED, ROKI MARYAM GAFARA

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA son wannan mujalla, mai farin jini ta bani dama in dan tofa albalrkacin bakina dangane da hirar da kuka yi da Ahmed S. Nuhu a mujallar watan Mayu.

A gaskiya Ahmed ban ji dadin wadansu bayanai da ka yi ba ta bangare guda. Domin kuma Hausawa na cewa duk wanda yar rufa asirin wani, to fa Allah zai rufa nasa. Abin da nake gani yau, ko da Maryam Aliyu tana sayar da tsiya ne ai kai mai rufa mata asiri ne. Bai kamata ka fito ka tona mata asiri haka ba. Kai ne ka fada da bakinka cewar ka neme ta, kuma kun rabu amma kuna nan kuna harkar arziki da ita, amma kuma daga baya ka zo kana shaida wa duniya cewar wai kana zarginta ne shi ya sa ka ki aurenta. A gaskiya idan har kuna mutunci da ita, to ina mai ba ka shawara ka je ka roke ta ta yafe maka, don kuwa na ga a mujalla an ce ita ma ta yi saurayi dan uban ubansu.

A karshe gaisuwa ga jan gwarzo, mai jan hali, jan namiji, Aliyu A. Gora II, da jaruma Sadiya Abdu Rano.

Alh. Suleiman Bello Lere, Senior Agric Field Overseer, Sanga Local Government, Jihar Kaduna.

INA GIDAN DABINO DA BURHAN?

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

NA rubuto wasika kusan guda biyar bara (2002) ina tambaya da neman sanin inda wadannan 'yan wasa suke: Ado Ahmed Gidan Dabino da Sanusi Burhan Daneji. Ko suna fim har yanzu ko kuma sun daina?

Gaisuwa ga babban oga Ibrahim Mandawari, Ibrahim Maishuku, Shu'aibu Kumurci da Maryam Mashahama. Ma'assalam.

Abdul Mumin Abdulfatah, Gidan Limamin Jumma'a, Unguwar Malam Dahiru, Suleja, Jihar Neja

Ado da Sunusi suna nan a Kano suna ci gaba da harkokinsu. Ado bai daina fim ba, amma shi Sunusi ya yi ritaya daga sana'ar, yana harkar komfuta a 'CBC Business Centre,' Daneji.

KU SANYA KALA CIKIN MUJALLAR

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA matukar yabawa da yadda kuke ilimantarwa, sadarwa da kuma nishadantar da dimbin masu karatu da mujalla mai kala mai kyau, takarda fara fes rubutu tsaf tsaf, ba maimaitawa (repetition), ba kurakurai sai dan abin da ba a rasa ba. A gaskiya, ba Bahaushe ba ko wani mai jin Hausa, har wanda bai san 'zo karbi' ba da Hausa, idan ya ga Fim sai ya sake dubawa, sai in ya ga Hausa ce tunda ba ya iya karantawa zai aje.

Saboda haka, ina mai ra'ayin ku mayarda shafin nan na Fitattun Taurari gaba daya ko kuma hotunan da ke cikinsa na kala. Idan kun yi haka, tabbas farin jinin mujallar zai karu, bukatar kara buga kwafin mujallar zai karu fiye da yadda kuke zato, musamman idan ba ta shafi mu masu saye ba wajen farashi. Da fatan za ku duba da idon basira.

A mika gaisuwata ga Sadiya Abdu Rano, Rukayya Umar Santa, Maryam Aliyu, Hauwa Maina, Maryam Mashahama, Alasan Kwalle, Misbau M. Ahmad, Ahmed S. Nuhu, Mal. Kabiru Nakwango, Hajiya Hajara da dattijo Isa Bello Ja.

Mohammed Namakka Shehu Gwadabawa, NITEL Plc., P. M. B. 2409, Sokoto.

GAISUWA GA MAIJIDDA IBRAHIM

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA so ku shigar min da gaisuwata zuwa ga fitacciyar 'yar wasan nan da ta fito a Khusufi, wato Maijidda Ibrahim, kuma ku ba ni lambar wayarta da kuma adireshinta. Ina gaida Hadiza Kabara da sauransu.

Jummai Adamu kofa ran burchi Opp. Abdullahi Manager's House, Bauchi.

WAI FATI MOH'D ZA TA AURI BATURE?

ZUWA GA MUJALLAR FIM,

DON Allah ina so ku yi mani karin haske dangane da halin da Fati Mohammed ke ciki tare da maigidanta Sani Musa Mai Iska a Ingila. Jama'a na ta yada ji-ta-ji-tar cewar wai ta hadu da wani Bature dan asalin Ingila, ya nuna bukatar aurenta tare da lasa mata zuma a baki, wanda hakan ya sa ta bude wa Mai Iska wuta sai lallai ya ba ta takardar saki. Aka ce hakan ya sa suna cikin halin zaman doya da manja a can kasar ta Birtaniya.

Abdulrahman Abdullahi Ringim,

No. 260 S/Gari Qrts, P. O. Box 036 Ringim, Jihar Jigawa.

Mujallar Fim ba ta yarda da yada ji-ta-ji-ta ba. Can a kwanan baya mun yi magana da Fati da Sani ta wayar tarho, kuma sun karyata batun wai sun rabu. Kuma har yanzu suna Ingila. Ba mu yi maganar da su kan a buga a mujalla ba, shi ya sa ba ka ga labarin ba. Matsayin kan wannan magana shi ne, karya ce kawai ake yadawa game da su. In da akwai hujja, to a wannan mujallar za ka fara ganin cikakken labarin. Mun gode.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin