Sunan SHU'AIBU LAWAN ba ya bukatar gabatarwa ga masu karatu. Baya ga cewa fitaccen dan wasa ne, shi ne wanda labarinsu ya game ko'ina a kasar nan a watan da ya gabata dangane da rasuwar amaryarsa, fitacciyar 'yar wasa Balaraba Mohammed. Kwana daya da daura auren, amaryar da wasu danginta mutum uku suka riga mu gidan gaskiya ta hanyar mummunan hadarin mota da ya rutsa da su a kan hanyarsu ta zuwa Kano daga Kaduna.
A wancan lokacin Shu'aibu ya ga fari ya kuma ga baki: farin cikin aurensa da kuma bakin cikin rabuwa da masoyiyarsa. Mujallar Fim ta kawo cikakkaen bayani a kan bikin da kuma mummunan labarin a watan jiya. Sai dai an rage abu daya: ba ku ji ta bakin Shu'aibu ba ko kuma halin da ya shiga a sakamakon abin bakin cikin da ya faru, kuma ba ku ji ta bakin surukansa ba. Dalilin rashin jin takamaiman abin da Shu'aibu yake ciki ya sa dimbin jama'a suka yi ta yada ji-ta-ji-ta a kansa. Daga masu cewa shi ma ya yi hadari ya mutu, sai masu cewa wai ya kuma kansa da bango ya gigita an kwantar da shi a asibiti, kuma wasu suka ce wai ya zautu; wasu har gida sukan same shi don su yi masa ta'aziyyar ganinsa da ido.
"Ashafa, ka san abin da ke kawo wasu 'yan mata nan gidan?"
Wannan tambayar ce Shu'aibu ya yi mani lokacin da na je muna tattaunawa.
Ya ci gaba da cewa, "To wallahi labari ake kai masu cewa wai na zautu ko na haukace; shi ne ya sa suke zuwa don su kalli mahaukaci."
Shu'aibu dai bai haukace ba; ya samu kansa a cikin wani hali wanda zai fi kyau ku karanta ku ji dalla-dalla daga bakinsa. A cikin hirar da ke cikin wannan mujallar babu abin da Kumurci ya rufe sai fa wanda bai sani ba kan tsakaninsa da Balaraba. Duk za ku ji har yadda tun kafin a daura auren ta yi masa bayani kan wasu mutane da suka ce "ba za ta wuce kwana uku ba idan an daura mata aure da Kumurci."
Ban da Shu'aibu, akwai iyayen marigayiya Balaraba. Su ma ba ku ji ta-bakinsu ba a kan mutuwar 'ya'yansu a fitowarmu ta watan jiya. Mun yi duk bakin kokarinmu don samun jin ta-bakinsu, amma abin ya faskara a lokacin saboda suna cikin mawuyacin hali, har an kwantar da su a asibiti. Akwai lokacin da mahaifin marigayiya Balaraba da yayarta marigayiya Jummai, Malam Muhammadu Kaura, ya dan yi wa wakilinmu Aliyu Abdullahi Gora II bayanai a asibiti jim kadan bayan rasuwar. To amma sai ya ce bai so Gora ya dauki bayanan a faifai har sai can gaba. Ya tabbatar masa da cewa za su tattauna.
To, sun tattauna din kuwa. Bugu da kari, Gora ya samu damar tattaunawa da mahaifiyar amaryar da yayarta, wato Malama Binta. Sa'annan marubucinmu na musamman, Shafi'u Magaji Usman (editan mujallar Bidiyo), ya tattauna da limamin masallacin Alhaji Sani Zangon Daura da ke kusa da gidan su Balaraba, wanda shi ne ya koyar da ita karatun allo, kuma shi ne ya daura mata aure, sa'annan shi ne ya sallaci gawarta. Duk a cikin wannan fitowar za ku ji bayanan wadannan bayin Allah wadanda babu abin da za mu yi masu illa addu'a da ci gaba da tausaya masu kan abin da ya faru gare su wanda mu ma duk ya shafe mu a matsayinmu na abokai kuma masoyan Balaraba.
Hasali ma dai yadda abin ya shafe mu din ne ya sa muka yanke shawarar ci gaba da kaddamar da Gidauniya ta musamman don tara wani abu na taimako da za mu mika ga hannun magadan Balaraba. Akwai bayanin gidauniyar a cikin mujallar. Muna fatan ku da sauran jama'a za ku taimaka bakin iyawarku. Malamai sun ce mana yin hakan ba laifi ba ne, kuma duk wanda ya taimaka, sakayyarsa tana wurin Allah.
Idan kun duba sauran shafukanmu kuma za ku samu sauran labarai da bayanai masu gamsarwa kamar yadda kukan samu a kowane wata. Misali, me ya yi zafi har mijin marigayiya Jummai Mohammed ya kai wasu 'yan fim na Kano kara a Abuja bayan rasuwar su Balarabar? Kuma me ya yi zafi har aka mari Rukayya Dawayya a Zariya?
A sha karatu lafiya. Kuma Allah ya kai mu watan gobe ku sha wasu labaran.