Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 30   Yuni 2002
ZUWA GA MASU KARATU


BABBAN SHAFI
RA'AYI
Zuwa Ga Masu Karatu
Wasiku
Balaraba Muhammad (1983-2002) 
Rayuwarmu
Duk Sun Yi Aure
Malam Zurke
Ra'ayin Mujallar Fim
Bukukuwa
Sauran Labarai
Ra'ayi Ba Gaba ne
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka Bangon FIM ta 29
Bangon FIM ta 28
Bangon FIM ta 27
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da ra'ayin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


Gidauniyar Tunawa Da Balaraba

Balaraba
Balaraba Mohammed
KWANAN nan wadansu bayin Allah daga cikin masu harkar shirya finafinan Hausa suka taru suka kafa wani kwamiti wanda suka rada wa suna 'Gidauniyar Tunawa Da Balaraba.' An kafa kwamitin ne domin a samu hanyoyin da za a bi don karrama shahararriyar 'yar wasan nan Balaraba Mohammed, wadda Allah ya karbi ranta a ran 16 ga Maris, 2002, kwana daya bayan an daura mata aure da Shu'aibu Lawan. 'Ya'yan wannan kwamiti ba wasu ba ne illa wasu wadanda suke ganin yin Gidauniyar ya fi rashin yin ta alfanu.

Duk wanda ka dauka a cikinsu kuma za ka tarar yana da matsayi na girmamawa ko mai daraja a cikin da'irar shirin fim. Shugaban kwamitin dai fitaccen darakta din nan ne kuma dan wasa, Malam Ishaq Sidi Ishaq. A cikin membobi kuma akwai Hajiya Balaraba Ramata Yakubu, fitacciyar marubuciya kuma jagora a cikin furodusoshi mata da maza. Akwai Malam Hafizu Bello, fitaccen daraktan finafinai kamar su Huznee, Hauwa 1&2, So..., Gagarabadau, da sauransu. Sai Malam Bala Makosa Zariya, daraktan shirin Karbala kuma editan mujallar Nishadi. Akwai Malam Ahmad Salihu Alkanawy, furodusan finafinai kamar su A'isha da Dawayya; sai Malam Nata'ala Aliyu, furodusan finafinai kamar su Tabbas da Mutum Ko Aljan? kuma shugaban kamfanin 'Jari Film Production,' Zariya. Sa'annan akwai Hajiya Saratu Gidado, fitacciyar 'yar wasa. Akwai kuma dan sanda Muhammad Bashir Yahuza Malumfashi, da editan mujallar Fim Ashafa Murnai Barkiya (sakataren kwamiti), da mawallafin mujallar Fim, Ibrahim Sheme.

Jera wadannan sunayen a haka yana da muhimmanci domin a san cewa ba mutane ba ne masu wasa da abin da bai kamata a yi wasa da shi ba. Mutane ne wadanda ba za su yarda su sa kansu cikin wani sha'ani inda sunansu zai baci ba. Sun yi amanna da cewa yin Gidauniyar Balaraba ya dace saboda gudunmawar da ta bayar ga ci-gaban shirin fim, kuma tare da la'akari da cewa mutuwa tana kan kowa. Wannan yunkurin ya zo a daidai lokacin da ya kamata 'yan fim su yi wa kansu kiyamul laili suna taimaka wa kansu da kansu.

Fatan 'yan wannan kwamiti ne, da kuma duk mai kaunar Balaraba, a tara kudi ko wani nau'i na karramawa, don a ba magadan marigayiyar. Babu wani memba na kwamitin da ya shiga cikin shirye-shiryen aiwatar da Gidauniyar da nufin ya samu kwabo daga ciki, ko wani abu. Ya zuwa yanzu, kwamitin ya yi taro har sau uku a Kano, yana tsara babban taron kaddamar da Gidauniyar. Abin sha'awa shi ne har masoyan Balaraba da 'yan fim sun fara tambayar yaushe za a kaddamar da Gidauniyar, kuma me ake so su bayar. Fatanmu shi ne masu karanta mujallar Fim da duk wani mai kaunar 'yan fim su goyi bayan wannan yunkuri na kafa tarihin kaddamar da Gidauniyar Balaraba.

A cikin wannan mujallar, shugaban kwamitin, Ishaq, ya yi bayani a kan manufar Gidauniyar. Za a kaddamar da Gidaunbiyar a ran Asabar, 6 ga watan gobe (Yuli) a 'Marhaba Cinema' da ke Kano. Muna fatan jama'a za su zo. I B R A H I M S H E M E

Komawa babban shafinmu

Komawa saman wannan shafin