|
Gaba ta fi baya yawa
Daga SANI AHMED SASA a Gombe
Malam Musa Audu Maijama'a Shugaban 'Maijama'a Video Centre
|
BA sai an fadi an nanata ba, finafinan Hausa tuni sun sami gindin zama. Finafinan Indiya da na Caina wadanda a da su ne suka cika gidaje da sinimu sun fara ja baya. Shi ya sa a yanzu a ko'ina cikin arewacin kasar nan an raja'a da kallo da kuma sayen finafinan Hausa. Saboda tasirin finafinan da kuma yadda ake samun riba, yanzu sai furodusohi ke ta barkowa ta ko'ina suna shiga harkar.
To haka abin yake a garin Gombe wanda cike yake da 'yan wasa da furodusoshi, kai har da daraktoci. Gombe gari ne mai tashen ci gaban kasuwanci, shi ya sa ake samun kasaitar harkar finafinai a halin yanzu. Akwai kwararrun 'yan wasan kwaikwayo birjik da ke ta kokarin fara shiga harkar fim da kuma furodusoshi da daraktoci masu dimbin basira.
Duk da cewa finafinan wasu furodusoshi sun shiga kasuwa, akwai finafinan wasu furodusoshi masu yawa da har yanzu ba su shiga kasuwa ba. Daga cikin wadanda suka shiga kasuwa akwai Rigar 'Yanci na Alhaji Sulaiman Bello, sai Ido Ga Na Wani na Sa'adu Mohammed da kuma wasu duk nasa, wato Mahaukaci Da Wuka, da Allah Gatan Kowa. Akwai Ba A Nan Take Ba na Abdulrashid Bello, sai kuma Ciki Da Gaskiya na Hajiya Bebi Gafa. Daga cikin wadanda ke kan hanyar fitowa kuwa, akwai fim din Sadiya na 1na kamfanin 'Gwambawa Film Production,' da kuma Azzalumi, fim din Musa A. Maijama'a.
A halin yanzu akwai furodusoshi kusan 25 a Gombe da kuma finafinai 35 wadanda wasunsu da dama ana kan hanyar kammala su. Don jin halin da harkar fim ke ciki a jihar, mujallar Fim ta tattauna da Malam Musa Maijama'a wanda shi ne manajan darakta na 'Maijama'a Video and Film Production' a Gombe. Ga yadda hirar tamu ta kasance.
Fim: To mu dan fara jin tarihinka tukuna.
MAIJAMA'A: A takaice ni daga Jihar Kaduna na zo nan. Amma an haife ni ne a Jihar Filato. Na yi karatu a Filato. Bayan na yi karatu sai na fara aikin gidan talbijin.
Dadewa da kawarewata a harkar talbijin suka sa na ziyarci kasashe da dama. Zuwana kasar wajen ya ba ni damar yin karatu a can ko kuma wata tafiya da ta jibinci aikin fim.
FIM: Me ya ba ka sha'awa har ka shiga harkar fim?
MAIJAMA'A: Da farko ji na yi wata dama ce wadda zan ba da gudunmawata a matsayina na dan kasa. To lokacin da aka buga wata sanarwa ta neman ma'aikata, sai na yi sauri na ba da sunana. To ta haka ne na tsinci kaina a aikin talbijin. Kafin sa'annan kuwa na yi wasa na shekara goma, bayan na yi aiki na shekara goma a gidan talbijin.
FIM: Ya mu'amalarka take da sauran furodusoshi?
MAIJAMA'A: Dangantaka ta da sauran furodusoshi tana da armashi kwarai.
FIM: Ya zuwa yanzu finafinai nawa ka shirya?
MAIJAMA'A: To na yi finafinai masu yawa na gidan talbijin, musamman wasan kwaikwayo; amma a shirin fim guda daya kawai na yi wanda shi kuwa aiki ya mika.
FIM: A ina ka samo 'yan wasanka?
MAIJAMA'A: Ka san mukan gayyato kwararru da kuma sababbin jini, to sai a gwada su (audition) kafin a bai wa kowa abin da zai yi.
FIM: Wadanne matsaloli ka fuskanta lokacin da kake shirya fim dinka?
MAIJAMA'A: Ka san matsaloli sun danganta daga wuri zuwa wuri. Misali, rashin kyakkyawan shiri kan jawo wa furodusa karin kashe kudin da suka wuce yadda ya yi niyya da farko.
FIM: Akan kashe nawa wurin shirya fim guda daya?
MAIJAMA'A: To wanda ba za a ya wa tir ba, akan kashe masa N180,000; nagari sosai kuwa, daga N250,000 zuwa abin ya kai miliyan daya.
FIM: Wane irin sharhi za ka yi kan finafinai a Jihar Gombe da kuma sauran jihohi gaba daya?
MAIJAMA'A: Ina ganin akwai yiwuwar gaba ta fi baya armashi sosai daga nan Gomben har sauran yankuna a Nijeriya. Don ka ga ba a nan kadai ake sayar da su ba, har wasu kasashe wadanda ke da al'umma masu magana da harshen Hausa, misali, Ghana, Nijar, Burkina Faso, Kamaru, Gabon da Chadi. Kuma ka ga a hankali finafinan Hausa sun fara korar na Indiya da na Cana.
FIM: Me za ka ce dangane da ingancin finafinan Hausa ko rashin ingancinsu?
MAIJAMA'A: Idan ka dubi dogon tarihin finafinan Amerika da na Indiya, na Cana da na Larabawa, za ka ga cewa sun keto hazo mai nisa. Kuma ta wadansu finafinai ne har suke da bakin fada a ji a duniya. Amma idan ka dubi finafinan Hausa za ka ga tamkar abin nan ne da ake cewa neman ruwa a fako. Wato abin da ake ganin kamar ba zai yiwu ba, sai kuma a ga ya yiwu din.
FIM: Kamar da su wa ka taba yin aiki?
MAIJAMA'A: Na yi aiki da irin su Kabiru Nakwango, Ishaq Sidi Ishaq, Sulaiman Bello (Gwamabawa Films), Hajara Usman, Kabiru Maikaba, Shehu Hassan Kano, Aina'u Ade, Saima Mohammed, da wasu da dama.
FIM: A karshe wane fim ka fi sha'awa?
MAIJAMA'A: Suna da yawa, amma fim din Akasi 1 shi ya karkato ni ga kallon finafinan Hausa. Akwai kuma Aisha 1, Ukuba, Dan Halak, Mujadala 1 da kuma wani na kwanan nan mai suna Mashi 1.
FIM: Yallabai mun gode.
MAIJAMA'A: Ni ba na son godiya.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin
|