Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 28   Afrilu 2002


BABBAN SHAFI
Mu Leka Mu Gani
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 1
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 2
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 3
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 4
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 5
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 6
Malam Zurke
Ra'ayin Mujallar Fim
Hajjin Bana
Sauran Labarai
Ra'ayi Ba Gaba ne
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN

 
If you had a new browser, you would be able to view this java applet. Akwai:  


Baban Amarya (rike da 'yar autarsa), da Jibrin Kwality, da Uwar Amarya rike da amaryar, da Darakta Hafizu Bello da dan wasa Rabi'u Muhammad Rikadawa
Yadda Shu'aibu da Balaraba suka yi auren tarihi

Rabon mutane su ga taron daurin auren 'yan fim irin wannan tun lokacin auren Fati Moh'd

ABU kamar wasa, karamar magana ta zama babba, inji Garba Supa. Kuma karshen tika-tika, tik! Duk wata hassada, kyashi da kuma kushe daga makiya auren Shu'aibu da Balaraba ba su hana daurin auren ba. Zakaran da Allah ya nufa da cara, ko ana mazuru ana shaho sai ya yi!

Dogon Gida, sanannen gida ne a Unguwar Kaji, wadda ke kan hanyar Kaduna zuwa Zariya a bayan garin Kaduna. Akwai akalla dakuna 50 a gidan. A wannan gidan ne aka haifi fitacciyar 'yar wasa Balaraba Mohammed a cikin 1982. A nan ta girma. A nan aka daura aure a ran Jumma'a, 15 ga Maris, 2002.

Tun ran Alhamis, wato jajibirin daurin auren, gidan ya fara cika da 'yan'uwa da abokan arziki, wadanda suka zo biki. Ita Balaraba, ta zo garin daga Kano a ran Laraba.

Ran Jumma'a, tun da safe, jama'ar da aka gayyato ta hanyar kati ko tarho ko sanarwa a rediyo, ko suka karanta labarin a mujallar Fim, suka fara durarowa zuwa gidan. Kan ka ce kwabo, gidan ya cika makil da jama'ar gari. Su ko 'yan fim, ya kasance 'abu namu', wai kura da kallabin kitse; mazansu da matansu sun hallara domin taya 'yan'uwansu murna. Rabon mutane su ga taron auren wani dan fim tun lokacin na su Fati Mohammed da Sani Musa (Mai Iska).

A Kano, Shu'aibu ya nuna wasu halaye a ranar daurin auren, ya ba mutane mamaki. Misali, har kusan karfe 9 na safe, bai shirya ya fara haramar tafiya Kaduna ba. Wakilinmujallar Fim ya same shi kusa da gidansu yana wasan 'yar zungure (snooker). Duk wanda ya same shi ya ce, "Ya ba ka shirya ba?", sai ya ce, "Ai ba ji."

A gidan su Kumurci, da misalin karfe 9 na safe aka fara haduwa. Jama'a sun ci ado, akwai kuma manyan abokan Ango da suka yi anko (suka sa kaya iri daya). Daga cikinsu akwai Sani Musa Mai Iska, Shu'aibu Idris Lilisco, Tijjani Asase, Jazuli Kazaza, Ibrahim Sinana, da wasu. Ango da wasu abokansa suka shiga motar furodusan fim din Kwandala. An kuma samu wasu zaratan 'yan acaba da suka isa Kaduna a kan baburan hayarsu daga Kano. 'Yan acabar dai tun da safe suka dirkaki hanyar Kaduna suka yi ta barin wuta.

Wani wakilin Fim da ya je Kaduna daga Kano ya ce lokaci daya suka tashi tare da tawagar ango, da misalin karfe 12 na rana. Ko kafin su iso gidan Amarya, wurin ya dinke, ba masaka tsinke.

DA misalin karfe 2:38 aka daura auren. Amma saboda yawan jama'a, da yawa ba su san an daura din ba. Sadakin da Shu'aibu yabiya shi ne N20,000 lakadan, kuma an biya sadakin tun makwanni kafin ranar.

Har zuwa bayan daurin auren mutane sun ci gaba da kwararowa kamar farin dango, kowa ka gani yana cike da murna. Har wasu na gardama suna cewa tun da aka Kaduna, ba a taba samun daurin auren da ya tara mutane haka ba. Yadda su Fati da Sani suka kafa tarihi a Kano, haka Balaraba da Shu'aibu suka kafa a Kaduna.

Da yawa daga cikin 'yan wasan da suka zo daga Kano, duk wanda ya diro sai masoyansa su yi masa caa, wasu na so su yi magana da dan wasa ko kuma ko da rigarsa ko rigarta ce su taba don neman tubarraki. 'Yan fim sun hada da Auwalu Marshal, Ibrahim Mandawari, Adamu Bello Ability, Abdullahi Maikano Usman, Hafizu Bello, Jibrin Kwality, Muktar MD, Abdulmunafi Sani, Ashiru Sani Bazanga, Tahir Fagge, Cinnaka, Aliyu Abdullahi, Shu'aibu Lilisco, Sani Mai Iska, Ibrahim Y. Ibrahim (Dumbadis), Ali Nuhu, Muhammad Inuwa Auwal, Al-Amin Ciroma, Bala Anas Babinlata, Ahmad Alkanawy, Mu'azzam Boss, da sauransu. A mata kuma akwai Saima Mohammed, Rukayya Umar Santa, Maryam Umar Aliyu, Usaina Gombe (Tsigai), A'isha Ibrahim (Saliha), A'isha Musa, da sauransu.

