|
A Saida Rai A Nemo Suna
Daga Ashafa Murnai Barkiya
Editan Fim, Ashafa Murnai Barkiya
|
KU da kuke karanta mujalla kuma kuke kallon finafinai, ba ku san bakar wahalar da 'yan fim ke ci (ko sha) ba. Ban da wahalhalun da akan ci karo da su, a wadansu kasashen har asarar rai ake yi a wurin daukar fim. Da yake ku ba kowanenku ya san abin sosai ba, sai dai kawai ku rika kallonsu a cikin akwatunan talbijin. Wanda ya burge ku, ku ce masa ya yi da kyau.
Ahmed S. Nuhu. Arnold Schwarzenegger. Zhang Ziyi. Duk 'yan fim ne. Ahmed dan Nijeriya, Arnold Ba'amurke, ita kuma Zhang 'yar kasar Cana. Idan ana wahala lokacin daukar fim, to wadannan ukun duk sun dandana ta sosai, kuma sun saida rai don nemo suna. Schwarzenegger doki ya hau a kan rufin ginin wani otal a lokacin da ake daukar shirin True Lies. Ana cikin dauka ne sai turken kyamara ya subuce ya fado a gaban dokin da yake a kai. Hakan ya sa dokin ya firgita, ya yi haninya, ya kuma tuma tsalle. Jarumin ya mirgino. Bai fado ba, sai ya makalkale a jikin rufin, shi kuwa dokin ya fado tim kan rufin wani gida.
Ita ma Zhang, bakin jidali ta fada a lokacin da ake daukar fim din da ta fito jaruma, wato Crouching Tiger, Hidden Dragon, wanda ya ci kyautar duniya a bara. Akwai inda aka yi kazamin fadan cin kasuwar sama, sokekeniya da bugayya (martial arts) tare da jarumin fim din a kan bishiyoyi a shirin. Da yake ba tashi sama ne suke yi a zahiri ba (igiyoyi aka daura masu, wasu katti kamar 70 suna aika su sama) to da wuya ta yi wuya sai da jarumar ta saki fitsari a sama, tana jika mutane. Kuma har aka yi kwanaki ana daukar wannan bangare (scene) na fim din, duk lokacin da Zhang ta sauko kasa sai ta kyara amai.
Arnold da Zhang sun saida ransu sun samo suna. A kundin tarihin abubuwa mafi ban mamaki da bunkasa a duniya (Guinness Book of World Record), an ce Arnold ne kammalallen dan'adam din da aka fi inganta wa halittarsa a duniya. Ita ko Zhang, sunan da ta yi shi ne duk da yake a Caina aka shirya fim din nata, sai da fim din ya koma gida da kyaututtukan duniya (Oscars) guda hudu. Zhang ba ta yi fitsari da amai a banza ba.
Mu a nan kasar Hausa, Ahmed S. Nuhu yana daya daga cikin fitatttun 'yan wasa, kuma yana daya daga cikin wadanda suka dandana wahala a lokacin daukar fim. "Babbar wahalar da ta fi kidima ni har na ji kamar raina zai fita, ita ce wadda na sha a wurin daukar Sharadi," inji shi, a wata kwarya-kwaryar hira da muka yi da shi a 'yan watannin baya.
Idan kuka bi hirar da kyau, za ku ji irin wahalar da ya sha. Hasali ma dai yanzu wani furodusa ya dora masa karan-tsana don kurum ya ji labarin ya fito a fim din wani. To amma kamar Arnold da Zhang, duk wahala ba za ta hana jarumin da Allah ke so yin tashe ba. Sai ma dai ta kara masa kwazo da fice da samun masoya a cikin jama'a. Waye zai ce ba a son Ahmed, wanda ake ganin tuni ya gaji Ali Nuhu, har sun maida farin jini gadon gidansu? Ku ba ni amsa.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin
|
|