Can a cikin gida, taf yake da dan'adam. Dakunan gidan, duk yawansu, sun cika da 'yan biki. Tsakar gida kuwa ba a cewa komai, domin saboda cika har sai da mutum biyu suka suma, daya sai da aka kai ta asibiti.

Ita ko Amarya, ta kasa zaune ta kasa tsaye saboda hidima. Ta yi kyau a cikin kayan Fulani, farare, da yake jikar Sarkin Fulani ce. Fara'a a gun ta kuwa, sai ka ce gonar auduga. 'Yan matan amarya, irin su Babbar Kawa, 'yar wasan nan Safiya Mu'azu, sun saje da iyayen Amarya a cikin anko na atamfa, har da Binta uwar Balaraba.

Shi kuma Ango, dole ya zama abin tausayi. Tun da ya iso mutane suka rufe shi da gaisuwa. Tun yana amsawa, har ta kai ga bai iya magana, murmushinsa kuma ya koma yake. Da abin ya yi kamari, sai da aka kai shi wani daki can nesa da gidan, aka kulle shi shi kadai. Maroka da makada da sauran masoya suka yi dafifi a bakin kofar, bawanda suke so su gani sai Kumurci.

Wani wakilinmu ya kewaya ya tsallaka ta kan katanga ya dira cikin gidan. Sai ya tarar da ita ma Amarya ana so a kulle dakin da take a ciki, amma abu ya faskara.

Iyalin Gambu (wato barayi) su ma sun ci bikin. Domin ba a ankara ba sun yi ta tsinke sarkar wuyan mata. Wannan ta sa tilas mata suka rika cire sarkarsu da awarwaro suna sawa cikin jaka. Wakilin Fim ya ji wata tana cewa, "Wallahi naira dubu sha ukku na sayi sarkata, amma wani katon banza ya fizge. Allah ya isa!" Kuma ya ga inda wasu bata-garin samari suka kama 'yan kunnen wata yarinya suka fizge da karfin tsiya, suka bar ta nan tana sharbar kuka.

Murna a gun mahaifan Balaraba, ba a cewa komai. Tun uwarta tana dariya, har ta koma tana hawaye don murna. Shi kuma maigidanta, Malam Muhammadu Kaura, ba kalmar da ke ta fitowa daga bakinsa sai, "Na gode! Na gode!" Kuma ya kasa zaune ya kasa tsaye.

Masu daukar hoto, na kati da na bidiyo, suna ta yin aikinsu.

Zuwa misalin karfe 4:30, Amarya ta canza kaya, ta shiga atamfa da goggoro. Aka yi haramar zuwa wajen walima wadda aka shirya yi a zauren taro na harabar Kasuwar Baje Koli ta duniya wadda ke kusa da unguwar su Balaraba. To, walimar dai ba ta yiwu ba. Dalili shi ne yawan jama'ar da ke kwarara ciki ya tsorata ma'aikatan wurin, suka ga abin zai iya jawo masu mummunar asara, sai suka dakatar da bikin, suka ce don Allah a tashi. 'Yan asharalle suka hada nasu-ya-nasu suka koma gidan Amarya wai ko a ce masu an sake wani wuri. Shagalin dai bai yiwu ba a ranar, domin duk inda aka koma abin da ake gudu zai iya faruwa. Wannan ya sa abokan Ango suka yanke shawarar cewa a bari sai gobe in an je Kano a shirya wa Amarya da Ango walimar (Gala) a can.

Haka dai aka yi ta hada-hada, jama'a sun ki raguwa, domin duk wanda ya ji abin da ake yi a garin sai ya yi wa gidan su Balaraba tsinke.

A ran Asabar, tun da asuba aka fara shirye-shiryen tafiya Kano. Da misalin karfe 12:00 na rana Ango ya je ya yi sallama da Amarya ya yi gaba don ya kimtsa zuwa Gala. Wannan mujallar ta gano cewa iyayen Balaraba da ita kanta Balaraba ba su so ta je Kano domin walimar ba. Shi uban, so yake a bar Balaraba a gida har mako biyu sannan a kai ta gidan miji. Yayar Balaraba, da Kumurci da abokansa su Sani Mai Iska, su ne suka roke shi a kan ya amince ta je ta dawo, inji wata majiya. Da kyar ya yarda. Majiyarmu ta ce wannan bai rasa nasaba da labarin da Balaraba ta zo da shi daga Kano cewa wasu mutane uku sun same ta a can sun ce mata idan ta bari aka daura auren, to za ta mutu. Yayan Balaraba, Abubakar (Bunari, da shi kansa babansu, sun tabbatar mana da labarin.

Amarya da 'yan'uwanta da kuma 'yan rakiya sun ci gaba da shiri har zuwa karfe 2:45. An dan tsaya jiran Safiya, babbar kawa, wadda ta tafi unguwarsu Kurmin Mashi don ta ci abinci ta shiryo, amma da ba ta zo ba sai kanwar uwar Balaraba, Hafsatu, ta shiga motar ta zauna a inda Safiyar za ta zauna. Motocin biyu da za su kai matafiyan Kano suka tafi, daya karama (ta mijin Jummai yayar Balaraba), daya kuma bas ce da aka dauko shata.

Da za a tafi, Balaraba ta roki gafarar iyayenta, suka ce sun yafe mata. Suka kuma yi sallama da sauran dangi da ke wurin, wasu na ta hawaye (duk da yake an shirya cewa gobe-goben nan su Balaraba za su dawo daga Kano). Balaraba ba ta daina dago wa mutane hannu ba har motarsu ta sha kwana, ta hau kwaltar barin Kaduna.

Wayyo, ashe tafiyar kenan wadda babu dawowa.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin